Makauniyar Hanya

CHAPTER 21

by @hindatuauwal

"Waye kai"

Wani daga cikin su ya tambaya.

Abubuwa biyu na wahal sheshi arayuwa na farko dogon bayani, na biyu bada labari.

"Bakon da ya gayyata"

Kallon sa sukayi cikeda shakku acikin idanuwansu, zuciyoyinsu kamar zasu fito saboda bugun da sukeyi, kallon da yake musu ya dagula musu lissafi.

zasu rantse yana bayyana agun iskar wurin yasauya sosai abinda suka gani acikin idanuwanshi yabasu tsoro, gadai shi mutum kaman su amma yana tattare da wani abu me girma da ya shallake tinanin su.

"Muje ciki"

Wani murɗaɗɗen mutum da yasauke waya akunnin shi yafada.

Kamar yadda ya bukata haka yabishi abaya har zuwa cikin wani babban gida, sosai gidan yatsaru da ginin zamani.

Shi kadai suka sameshi yana hakimce akan daya daga cikin royal chairs din da suka ƙawata falon, kwalban giya ne a gabansa da yake ta rabar sanyi.

Bejira se an bashi izinin zamaba yazauna yai crossing legs dinsa.

Guy din daya kawo shi yadan ran kwafa agaban shi cikin gir mamawa, da hannu yemai alama da yabasu waje.

Kallo mai cikeda ma'anoni maban banta yake bin A.Maleek dashi.

"Nasan baka sanniba kamar yadda Nima ban san kaba. Ɗan uwana nazo nima anan wurin idan kudi kake bukata ka gaya min insha Allah baze....."

"Waya baka izinin shigowa muhallina?"

Ya katse shi da tambayan cikin murya irin ta mutanen da suka fara buguwa.

"Dan uwana!"

"Kai yanzu kana tinanin zaka iya barin wurin nan araye balle har ka dauki wani ɗan uwanka? Idan baka saniba inaso kasani hakan betaɓa faruwaba ba kuma ze faru akanka kaba."

Yaƙarke yana nuna shi da bindiga.

Shamma tanshi yayi yaware tafin hannunsa ya zabga mai mari akunni da iya ƙarfinsa ba komai yasan yashi yin hakan ba se idan kadaki mutum akunni kai tsaye zafin yake zuwa ƙwaƙwal wansa.

Wani irin dummm yaji kansa yayi, so yakeyi yadawo hayya cinsa amma yakasa.

Bindigar da yasaki Abdul Maleek yadauka ye pointing dinsa dashi yana fadin

"Ina dan uwana yake?"

"Karka kashe Ni don Allah ka gaya min sunansa."

Roƙon sa yake cikin tsananin azaba da tashin hankali, jikinsa gaba daya ɓari yake.

"Arshad"

Ai ko gama rufe baki beyiba yajawo wayanshi dake kan table ye dialing numbern aka dauka a bugun farko.

"Nabaka 1 second ka binciko min waye Arshad duk inda yake a fito dashi..." ajiye minshi a motar da take kofar shigowa da jinnan"

A.Maleek yafada muryarsa aɗage yanda na cikin wayan zeji.

A idanuwanshi kadai zaka gane a firgice yake, tsoron mutuwa yakeji da gaske.

Wani kasalallen murmushi Abdul Maleek yasaki,

Wayarsa na motsawa yadauka yace"Tom"

Bayan yasauke wayar yakalli Abdul Maleek"sun kai mashi ranka shi daɗe"

Mikewa yayi fuskarsa dauke da murmushi, wuyanshi yadamƙo yasaita kansa da bindigar ya ingiza shi waje.

Yaran shi na ganin su ahaka suka yunƙuro, cikin har gowwa shugaban su yace

"Dan ubanku ku koma baya kar wanda yamatso"

Cak suka tsaya suna binsa da mugun kallo har suka fito wajen dajin.

Ganin Arshad zaune agaban mota yasan yashi sakin numfashi mai nauyi, sakinshi yayi ya shiga mota seda ya kunnata yakalleshi ya mikamai bindigar yace dashi.

"Ka yahakuri bahaka nasoba kawai banada zaɓi ne."

Kanshi kawai yajin jina mishi ƙwalla na ciko idanunsa, betaɓa ganin soyayyan ƴan uwan taka irin wanda ya gani acikin idanuwan wannan mutumin ba, inama ace shima nashi ƴan uwan zasu soshi haka!da ba abinda zesan yashi zama a dajin nan.

Haka yaja ƙafafuwan shi da sukai mai nauyi yakoma ciki yana jin kewar nashi ƴan uwan na taso mai.

*

Tafiya sukeyi babu mecema kowwa komai sedai Arshad ya kafeshi da ido yana kallonsa da wani irin yanayi so yikeyi yemai magana but yasan yana bude bakinshi ba abinda ze fito imbanda gunjin kuka se kawai yahakura ye shiru.

Wayanshi yazaro ye dialing numbern da akai saving da Doctor Salis tare sukai karatu, tambayar shi yayi yaji yana asibiti yace "Eh"

Arshad na kallonsa suka shiga Queen Elizabeth Road asibitin El-Madina suka shiga.

Jikinsa dake matuƙar ciwo na dukan da akai masa yake motsawa daƙyar yana bin shi abaya.

Bakinsu dau keda sallama suka shiga bayan sun gama gaisawa Abdul Maleek yace

"General test za aimai inda abinda yake damunshi se abashi magani"

Da murmushi akan fuskar Doctor Salis yema Arshad jagora zuwa lab, yana tsaye agun aka gama komai suka dawo.

Magun guna ya rubuta mai wadan da zasu tai maka ma jikinsa dayasha duka yawar ware.

Godiya Abdul Maleek yemai suka fito yatsaya a pharmacy ya sai magani sannan suka shiga mota.

Yana packing ya fito batareda yako kalleshi ba. Beyi mamakin ganin su har yanzu suna nan a'inda yabar suba, sema da yakallesu ya tina asheda D.P.O sukaje wurin ko ina yaje oho!

Bedroom din sa yashige yabarsu da Arshad, kayan jikinshi yafara ragewa kafin ya shiga ye wanka.

Yana fitowa yamur zamai da tiraren da yake amfani dashi yasaka kayan bacci, abincin sa guda daya da yarage mai aduniyar sa yadauko a fridge yasha fresh milk yakoma ya kwanta.

Yana jin lokacin da sukaima su Abbu sallama suka tafi.

*ARSHAD*

Zaune yake akan sallahya bayan yagama biyan bashin sallolin da ake binshi.

Yana jin yanda magun gunan daya sha suka fara mai aiki, shikan shi yasan bacci yaka mata yayi amma hakan yaki samuwa saboda abinda ke cikin zuciyarsa da ƙwaƙwal wansa yafi karfinsa.

Abdul Maleek da sauran family dinsa sukai mai tsaye a zuciya da wani irin yanayi mai ciwon gaske.

Ya lumshe idanunsa kansa daye nauyi yabuɗe yadauko wasu hutuna da suka shuɗe abaya ya shiga hadasu suna maida abinda yafaru a shekarun baya tamkar yanzu suke wanzuwa.

Masu karatu nasan kun dade kuna son sanin cikakken tarihin Abdul Maleek?....

Wata iriyar alakace atsakanin sa da Arshad wadda mahaifiyarsu daya Amma iyayensu maza daban daban bayan family dinsu daya?........

Meye tushen wannan gaban dake tsakanin su........waye Kuma silar hakan?