CHAPTER 18
Da wannan shawarar Baffa ye amfani ita kuma Goggo farin ciki ya cikata, ji takeyi kamar ta taka rawa don murna wannan shine karo na ba adadi da nasara tai mata lamuni wajen cikan mafarkanta. *KAWU SHATTIMA*
Shiru dakin yayi kamar babu ababen halitta masu rai aciki se agogo dayake bugawa yana alamta musu lokaci baya jira sedai ajirashi.
Kawu Shattima yaciro wayanshi yana dannawa ya kama faɗin"Yakumbo bari in kira Dawood inji inyana wurin aikin shi inje in shigarda report "
Dasauri Yadikko ta katse shi"meze hana kafara kiran Hafsatu muji ko can taje."
Beyi musuba ya kira numbern Aunty Hafsat da ke tsaye tana kallon yanda manyan Doctor's suke sanya nakasa dasu suna zuwa yin tests suna kawo musu results, wanda duk baya rasa nasaba da kasan cewar su manya a hospital din.
Wayanta yahau ringing se data matsa can gefe tadauka taname gai dashi, bayan ya amsa se ye shiru yana jin jina yanda zai mata tambayar.
Jin ye shiru yakasa magana yasan ya tinaninta bata sakon batan Diyana yariskesu. Hakan yasa ita tasoma magana.
"Kawu Diyana ko?"
"Eh tazo gidan kine?" Yafaɗa bakinshi har yana kyarma.
Tace"da athuba tazo yanzu ma haka muna asibiti da ita"
Tana jinsa yasauke nannau yar ajiyar zuciya beriga ya katse wayarba taji yana gayama su Yadikko.
Katse wayan tayi asanda taga sauran likitocin sun fito sun wuce saura mijinta kawai.
Takawa tayi zuwa inda yake tsaye, idanu ta zuba mai cikeda neman karin bayani, ganin yayi shiru yasan yata cewa
"Ya tabbata tanada ciki ko?"
Kai yagir giza mata alamar"a'a "
"To menene?"
Tasake tambaya hawaye na kwaranyo mata.
Rungume ta yayi murya atausashe yasoma mata bayani.
"Ki kwantar da hankalin ki komai zedawo dai dai, mun tabbatar da she's full virgin sedai we are very confused da muka ganta da ciki but Allah ze kawo mafita.
Then I'm sorry to say Diyana ta kamu da depression"
Jirine taji yana dibanta bai cin ajikinsa take da ba abinda ze hanata zubewa aƙasa, hawayen tausayin kanwarta suka ciga bada saukar mata shikenan ƴar uwanta ta nakasa......
"Ki natsu don Allah ba abinda ze sameta matukar akabi dokokin da likitoci suka sanya da kuma gujema sanyata acikin damuwa ko bakin ciki"
Shiru tayi tana sauraronsa ahankali take jin natsuwa da kwanciyar hankalin da ta rasa suna dawo mata.
Tabbas duk macen da tai dacen miji nagari to ta godema Allah.
Wasu ma aika tane guda biyu suka shigo da gadon ɗaukan mara lafiya atare dasu akwai Doctor Mukhtar.
Daki aka sauya ma Diyana zuwa VIP because condition din da take ciki.
*ABDUL MALEEK*
Zaune yake a sabon offfice din shi na New Life Specialist Hospital daya nimi transfer yadawo tun kwanaki biyu da suka wuce.
As usual wayar Diyana yake dialing switch off, rabonshi da ita tun ranar da suka rabu a gidan Inna duk kiran da take mai yana gani yake kin ɗauka amma daga jiya zuwa yau da ye mafarkin ta cikin wani mummunar yanayi yake kiranta wayarta akashe.
Numbern Musaddiq ya lalubo da niyyar yace mai yaje gidan ya duba mai Diyanan.
"Idan tai aure ya za kayi? Kana ganin Arshad ze lamunci ka rinka kiran mai mata?!...."
Tambayo yin suka fito daga wani kusurwa na zuciyarshi zuwa ƙwaƙwal wanshi, dasauri ya datse kiran.
"To amma alƙawari kai mata na zaka kasance atare da ita a kowani lokaci matukar Kanada rai da lafiya"
Wani kusurwa na zuciyarshi ta tina tar dashi, nan take wani kusurwan ye raddi ta hanyar cewa
"Yakamata ka nisanta kanka daga gareta saboda igiyoyin aure da zasu rataya akanta, aduk lokacin da kake tare da ita kana shiga wani yanayi k.....
"haramunne nasani please stop!"
Yakatse zancen zucin da faɗin haka afili cikin wata raunann niyar murya.
Nan take kanshi yahau sarawa, zuciyarshi ta shiga dokawa dasauri dasauri, amatsayin shi na likita yasani idan har aka auna jininshi ayanzu ba makawa se anga yahau.
Cikin shine ya murda tare da bada sauti alamar jin yunwa, se yanzu abinci ya fado mai arai wanda rabonshi dashi tun jiya da rana.
Daƙyar ya iya mikewa yaje fridge yadauko fresh milk ya bude daga tsayen da yake ya kafa bakinshi agoran yasha.
Seda yaji yakai mai limit ya rufe ya mai dashi ciki shi kuma yakoma yazauna yana sauke numfashi daƙyar.
*BAYAN KWANAKI BIYU*
FAIZA
Tsaye take a kitchen tana hada kayan da za'a kai asibiti.
Muryar Faizan taji yana kiranta kamar ze tada gidan, dagudu tafito tana amsa kiransa.
Kayan wankin da ke hannunsa se tsami da warin abu da takasa gane ko na menene ya watso mata.
"Gayinan ki wanke mun idan an kawo nepa ki goge su se ki kaimin ɗakina"
Ye maganar yana wani ciccijewa, idanunsa sunyi jajir alamar ba acikin hayyacinsa yakeba inda ace hankalin Baffa yana jikinshi, Goggo ta sanya mai ido bayan kudaden da take bashi da zata gane dabiun Faizan sun sauya.
Jajayen laɓɓansa sunyi duhu sun ture sun zama marun alamar yana ban kama cikinsa hayaƙi. To son ƴaƴan kawai aka iya amma tarbiyyar su ko oho!
Tana nan tsaye idanunta suka sauka akan Baffa dake tsaye yana jiran Goggo suje asibiti wurin Inna tun ranar da aka kaita bata sake komawa ba yau ɗinnan ma zata je ne saboda taji Shatu tace zata zo.
Adaren ranar ma aka sallame su suka dawo gida. Shatu na zaune itada Inna Baffa yashigo shida Goggo suke gaya mata abinda Diyana ta aikata.
Baffa yaƙara da"adon hakama na yanke hukuncin auradda Faiza"
Shatu ta nisa tace"tasamu wani mijinne?"
"A'a" Baffa yabata amsa.
"Kanada wanda zaka ba kenan"
Baffa yabuɗe baki zai magana Goggo ta katse shi da faɗin"A'a nidai aganina auradda Faizan shine dai dai wutarda yaƙone ka shine wuta."
Emotions din da suke yawo akan Shatu ne suka zama sanadin sauya wan wasu al'amura, sanadin tsaida wasu hawaye dake kwaranya, sanadin sauya wan mutumin da ba'a zataba, sanadin gano makauniyar hanyar da suke bi bisa son zuciya, sanadin gyaruwar zumuncin da ya lalace samada shekaru 50.
"Shikenan amaida auren kan Arshad"
Shiru Goggo tayi ita ayanzu batada wata matsala da auren Faiza tunda Suhaima zatai aure ga kuɗaɗen da takarɓa wurin Baffa zata soma business.
*
Shatu na komawa gida suka zauna tagaya ma Alh Usman ansami sauyi daga yarinyar da Arshad ze aura.
Amemakon tace Diyana tayi cikin shege tagudu se ta sauya tace yarinyar ba ta son Arshad wani daban takeso Baffa yamatsa mata tagudu dangin mahaifiyarta.
Yanzu da taje ta yanke hukuncin akan abarta da zabinta a maida auren kan kanwarta Faiza.
Sosai ya fahimce ta ya mara mata baya ita harseda tai mamakin yanda yafita farinciki da maganar tun adaren yaso kiran Arshad yagaya mai ta hanashi seda safe.
Readers kuna tinanin Arshad zai yarda ya'auri wata ba Diyana ba?!...duk da itama Diyanar auren manufa zeyi da ita?!!....
Ga lover guy Abdul Maleek yana feeling halinda masoyiyar sa take ciki.