CHAPTER 11
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA SHA ƊAYA
Ya riƙe fuskarsa yana kallonta, “Ke, wacce irin mara hankali ce kidahuma, hanunki a fuskata?”
Ya ɗaga hannu yana ƙoƙarin maida mata da marin, da sauri abokinsa ya riƙe shi yana, “Aa, Kwaro, ba anan ba za a iya samun e yane.” Ya ƙarasa maganar yana kifta masa ido.
Kaucewa Farida ta yi za ta wuce da sauri, ya sha gabanta yana nuna mata yatsa, “Ke, kin san wane ne ni kuwa? Sai na yi silar da za ki gagara zama a cikin makarantar nan, katuwar banza kawai! Don ma kin samu na ɗan taya ki, kina nan kina fama da jiki kamar dilar gwanjo, kin ci bashin da sai kin biya ta babbar siga.”
Ƙarfin hali Farida ta yi tana tsaye kamar gunki, zuciyarta sai bugawa take, musamman da ta lura da yanayinsu. Irin yaran nan ne marasa ji, ’yan shaye-shaye. Yana tafiya, ta yi sauri ta shige office.
Ganin yanayinta da Hod ya yi ne yake tambayarta me ya faru.
Tana faɗa masa kafin ma ta faɗi sunan, ya ce, “Suhail ko?”
Farida ta amsa da, “E.”
Hod ya girgiza kai kafin ya ce, “Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki, za a yi maganinsa. Dama akwai ƙorafe-korafe masu yawa akansa, kar ki ji tsoro, ba zai iya miki komai ba.”
Farida ta numfasa kafin ta ce, “Yanayinsu ma kaɗai abin tsoro ne, bare furucinsu. Wallahi ni duk na kiɗime, Sir.”
Murmushi Hod ya yi ya ce, “Haba, babbar mace irin ki, matar manya, ki tsaya jin tsoron yaran nan? Ai ko a ranki kina jin tsoro, kada ki taɓa bari su gane, domin ta nan ne za a samu lagonki. Ki kwantar da hankalinki. Yanzu wane class kike da shi?”
“300 level ne,” Farida ta faɗa.
Hod ya ce, “To shikenan, yanzu ki je. In kin gama ki dawo nan tukunna.”
Tashi ta yi ta nufi class ɗin. Tana shiga ta fara yi musu karatu tana rubutu a white board. Duk abin da take, tana lura da Sufyan; ko saurarenta baya yi, ya saka earphone ne ma, yana ta girgiza kai, wanda ke nuna cewa waƙa yake saurare.
Kwafa Farida ta yi a ranta tana cewa, “Ai ko sai na yi maganinka, sai ka san ƙarfin ikon da nake da shi a nan.”
Dakatawa da rubutun da take yi ta yi tana gyaran murya.
“Heeey… Please, ɗan taɓa min abokinka.”
Ta yi wa Habib magana. Taba Sufyan ya yi yana nuna masa Farida na magana.
Zare earphone ɗin ɗaya ya yi yana kallonta.
Ta ce, “Please, ko za ka iya taimakawa ka goge min white board ɗinnan?”
Binta da kallo Sufyan ya yi yana karewa class ɗin kallo. Gabadaya sun zarce mutane casa’in a class ɗin, sannan desk ɗin da yake shi ne na kusa da na ƙarshe. Ta tsallake ’yan gaba da kowa sai shi, da yake can lullukin duniya, ta ce ya fito ya goge board. Maganar da ta ƙara yi ce ta katse masa tunanin da ya fara.
“Mr Man, kai muke jira.”
Ba yadda ya iya, haka ya tashi ya fita. Yana zuwa gabanta ya bita da wani irin kallo, ita kuwa murmushi ta sakar masa ta matsa gefe.
Karasawa ya yi ya fara goge board ɗin, a ransa yana cewa, “Tunda nake a school ɗinnan, yau ne rana ta farko da aka sanya ni goge board. Kuma ma wai Farida! Ga alamu tana so in fara nuna mata cewa ni namiji ne fa.”
Ya yi kwafa, ya ƙarasa gogewa sannan ya juya zai koma wajensa. Har ya kusa seat ɗinsu, Farida ta dakatar da shi.
“Mr Man, excuse me, please.”
Sufyan ya juya yana binta da wani fusataccen kallo.
Farida ta ciro kuɗi daga cikin jakarta, sannan ta ɗan lankwasar da kanta tana cewa, “Ka taimaka min da Faro ko Swan Water, don Allah.”
Ta ƙarasa maganar tana miƙa masa kuɗin.
Wani basamuden takaici ya turnuke Sufyan a ƙirji.
“Kambala’i! Bayan goge board ɗin ma yanzu ta samu dama har da aika,” abin da ya tsaya yana faɗa a ransa ke nan, kafin ta katse tunaninsa da cewa,
“Taimako za ka yi, I’m thirsty, please.”
Tafiya yake kamar ba zai yi ba, har ya ƙarasa gabanta ya karɓi kuɗin.
Yana karɓa ya fice daga class ɗin.
Binsa da kallo tare da murmushin mugunta Farida ta yi daga cikin niƙabinta.
Ta girgiza kai tana faɗin, “Sorry ko, ina ma muke?”
Ci gaba da yi musu lecture ta yi.
Sufyan yana fita ya je ya siyo mata ledar pure water guda, ya riƙo a hannunsa har cikin class ɗin.
Yana shiga, duk suka zura masa ido kamar mujiya.
Daidai gabanta ya je ya dire ruwan. Farida ta kalle shi tana cewa, “Ah, ya naga pure water kuma?”
Sufyan ya yi wata gajeriyar murmushi, yana ciza baki a gefe, ya ce, “Sorry ko, duk wanda kika faɗa ɗin nan babu. Maimakon kuma in dawo haka, sai na ce bari in siyo wannan ɗin. da yake ma na ji kin ce kina jin ƙishirwa, sai na yi tunanin cewa wannan ɗin ma zai fi miki, tunda na ga alamun za ki iya shanyewa duka ai.”
Ya ƙarasa maganar yana juyawa ko jiran amsarta bai yi ba.
Tsayawa Farida ta yi nadakiku tana binsa da kallo kafin daga bisani ta kawar da kanta, ta ci gaba da musu karatu.
Gulma ɗaliban class ɗin suka fara, suna faɗin cewa ko dai Farida na crushing kan Sufyan ne, ta ke takura masa hakan.
Wata mace dake gefe ta ce, “Ai ko zata gaji ta bari, ina zai kaita? Sufy handsome ɗin da mata kyawawa masu kyawun sura suke kai masa kansu ma yake wulakantawa, bare ita ai ko zuciyarta zata buga.”
Ta gefenta ta ce, “Sosai ma. Ni fa tun ranar farko na lura da take-takenta, da alama ta gagara samun ƙofa ne.”
Haka Farida ta gama lectures dinta ta fita a class ɗin.
Bayan ta fita ne Habib ya ji labarin da ’yan class ke yi kan cewa Farida na Crushing kan Sufyan, zuwa ya yi yake ba shi labari.
Sufyan ya ce, “Ka ga daga haka har za a samu mai gano haɗina da ita ai, ni da da hali fa wallahi daina shiga lectures dinta zan yi, amma matsalar makarantar. Nan yanzu akan ƙin zama sai a jefi mutum da kaya.”
Habib ya ce, “Aiko daurewa za ka yi, kawai dai ka taka mata birki ne ta bar shiga harkarka.”
“No, kar ka damu, ai iyaka zan mata kar ta kuskura ta kara shiga gonata.” Cewar Sufyan.
Sufyan da Habib sun fito, an gama classes ɗin ranar, za su shiga mota kenan suka hango Farida tare da HOD suna tafiya tare suna hira. Fuskarsa a sake, ga dukkan alamu yana jin daɗin tattaunawar da suke.
Habib ya ce, “Kai Sufy, ba ka gani nw? Sai washe baki yake fa.”
Sufyan ya ce, “Yoo, e mana, su yi harkarsu. Ni ina ruwana? Ɗan hannunta ne ai. Kila ma sun dawo daga hutawarsu ne. Ka zo mu tafi ni. in kuma ba yanzu za ka tafi ba, ni in yi gaba. Ina so in je in ɗan zuƙa sa shiru, hayaki no.”
Ya ƙarasa maganar yana shigewa motarsa. Bin sa ciki Habib ya yi yana cewa, “Mu je dai, ai ka san nima ina da buƙata ne.”
Sai da HOD ya raka Farida har bakin motarta ta shiga, sannan suka yi sallama, shi ma ya shiga tasa.
Farida na isa gida ta shiga ɗaki kenan, sai ga kiran Mama.
Bayan sun gaisa, cikin faɗa Mama ta fara yi mata magana.
“Yanzu Farida, don Allah rashin kunyar taki har ya kai ga haka? Yaushe kika kai wannan lalacewar ban sani ba?”
Cikin yanayin rashin fahimta Farida ta ce, “Mama, ni kuma? Me na yi?”
Mama ta ce, “Wai ko kunya babu? Ki buɗe baki ki faɗawa Inno cewa kina ɗauke da ciki jikinki, Farida! Haka rashin wayewar taki ta zo?”
Farida ta ce, “Mama, wallahi ban faɗa ba. Kawai ta zo ta same ni bana jin daɗi, shi ne ta ce wai ciki ne. Amma ke ma kin san ba zan taɓa aikata hakan ba.”
Mama ta numfasa ta ce, “To ai shikenan. Gashi nan anata baza ki lungu da saƙo har ƙauye. Ga kuma kayan haihuwa nan, ta je ta siyo tili guda. Yanzu ma an kawo min kayan jariran wai in wanke.”
Farida ta buɗe baki cikin mamaki.
“Kayan jarirai? Lallai ma Inno! Kuma fa wallahi Mama, ba ni da komai.”
Mama ta ƙara numfasawa ta ce, “To Allah ya kyauta dai. Babanku sai faɗa yake, yana faɗin cewa ku ba ku da sirri ne a rayuwa.”
Daga nan suka yi sallama da Mama, tukunna ta tashi ta cire kayan da ke jikinta.
Sai misalin ƙarfe 12 na dare Sufyan ya koma gidan. A lokacin Farida ta jima da yin nisa a barci. A buge ya dawo, don haka ya baje a falon. Har sai da abin ya ɗan fara sakarsa, can kuma kamar an tsikare shi, ya je ƙofar ɗakin Farida yana bugawa kamar an aike shi.
A firgice ta farka jin yadda ake buga ƙofar. Tashi ta yi ta buɗe. Ganinsa ta yi tsaye, hannu ya fara nuna mata yana faɗin,
“Ki fita a harkata! Na miki iyaka da ni. Kar ki ƙara kulani, bare ki sani wani abu a school. Kin san dai ni ba sa’an ki ba ne, ko? Wai ma ba ki da ladabi ne? Mijinki ne ni fa yanzu.”
Farida ta kalle shi sama da ƙasa, ta sakar masa da tsaki kafin ta ce,
“Ai indai ba za ka nutsu cikin aji ba, to ka sa a ranka cewa ba zan taɓa barinka ba. Kuma ai mashayi, mazinaci, ba mutum ba ne, bare ya amsa sunan miji.”
Tana faɗin hakan ta turo ƙofar ta kulle.
Sufyan ya cije baki yana cewa, “Ke? Ni kike faɗawa haka? To dame ma kwado ya fi gaya? Yau za ki gane cewa na isa mijinki kuwa.”
Komawa ɗakinsa ya yi, ya ɗebo tilin kaya ya zuba, sannan ya koma ƙofar ɗakinta yana bugawa tare da cewa,
“Na rantse da Allah, ko ki buɗe, ko na aikata abu biyu cikin ɗaya. Na farko, in kira Baba Haruna in shaida masa rayuwar da kike yi da batun cikin shegen da ke jikinki Na biyu kuma, in sake bidiyon tsaraicinki duniya ta gani. Kin san dai ban da asara, ko?”
Farida na jin hakan ta tashi cikin sauri ta buɗe ƙofar, don ta san Sufyan sarai zai aikata. Tunda har ya rasa imanin da zai hana shi ɗaukar hotonta tsirara, ba zai samu wahala wajen bazawa duniya ba don ya tozarta ta.
Tana buɗewa ta ce, “Gani.”
Dariya Sufyan ya fara yi ya ce, “Da kika ce ba kya ji, to wanki za ki min wa annan kayan da ke gabanki. Ai dama mata ita ce take yi wa miji hidima, ko?”
Farida ta kalle shi, ta kalli yawan wankin, sannan ta kalli lokacin da ke jikin agogo—ɗaya saura. Sai ta tsinci kanta da yi masa magana cikin sanyin murya,
“Haba, don Allah. Ka san fa babu wuta, solar kuma ba ya ɗaukar injin ɗin. Ka bari gobe, bana da lectures, sai in yi maka da rana.”
Sufyan ya haɗe rai yana cewa,