MATUKAR INA RAYE

Matukar Ina Raye 9

by @mrsisham12


MATUKAR INA RAYE

(As Long as i’m alive)

Writer — MRS ISHAM
*** (WhatsApp)

Page 09

Dawowa gurin tallarsu ta yi riƙe da kofuna ita kaɗai. Sai harare-harare take tana ta ƙunƙuni. Ta watsa kofunan cikin robar kunun nasu sannan ta tsuguna tana wanke su. Har yanzu bakinta bai yi shiru ba.

Wani mutum ya ce,

“Ke, ina yar uwarki?”

Yadda ya kira ta da “ke” ne ya sa ta ɗago tana masa kallon tara saura. Ta yi banza da shi, ta ci gaba da wanke kofunan.

Da ya ga ta yi masa banza, kuma Salma ba ta wajen, sai ya sake cewa,

“Ke kurma ce? Ina miki magana kina yi min banza? Ai ba a yi wa kwastoma wulakanci.”

Cikin daga murya ta ce,

“Dallah malam! Sunana ba ‘ke’ ba ne. Idan ba za ka kira ni da Waheeda, sunan da ubana ya raɗa min ba, ka yi tafiyarka.”

Da ɗan mamaki ya kalle ta, sannan ya yi murmushi, domin ya fahimci irin yaran nan ne masu tsiwa.

“Yi haƙuri Malama Waheeda. Ki ba ni kunun naira ɗari da alalen naira ɗari da hamsin.”

Ta zuba masa kunun a kofi, sannan ta sa masa alalen a roba. Yana karɓa ya ce,

“Yawwa, ga naira ɗari biyu. Idan kun zo karɓar robar zan cika muku hamsin ɗin.”

A hankali, yadda ita kaɗai za ta ji, ta ce,

“Kab uba!”

Nan take ta buɗe robar kunun ta mayar da wanda ta zuba masa ciki, tana girgiza kai. Ta rantse cewa muddin ita ce ke siyarwa ba Salma ba, ba za ta ba da bashi ba. Ta lura mutanen kasuwar nan ba su da ta ido,a wasa-a-wasa suke rike musu kuɗi, amma Salma babu ruwanta.

Mutumin ya ce cikin mamaki,

“Ke, me ya sa kika juye kuma?”

Ta miƙe tsaye, ta kalle shi tana yatsina fuska cike da tsiwa.

“Saboda ba ka shirya yin karin kumallo ba. Dan billahil-lazi, ko naira ɗaya ta rage a cikin kuɗin nan, ba zan karɓa ba.”

Ya ce,

“Ai ban ce ba zan ba ku hamsin ɗin ba. Canji ne kawai ba ni da shi. Idan kina haka za ki kashe muku kasuwa. Salma fa har bashi take ba ni.”

Ta nuna kanta da yatsa

“Kalli nan! Na yi maka kama da Salma? Ko ka ji sunanmu ya zo ɗaya? Ni daban, Salamatu daban! Dan haka ba zan siyar ba sai ka cika min kuɗina. Na lura ku ’yan kasuwar nan cin bashi ya muku katutu da shegen cuta.”

Mutumin da yanzu ya soma gajiya da iskanci da tsiwar yarinyar, ya haɗe fuska ya ce,

“Ke, ya ishe ki fa? Na fi ki bariki da duniyanci. Ki sake yi min irin wannan magana in ban ci uwar bakinki ba, shege nake.”

Waheeda ta watsa masa wata uwar harara, tana shirin mayar masa da martani kenan sai Salma ta iso tana cewa,

“Waheeda, lafiya kuwa?”

Ta faɗa tana riƙo hannunta.

Waheeda ta fisge hannunta da sauri tana cewa,

“Oho, ban sani ba. Kuma wallahi sai na faɗawa Ummah kina rabar mata kaya bashi, shi ya sa kuɗinta suke makalewa.”

Mauje mata baki Salma ta yi, sannan ta ɗan harare ta tana cewa,

“Ki fi ruwa gudu.”

Ta juya ta dubi mutumin da suka gama sa-in-sa da Waheeda, sannan ta tambaye shi,

“Musa, me za a ba ka?”

Ya gyara tsayuwarsa sannan ya faɗa mata abin da yake so ta ba shi.

Bayan tafiyarsa ne Salma ta saka Waheeda a gaba tana zazzaga mata masifa.

Ita ma Waheeda ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta dinga mayar mata da martani ba tare da tsoro ba, har Salma ta gaji ta yi shiru ta ƙyaleta.

Suna cikin motar, driver ɗinsu ne ke tuƙa su a hankali cikin nutsuwa. Glass ɗin motar a sauke yake, iska na shigowa tana gaurayawa da ƙamshin turaren cikin motar.

A gefe guda kuwa, Nini da Zanaya ne suka cika motar da surutu, suna ta hira da dariya kamar ƙananan yara.

BK kuwa ya lumshe idanunsa a kasalance, ya ɗan jingina kansa jikin window ɗin motar. Sai bayan wasu daƙiƙu ya buɗe idanunsa a hankali, yana kallon unguwar da motar ke ratsawa.

Yau ce rana ta farko da ya fita unguwar a mota tun bayan dawowarsu daga Amurka. Ba kamar Zannor ba, wanda kusan kullum idan ya fita da yamma sai dare yake dawowa.

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana ci gaba da kare wa sabuwar unguwar tasu kallo.

Nan take idanunsa suka sauka kan wasu ’yan mata uku da ke ƙoƙarin tsallaka titi, kowacce na ɗauke da empty kayan tallanta da alamar sun gama siyarwa.

Ya lura biyu daga cikinsu sun riga sun tsallaka, amma ɗayar ta tsaya a bakin hanya tana ta musu magana tare da yatsina fuska. Su kuma suna yi mata alamar ta zo ta tsallako, amma ta ƙi motsawa.

Na wasu daƙiƙu BK ya zuba mata ido, kafin ya fahimci rashin kunya take musu, tana ta surutu ba tare da ta damu da maganarsu ba.

Da suka gaji da jiranta, sai suka juya suka ci gaba da tafiyarsu, suka barta ita kaɗai a bakin hanya.

A dai-dai lokacin ne motarsu ta ratsa junction ɗin.

A hankali ya maida idanunsa ya sake lumshe su, sannan cikin ƙaramar murya ya furta,

“Very rude girl.”

Zanaya, wacce ke zaune a gefensa, ta juya ta dube shi cikin mamaki, domin ba ta fahimci wanda yake nufi ba.

A babban gate ɗin Masarauta, jami’an tsaro ne sanye da cikakken kayan aiki suke tsaye cikin tsantsar shiri. Kowannensu na riƙe da bindiga, idanunsa na sintiri ba tare da wasa ba.

Duk motocin da ke shiga suna tsayawa domin bincike, ana tantance lambobin mota da waɗanda ke cikinsu kafin a ba su izinin shiga.

Da motarsu ta iso, jami’an tsaron suka yi saurin gane ta, kasancewar motocin iyalan Mai Martaba ne. Nan take suka ɗaga katangar shiga cikin girmamawa, tare da yi musu sallama.

Motar ta ci gaba da kutsawa cikin harabar Masarauta, tana ratsawa ta wani dogon titi mai shimfiɗar kwalta mai sheƙi. Gefensa kuwa cike yake da bishiyoyi masu inuwa da furanni kala-kala da aka tsara cikin tsari na musamman.

A wani ɓangaren kuma, ruwan fountain na tashi sama yana saukowa cikin sauti mai sanyaya zuciya, yayin da manyan fitilun ado suka yi jerin gwano a bakin hanyar.

Bayan ɗan lokaci suka isa babban ginin da ake karɓar baƙi.

Fadawa tare da masu tsaro suka ƙaraso cikin ladabi suka buɗe musu ƙofar motar. Saboda su iyalan Mai Martaba ne, babu wata wahala ta tantancewa.

Cikin girmamawa aka yi musu jagora ta wani katafaren corridor mai yalwa, wanda bangonsa ke cike da hotunan manyan shugabanni da manyan sarakuna, yayin da kafet ja mai laushi ya rufe ƙasa tun daga ƙofar shiga har zuwa babban falon baƙi.

Daga nan aka kai su zuwa ƙofar babban ofishin Mai Martaba.

Wani Bafade ya yi sallama cikin ladabi kafin ya buɗe ƙofar a hankali yana cewa,

“Allah ya ja zamanin Sarki,ya Kara maka lafiya da tsawon , kana da baki,ƴaƴan Yarima Almustapha ne suka kawo maka ziyara.”

Daga ciki aka ba da umarnin a shigo da su.

Cikin nutsuwa suka shiga ofishin, inda suka tarar da Mai Martaba Sarki zaune cikin isa a kan kujerarsa ta alfarma. Fuskarsa cike take da yalwatacciyar murmushi da tsantsar farin cikin ganinsu.

Nan take ya miƙe tsaye, ya buɗe hannayensa zuwa ga BK yana cewa,

“It’s been a long time, my boy. Na yi matuƙar farin cikin sake ganinka, ɗana.”

Rungume shi sosai BK ya yi, yana sauke numfashi a hankali tare da jin wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali suna ratsawa zuciyarsa.

Mai Martaba  ya ɗago shi kaɗan, ya zuba masa ido yana kallon fuskarsa cike da kulawa.

Cikin murya mai nuna damuwa ya ce,

“Fatan kana lafiya ko? Ya jikinka yanzu?”

Ɗan slide smile ya yi kafin ya amsa,

“Alhamdulillah Uncle, ina lafiya. Sai dai abin da ba za a rasa ba.”

Kai ya jinjina cikin gamsuwa.

“Masha Allah. Allah Ya ƙara maka lafiya, Muhammad.”

“Ameen.”

Sai ya juya kallonsa zuwa ga Nini da Zanaya.

“Yan matan Uncle, ku zo nan.”

Da murmushi suka ƙarasa gare shi, suka rungume shi sannan suka zauna suna gaishe shi cikin ladabi.

Mai Martaba  kuwa gaba ɗaya hankalinsa yana kan BK. Bayan ya amsa gaisuwarsu ne ya ce,

“Na yi tunanin tare da Zannor za ku zo.”

Nini ta yi saurin cewa,

“Mamie da Ya Zannor sun yi faɗa. Yana ɗaki ya yi fushi, ya ƙi kula kowa.”

Dariya kawai Mai Martaba Sarki ya yi kafin ya ɗaga wa BK gira alamar tambaya.

Kai BK ya gyada masa kawai.

Wani bell da ke saman teburinsa ya taɓa.

Ba a jima ba Bafaden ɗin da ya shigar da su ya sake bayyana.

“Sarkinmu sarkin ado wane Ɗawisu,”

“Ka kai su bangaren cikin gida.”

“Certainly, Sir.”

Da ladabi ya yi musu jagora, Nini da Zanaya suka bi bayansa suka fita daga office ɗin.

Bayan sun tafi ne Mai Martaba  ya gyara zamansa, ya zuba wa BK ido sosai kafin ya furta,

“Wannan karon ma akan ka twin ɗinka suka yi faɗa?”

A kasalance BK ya gyada kai.

Yanayinsa kaɗai ya isa ya nuna gajiya da komai.

Daga nan ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da shi.

Mai Martaba  ya sauke numfashi tare da yin murmushin takaici.

A zuciyarsa kuwa yana jin wani irin kunci.

“Ka yi hakuri soyayyar da suke maka ne ya jawo hakan. Daga lokacin da ka gama samun lafiya komai zai daidaita, In Sha Allah.”

Murmushi kawai BK ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin Mai Martaba Sarki ya sake cewa,

“Ya batun karatunka da kuma signing ɗin da za ka yi da ƙungiyar kwallon kafa ta PSG? Zannor ya sanar da ni komai.”

Da wannan cold expression ɗin nasa da ba kasafai yake sauya wa ba ya ce,

“Ba na jin zan yi signing ɗin. Na sauya ra’ayi.”

“Ka sauya ra’ayi ne… ko kuma ba ka da wani zaɓi?”

Muryar da ta katse maganarsu ta sa duk suka juya.

Wani ne ya shigo cikin office ɗin sanye da suit mai tsananin tsada da ɗaukar ido.

Murmushi ne kwance a fuskarsa.

Abu na farko da zai ja hankalin duk wanda ya gan shi shi ne irin mugun kamannin da yake yi da BK.

Da sauri BK ya miƙe tsaye.

Kafin kowa ya ce komai ya nufi sa, ya rungume shi da ƙarfi cikin tsantsar ƙauna.

“Na yi kewarka, Ya Abdul-Jalal.”

Dariya Mai Martaba Sarki da Abdul-Jalal suka yi lokaci guda.

Abdul-Jalal ya dafa bayansa yana cewa,

“Ni ma na yi kewarka, ƙaramin kanina.”

Ya ɗan ja baya yana kallonsa.

“Wato sai yau za ka kwaso jikinka ka zo? Bayan na ji labarin yanzu kusan kwana goma kenan da shigowarku Najeriya?”

Miskilan murmushi BK ya yi.

“Tuba nake, ranka shi daɗe, Minister.”

“Kai!”

Abdul-Jalal ya kama kunnensa ya ja kaɗan.

Suna dariya suka ƙarasa wajen zaman da ke gaban teburin Mai Martaba , har yanzu yana riƙe da kunnensa.

Da wasa ya ce,

“Abba, wannan yaron naka kullum ƙara sangarcewa yake yi.”

Mai Martaba  ya kwashe da dariya.

Nan take office ɗin ya cika da dariya da annashuwa, yanayin da ya sa BK ya ji kamar ya dawo cikin wani ɓangaren rayuwarsa da ya daɗe bai samu irin wannan kwanciyar hankalin ba.

Sosai suka sha hira. Lokacin da suka yi tare baƙaramin faranta ran Bk yayi ba. Ya ji zuciyarsa ta yi fes, domin ya daɗe bai samu irin wannan farin cikin ba.

Daga office ɗin bangaren cikin gida suka fito, shi da Ya Jalal, suka bar Mai Martaba  yana ci gaba da karɓar baƙi.

A babban falon gidan kuwa suka tarar da sauran ‘ya’yan Mai Martaba  maza suna zaune suna hira. Dukkansu sun girmi Bk. Su uku ne ƴaƴan Mai Martaba Sarki. Ya Abdul-Jalal, sai Ya AbdulSamad, sannan Ya Mutallab.

Da ganin Bk, suka tarbe shi cikin fara’a, suna ta zolaya da barkwanci kamar yadda suka saba. Hakan ya sa falon ya cika da dariya da annashuwa.

Sai da dare ya yi sannan driver ya mayar da su gida.

Zaune take a kan tabarma a bakin ƙofar ɗakin Ummah, kanta kwance a cinyarta yayin da Ummah ke taje mata dogon gashinta tana shirin yi mata kitso.

Tun da ta kama kitson kusan sa’a guda kenan tana faman yi mata nasiha kan rashin son gyara gashi. A zahiri ma sai da ta mata jan ido da faɗa kafin ta amince ta zauna.

Ummah tana kitso tana cewa,

“Kina mace amma a ce sam ba kya son gyara gashinki. Kai Waheeda, Allah Ya kyauta miki kawai wallahi.”

Waheeda ta tura baki gaba tana ƙunƙuni.

“Ummah ni bana son kitson gabaɗaya.”

Wani kallo Ummah ta watsa mata kafin ta ce,

“Za ki yi min shiru ne ko sai na dagargaji bakinki?”

Nan take Waheeda ta yi tsit.

Ba ta sake cewa komai ba.

Ikilima da ke zaune kusa da su ta ce,

“Ummah, ranan ma har dukanta wata malama tayi a school saboda rashin kitso.”

Ummah ta ɗan rankwashi kan Waheeda.

Tun da aka fara kitson ta kasa zama guri daya sai motsi take kamar wacce aka ɗora kan ƙaya.

“Bar ni da ita. Zan yi maganin wannan kazantar.”

Ikilima ta yi mata gwalo.

A fusace Waheeda ta ce,

“Wallahi zan yi maganinki. Kar ki ga kaina yana hannun Ummah.”

“Dallah, rufe min baki.”

Ummah ta katse ta.

A daidai lokacin ne Baffa ya shigo gidan.

Gyaran murya da ya yi ya sa duk suka waigo.

Ummah ta amsa masa sannu da zuwa, sannan ta miƙe ta je ta ɗauko wata tabarma ta shimfiɗa masa.

Bayan ya zauna ne ya dubi Waheeda yana murmushi.

“Mamana, kitso ake miki ne?”

Fuskarta a murtuke kamar za ta yi kuka ta ce,

“Baffa, kitson fa zafi yake min kamar kaina zai fashe.”

Duban Ummah ya yi.

“Maimunatu, du Allah ki bar ta haka. Kar ya yi mata ciwo.”

Ummah ba ta ce masa komai ba.

Sai kallon Waheeda da ta yi sannan ta girgiza kai.

Daga bisani Baffa ya ce,

“Ke, je ki kira min Jamila da Sadiya.”

Da sauri Rabi ta miƙe ta je ta kira su daga ɗakunansu.

Bayan sun fito ne ya haɗa su gaba ɗaya ya sanar da su cewa zai yi tafiya zuwa kasuwar ƙauye neman kuɗi. Sannan ya roƙe su da su haɗa kai su zauna lafiya.

Mama Sadiya ta tabe baki.

“To Allah Ya taimaka.”

Tana gama faɗin haka ta juya ta shige ɗakinta.

Baffa ya girgiza kai kawai.

Sannan ya juya ga Mama Jamila.

“Gobe in Allah Ya kaimu, ko su Waheeda ne a tura su gidan Mallumjo. Akwai shinkafa da ya ce min a turo a karɓo muku, da tiyya uku na gero. Ni zan wuce, motarmu ta iso tana jira.”

Mama Jamila ta gyada kai.

“To Baffah, in ka gadama ka dawo da sabuwar mata,Allah Ya kai ku lafiya.”

Kai ya girgiza be kula ta ba ko amsa addu’ar be yi ba.

Bayan ya tashi tafiya, har ƙofar gida Ummah ta raka shi tana masa addu’ar hanya.

Da ta dawo ɗaki ne Waheeda ta bi bayanta.

“Ummanmu, wai sai yaushe Baffa zai dawo?”

Ummah ta zauna tana gyara kayan kitsonta kafin ta ce,

“Gaskiya bai faɗa min ba. Amma akwai yiwuwar su yi wata ɗaya ko biyu.”

“Amma ni fa Ummah, idan na je gidan Mallumjo gobe sai jibi zan dawo. Kin ga ai na jima ban je ba.”

Ummah ta ɗaga gira.

“To Waheeda, tallanki fa? Ko har ya gundure ki?”

Nan take fuskarta ta sauya.

Ta tuna walakancin da Salma da Zuwaira suka yi mata lokacin da suka tsallaka titi suka barta ita kaɗai.

“Ni gaskiya Ummah ki raba ni da Yaya Salma a talla. Kin ga ita raba miki kaya bashi take yi, ni kuma bana bayar da bashi. Haka dazun ma ita da Yaya Zuwaira suka tsallaka titi suka bar ni. Da ƙyar na iya tsallakawa. Saura kaɗan ma mota ta kwashe ni ta watsar a lambatu.”

Tun da ta fara magana ba ta yi shiru ba sai da ta gama.

Sosai hankalin Ummah ya tashi. Da sauri ta jawo Waheeda jikinta.

Cikin damuwa ta ce,

“Ina babu dai wani abu da ya same ki?”

Waheeda ta girgiza kai.

“Iyi, babu. Ni dai kawai damuwana ki raba ni da ita. Ba zan sake binta ba,kin ji na rantse.”

Ajiyar zuciya Ummah ta sauke.

“In Sha Allah ba za ki sake binta ba. Zan dinga cire miki naki kosan kina siyarwa a ƙofar gida. Ai za a yi ciniki.”

Wani irin daɗi ne ya mamaye Waheeda.

Ta rungume Ummah da ƙarfi tana cewa,

“Shi ya sa nake son ki, Ummanmu. Allah Ya bar min ke.”

Dariya Ummah ta yi.

Ita ma ta rungume ta tare da manna mata kiss a kai.

A ranta ta amsa da,

Ameen.

Sai kuma ta ce a fili,

“Gobe ki bar su Ikilima da Rabi su je gidan Kakanku. Ke kuma ki je gidan Baba Karami ki yi wa Labiba aiki, kin ga ba ta da lafiya.”

Waheeda na kwance shame-shame a jikinta ta ɗaga kai.

“Me yake damunta to?”

Sai da Ummah ta yi ɗan jim. Daga bisani ta ce,

“Laulayi take yi.”

Idon Waheeda ya waro.

“Ummah… laulayin ciki? Kenan haihuwa za ta yi?”

Da sauri Ummah ta kau da maganar.

“Eh. Tashi maza mu ƙarasa kitson nan naki.”

Ko da suka shigo gida, Ummah ta yi wa Salma faɗa sosai kan barin Waheeda ita kaɗai a bakin hanya.

Washegari kuwa, bayan Waheeda ta yi wankanta, Ummah ta yi mata kwalliya. Daga bisani Ya Ado ya zo ya ɗauke ta zuwa gidan Baba Karami.

Ba su same shi a gida ba, domin ya fita shago.

Labiba kuwa ta yi matuƙar farin ciki da zuwan Waheeda, domin a cikin duk ƙannen mijinta, ta fi shakuwa da Waheeda. Duk wasu ayyukan gidan da ba ta yi ba, sai da Waheeda ta kammala musu tsaf. Ita kam ba ta da gajiyar aiki, sai dai idan ba ta ga damar yi ba.

Bayan ta gama ayyukan, Labiba ta girka musu taliyar murji tare da miyar sauce.

“Heedah, amma kwana za ki yi min ko?” Labiba ta tambayeta cikin marairaicewa.

“Karfe nawa ne yanzu?” Waheeda ta tambaya.

Labiba ta ɗauki wayarta ta duba lokaci.

“Yanzu ƙarfe shida saura.”

“Anty Labiba, tafiya zan yi. Ba zan ma jira Baba Karami ba. Kin ga zan fita tallan awara an jima.”

Labiba ta ce, “Yanzu da gaske ba za ki kwana ba?”

Waheeda ta miƙe ta ɗauki hijabinta ta saka, sannan ta ce,

“Ni wallahi ba zan kwana ba. Kawai ki ba ni kuɗin mashin.”

Ta girgiza kai cikin rashin jin daɗi, sannan ta shiga ɗaki. Ta so Waheeda ta kwana domin su yi hira, tunda Baba Karami ba kullum yake dawowa gida da wuri ba.

Can ta fito ɗauke da kuɗi a hannu. A ɗaya hannun kuma tana riƙe da wata ƙaramar roba mai kyau cike da tuwon madara.

“Shegiya mai taurin kai! Ga kuɗin mashin ɗin. Wannan alawar madarar kuma taki ce, sai ki dibawa su Rabi.”

Waheeda ta karɓa sannan ta yi murmushi.

“Wallahi ko kamshinsa ma ba za su ji ba. Sai an jima, Anty Labiba.”

Ta faɗa tana fita daga gidan. Labiba ta bi bayanta da murmushi kafin ta koma cikin ɗaki.