Makauniyar Hanya

CHAPTER 19

by @hindatuauwal

Sosai ya fahimce ta ya mara mata baya ita harseda tai mamakin yanda yafita farinciki da maganar tun adaren yaso kiran Arshad yagaya mai ta hanashi seda safe.

*DIYANA*

Zaune take akan tsakiyar gado tana kurban shayin hannunta ahankali.

Kwanaki biyun nan da ta samu a asibitin taji dadin jikinta sosai ga magun gunan da Aunty Hafsat tasa aka karbo mata daga islamic chemist na karya sammu da sihiri.

Amsa su Hidayat kawai take yi amma gabaɗaya hankalin ta na can wurin Aunty da taje karbo result ɗin pregnant test ɗin da aka sake mata.

Idan tace faduwar gaba ta takaita abinda takeji, zuciyarta ta tace take zillo tana ƙoƙarin tsaga kashin hakar karinta ta fito.

Bude kofar akayi wanda ye dai dai da bugawan da zuciyar Diyana tayi hakan yasan yata runtse idanunta.

Hannun Aunty taji acikin nata dake rawa, ko bata fadiba tasan kwarin guiwa take bata, jin shesh sheƙan kuka yasanya ta bude idanuwanta ahankali.

Aunty ta gani fuskarta shar kaph da hawaye. Sororo tayi tana kallon ta batareda tayi zato ko tsamma niba taji Aunty ta rungume ta cikin kuka take faɗin

"Allah ya rabaki da duk wani abu dake damunki, result ya fito da sakamako mai kyau."

Numfashi mai nauyi ta sauke zuciyarta na natsawa awuri guda.

Jikinta ne yai sanyi asanda wani sashi na zuciyarta ta sanar da ita su kaɗai ne suka san cewa ba tai cikin shege ba.

Jitakeyi ina ma tanada dama data kira Ummah Sumayya ta sanar da ita sedai maganan Yakumbo akullum idan sukai waya baze barta ba.

Akullum cewa take"Bazaki taɓa komawa gidanku yanzuba insha Allah se kin zama abar SO abar alfahari acikin al'umma gaba daya, shi dayake cewa yatsani kanshi saboda auren mahaifiyarki se kin zaman mai inuwar gajimare"

Akaran kanta tun sanda taji abinda Baffa yace taji wani irin tsanar shi yashigeta kamar yadda baya bukatar ta arayuwar shi haka itama bata bukatar shi, ta....

"Diyana tinanin me kikeyi haka"

Kasalallen murmushi tasaki tana amsata"tinani nakeyi menayi da na cancanci wannan tai makon daga ubangiji"

"Hakuri da yarda da ƙaddara yanzu dai godiya yakamata kiyima Allah se kiga yaƙara miki wani kyautar da baki taɓa zato ba"

Aunty tafaɗa cikeda tabbatar wa.

*NUAIM*

"waye ya dake ka?"

"Forget about it"

Yafadi da son yabar maganan kamar yadda yabu kata.

Kallon fuskarsa yakarayi bacin rai na ƙara cikoshi har wuya.

"Kaga yamin waye ya dake ka?!"

Koshi da ya haifeshi beta ɓamai irin wannan dukan ba, riri tashi yake sakamakon shi kadai ne mai aduniya bayan tarin shekarun daya ɗauka yana addu'a.

"Arshad ne"

Kai yajin jina yasan yaron sosai, yasan ze aikata amma daga kan dansa baze kara marmarin dukan dan waniba.

*ARSHAD*

Kamar ta tsuniya haka yaji abinda suke fada mai ayanzu, ye wani smacking face yana kallon su

"Nipha ba wata yarinya da zan aura ita kanta Diyanan plan ne so forget about it ko yanzu naga benefit din abinda nayi."

Yaƙarke maganan yana mikewa, maganar da Daddy yai yadaka tar dashi

"Koda baka sonta dole ka aureta saboda mu"

Wani dariya mai cikeda raini yasaki wai yau shi Arshad ake kokarin tilasta wa, tilas cin ba akan komai ba se akan aure this is unbelievable.

"Kaga Daddy wannan ba maganar da zamu tsaya jaa in jaa bane this is my final decision"

Ko kallon fuskokin su bai yiba balle yaga halinda magan ganun shi suka jefa su yasa kafa yasoma takawa yana kallon kayan jikinsa daye squizing saboda fadan da sukayi da abokinsa Nuaim.

Akaro na farko cikin shekaru ashirin da biyar na rayuwar Arshad da ya ɗauka yana tsallake iya kokin daya sanya mai yaji baze iya tolerating ba.

"Muma mun riga mun tsaida magana bazamu sauya ba."

Shatu dake zaune tai shiru ba ita kadai ba kuwwa agidan yasan halin Arshad kamar yunwar cikinsu, kafiyane dashi da rashin jin magana se kace arnan farko abin da yasama ranshi kawai yake yi, maganar da Arshad yafadi yasan yata kallon sa dasauri.

"Idan ka aura mun ita seka zauna da ita nabar maka ba......

Kauuuu.....sautin marin da Daddy yemai yakatse maganar da yake yi.

"Marina kayi?"

Arshad ya tambaya kamar amsan da za'a bashi shi ze sauya abinda ya faru.

Ye scrolling idanunsa yana dariya mai ciwo yace"mari!akan wannan maganar ka mareni to ai shikenan but kasani wallahi bazan taɓa yin abinda kake soba."

Yana rufe baki yajuya ya bar musu falon.

Kansa yadafe magan ganun Arshad namai amsa kuwwa daga zuriyarsa zuwa ƙwaƙwal wansa.

Yasha ganin iyaye suna bama ƴaƴan su umarni sunabi koda kuwa hakan yasaɓama ra'ayin su, to amma meyasa shi Arshad baze mai wannan alfarman ba?

meye mai da zafi da baze mai biyayya kamar sauran ƴaƴaba? shidai a iya saninshi yadauki duk wani responsibility nashi na uba da yawan lokaci yakan sadaukar da farin cikinshi don shi ye farin.....

Begama tinanin ba yaji kanshi na sara mai, wani duhu yagil mamai ta cikin idanunsa, ƙafafunsa suka lauye, jikinshi ya rinjayi karfinsa.

Ihu Shatu tasaki tana kiran sunan Daddy da yafadi.

Hankali atashe Hajiya Rukayyat abokiyar zamanta da Amma mahaifiyar sa suka shigo.

Da tai makon ma aikatan gidan maza aka dauke shi aka kaishi asibiti.

*

Imbanda huci ba abinda yake yi, lokaci zuwa lokaci yakan saki tsaki yadaki sitiyari daga yanda yake tukin zaka fahimci ba lafiya ba.

Yana gabda fita anguwar yaga wata mota tai packing a tsakiyar hanya, horn yayi akai mai banza hakan yasan yashi fitowa a harzuke.

Ƙwan kwasa glass ɗin motar yayi, kanshi ne yaji yana juya mai wani abu dayafi karfin bacci na neman kaishi kasa ta kowani hali,

baze iya cewa ga abinda ya faru ba amma yasan da zuge glass ɗin da fesa mai wani abu da besan ko meyeba ya faru ne aƙasada daƙiƙu uku.

Idanunshi ne sukai nauyi hakan yasan yashi lumshesu badon ranshi yasoba, yanaji wadansu mutane da besan ko suwaye ba suka kamashi suka sanya shi amota.

Anya kuwa tom Arshad dai yafada hannun Yan sari ko ya zata kaya?...

Wazai kar bosa bayan bangonsa yafadi?...

Kada kumanta chapter 20 ne nagaba da wannan.

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰

🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌗

♏ HINDATU AUWAL

AMANAR SADI-SAKHNA 🥰