MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 8

by @mrsisham12

MATUƘAR INA RAYE

(As Long as i’m alive)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)

Page 08

Yau da asuban fari ta riga kowa tashi a gidan. Bata tsaya ko’ina ba sai a ɗakin Ummah.

Jin kamar mutum na tsaye a kanta ne ya sa ta buɗe ido. Kasancewar ɗakin babu wadataccen haske, bata ga fuskarta ba sai hasken idanunta. Da sauri Ummah ta miƙe a ɗan tsorace tana faɗin,

“Subhanallahi!”

Waheeda ta kyalkyale da dariya ganin yadda Ummah ta tsorata.

“Ummanmu, wai tsorata ki na yi?”

Ummah ta dafe goshinta tana gode wa Ubangiji da ya ba ta Waheeda.

“Allah ya shirye ki. Me ya kawo ki a wannan lokacin? Karfe biyar saura fa.”

Waheeda ta zauna a bakin gadon tana jujjuya ɗan ƙaramin bakinta da ta cure wuri ɗaya, sannan ta ce,

“Dama fa so nake in ji me za a fara yi na abin da za mu tafi da shi talla yau. Kin san mu biyu ne ai, gwara a fara da wuri kar mu makara mu je mu yi kwantai.”

Ummah ta girgiza kai. Yoo, in ba yarinta ba, don an ba ki hutu a makaranta sai ki yi ta murna.

Ummah ta ce,

“Yanzu wannan dama ita ta so ki haka?”

Kai ta gyada tana sakin murmushi.

“To, yayi kyau. Tashi ki je ki ɗauro alwala, an kusa kiran assalatu.”

Ta fita daga ɗakin tana cewa,

“Yawwa, Ummanmu.”

Dariya abin ya ba Ummah, musamman yadda ta tsorata da kuma shirmen maganganun Waheeda.

“Allah ka shirya min yaran nan.”

Da ta fita kuwa, ba alwala ta fara yi ba. Sai da ta fara fitar da kayan aikin su, sannan ta yi alwala. Tana kokarin shiga ɗakin Ummah, sai ga Ummah ta fito hannunta riƙe da butar ƙarfe.

Bayan Ummah ta idar da alwala, dai-dai aka fara kiran sallah a masallaci. Bata koma ɗakinta ba sai da ta bugawa kowa a gidan ya farka, sannan ta shiga ciki.

Kafin karfe bakwai da rabi sun gama komai an zuba a robobi. Su Ikilima kuma sun gama karyawa, za su tafi makaranta.

Rabi ta kalli Waheeda da ke manne kusa da Salma ta ce,

“Waheeda, mun tafi. Sai mun dawo.”

Ko kallonsu bata yi ba. Tana cikin murnar fita talla ta ce,

“Sai kun dawo.”

Fita suka yi.

A yayin da suke tafiya, Mama Jamila ta yi wani makirin murmushi.

“Bakin ciki ai ba zai barta ta ɗago ta kalle su ba. To ba yadda za ki yi, kina ji kina gani haka za su yi candy su bar ki. Ke da boko kam kun yi hannun riga.”

Mama Sadiya ta ƙara da cewa,

“Yoo, wa zai kuma yarda ta je masa makaranta tunda ita ba ta da abin yi sai jan magana?”

Salma ce ta buɗe baki za ta mayar musu da martani, amma Ummah ta yi mata alama da ido da ta yi shiru. Hakan ya sa ta tsuke bakinta, amma ba don hakan ta so ba.

Waheeda kuwa ta taɓe baki.

“Ku boko ta dama. In wahalarta ce, suma sai sun gudo da ƙafafunsu. Kuma Allah ya sutura in musu bakin ciki. Na fi ƙarfin in wa mutum bakin ciki, sai dai ni a yi min.”

Ta ƙarasa maganar tana murguda musu ɗan bakinta.

Sam Ummah ba ta yi tsammanin Waheeda za ta tanka musu ba. Da ta dakatar da ita tun farko.wai ganin da ta yi hankalinta baya kansu, ta raba hankalinta gida biyu ne.

Murmushi kawai ta yi a ranta tana mamakin Waheeda. Wani lokaci sai ta yi mamakin a ina take jin irin waɗannan maganganun da take furtawa, sai ka ce wacce aka zaunar aka koyar.

Ita kanta Salma sai da ta murmusa jin amsar da ta ba su.

“Tashi ki je ki yi wanka kar mu makara, ƴar autar Ummah.”

Ta yi wanka, ta saka riga da skirt na atamfa da Ummah ta ɗinka mata a Babbar Sallah. Kayan ya yi mata kyau, duk da ba wani tsada sosai ba. Ta saka hijabinta roba-roba da ta nace ma, ta zabga uban jambaki, sannan ta ƙara da kewaye bakinta da kwalli.

Ta juya tana murmushi.

“Ummanmu, na yi kyau?”

Ummah ta kalleta tana murmushi.

“Sosai ma kuwa, auta.”

Washe baki ta yi, ta ɗauki robar kosanta ta ɗora a kanta, sannan ita da Salma suka fita. Tuni Zuwaira da yarinyar da take yi wa Mama Jamila talla suka riga su fita.


Yau sati ɗaya kenan da Waheeda ta fara fita talla tare da Salma.

Kamar yadda suka saba, suna zaune a ƙofar gida suna suyar awara da doya suna hira, sai suka ga jerin baƙaƙen motoci suna kutsowa layinsu.

Duk mutanen anguwar suka tsaya suna kallo. Har waɗanda suke cikin gida sai da suka leƙo saboda yawan motocin.

Kai tsaye motocin suka nufi katafaren gidan da aka ƙera. Mai gadi ya wangale musu gate, suka kutsa ciki, sannan aka sake rufe gate ɗin.

Salma ce ta yi saurin taɓa Zuwaira.

“Laa! Kin ga har masu gidan nan sun ƙaura.”

Zuwaira ta girgiza kai.

“Ke, wannan ne ya dame ki? Salma, ba ki ga harabar gidan ba lokacin da aka wangale gate? Innalillahi! Kuɗi na inda suke.”

Haka suka ci gaba da hirar gidan. Waheeda kuwa tana jin su ne kawai, tana suya tana cin awarar da ta zabgawa yaji.



Washegari, sai da Salma ta bar Waheeda ta gama shiryawa sannan ta ba ta kuɗi.

Ta ce,

“Ga kuɗi nan, je ki siyo min abin da nake buƙata a shagon Imamu.”

Waheeda ta fara bubbuga ƙafa.

“Ni wallahi ba zan je ba. Tun dazun ba ki san za ki aike ni ba sai yanzu da muka kusa fita? Dole ne sai a yanzu za ki yi amfani da shi? Ki bari idan muna hanyar dawowa sai ki siya mana.”

Salma ta lallabata tare da  bata kyautar murtala. Da ƙyar ta amince ta tafi.

Tana tafiya tana rera waƙoƙinta har ta isa shagon.

Ta tarar Imamu yana sallamar wani mutum. Bayansa kawai ta kalla, sannan ta ayyana a ranta,

“Ko me ya kawo bature anguwarmu oho”

Ganin har yanzu Imamu bai gama da mutumin ba, sai ta ce,

“Ni kam, dallah Imamu, ka ba ni Always. Sauri nake, zan tafi talla. Kar ka bata mana lokaci.”

“To, matso ki karɓa, Hajiya Masifatu.”

Ya faɗa yana juyawa ya ɗauko mata.

Da sauri ta tako ta matso jikin shagon, ba tare da ta san ta taka masa ƙafa ba.

“Shisssh…”

Sautin ya fitar a can ƙasan maƙoshinsa.

Da sauri ta dubi ƙafarta, jin sautin da ya yi. Ta ga ashe ƙafarsa ta taka.

Sai da ta dubi fuskarsa sannan ta ce,

“Dube sa da wani jan fuska kamar kosan da Ummanmu take soyawa na talla. Ya wani ajiye ƙafa irin a ce na taka sa ɗin nan. Ni in bai ɗaga ba ma murje ta zan yi. Dama Safara’u ta ce turawa jikinsu kamar ƙwai yake, ba sa son wahala.”

Duk wannan maganar da take yi, ba ta ɗauke ƙafarta ba. Sai da ta gama kare masa kallo up and down, kamar wata mai neman wani abu a tattare da shi, sannan ta ɗage ƙafarta tana yatsina fuska.

“Na ɗauka zai yi magana ne da na koya masa hankali. Da jan fuska, uwa kosai.”

Out of nowhere, ta ji sautin muryarsa a kunnenta.

“Yaya take da ta ki jan fuskar? Kamar manja? Ko kuma ke ma kamar kosan Ummanku ne?”

Zaro ido ta yi a mamakance tana kallonsa.

Sam bata yi tsammanin wannan baturen zai ji Hausa ba, balle har ya fahimci abin da ta faɗa ya kuma bata amsa. Abin mamakin ma, ya yi maganar ba tare da ya kalleta ba, tamkar ma ba shi ne ya yi ba.

Ta sake tsuke fuska, ta riƙe ƙugu cike da tsiwa.

“Ni de fuskata ba ja ba ce. Ni fara ce… ehen.”

Ya ɗan ɗago idanunsa ya kalleta sau ɗaya, sannan ya girgiza kai.

Yar ƙaramar yarinya ce a gefensa. Da farko ya ɗauka zai ga wacce ta fita shekaru ce ke wannan surutan, ashe duk ba ta wuce sa’ar su Ninin su ba. Yar autar Mamie.

Imamu, wanda yake jin hirarsu, ya miƙa mata pad ɗin sannan ya kalli mutumin.

“Kai ma ta yi maka rashin kunya ko? Sai haƙurin ranka shidaɗe. Haka take wallahi, sam ba ta da ko digon kunya.”

Waheeda ta galla wa Imamu harara, ta fisge pad ɗinta, ta ajiye masa kuɗin sannan ta juya ta tafi.

Imamu ya haɗa masa packet-packet na sweets a leda, sannan ya miƙa masa.

ATM card ɗinsa ya ba shi, ya cire kuɗin.

Waheeda ta labe a jikin wata bishiya tana kallonsa yana tafiya. So take ta ga inda zai shiga, domin ta san ba ɗan anguwar ba ne.
Tana labe kuwa, sai ta ga ya nufi katafaren gidan da aka ƙaura jiya.

“Ohh… kenan daga gida mai kyau ɗin nan yake.”

Ta faɗa tana jinjina kai, sannan ta nufi gida.

Mai gadi da ya hango shi ya yi saurin buɗe masa ƙaramar ƙofa.

“Sannu da dawowa, sir.”

Kai kawai ya gyada yana shigewa ciki.

Ya wuce ta gaban ma’aikatan gidan. Kowa na gudanar da aikinsa. Da suka gan shi, suka hau gaishe shi.

Hannu kawai ya ɗaga musu yana nufar ƙofar katafaren falon gidan.
Da ya shiga, ya hango su gaba ɗayansu a tsaye cikin wani irin yanayi Ya sauke idanunsa a kansu, sannan ya fara takowa zuwa ciki.

Da hanzari wata hamshaƙiyar mata, kyakkyawa sosai, ta nufe shi cike da damuwa. Ta dafa kafaɗunsa.

Da murya a karye ta ce…

“Muhammad BK, ina ne ka je? Gaba ɗaya ka daga mana hankali. Me yasa  za ka fita ba tare da ka sanar da wani a cikinmu ba? Wannan sabuwar unguwa ce. Idan ka rasa hanya fa?”

Ya kura mata ido yana kallonta ido cikin ido. A hankali ya ɗora tafin hannunsa a kan kumatunta.

“Na je siyan alewa ne, Mamie. Ki yi haƙuri.”

Sai yanzu ta sauke ajiyar zuciya cikin relief.

“Don Allah kar ka sake makamancin haka. Idan za ka yi nisa, ka dinga sanar da ni. Kar hawan jinina ya dinga tashi. Ba zan so ka yi nesa da ni ba, ko na second ɗaya.”

BK, wanda har yanzu idanunsa ke cikin nata, ya ce,

“Na sani, Mamie. Ba zan sake ba.”

Ta riƙe hannunsa, sannan ta karɓi ledar daga hannunsa. Ta dubi ƴar autarta.

“Nini, zo ki kai masa bedroom ɗinsa.”

Da gudu ta zo ta karɓa, sannan ta haura upstairs.

Zannor, wanda yake tsaye ya harde hannayensa a ƙirji, ya dubi mahaifinsu, sannan ya dubi sauran ƙannensu da kuma matashiyar budurwar da mahaifinsu ya aura last year. Duk sun zubawa Mamie da BK ido.

Ya ɗan yi taku biyu zuwa gare su.

“Daddy, ya kamata a ce an zo matakin da Mamie ta daina irin waɗannan abubuwan. BK fa ba yaro ba ne. He’s an adult now. Ya san ciwon kansa. You people should stop treating him like a child. Wannan ba soyayya ba ce, tauye haƙƙinsa ne.”

A ɗan kausashe BK ya furta,

“Zannor… zip it.”

Zannor ya girgiza kai yana jin zafin abin da ake yi wa ɗan uwansa saboda kawai ya kasance wani irin mutum na daban.

Duk da BK bai taɓa fitowa ya sanar da shi komai ba, ya san cewa saboda irin waɗannan abubuwan ne ya sa baya son dawowa.

Ya ci gaba da cewa,

“For God’s sake, sai yaushe za ka yi abu dan ra’ayin kanka? Sai yaushe za ka fahimci kai ma kana da naka buruka da muradan? Ba zai yiwu ka ci gaba da rayuwa a ƙarƙashin ikonsu ba.”

“How dare you, Zannor!”

Mamie ta faɗa cikin tsawa tana wurga masa mummunan kallo.

“Yaushe aka haife ka da za ka tsaya kana lecturing namu? Kana nufin ka fi mu sonsa ne?”

Shi ma cikin ɗaga murya ya ce,

“Ƙwarai kuwa, Mamie! Na fi ku sonsa. Domin tare muka zauna a mahaifa, sannan muka fito duniya rana ɗaya, lokaci ɗaya. He’s my twin brother. Soyayyarsa tana cikin jinina. Duk duniya babu wanda zai nuna min sonsa fiye da ni.”

Mamie ta saki murmushi a gadarance.

“Mu kuma mu ne muka tsuguna muka haife ku. Whatever we’re doing, we’re doing it to protect him. Muhammad ba kamar sauran mutane ba ne. Yana da rauni a zuciyarsa, dole mu ninka kulawar da muke masa sau ɗari. Don haka daga yau, ka sake gaya min irin waɗannan maganganun, za ka sha mamakina, Zannor.”

A fusace Zannor ya juya ya haura upstairs kamar zai tashi sama.

Duk suka bi bayansa da kallo.

Mamie ta shafa hannunsa cikin kulawa.

“Don’t mind your twin brother. He loves creating scenes.”

Hannunsa na cikin nata, suka nufi dining table.

Ita da kanta ta yi masa serving na abinci. Fuska ɗauke da murmushi ta ce,

“Maza ka ci abinci, kar lokacin breakfast ɗinka ya wuce.”

Amaryar Daddy, wadda suke kira da Anty Sima, cikin salo na shagwaɓa ta dubi Daddy da ke zaune kusa da ita.

“Baby, ina fatan ba ka manta da maganar da muka yi daren jiya ba. Ni yanzu na gama shiri.”

Daddy ya yi murmushi.

“Ahh, ban manta ba, Gimbiya Sima. Mu gama breakfast sai mu tafi.”

Ya faɗa yana murmushi.

Mamie ta kalle su sau ɗaya, sannan ta ci gaba da cin abincinta.

Zanaya da Nini kuwa suka tabe baki tare da aika wa Anty Sima harara, yayin da BK ko ɗago kai bai yi ba, tamkar ma ba ya dining ɗin. Cin abincinsa kawai yake yi cikin nutsuwa.

Anty Sima ta kafe shi da ido tana sakin wani makirin murmushi. Ganin gaba ɗaya ya ƙi ɗagowa ya kalleta ne ya sa ta ce,

“Muhammad, ko za mu je tare? Na ga tun dawowarku daga U.S. ba ka fita ba.”

BK ya dubi Mamie, ya ga ta kura masa ido. Daga bisani ta girgiza masa kai.

Hakan ya sa ya ce,

“Mamie ta ce akwai inda za mu je.”

A siyasance Anty Sima ta galla wa Mamie harara.

“Na sani ai dama. Ba za ta taɓa barinka ba. Wai me ya sa umarninta kawai da na Baby kake bi? Ni ba a matsayin Mama nake a wajenka ba?”

Ta yi maganar tana danne fusatarta.

Hankali kwance, Mamie da ke shan tea ta furta,

“A cikin shekara ashirin da shida, idan aka cire ashirin da huɗu, saura biyu. Hakan na nufin shekara biyu kika ba wa Zannor da Muhammad. Kin ga kuwa ba ki isa ki haife su ba, Sima. Lokacin da na yi naƙudar yayana, ko wayo ba ki da shi a duniya.”

Sima ta juya ta dubi Daddy.

“Baby, ni na kammala. Ka same ni a sama.”

Ta faɗa tana ci gaba da wurga wa Mamie mugun kallo, sannan ta dungure spoon ɗin hannunta ta miƙe tsaye.

Cikin kulawa Daddy ya ce,

“Amma ai ko ba komai, ki tsaya ki kammala cin abincinki mana, Sima.”

Tana ƙoƙarin barin gurin ta ce,

“Matarka ta sa na yi lossing appetite.”

Tana gama faɗin haka ta bar dining ɗin ta haura sama.

Babu wanda ya sake cewa komai har suka gama cin abinci, kafin Mamie ta umarci Zanaya da ta kai wa Zannor nasa abincin.

“Yarona BK.”

“Naam, Daddy.”

Ya amsa yana maida hankalinsa kansa.

Daddy ya ɗora da cewa,

“Uncle ɗinku, mai Martaba, ya buƙaci ganin ka. Ya ce tun da kuka dawo ko kiransa ba ka yi ba. Gara ma Zannor ya ziyarce shi. An jima ka shirya ku tafi, kai da  su Nini.”

“In sha Allah.”

Ya faɗa yana miƙewa ya bar falon.

Da kallo suka bi shi har sai da ya ɓace musu.

Sai Daddy ya juya ya dubi Mamie.

“Amma menene manufar abin da ka yi, Almustapha?”

Mamie ta tambaya cikin mamaki.

“Ba na buƙatar in yi miki wani bayani.”

Yana gama faɗin haka ya goge bakinsa da tissue, sannan ya miƙe ya bar ta ita kaɗai a dining ɗin.