CHAPTER 24
Amma, Mommy, Kausar da Arshad dake maƙale abayansu suka shigo.
Tunda Kausar tazo dakinsa ta gaya mai Daddy na asibiti yaji wani abu da besan ko meyeba ya kulle acikinsa.
Yasan duk abinda yasamu Daddy laifinsa sane, be taɓa tsintar kansa acikin kogin nadama ba seyau inda yasan magan ganunsa zasui hitting dinsa har haka da beyiba.
"Im sorry Daddy...."
Yafadi daga inda yake tsaye yana jin tsayuwar idanunsa akansa tun lokacin da ya shigo.
Out of the blue yaji Kausar tajawo sa takaisa gaban gadon, magan ganun da suka fito daga bakin Daddy yasan yashi kallonsa da sauri.
"Bakai ya kamata ka roki yafiya naba nine wanda yakamata yai haka, na cutar da kai pls......"
"No Daddy please kai shiru kayafe mun Ni....."
Se kuma kukan dayake riƙewa tun daren jiya ya kwace masa, Daddy yarun gumesa shima yana kuka.
Atare suka roki yafiyar juna cikin zubar hawaye.
Bayan tarin shekaru masu yawa Amma tai dana sani akan duk wani abu da ta aikata ma Ummu.
Allah ne kaɗai masanin gaskiyar abinda yake kasan zuciyarta adaren jiya tayi matukar nadama akan komai data aikata.
Tajefa iyalanta a makauniyar hanya mara ɓullewa, wacce take cikeda kwazaz zabai da ramuka marasa iyaka daga yanda kai zurfi a tafiya da yanda zaka tsinci kanka a kogin nadama.
I can't explain this golden moment da ya wanzu asanda Abbu da Ummu suka zoba se Mubaraka da tai musu rakiya shi Abdul Maleek ya tafi Saidi asafiyar.
Bayan tarin shekaru iyalan Sheik Buhari sun hadu a inuwa daya, sunyi kuka tare, sun nimi yafiyar juna, sun amshi kusa kurensu at the end suka kauda shi agefe suka soma hira cikeda nishaɗi.
*Abdul Maleek*
Da kansa yake jan motar yana bin karatun alqurani cikin kira'ar Sheik Minshawi.
Ƙarfe 1:00pm ya shiga Saidi seda yafara tsayawa a masallacin dake bakin layin yai sallah kafin yakarisa.
Bakinsa dau keda sallama ya shiga gidan. Ummah Iklima da Faiza dake kitchen suka amsa.
Tsayawa yai suka gaisa da Ummah Iklima ita kuma Faiza ta gaidasa.
Jin hayaniya na tashi daga cikin babban falo yasa shi gane sunada baki wadanda ba kowwa bane face kawayen Goggo.
Sashin Inna yashiga sallama yadinga yi ba'a amsaba, Faiza data biyo bayan sa sugaisa ta amsa.
Murmushi ya sakar mata batareda yace komai ba ya shiga dakin bakinsa ɗauke da wani sallamar.
Kai tsaye kitchen tanufa ta dauko trey ta zubomai ruwa da drink se glass cup.
"Nace bah please ina Diyana take?"
A.Maleek yafada bayan sun gama gaisawa da Faiza.
Shiru tayi tana jin wasu hawaye na taran mata. Ganin haka yasa hankalin sa tashi.
Habiba ce tashigo da sallamar ta hannunta dauke da flask din abincin da Ummah Iklima ta aikota dashi.
Abdul Maleek ya amsa yana tambayar ta"Ke ina Adda Diyana take?"
"Batanan" ta bashi amsa da iya gaskiyar ta.
Faiza dake rizƙar kuka yakalla idanunshi cikeda magiya agareta.
Daƙyar ta iya bude cikin kukan da takeyi "Hamma...Diyana nada ciki wata uku kuma tabar gida ba wanda yasan inda take.....!!!"
Taƙarshe tana rushewa da kuka mai cin rai.
Kalmomin huɗun farko data fadi na 'tanada ciki wata uku' sune sukai mai tsaye a kahon zuci sauran kalaman suka gan gara zuwa wani wuri mai ciwo azuciyar sa.
Baki yabuɗe zai magana sautin muryanshi yakasa fitowa daga maƙo gwaronshi.
Inna dake daki tana bacci saboda magun gunan da take shaa tafito fuskarta ɗaukeda mamaki take kallonsu.
Cikin ƙarfin hali yamiƙe daga zaunen dayake bebi takan Inna dake kiran sunan shiba ya fice daga gidan gaba daya.
Seda yasanya duk kan wani karfi nasa ya iya kunna motar daƙyar, biji biji yake ganin titi, kanshi na bugawa saboda damuwar da yake ciki.
Besan yanda akayi ba yazo Zaria kawai tsintan kansa yai abakin gate yana horn aka bude mai yashigar da motarsa ciki.
Ko kashe motar beyiba ya ɓalle murfin yafito se asannan ƙafafunsa dake rawa suka lauye, kansa daye nauyi yai shiru komai yatsaya cak!
Hankali atashe waɗanda ke aiki awurin maza sukai kansa, Su Abbu da dawowar su kenan daga asibiti wurin Daddy suka fito.
Cikeda zafin nama suka sanyashi amota se asibitin da suke zuwa a kodayaushe.
*
Sunan a tsaye aƙofar emergency hankulansu atashe ba mai iya cema dan uwansa wani abu har aka fito dashi daga emergency zuwa wani dakin daban.
Basu tsaya sanyaba suka rufa musu baya zuwa dakin da aka kwantar dashi.
Babban likitan yajuyo zeyi musu magana ganin expression ɗin dake kan fuskokinsu yasan yashi yin shiru yasoma musu bayani.
"I'm sorry to say jininshi ayanzu haka yayi kasa ga chronic ulcer so munada bukatar jini se ku turo wanda za'a dibi nashi in kuma siya zakuyi tom amma a hanzarta."
Kai kurum Abbu yagyaɗa masa mutum ɗayane yanzu ze iya bashi jini Arshad suma sun san hakane sanda Arshad din yai hatsari Abdul Maleek yabashi jini.
Nan take Mubaraka ta turama duk wani wanda yakeda hakkin sanin Abdul Maleek bayida lafiya text message.
Ko mintina sha biyar basu dauka ba sega Arshad da Amma da Mommy da Khausar sunzo.
Abbu ne yagaya mai ana bukatar jini kai tsaye yaje aka diba basu wani ɓata lokaci ba sukazo suka sanya mai.
Asannan har Aunty Maimunat da Aunty Liya sunzo.
Suna zaz zaune suna kallonsa yana baccin alluran da akai masa.
Da duk kallon da Arshad zai masa da yanda zuciyarsa ke cikada farin cikin ganin jininshi na shiga jikin Abdul Maleek.
Ƙarfe 8:00pm Abdul Maleek yabuɗe idanun sa ahankali.
Fan kan dakin yakurama ido yana yamutse fuska alamar yana son sanin abinda ya kawo shi wurin.
Ledan jinin dake shiga jikinshi yabida kallo kamar wanda aka kwadama guduma haka duk abinda ya faru ya shiga dawo mai.
"Diyana"
Yafurta sunan asaman laɓɓansa batareda wani sauti ya fito ba se wasu irin emotions marasa limits da betaɓa tinanin mutum ze iya jii alokaci dayaba ya dannesa.
Kuwwa kallonsa yake tun lokacin da yabuɗe ido anrasa mai jarumtar daze je kusa dashi, a fuskokinsu kaɗai zaka fahimci kalan damuwar da suke ciki agameda ciwon nashi.
Aunty Maimunat ce tamatsa kusa dashi ta kamo hannun sa mara cannular tana kallon fuskarsa daye wani irin rama lokaci guda.
Kansa ya sunkuyar hawaye masu zafi suka wanke mai fuska, yakasa yarda yai sakacin da yarasa Diyana.
kwanakin da yadauka batareda yaji daga gareta ba shi kadai yasan kalan ukubar da ya fuskanta ayanzu kuma da babu ita besan yanda rayuwa zatayi dashiba.
Bazan iya cigaba da rike hawaye😭😭😭 naba kawai mutsaya anan semun hadu a chapter 25
Taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰
🌒 MAKAUNIYAR HANYA 🌗
♏ HINDATU AUWAL
AMANAR SADI-SAKHNA 🥰