Makauniyar Hanya

CHAPTER 25

by @hindatuauwal

kwanakin da yadauka batareda yaji daga gareta ba shi kadai yasan kalan ukubar da ya fuskanta ayanzu kuma da babu ita besan yanda rayuwa zatayi dashiba.

"Sannu Abdul Maleek ya jikin naka?"

Aunty Maimunat tafaɗa.

Be iya amsawa ba se kansa da yaɗaga mata.

Kuwwa yadinga mai sannu cikin tau sayawa.

Agefen gadon Arshad yazauna tun daren jiya yake son bashi hakuri amma kunya da nadama suka dannesa.

Daƙyar yabuɗe bakin sa yafurta kalaman agaresa"Don Allah ka yafe....."

Kallon da Abdul Maleek yemai ya sanya haruffan ƙarke makalewa acan kasar makogwa ronsa.

"Yawuce"

Abdul Maleek yafada yana sakin mai murmushi.

Shima murmushin ya sakin mai"Nagode ba iya nayau ba....akan komai da yafaru da ace awancan lokacin baka ƙi samun hannu ba da yanzu banyi karatu ba da....."

"Kanason batamin raiko "

Abdul Maleek ya katse shi agajiye.

Hannayensa biyu yahaɗe wuri ɗaya alamar yatuba.

Dariya mutanen dakin sukayi. Abbu dake gefe yashare hawayen farin cikin da suka taran masa fuskarsa ɗauke da murmushin dayake jinsa har ransa.

Hannu yaɗaga sama yana godema Allah da yanuna masa wannan rana, bayan shekaru masu yawa yau ga iyalansa a inuwa daya cikin farin ciki da ƙaunar juna.

Yasan ba kowwa ne ze fahimci dadin yanayin ba se mutumin da ya fuskanci kalubale irin nasa.

Likita na shigowa ya sallame su saboda hayaniyar da suke tayi.

Arshad kadai aka bari ya kwana dashi.

Kwanakin sa biyu a asibitin aka sallame sa suka koma gida.

Shirye shiryen bikin Arshad akeyi ba wasa shi kuma Abdul Maleek yamaida hankalinsa wajen cuku cukun barin kasar zuwa University Of America karo karatu, aganinsa wannan shine kadai hanya mafi sauki daze iya samarma kansa don yarage abinda yakeji akan Diyana.

*DIYANA*

Zaune take abakin gado ta kurama takaddar da Aunty ta miƙo mata na Admission ɗin da tasamu anan Ahmadu Bello University Zaria.

Damuwar ta ba akan yadda tasamu daman shiga makarantar bane, damuwanta akan kallonda mutane suke matane acan Saidi.

Musamman Ummah Sumayya da Faiza akoda yaushe sotakeyi tai musu text ko takirasu tagaya musu batada ciki, tanaso tagoge wannan shakkun da kokonton data gani acikin idanuwan Faiza tun kafin zuciyarta ta yarda.

Sedai me!tana ɗaukar wayan nata daniyyar kiran Faiza seta tina maganar Yakumbo agareta.

Ita kanta tanaso taga tazama educated tasamu exposure na rayuwa kafin taje garesu.

"Tinanin me kikeyi?"

Aunty ta tambaya ganin bata tareda ita.

"Mutane"

Ta amsata kanta tsaye.

"Mutane!"

Aunty ta mai maita cikin salon son fahimtar abinda hakan yake nufi.

Ganin haka yasa Diyana cigaba"bakya ganin yakamata ko mutum ɗayane acikin gidanmu yasan cewa banada ciki"

Murmushi taga Aunty tayi wanda takasa gane ko na menene tukun tasoma magana.

"Tsoron abinda mutane zasu rinƙa cewa ki keyi ko?"

Kai tagyaɗa mata.

"Idan baki daina tsoron abinda mutane zasu ceba to bazaki rabuda fargaba ba,

abinda yafaru ƙaddara ce ki daukeshi amatsayin wata ƴar jarabawa ce ubangiji yemiki don ya gwada imaninki kuma kin karbe shi hakan yasa ubangiji yemiki sakayya yarabaki da wancar ƙas ƙantacciyar rayuwar da babu komai acikinta se wahala.

Ina so ki saurareni da kyau kiji abinda mutane zasuce baze sauya rashin dangin mahaifin ki da kikayi ba.

Magan ganunsu baze sanyaki ki goge abinda ya sanya aka ganki da cikiba. halayyar mutanene yin magana akan ƴan uwansu mutane, da yawansu basa faɗin alkhairi se sharri.

Kisanya ma ranki kinfi karfin mutanen duniya, kina rayuwane saboda kanki, da wani arayuwarki ko babu shi zaki farinciki"

Murmushi tayi aƙangin kanta tasani abinda take shirin yi yanzu bashi zesa tasamu soyayyan ƴan uwanta data rasaba kona mahaifinta da yace yatsani kansa saboda auren mahai.....

Dasauri ta runtse idanunta tanajin yanda kalaman nashi ke dukan zuciyarta da wani irin yanayi data kasa kwatan tashi da komai, ita kanta batason wannan yanayin da takeji agameda Baffa.

Jin ƙarar rufe kofa yasanyata buɗe idanuwanta gefenta takalla inda Aunty take zaune taga batanan.

Tasani fushi tayi shiyasa ta fice batace mata komai ba, murmushi tasaki harga Allah tana jin daɗin yanda ƴan uwanta suke kulawa da ita akullum se sunyi wayada kowwa a gidan Yakumbo wani zubimma video call ne.

Tasan duk sunayi ne don kawai kar tashiga damuwa, a irin wannan lokacin bawanda take tinawa se Abdul Maleek.

Ƙarya takeyi idan tace soyayyar shi da kewarshi sun barta tashaki iska batareda suba, dannewa kawai takeyi ayanzu tasan shima yasan abinda yake faruwa hakan yasan yata gina bangwaye masu karfi da zasu kareta daga buƙatun shi.

❇️BAYAN WASU KWANAKI❇️

Akace rana bata karya sedai uwar diya taji kunya.

Kamar yadda aka tsaida bikin Arshad da Faiza, Suhaima da Imran. awannan ranar ta jumma'a bayan sallahn azuhur aka daura aure.

Kasan cewar Faiza tanada nisa shiyasa ana gama daura aure aka ɗauki amarya Faiza tana ta kuka aka tafi da ita.

Taro yarage saura na Suhaima ita kadai wacce se bayan sallahn isha'i za'a kaita.

Sedai tun azuhur bayan angama daura aure take kiranshi awaya kan maganar dinner da za'ayi amma baya ɗauka.

Inta soma ringing har se takatse ba adauka ba, tun hankalin ta bai tashiba har yatashi iyanzu da aka kai la'asar.

Hankali atashe tashigo cikin gidansu dayake cike taph da jama'a anata hayaniyar biki.

Atsakar gidan ta hango Goggo da Baffa suna tsaye cikin wani irin yanayi mai wuyar fadi.

Isanta wurin ye dai dai da saukar wasu kalamai masu zafi acikin kunnuwanta.

"Allah yema Imran rasuwa tun barinsu kofar gidannan bayan daurin aure ciwon ciki yamurdesa sadda sukaje reception....."

Ihunda Suhaima ta kurma ne yasan yasu juyowa afirgice, jakarta da wayarta dake hannun ta tai jifa dasu cikin fitan hayyaci tazo gaban Goggo cikin hargowwa

"Menaji yana fadi! Karya ne ko! Kice min karya ne"

"Se hakuri Suhaima Allah yema Imran rasuwa"

Baffa ya mai maita muryanshi akarye se alokacin hawaye suka samu damar zubo mai.

"Baze yuwuba Imran baze taba mutuwa yabar niba duk wuyar da muka sha yazama na banza kenan"

Tafaɗa tana shako wuyar Goggo. Tsoro da firgici ya hana Baffa da Goggo motsawa.

Cikin daga murya taci gaba"ayanzu kenan Faiza tazar ceni....Diyana ma da mukaima asiri kilama itama tana can zatai aure oh! Natina ita kin mata asirin da har abada bazata taɓa aureba to wama ze aureta tunda ansa aljannu sun mata ajiya aciki kuma ai kin cemin boka yace indai tai aure to dukkan wani asiri da kikai ma mutanen gidannan zekarye....."

Mamaki, firgici da tashin hankali sune sukai dabai bayi ga duk wani mutumin da yake cikin gidan.

Ganin Suhaima ta sake bude baki daniyyar yin magana ya sanya Goggo sake sauke mata wani lafiyayyen marinda yafi na farko.

Tsoro ne yakama su lokacin da sukaji Suhaima tasaki wani dariya mai amo da sautinsa yacika gidan gaba daya, se kuma ga hawaye sun shiga tsere a kumatunta duk da haka wani busash shen murmushi ne kwance a fuskar ta tace

"Kema yau marina ki kayi shikenan ba komai ai nesa tazo kusa ana kaini gidan masoyina babu wanda zekara dukana, zamuje mui rayuwar farinciki bata...."

Sauran kalaman suka suɓuce mata tasaki gunjin kuka tana zubewa aƙasa bisa guiwoyinta.

Kaman sakara haka Goggo take kallonta, base angaya mataba tasan Suhaima tasamu matsala.

Laifin dadi karewa masu karatu duka duka anan na kawo karshen littafin Makauniyar Hanya na farko.

Nasan zuciyoyin ku cike suke da tarin tambayoyi game da abubuwan da zasu faru anan gaba kamar dai:

Shin Suhaima zata iya jure rashin Imran ko shikenan ta zautu?

Wani irin rayuwa Diyana zatayi anan gaba?

Burin ta dana ƴan uwanta zai cika?

Shin zasu kara haduwa da Abdul Maleek ko shikenan sun rabu?

Wani kalan rayuwa Faiza zatayi agidan Arshad?

Buri kan Goggo sun cika kenan ko akwai wasu anan gaba?

Abdul Maleek da ya tafi kasar waje zai iya zama yajure ma rashin Diyana?

Anya haduwan kan Family ɗinsu zai tabbata ko zai ruguje?

Da sauransu da sauransu.........

Ni Hindatu Auwal ina me baku tabbacin zaku sami amsoshin duka tambayo yinku a book two wanda zai zo muku a farashi mai sauki kan 700 Naira kacal.

Domin ni mana kai tsaye:***

Kusani rayuwar wadannan mutanen bata fara anan ba bakuma zata ƙare anan ba.

Se mun hadu a book two taku AMANAR SADI-SAKHNA 🥰