CHAPTER 20
Idanunshi ne sukai nauyi hakan yasan yashi lumshesu badon ranshi yasoba, yanaji wadansu mutane da besan ko suwaye ba suka kamashi suka sanya shi amota.
*SHATU*
Tsaye suke suna sauraron abinda Doctor ke fadi, Khausar da tazo daga makaranta tana gefe tana trying numbern Arshad.
"Jinin shine yahau sosai shiyasa ya shiga wannan halin but insha Allah zai farfaɗo lafiya kalau"
Jiki a sake sukai mai godiya yawuce.
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un"
Khausar dake kange da waya akunni tafaɗa cikeda tashin hankali.
Fuskokinsu dau keda wani yanayi daya girmi tashin hankali suke kallonta gaba daya anrasa mai jarumtar daze tambayeta abinda ke faruwa.
"Yaya ne ƴan sanda suka tsinci motanshi da komai nashi aciki amma shiɗin babu shi"
Takar ke tana sakin gunjin kuka. Shiru dakin yayi ba abinda ka keji se salatin Amma da kukan Khausar.
Hajiya Rukayyat da suke kirada Mommy na tsaye wasu irin hawaye masu zafi da radadi ne suka shiga wanke mata fuska.
ahankali take kukan da ya fito tun daga kasan zuciyarta, tana rufe idanunta taji kanta yasara daga ita se uban gijin daya halicce ta ne yasan irin sonda takema Arshad.
hai huwar shine kawai batayi ba amma duk wani dau dalanshi atare da ita yayi su, batasan dadin haihuwa ba se akan Arshad, samunshi ya mantar da ita zafin rashin ɗaa idan tarashi.......
Kasa karisawa tayi saboda kuka mai sauti daya kwace mata.
Shatu ko nace Ummy kamar yadda ƴaƴanta suke kiranta tai tsaye kalaman na shiganta.
"Arshad..... Arshad ne yabace akwai abinda yakamata inyi!"
Haka ƙwaƙwal wanta ke fadi yana mai mai tawa, addu'a take sonyi ko zata samu natsuwan ta yadawo gareta sedai bata samu komaiba, tamanta komai.
Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'un da Amma tariƙe tamau tana fadi tasamu itama tasoma karan tawa kamar mai koyan hakan.
Tun daga yatsar kafanta take jin wani irin natsuwa na ratsata, seda taji ta sami natsuwar da zai ishe ta yin abinda ya dace sannan takalli sauran matan da basa cikin hayyacin su.
A yanayin da suke ko tayi magana ba jinta zasu yiba hakan yasan yata fita batareda tayi musu magana ba.
Tana fitowa reception sukai kaciɓiss da Abbu da Ummu.
"Ina kwanan ku"
"Ina zuwa haka?"
Ummu ta tambayeta bayan sun amsa gaisuwar ta.
"Dama wurin ku zan zo Arshad ne yabata......"
Nan tagaya musu komai ta ƙarke tana fashewa da kuka me ratsa zuciya.
"Ku koma ciki Fadima, Ni se inje police station in kai report"
Hannunta Ummu takama suka koma ciki shi kuma Abbu ya juya ya shiga mota driver yaja zuwa police station.
Suna zuwa suka shigarda report inda Allah yatai makesu D.P.O din dalibin Abbu ne.
Officer's aka shirya mota guda sukaje inda akaga motar, CCTV camera dake wurin aka duba anan ne sukaga numbern motar sedai fuskokinsu akwai face mask.
Hukumar kula da ababen hawa suka turama numbern sannan aka kira officer's din dake duty ahanyar da motar masu laifin tabi.
D.P.O yakalli Abbu"kada kadamu insha Allah za'a ganshi ka koma gida duk abinda bincike yabamu zanzo in sanar dakai."
Godiya Abbu yemai yadawo asibiti hankalin kuwwa atashe. har yamma shiru babu motsin D.P.O shima Daddy bai farkaba daga karkema se likita yace musu su koma gida abar mai jinya.
Shatu kawai aka bari su suka dunguma tare da Abbu suka dawo gidansa don bazasu iya zama nesa dashiba basajin halinda ake ciki, zasufi samun natsuwa idan komai nafaruwa agabansu.
Amma ce kawai tahau motan daya kawo su takoma gida.
*ABDUL MALEEK*
Da sallama ya shiga babban falon su, murya acun kushe suka amsa suna kallon sa.
Jikin shine ye sanyi ganin fuskar Mommy da ya kumbura saboda kuka.
Ita kanta Mubaraka idanun ta sunyi lufu lufu alamar taci kuka har ta gode Allah.
Ummu na gefen Abbu tana jan carbi, idanun shine suka sauka kan Abbu zuciyarsa ta doka da karfin gaske ganin wani irin yanayi shimfide a fuskarsa daya zarce tinanin duk mai tinani.
Ahankali yafara jan gaji yayyun ƙafafu wansa yana gabda kaiwa inda Abbu ke zaune yaji an rungume shi tabaya.
hannu wanta da suka zagaye kugunshi yakalla kafin yafara jin dumin ruwan hawayenta na jika mai riga, be motsaba saboda yanaso tai kukan ko zata samu sauƙin abinda takeji.
Sallama akayi a kofar falon suka amsa D.P.O yashigo yazauna.
Abdul Maleek ma kama Khausar yayi suka zauna, damtsen hannun shi tasamu taɗora kanta.
"Amm....gaskiya Sheik ina matukar baka hakuri akan abinda zakaji daga bakina, ba zance ba musan inda Arshad yakeba sedai ya shiga inda bazamu iya yin komai ba. Kutaya shi kawai da addu'a."
Takaici ne yadanne mamakin da yabasu, sun shaa jin ana cewa ƴan sanda na haka amma basui zaton D.P.O da kanshi ze iya kallon su ya gaya musu hakaba.
"Ina ya shiga?"
Abdul Maleek ya tambaya muryanshi dauke da wani yanayi da suka kasa gane ko menene.
"Idan kafita G.R.A sosai tabaya akwai wani dan karamin daji to wannan dajinne suka tsare shi ba wanda yake iya shiga wurin hasalima kanasa kafanka awurin zakaga yazama makeken kogi.
Munada case's sosai akansu sedai bamada yanda zamuyi mu ka masu sunfi karfin mu."
"Okay muje waje ina son magana dakai"
Ganin yamiƙe yasanya Abbu kallon sa, kai yagyaɗa masa alamar kar yadamu.
Kamar yadda ya buƙata haka D.P.O yamiƙe suka fito.
"Zaka iya rakani?"
Abdul Maleek yafaɗa yana zuba ma D.P.O ido.
Bude baki D.P.O din yayi kamar zeyi magana se kuma yafasa. Besan me yasaba amma akwai wani abu tattare da matashin dake gaban shi dabaze barshi yemai musuba.
Se yatsinci kansa da daga kai alamar"Eh"
Drivern da ya dawo dashi yakira ya amshi key, dakanshi yaja motar D.P.O na mazaunin me zaman banza.
Tafe suke babu me cewa komai, jan motan kawai yakeyi with empty emotions, shi kanshi be taɓa sanin yanada ƙarfin hali da kwarin guiwa ba irin na yau.
Ko sau daya betaɓa jin haushin abinda Arshad ɗin yake maiba amma yakan tsinci kanshi cikin bakin ciki idan yatina dabi'unshi, ya kanji tausayin shi idan yaga yanama Ummy wasu abubuwan sau......"
"Mun iso!"
D.P.O yakatse mai tinani da faɗin haka.
Murfin yabuɗe ya fito kai tsaye dajin yadin kara yana jin muryan D.P.O yana cemai ya kula.
Ko takanshi be biba domin batun yau ba yarigada yagama imani da ba abinda ze sameshi arayuwa batareda Ubangiji yasaniba kuma baze barshi hakaba se ya kawo mai dauki saboda addu'an bawa baya taɓa faduwa kasa banza ako wace safiya da maraice seyayi addu'an niman tsari daga shaidanun mutane da aljannu.
ayanzu ma se daye addu'a aƙofar dajin yasanya ƙafansa na dama ze iya rantse wa ko ɗarr bejiba aranshi se ma wani kwarin gwuiwan shiga wurin daya damu.
Wata ƴar siririyar hanyace anyi mata kwalta, side by side bishiyoyi ne, hanyar yamiƙe.
Hayaniya yafaraji sosai, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su dashi, imbanda iskar dake kadawa baka jin motsin komai ga wani irin yanayi da ya girme ma mamaki zane a allon fuskokinsu.
Yalura shi suke so yafara magana hakan yasan yashi yamutse fuska yana cewa
"Shugaban ku nake son gani"
"Waye kai"
........Wani amsa Abdul Maleek zai bayar?!......
Shin mai zai faru awannan waje?!.....
Arshad zai nuna yasan Abdul Maleek kuwa?.....
An yama zaa sami Arshad din araye?....
Zaku sami duka wadannan amsoshin a chapter 21
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌗
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰