CHAPTER 23
"Ban taɓa tinanin akwai ranar da zezo wanda zan nimi wani abu awurin kaba, se gashi yau nazo ina rokonka kasa hannu Arshad ye free"
Kansa ya sunkuyar da girma mawa amuryansa da jin nauyi yasoma magana
"Daddy kaya hakuri akan Arshad ko baka roƙeni ba zanyi duk wani abu da nasan zai tai makesa.
Arshad jinina nane idan wani abu yasa meshi bakai kaɗai zaka cutuba Nima na cutu to amma meze hana mubar doka tai aiki akansa?
Hukuncin da za'ai mai tayu yazama hanyar kin tsuwar shi, gyaruwar shi ba iya namu bane mu kadai na al'umma ne gaba daya.
Ubane na gobe pha nan da wasu ƴan shekaru ze zama mahaifi don Allah kasanya ma zuciyarka hakuri case din nan zezo da sauki fiyeda yadda kake tinani, yarinyar ita takai kan......."
"Yi shirun ka don Allah....."
Daddy yacigaba da faɗin"duk abinda zanyi aduniyar nan don shi nakeyi nemana, wahalana, dukiyana duk nasa ne.
Indai dukiya na maganin bakin cikin duniya to nawa zasui min amma kasani Arsha da kake kira ɗan uwanka daga yau kada ka sake"
Yana gama fadi ya fice abinshi. Kafin Daddy yasamu belin Arshad se daya sha matukar wahala seda akai mai sharadi akan yaɗau keshi yabar dashi kasar.
Arshad ya tafi yabar kasar zuciyarshi cike phall da kiyayyar Abdul Maleek mai tsananin gaske.
Acan Uk ye karanci accountants yanzu haka yana aiki ne a Company din Daddy.
Kai tsaye ze iya cewa ƙaddara ce ta kaishi Saidi awancan lokacin har yaga Abdul Maleek da Diyana ta wani bangaren kuma ze dan gan tashi da abinda ya kaishi garin kai tsaye wato bikin wani abokinsa da suka haɗu a Uk.
Saukan ruwan hawaye a fuskar sa karo na ba adadi da numfashin shi dake neman ɗaukewa ya sanya tinanin sa katse wa.
Be damu da yashare hawayen saba yadafa kasa daƙyar yamiƙe yahaye gado cikeda ƙarfin hali.
Zuciyarshi na wani irin matsewa aƙirjinsa ya lumshe idanuwansa ba wai don ye bacciba se don bayada abinda zeyi mai sauki arayuwar sa dayafi wannan.
Yanajin yanda lokaci ke tafiya har aka kira sallahn athuba yamiƙe daƙyar kansa kamar zai tsage yatar watse a filin wurin don ciwo.
Be iya zuwa masallaci ba anan dakinsa yai sallah yana idarwa yamaida kansa ya kwanta a prayer mat.
*FAIZA*
Tasaba jin kalmar hakuri a rayuwar ta, ma'anarsa be taɓa zama akanta da nauyi mai girmaba se jiya da Ummah Iklima ke bata haƙuri bayan tadawo daga dakin Baffa yagama sanar da ita an tsaida aurenta da Arshad.
Tasan bazata sha wahalar rayuwa da shiba tunda bangaren dake dauke da soyayya acikin zuciyarta ta dade da mutuwa since lokacin da tarasa masoyinta Faisal.
Kodama hakan be faruba tasan wahalar banza kawai zata bama kanta in tace zataki aurennan.
He's so stubborn tasani da yawan wasu case's da rashin kunyarda yakema Goggo Shatu da Mahaifinsa yana zuwa gidan, ko tsanar da Inna taima Abdul Maleek akan sane lokacin da yaki sanya hannu a fito dashi daga wurin ƴan sanda.
Rayuwa kenan ko dayaushe sabon ƙaddara ce ke biyeda rayuwar dan adam zuwa duk inda yaga dama.
Hayaniya taji atsakar gida jin kamar muryar Ummah Sumayya yasan yata fitowa daga kuryar gadon Ummah Iklima data samu ta lafe.
Tana fitowa taga Ummah Sumayya ta hado kayanta a akwati zata bar gidan, Ummah Iklima da Inna na riƙe da ita suna bata haƙuri taki sai kuka takeyi.
Da gudunta taƙarisa wurin ta zube akan guiwoyinta tariƙe akwatin tana bata haƙuri
"Ummah don Allah ki yahakuri karki tafi kibarni, Diyana ta tafi yanzu kema zaki tafi yaku keso nayi da rayuwa ta!"
"Ba tafiya zanyi inbar kiba kawai zuciya tace bazata iya jure zama babu Diyana ba."
"Amma Ummah indai har akan Diyana ce to zama yakamata kiyi ki tsumayi dawo warta da addu'ar fatan alkhairi agareta"
Haka suka haɗu suka dinga bata haƙuri suna lallashinta daƙyar suka samu ta hakura.
. . .
"Da sanin ki aka sanyama Faiza rana da Arshad?"
Goggo dake zaune tana chatting da wata sabuwar ƙawarta da suka haɗu a shopping mall jiya taji amon muryan Suhaima na mata magana.
Wani irin abune ya tokarema Suhaima kahon zuci ta lailayo wani ashar tana cewa
"Wannan matsiya ciyar yarinyar yace zata auri mijin dayafi nawa?"
"Eh"
Goggo ta amsata batareda wani damuwa ba.
"Eh pha kikace anya kina cikin hayyacin ki?"
Murmushi mai kunshe da ma'anoni maban banta tasaki bata ceda Suhaima komaiba.
Suhaima ta cigaba da ban bami tana zage zage kamar Goggo bazata tan kaba seta bude baki tai magana.
"Arshad baze taba zama mijin dayafi nakiba ko kin manta waye shi? Ni bana jin ma wannan auren zeyu idan kuma yakarɓi auren to kitabbata ciwon zuciya ko hawan jini ne zeyi ajalin Faiza"
Dariyar jin dadi tasaki tabama Goggo hannu suka tafa suna shewa a tsakanin su.
........Inda ace bawa yasan ƙaddarar da yake jiransa arayuwa da ayau Goggo da Suhaima ba sui farin ciki akan auren Faiza da Arshad ba.
Da Suhaima zata gujema auren Imran tun kafin ranar da zuciyarta zata tar watse rayuwa tajuya mata baya allon ƙaddara yakalleta ya kifar da duniyar ta agaban ɗimbin jama'ar duniya.
*DADDY*
Zaune yake ajikin gadon yana kallon Ummy dake zaune tana amsa waya akan Arshad tun adaren jiya da yafarka Mommy ta kira taga yama Ummy Abdul Maleek yakarɓo Arshad yasan maganar batansa.
Wanda hakan yasa zuciyarsa tai nauyi nadama tacikata har baya, akaran kansa yasan shine wanda ya lalata Arshad, hudubar da Amma ke masa akan kada yayarda yasaki jiki dasu Abdul Maleek yai tasiri sosai wajen ruguza alakarsu.
Betaba tsin tan kansa cikin matsanan ciyar kunya irin wanda yake nukur kusan sa ayanzuba.
Abu na karshe da zeyi fata yanzu arayuwa shine yanimi yafiyar Abdul Maleek da ƴan uwansa musamman ma mahaifinsa da Ummu.
"Alhaji yaka mata kadai na sanyama kanka damuwa ka daiji abinda Doctor yafadi"
Maganar Ummy bayan ta sauke waya yasanya shi kallonta ba wai don ya daina jin abinda yake jiba.
"Shatu damuwa ta zamemun dole acikin kusakurai na ban san wanne zansoma gyarawa ba, acikin mutanen da na cutar bansan wa zan fara roƙo yafiya ba.
Ko ke da kike zaune nasan na cutar dake, nine kashin bayan lalacewar tar biyayyan Arshad, nine wanda na nuna masa bakar soyayyar da ta lulluɓe tsafta tacciyar soyayyar da kika nuna masa, nine wanda na sanya tsanar danki acikin......"
"Don Allah Alhaji....."
Idanuwansa da besan ƙwalla sun taru acikiba yalumshe hawaye masu zafi suka sauka akan kuncin sa, maganan Shatu yasan yashi bude su akanta.
"Duk abinda yafaru ƙaddara ce tarigada ta wuce abu mafi dacewa yanzu shine kadau hanyar gyara bayan kanimi yafiyar wadanda ka bata mawa musamman Abbu da Ummu"
Kai yagirgiza cikin kukan da yake yi yaja hanci yana kallon ta"kina ganin zasu yafemun bayan duk abinda nai musu?"
Kai tajin jina mai cikeda tabbatar wa tabuɗe baki zatai magana aka turo kofa.
Amma, Mommy, Kausar da Arshad dake maƙale abayansu suka shigo.
Uhhm naceba wai Arshad ne yazo asibiti tom mai zai cema Daddy bayan duk laifin daye masa?.......
Koda naga pha kamar akwai dan nadama a zuciyarsa amma bari mu karanta chapter 24 zamuga abinda zai faru.
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌗
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰