CHAPTER 22
Ya lumshe idanunsa kansa daye nauyi yabuɗe yadauko wasu hutuna da suka shuɗe abaya ya shiga hadasu suna maida abinda yafaru a shekarun baya tamkar yanzu suke wanzuwa.
Sheikh Buhari asalinsa ba zazzage ne, tun daa da ilimi ke wahala ya kasance mai ilimin boko da arabic saboda wannan baiwar ilimi da Allah yemasa yasa duk azumi yake zuwa gari gari yin tafsir.
Ana haka se watarana ya sauka a Kano a cikin masarauta kunsan mutanen daa masu girma ma jama'a ne musamman masu ilimi shiyasa suka karbi Sheik Buhari da hannu bibbiyu.
Alokacin be wuce shekaru 27 ba, adan zaman da yayi dasu se alaƙa mai ƙarfi ya shiga tsakanin sa da yarinyar gidan sunanta Fadima.
Ranar daze tafi ya bayyana mata soyayyan sa aiko tai na'am dashi, yatafi akan baze jimaba ze dawo.
Asanda ya isa gida se ya tarar da mata aɗaki limamin garin abokin mahaifinsa ya bashi diyarsa salaka an daura auren yana can.
Da yaga haka se yeshiru da bakinsa yaƙi gayama kuwwa, acikin zuciyarshi ya ƙudurce se yasan ya matarsa Abida tagudu da ƙafanta.
Kullum cikin wulaƙanci, tsakanin sa da ita ido, bayacin abincin ta, baya hira da ita, baya hada shimfida da ita, miƙomin, ɗauko min ko kawar min betaɓa nima daga gareta ba kullum sedai ya ajiye mata kudin cefane aƙasan matashi.
Duk sati ye siyayya yakaima ƴar budurwan sa da bata wuce shekaru goma sha ukuba, duk da itama Abida din bazata wuce shekaru goma sha biyar ba.
Ahaka seda ta shafe watanni shida yakaima har Abida ta ɓara su kuma gidansu Fadima sun kunno mai wuta akan in baze yiba yafada.
Ganin yana shirin rasa abar sonsa yasan yashi tura iyayensa akai maganan aure.
Abida sam batada labari seda aka sanya rana biki saura mako biyu ya sanar mata ze ƙara aure, tai kukan da ya isheta akai aure aka kawo amarya.
Nan ma bata sami ƴan ciba seda tasamu soyuwa awurin Fadima sannan ta sami kan mijinta yasoma kulata amatsayin matar sa.
Atare suka sami ciki Abida ce tasoma haihuwa, bayan kwanaki biyu Fadima ta haihu.
Dukan su ya tambaye su sunan da suke so sukace sunan iyayen su maza se akai rashin sa'a sunan yazo daya.
Amemakon Sheik Buhari ye adalci yabama Abida girmanta se ya biye ma son zuciyarsa ya sanya ma Fadima sunan da takeso wato Al-ameen, Abida yace ta hakura ita kuma ta kafe akan dole se ya sanyama ɗanta sunan da takeso.
Shi kam yaƙi bayan yemai huduba da Usman ta sauya mai da Al-ameen, ranar suna dukansu sukaima ɗa haƙiƙa da maban bantan suna.
Jin haushin wannan abu da Abida tayi yasanya Sheik Buhari ya saketa saki daya kuma yace inta sami miji tai aure.
Jin zafin wannan abin ya sanya Abida yin alkawarin yanda ya wulakanta ta itama se ta wulaƙan tasa ta hanyar farin cikinsa da abinda yafiso wato Fadima.
Tun daga nan ta hauyin asiri kala da iri har hauka seda Fadima tayi amma Sheik Buhari be rabu da ita ba har tasami sauki ta warke.
Abida taga asiri yaƙi aiki akansa ta sauya salo tai mata sharri watarana Fadima zata dawo anguwa awannan lokacin da daddare mata ke fita anguwa tasa maza suka tare ta ahanya sui mata fyade.
Daƙyar tasamu tasha sedai tadawo bazani ajikinta. Tambaya daya yemata data dawo.
"Ki gayamin tsakanin ki da Allah meye abinda sukai miki"
Bata ɓoye mai komai ba ta gaya mai gaskiyar abinda ya faru,dayaji kuma be ƙaryata taba suka cigaba da zamansu.
Sedai Sheik Buhari kullum cikin addu'a yake akan Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Tun Fadima batasan me neman rabata da mijin taba har ta gano Abida ce, haka rayuwa ta cigabada tafiya Abida dai batai aureba ita kuma Fadima bata sake haihuwa ba.
Sheikh Buhari ya sanya Al-ameen da Usman a makaranta daya komai nasu tare sukeyi ananne aka samu shakuwa meƙarfi a tsakanin su sedai iyayensu basa farin ciki da alakarsu.
Ahaka suka girma, sukai aure. Usman betaɓa samun haihuwa ba, matar Al-ameen har ta haifi ƴaƴa yenta huɗu.
Maimuna, Aliya, Abdul Maleek, Musaddiq da ciki wata takwas ye hatsarin mota yarasu.
Data haihu yarinya taci sunan Mubaraka. Bayan shekara daya Usman yace yanason Shatu da aure da yike anan gidan take zaune tana tare da Hajiya Fadima wacce suke kira Ummu ta daka tsalle tace wallahi bata yarda ba in kuma har ta aureshi bazata tafin mata da jika ko dayaba.
Shatu ta yarda akan haka taje ta auri Usman seda ta shekara uku agidan ta haifi ɗana miji yaci sunan Arshad, bayan ta yayesa Hajiya Rukayyat ta daukesa ta cigaba da rainonsa.
Tazaran shekaru biyu akai mai kanwa Khausar har wannan lokacin bata taɓa zuwa ganinsu Abdul Maleek ba haka Ummu bata kawosu ko ta turo suba.
Bayan shekaru goma auren Maimuna yataso Ummu ta aiko drivern gidanta da invitation card.
Daddy yace"uni daya yabar su suje su dawo"
Haka ko akayi, abin yema Ummu da Abbu zafi. Bata kara zuwa gidan ba se graduation din Abdul Maleek da yagama first degree dinsa
Ana cikin pictures Shatu ko nace Ummy tafaɗi jini ya ɓalle mata ana kaita asibiti sukaçe cikine 3 months ya kuma zoda gardama taja dogon lokaci rabonta da haihuwar ga shekarunta sun jaa.
Abdul Maleek be tsaya tinanin komai ba ya sanya akai mata wankin ciki. Da Daddy yazo yaji ranshi ye matukar ɓaci ko da Abdul Maleek yazo ya gaida shi yaki amsawa agabansa yahau fadin
"Ban taɓa sanin ke wawiya bace seyau ashe banzan cinki yakai haka ?"
Haka yadinga zaginta agabansa agaban Arshad, kwayar idon Abdul Maleek kadai zaka kalla ka shaida kalan bacin ran da yake ciki.
Shi Arshad a wannan lokacin sam abin be ɓata mai rai ba don inda sabo yasaba gani, Daddy mutum ne da be iya controlling kansa ba duk abinda yazo bakinsa ze gayama matarsa kuma ko agaban waye, sumutu ko sui rai beda muba.
Kwanakin ta uku aka sallame ta se Abdul Maleek yamaida zuwan sa duk weak end amma ko yagaida Daddy baya amsawa.
Befi one month da faruwar hakaba Arshad yafita wani party da abokansa a motar Daddy akai rashin sa'a sukai accident aka daukesu aka kaisu bareak hospital.
Emergency room aka kaisa because shine drivern gashi besanya seat belt ba hakan yasa yafi kuwwa jin rauni.
Daddy bayanan ranar yaje clearings ɗin wasu kaya daye order, Ummy takira Abdul Maleek ya sanya hannu aka shigarda shi theater.
Likitocin suka nimi tai makonsa akai theatern dashi bayan yabashi jini.
Da Daddy yadawo ko godiya be maiba sema yahau jin haushin shi fiyeda daa.
Duk rawan kan Arshad a wannan lokacin seda yaji haushin sa yakama shi har yemai magana
"Daddy meyasa bakasan Yaya A.Maleek bayan shima ɗaan kane kuma duk abinda yayi kai yatai maka, da ace besanya hannu ba antsaya jiranka da yanzu na mutu"
Daddy yakirne fuska yaname kamo hannun Arshad yace"shigowar Abdul Maleek cikin zuriyata alamune nason rabani da farin cikina wato mahaifiyar ka.
Tun asali Ummu batason auren mu domin rabamu seta turoshi. Nasan ba lallai yanzu ka fahimta ba but with time zaka fahimta."
Awannan lokacin Arshad be yarda da abinda Daddy yafada ba se watarana suna zaune duka afalo harda Daddy ranar Abdul Maleek yazo Arshad na kallon pics din da girl friend dinsa ta turo mai because some times takan turo mai kuma tare da Mommy suke kallo kuma bata nuna mai illahn hakanba.
Domin itada Daddy da Amma basa mai fado komai yai arayuwar sa dai dai ne.
Yana cikin kallo se yamiƙe dasauri da niyyar kiranta, da yike hankalinsa yana can wani waje se ye tuntuɓe wayar yafadi yazo dauka idanuwan Ummy suka sauka akan sexy pictures din da yake kallo.
Unexpected suka ga tamiƙe ta dauke sa da mari tana faɗin"wannan wani irin iskanci ne haka? Dama yanzu abinda kake kallo kenan almost 18 years ka ke dashi pha ba......"
Takasa karisawa saboda marin da Daddy yakai mata Abdul Maleek yarike hannun sa.
Cikin fushi ya dubesa"zan iya jure duk wulaƙan cin da zakai min amma bazan iya zuba ido inga kana cin zarafin mahaifiyata ba.
Idan baka santa to kasa keta amma idan har wani abu yasameta ta sanadin ka to kai kuka da kanka."
Tsaban mamaki ya hana Daddy yin magana har Abdul Maleek yasa kafa yabar gidan.
Sanadin haka Abdul Maleek yarage zuwa gidan adaa duk weak end yake zuwa yakoma se yai sati biyu of to that bejeba.
Sakamakon abinda ya faru Daddy yaɗau fushi da Ummy ko abincin ta bayaci dai dai da magana ya daina yi da ita,
Inkaga dariyar Ummy to se Abdul Maleek yazo hira, samun natsuwa, ƙafewar hawaye duka tana samune a wurinsa.
Dama jefi jefi Arshad ke zuwa part din ta da haka ya faru shima yai mata kaura yabarta da ɗan so wanda baya laiphi,
Ya yarda da maganar Daddy da yace"Abdul Maleek yazone don yarusa farin cikin shi yaraba shida Ummy"
Arshad yasoma tsanar Abdul Maleek ne aranar da ya kammala S.S.C.E ana tsakiya da shagali acikin gidan dangi sun hadu tako ina.
Yayinda me ɗaukan hoto yazo Arshad na part dinsa shida abokan shi guda uku se girl friend dinsa Raheelat.
Batareda sanin Arshad ba suka sanya musu desire tablet acikin lemu ita kanta bata saniba, romantic kawai sukeyi basa sex.
Kukan Raheelat yajawo hankalin mutane zuwa part dinsa, hankali atashe aka ɗauki Raheelat aka kaita asibiti ƴan sandan da ba asan ko waye ya kira suba suka dauki su Arshad.
Daddy ye iya kokarin sa wajen ganin yayi free, ye loosing kuɗaɗen sa dayawa akaro mara adadi aka sanar dashi maganin matsalar shi na gida.
Don babu lawyern daze iya kare Arshad tun da abin abayyane yake yakaima har ƴan jarida sunyi magana akai, Ashema yarinyar marai niyace wani mutum ne yadauki nauyin karatun ta.
Abdul Maleek ne kaɗai ze iya yin mai abinda kudaɗensa bazasu iya yin maiba, da yin magana kaɗai za'a rufe case din.
Daddy beyi kasa agwuiwaba yaje ya sameshi a offfice dinsa.
"Ban taɓa tinanin akwai ranar da zezo wanda zan nimi wani abu awurin kaba, se gashi yau nazo ina rokonka kasa hannu Arshad ye free"
Anzo wajen aganina anya wannan bashine yazama silar kullatar Abdul Maleek da Arshad yayiba?......
Tom zai sanya hannun ko zaiki yatsaya akan aikinsa.........
Meze faru anan gaba?.....