CHAPTER 17
Bedroom din mijinta tashige tana maida ƙofan tarufe ta jin gina bayanta dashi ta silale aƙasa tafashe da kuka mai cin rai, dama taki yarda tayi agaban Diyana ne saboda bataso ta kara karya mata zuciya.
"Ya Salam.....!!"
Tafaɗa asanda take dafe kanta dayake sara mata.
Jitayi ana buga kofar tare da kiran sunanta, cikin kukan da takeyi tamiƙe tabuɗe mai yashigo.
Yayi shirinsa tsaph na zuwa offfice dama tunda yadawo masallaci shida Aisar yaga began taba yatambayi Hidayat tagayamai abinda ke faruwa yasan akwai matsala.
Cikeda natsuwa da sanin yakamata yashiga kwantar matada hankali duk da besan abin da ke faruwa ba.
Aunty Hafsat tasa hannu tashare hawayen ta da bayan hannu
"Koda ƙaddara akawai laifin mu aciki da ace mun tsaya kai da fata akan al'amuran ta da yanzu ba wannan maganar akeyiba.
Har mutuwana bazan daina ganin laifin muba, ban saniba ko Inna zata yafe mana akan wofan tar matada ƴaa da mukayi saboda kawa zucin mu...."
Ta ƙarke tana sake fashewa da kuka, yarun gumeta yana shafa bayanta gamida hura mata iska akunnin ta, se daya tabbatar tasamu natsuwa yai magana
"Can I help you"
Kai taɗaga mai.
Yagyara zama yana fadin"uhmmm hmmm"
Seda ta haɗiye wani mulmu lallen abu mai ɗacin gaske daye tsaye a maƙo gwaronta ta iya bude baki tagaya mai komai.
Shiru yayi yana nazari kamin daga bisani yace"abinda nake gani akwai shine test zan yi mata guda biyu acikin result ɗin dole zan gano gaskiyar lamarin."
"Shikenan bari inje in kirata se mu tafi asibitin yanzu"
Aunty tafaɗa asanda tamiƙe tanufi kofa batareda ta tsaya jin abinda zeceba.
Shiganta dakin ye dai dai jan numfashin da Diyana tayi sakamakon kukan da ta dinga yi.
da gudu Aunty ta hau kan gadon tana jijji gata, ajiyar zuciya ta saki asanda jikinta yake saki gabaɗaya.
Saboda rudewa gabaɗaya Aunty mantawa tayi da ita likita ce se baki tabuɗe tana kiran mijinta da sauran yaran.
Suduka arude suka shigo Doctor Mansur da Aisar suka dauke ta suka sanyata amota, Aunty ta zauna da ita a mazaunin baya Doctor Mansur yaja motar zuwa A.B.U. SHIKA.
Suna shiga aka karbe su saboda alfarmar Doctor Mansur dake aiki anan Ward din na dermatologist matsayin consultant. Ita kuma Aunty Hafsat tana aiki ne a cardiologist Ward.
Emergency room aka shigar da ita Aunty da Aisar na tsaye suna jiran tsammani yayinda komai tare da Doctor Mansur akeyi.
*SAIDI*
Koda Faiza ta fito bata ga Diyana ba seta ɗauka wani abune itama yasameta aka tafida ita asibiti.
Shiru tayi tana jin saukan hawaye masu zafi akan kuncin ta, ta silale ta kwanta akan doguwar kujera rub da ciki taname sakin kuka me ratsa zuciya.
Ana kiran sallahn athuba tabuɗe idanunta da sukai mata nauyi ga kanta da yasara mata daƙyar ta iya mikewa taje tai sallah.
Kitchen taje ta ɗora abin karyawa saboda jikin Ummah Sumayya babu daɗi, Ummah Iklima na can asibiti tare da Inna anbata gado.
Fulawa ta kwaba tai musu fanke, dama akwai kullun kunu se kawai ta dama.
Na dakin Goggo ta soma kaiwa sannan tadauki na dakin Ummah Iklima takai tunda duk matasan gidan da samarin anan dakinta suke karyawa.
Na Ummah Sumayya ta dauka takai mata daki yanayin da taganta aciki yaƙara karya mata zuciya tanada tabbacin ko mahaifiyar Diyana ce take raye iya halinda zata shiga kenan.
Lokaci guda ta fita a hayyacinta har wata ƴar raman azaba tayi, ga hawayen ta sunki daina zuba.
Awannan situation ɗin da ake ciki bazata iya jurema kallon Ummah Sumayya ba se kawai ta koma dakin Inna kewar Diyana na ƙara danneta.
Waya ta dauka daniyyar kiran wayar Ummah Iklima taji ya jikin Diyana idanuwanta suka sauka akan message ɗin data turo mata.
Asu kwane tafara karan tawa"Ban saniba dai dai ne ko rashin dai dai sedai inada tabbacin bazan iya cigaba da zaman gidan muba saboda bazan iya jurema kallon tsana daga gareki keda Ummah Sumayya ba.
Nasani da zaran kuka tabbatar da akwai cikin atare dani zaku tsaneni amma ayanzu da nake wannan rubutun inaji araina inada komai tunda inada soyayyar ku,
Ban san yadda zanyi in muku ban kwana ba haka bazan iya musa cewa banada cikiba saboda inada bukatar sanin gaskiyar lamarin, ina muku fatan alkhairi arayuwar da zakuyi babu Ni aciki."
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un......meyasa zaki min haka? Don Allah kidawo nai miki alƙawari bazan taɓa tasanar kiba....bazan rabu da keba....."
Haka ta dinga sumbatu cikin zubar hawaye dasauri tamiƙe tanufi dakin Baffa se dai a rufe taganshi.
Bataso takara tayar ma Ummah Sumayya da hankali fiyeda wanda take ciki yanzu.
Batace da kowwa komai ba ta koma daki ta dauko hijjab, tasani ba inda Diyana zataje bayan gidan Yakumbo.
*
Rashin sani yafi dare da duhu da ace Faiza tasan Diyana bata gidan da baza taje ta tambaye su tana kukaba.
Tashin hankalin da suka shiga kaɗai ya isa ya nuna maka girman soyayyan da suke mata.
Kawu Shattima beyi kasa agwuiwaba yasa dansa Abbas yaɗauko mota Faiza ta shiga suka zo gidan.
Ita tai mai jagora zuwa dakin Baffa dake zaune yana bama Goggo abinci abaki.
Seda taga Kawu Shattima sannan ta dakatar dashi suka gaisa ya soma da tambayar dake cimai zuciya.
"Ke Faiza ina Diyana take?"
Baffa yafaɗa yana zuba mata manyan idanunshi.
Cikin shesh sheƙan kuka tace"batanan tun jiya da daddare"
Goggo ce tasa hannu ta dauko ta kardar gwajin jiya na Diyana dama batai nisa da itaba ta bama Kawu Shattima
"Wannan abinda ta aikata ne yasan yata barin gida."
Amsa yayi jikinshi gabaɗaya yai sanyi, wani irin dokawa zuciyarshi tayi nan da nan zufa ya wankeshi duk da sanyin safiyar da yake kadawa, daƙyar ya iya lalubo muryanshi yace
"Yanzu Alhaji meye abinyi"
Baffa yagyara zama kai daga jin yanda ye gyaran murya kasan duk abinda ze fito daga bakinsa to yana under final decision ne.
"Nidai yanzu ba abinda se alhamdulillah abinda ta aikata taimako na tayi saboda ayanda naji zuciyana ajiya to inada tabbacin in tahaihu bugawa zatayi.
Ba iya haihuwar taba gabadaya se danaji na tsani kaina saboda auren uwarta da nayi, ban saniba ko Ku kuna bukatar ta azuri'arku amma nidai ko an ganta bana bukatar ta acikin rayuwana dana zuri'ana.
Kai in maka mai gabadaya wallahi nafi bukatar ganin azarailu da in sake ganin fuskar Diyana k......"
"Don Allah kai shiru maganar ta isa haka"
"Bashshi yafadi abinda yaga dama ai dama haka mutane suke basa taɓa tuna alkhairin mutum asanda ye musu kuskure, sharrin sa kawai suke tunawa ba don komai ba sedon sudinga hukunta mutum ta hanyar faɗin duk abinda yazo bakinsu.
Butulu kawai kana ciii kana shaa daga gareta kuma kanimi lafiya ba iyama nakaba harda iyalinka baki daya amma yau kaine kake cewa ka tsani kanka saboda auren Adda Aminatu da kayi.
Lallai ba komai tunda kace baka bukatar Diyana to mu muna bukatar ta da kuma dukiyar ta dayake hannun ka, se ka shirya."
Yana kaiwa nan ya fice adakin rai a matuƙar bace.
Imbanda kuka ba abinda Faiza takeyi haka tafita kamar zata shide don kuka.
In the same time wani irin zufa yakaryo ma Baffa da Goggo.
"Yanzu shikenan wahala na da fafutuka na yatashi abanza?...! Kai baze yuwuba"
Tafadi afili batareda ta saniba seda taga Baffa yazuba mata idanu tadan wayance da faɗin
"Eh mana! Ai baze yuwuba ga mari ga tsinka jaka."
"Me kike nufi da haka?"
Goggo tagyara zama taname cigaba da cewa"Eh man ga bakin cikin yarinya ta guntso cikin shege gashi za'a kwace kuɗinda ka ke samu kana rufa ma kanka asiri kaga shikenan ciwon zuciya se ya kashe ka"
Shiru Baffa yayi alamar tinani bayan shedewar wasu yan mintoci yadauki wayarsa.
Goggo tai saurin yin magana"me kake shirin yi ?"
Idanunshi nakan wayarshi yabata amsa da"akwai wani banufe da yake mun tsarin shaguna a kasuwa wannan mutumin akwai lakani shi zansa yarufe mun bakinsu gaba daya su manta dani Kinga shikenan"
"Idan kai haka ai ka kashe maciji ne baka sare kanshi ba"
"Kamar ya?"
Baffa ya tambaya cikeda neman karin bayani.
Goggo ta saki murmushin jin dadi alamar har yanzu nasara na tare da ita awannan tafiyar.
"Abinda nake nufi shine ko sun manta da kai to idan har Diyana ta haifi abinda yake cikin ta tabbas zata dawo don ta amshi dukiyar ta.
Nasani! Kasani yanzu dukiyar ta shine mafi rinjaye akan naka kaga shikenan ka tashi a fankin fayau."
Ba iya bakin shiba gaba daya jikinshi rawa yake tsabar tashin hankali, afirgice yabude idanun sa daya lumshe sakamakon has komai babban giɓin da rayuwarsa zata samu asanda hakan ya faru.
"Meye mafita"
Murmushin jin dadi Goggo tasaki, ganin sunyi ido hudu da Baffa yasan yata gane kato ɓaran da take shirin yi seta wayance da faɗin
"Abinda yaka mata kayi shine kasanya shi yemata abinda gaba daya zata tsaneka dama gidannan kaga shikenan ba kare bin damo"
Da wannan shawarar Baffa ye amfani ita kuma Goggo farin ciki ya cikata, ji takeyi kamar ta taka rawa don murna wannan shine karo na ba adadi da nasara tai mata lamuni wajen cikan mafarkanta.
Hmmm masu karatu labari pha yadau🔥 Shin abinda Goggo tafada zai zama gaske 🤔🤔 toh idan yazama gaskiya ya makomar Diyana zai kasance 🤷🤷
Muhadu a chapter 18 don Jin yadda zata kaya......
Na barku lafiya masoya na😍😘
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌗 MAKAUNIYAR HANYA 🌗
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰