CHAPTER 16
Ta lumshe idanunta kanta ye shiru sunayen da ake ambata na amsa kuwwa acikin kanta.
Sokoto to Zaria taji wani mutumi yafaɗa.
"Aunty Hafsat" zuciyarta tafaɗi.
Itace babban yayan su tanada saukin kai, hakuri da sanin yakamata sedai idan tai fushi abin ba kyau.
Tasha zuwa gidan ta hutu lokacin Inna nada rai.
Dama cikon passenger daya suke buƙata shiyasa tana shiga tabasu kudin mota driver yaja mota.
Wayarta taciro ta turama Faiza message se takashe wayar gaba daya.
Idanun ta da suke mata zugi da radadi ta lumshe dasauri ta bude sakamakon idanun Baffa da suka hasko wanda babu komai a cikinsu se tsana da kyama.
Batareda tako rintsaba suka iso fly over lokacin karfe 5:00am, daƙyar tasamu adai daitan da yakaita cikin zaria babban dodo.
A sakaye tasamu gidan sbd masu fita masallaci, a gate na biyu ta tsaya nan ne se datai knocking.
Muryan Hidayat taji tana tambayar ko waye duk da tinanin ta baya wuce mai zuwa taya Mommyn su aikin gida ne.
"Diyana ce"
Tafaɗa taname danne kukan da yake taso mata.
Jikinta har yana rawa tabuɗe don ganin da gaskene!
Idanuwanta ne suka sauka acikin nata, Diyana tai saurin kauda kanta.
Jikin Hidayat ne ye sanyi ƙalau daƙyar ta iya karban akwatin da yake hannun ta suka shiga ciki.
"Assalamu alaikum"
Diyana tafaɗa da karfi yanda na ciki zejita.
Aunty Hafsat dake kitchen tafito dasauri jin muryan autansu kamar amafarki dama ko jiya se datai wani mummunar mafarki akanta.
Ganin itace ɗin da gaske yasanyata zuwa dasauri tariƙota. Numfashin da batasan tana rike dashi bane tasaki.
"Diyana lafiya?"
Aunty ta faɗa tana kallon cikin ƙwayan nin idanuwanta da babu komai se tsan tsar damuwa da tashin hankali.
Baki tabuɗe zatai magana Diyana ta hanata ta hanyar dora yatsar ta akan laɓɓanta tana girgiza kanta alamar tai shiru.
Unexpected taji ta rungume ta, jin yanda ta rukun kume ta kamar zata shige jikinta yasanya nata jikin yin sanyi.
"Ga ruwa!"
Hidayat tafaɗa tana mikoma Aunty tabata, ɗagota tayi daga jikinta ta zaunar da ita akan kujera.
Ruwan tabuɗe ta dora mata abakin ta, se alokacin ne ta fashe da kuka, kuka takeyi na abinda ya sameta, kuka takeyi na kalan rayuwar da ta tsinci kanta aciki, kukan maraici takeyi daga jiya zuwa yau rasuwar Inna yadawo mata sabo feel.
Sosai take zubda hawaye wanda ko mutuwar Inna batayi shiba, ƙirjinta zafi yakeyi kaman ana hura mata wuta hakan yasa kowani gaɓa na jikinta ke kyarma.
Aunty Hafsat dai kallonta kawai takeyi se ayanzu take ganin girman kuskuren da suka aikata.
Sunci amanar mahaifiyarsu da zumunci, da ace Inna tana nan Diyana bazata zubda wannan hawayen ba wanda kana gani kasan babu komai aciki se tsan tsar baƙin ciki da maraici.
Fushin hanasu zaman makokin Inna da sukayi yasanya su kin zuwa gidan su dubata ko sau daya.
Batasan hawaye na zuban mata ba seda taji ansa hannu ana goge mata, koda taɗago idanuwanta bata sauke ako inaba se akan ɗiyarta Safiyya.
"Ummy lafiya kuke kuka? Ko wani ne yamutu?!!"
Tafaɗa kaman itama zatasa kukan. Kai kurum ta iya girgiza mata alamar ba komai, ta kalli Hidayat da idanun ta sukai rau rau alamar akoda yaushe zata iya sakin kuka itama.
Aunty Hafsat tace"Hidayat ki tashi ki karasa hada break fast din ina zuwa"
Hannun Diyana takama zuwa cikin bedroom din ta, da kanta ta tara mata ruwan wanka tace"ta shiga"
Diyana batace komaiba ta shiga. Falo ta koma ta dauki akwatin ta takai dakin su Hidayat.
Doguwar riga ta ciro mata mara nauyi takai mata bedroom din ta. Kitchen ta koma ta hado mata tea se indomie da kwai tana shiga taga har tafito tana saka riga da alama dai ko mai bata shafa ba.
Ajiye kayan hannunta tayi akan carpet din dake shimfide atsakar dakin, hannunta takamo ta zaunar da ita sannan itama ta zauna.
Cup ɗin tea ta ɗauko takai bakinta, Diyana ta sun kuyar da kanta yanayin da take ciki na ƙara danneta.
Ahankali tafurta"na koshi...!"
"Ai dama ban ce kina jin yunwa ba don haka bude bakin ki"
Aunty Hafsat tafaɗa cikin yanayin da babu halin yin musu.
Tana sha taji amai na taso mata duk da kuwa babu komai acikinta, ganin takara kusanto bakin ta da kofin alaman tasha yasan yata saurin cewa
"Idanna kara shaa zanyi amai"
Batareda ta sauke kofin ba tace"se kuma me?" Ta tambayeta idanunta akanta.
"Uhmmm hmmm"
Aunty tai mata alamar tana jinta.
Shiru tayi don batada abin cewa gashi kuma ba tason wannan kallon da take mata.
Bakinta ta kai ta kurba duk da zuciyarta cike phall tsoron yanda zata kalli Aunty ta gaya mata abinda ya baro da ita gida.
Seda tasha fin rabi taja jikinta ta jin gina da bayan gadon kamar yadda Aunty tayi.
Shiru ne yaratsa dakin na yan wasu daƙiƙu.
Aunty Hafsat ta kore shirun da maganar da tayi"akwai abinda yakamata in sani yanzu"
"Kimin alƙawari ba zaki tsane niba"
Dasauri Aunty tabata amsa"nayi alƙawari komai zai faru bazan tsane kiba arayuwa"
"Koda kuwa ina dauke da ciki ahalin yanzu"
Azuciyar ta tai maganar se gashi ya fito fili batareda tasani ba.
Kaman an kwada mata guduma a tsakiyar kai haka taji kalaman Diyana, ta runtse idanunta kanta na yin wani irin nauyi kaman an mata gammo da duniya da abinda ke cikin ta.
Shiru wasu yan daƙiƙu suka shuɗe ba abinda ka keji se bugun zuciyoyinsu da na agogo wanda yake nuna musu lokaci tafiya yake yi.
Aunty Hafsat ta katse shirun da faɗin
"bazan tambaye ki meyasa ko ya akayi hakan ya faru ba, tun farko laifin mune da ace mun kasance atare dake lokacin da kike bukatar mu da hakan be faruba koda ya zamuyi Allah ya ƙaddara hakan wayemu da zamu jada ikon shi.
Yanzu abinda yakamata shine mu fuskanci hanyar gyara. Shin kin san wanda ye miki cikin?!....."
Diyana tasaki wani murmushi mai ciwo, bata damu da hawayen da suke tsere akun cin taba tace
"Ya akayi?....waye mun?....Nima ban saniba."
Shiru Aunty Hafsat tayi tana tinanin wannan al'amari mai daure kai. Can dai takasa hakuri se datai magana
"Yanzu dai baki yarda ba kenan"
Kai tagirgiza"idan za'a bani qur'ani zan dafa akan banada ciki sedai idan na tina Ni da kaina na mika abu na karshe da yatabbatar da hakan se inji inaso inyarda akwai cikin ajikina"
Nan nauyar ajiyar zuciya Aunty tasauke ko babu komai tasamu sauki akan Diyana bata tabbatar da akwai cikin ba.
Hakan yabata daman lallashinta tafito ta barta kan ta kwanta tai bacci. Lokacin da tafito gaba ɗayansu suna kan dining har dashi mai gidan.
Bedroom din mijinta tashige tana maida ƙofan tarufe ta jin gina bayanta dashi ta silale aƙasa tafashe da kuka mai cin rai, dama taki yarda tayi agaban Diyana ne saboda bataso ta kara karya mata zuciya.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 17
Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌗
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰