BARA A KUFAI

Page 8.

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*

*Zeey Kumurya*


8.


BRIGHT PENS 2026

YOTA ID 003


Bismillahir rahmanir rahim.



Kamar ba amarya da aka sani da kunya da kawaici ba haka Zeenat ta cire mayafin jikinta ta tashi tana dudduba gidan, wani irin farinciki take ji da ba ta san ya za ta misalta shi ba, ta fara hango kanta a cikin haɗaɗɗun motoci na alfarma tana murza sitiyarinsu, ba ta taɓa sanin ana samun cikar buri ɗari bisa ɗari ba sai yau, kamar a mafarki haka take jin al'amarin, wannan ƙaton gidan da kayan alatun da a TV kaɗai take ganin su yau su ne a matsayin nata? Ga fridge ga gidan bene, ba ta san lokacin da ta buga tsalle ba gami da sakin ƙarar murna.
"Wayyo daɗi kashe ni!" Ta furta tana dariya kamar wadda ta zare. 

Daga ganin ɗakuna ta nufi kitchen, ta fara duddubawa, sai ta ga babu kayan kitchen a ciki, ga dai ginin na kitchen ne da komai amma ko tukunya babu, sai ta saka a ranta may be sai daga baya za a kawo ko kuma ɗaukar ta zai yi su je ta zaɓa da kanta, kayan kitchen ɗin Aunty Laure ta fara hasasowa, ta ƙudirce a ranta duk abin da yake cikinsa sai ta siyo ita ma, har ta ma ƙaro da wanda babu.

A nan Sita ya dawo ya same ta, da mamaki yake duban ta don ya yi zaton a lulluɓe a zaune a kan gado zai zo ya same ta, amma ita ko a jikinta, kanta tsaye ta gaishe shi tare da faɗin. "Ina dudduba gidan namu ne, to kuma sai na ga babu kayan kitchen, ko tukunyar da za mu dafa ruwan zafi babu." Ƙura mata ido ya yi kawai yana mamakin ƙarfin halinta, amma da ya tuno son kuɗi irin na babanta da gidan da ya ɗauko ta sai al'ajabin ya tafi, don fiye da haka ma idan ta yi ba abin mamaki ba ne.

Murmushi ya sakar mata ya ce. "Kayan suna gidanmu, za mu je yanzu ku gaisa da su Mum da ma, sai mu kwaso wasu abubuwan mu taho da su." 

Da rawar jiki ta je ta ɗauko mayafinta ta ƙara fesa turaren da ta zo da shi a jakar hannunta suka fice.

Murna kamar ta kashe ta saboda ganin ta a mota ga mijinta a gefe yana tuƙa su, suna tafe tana yi masa hira, ta kayan lefe da wayar da take burin ganin ta mallaka. Wani irin sanyi jikin Sita ya yi masa, tunda yake wa Yallaɓai aiki bai taɓa jin irin haka ba, kansa tsaye yake yin komai ya gama, amma yau sai yake jin tausayin Zeenat, yadda take wannan zumuɗin da zuciya ɗaya duk a zatonta mijinta ne shi na gaskiya, rayuwar aure za su yi mai cike da farinciki kamar kowa. Jiki a saɓule ya yi mata jagora suka shiga cikin guest house ɗin, Zeenat ta saki baki da hanci tana ba wa idonta abinci, a ranta tana ƙara gode wa Allah da wannan kyakkyawan kamun da ta yi, lallai dare ɗaya Allah kan yi Bature, wannan ƙaton gidan mai kama da aljannar duniya ne gidan sirukanta, gidan kakannin ƴaƴanta? Sai washe baki take ita kaɗai tana jin kamar ta taka rawa. 

Har sama suka hau kamar yadda Yallaɓai ya ce masa, ya ce ta zauna a parlour zai je ya kira Mum ɗinsa, yana ji yana gani haka ya fice ya bar ta a gidan, sosai yake jin ba daɗi a cikin ransa, duk da bai san dalilin auren da manufar yin shi ba, aiki kawai aka ba shi kuma ya aiwatar, amma ya san ba alkhairi ne zai biyo baya ba don ya san ubangidansa farin sani, ba ya ƙwansa sai da zakara. Sai da ya yi wa Yallaɓai text na kammala aikin sannan ya nufi motarsa ya buɗe zai shiga, ba zato kawai ya ji an buga masa abu a kai, a ɗimauce ya saki razananniyar ƙara tare da zubewa a gurin ba tare da ko shurawa ya yi ba. 

****** ******

Sauban ne zaune a falonsa ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana lallatsa wayar hannunsa, kamar wadda aka yi wa dole haka ya ɗauki mug ɗin gabansa ya kurɓi Black tea ya mayar ya ajiye. 

Ba tare da ya kara wayar a kunnensa ba ya fara magana. "Zaks ya ake ciki ne kana ina?" Ya yi shiru na wasu sakanni sannan ya gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya ce. "Ina gida ni, ka samo mini mai ɗan zafi-zafi zan ƙaraso yanzu, da na ce ba zan fito ba yau amma na dawo na tarar da waɗannan matan tsirara-tsirara duk na rasa nutsuwata." Dariya Zaks ya yi ya ce. "Sisters ɗin naka ne waɗannan matan? Gaskiya Sauban ba ka da kirki." Tsaki ya ja ya ce. "Ba za ka gane ba ne, ka samar mini kawai gani nan." Daga haka ya katse wayar yana yamutsa fuska. Cike da izza ya miƙe ya kwashi wayoyinsa ya fice daga part ɗin, bai haɗu da kowa ba har ya fice daga gidan gabaɗaya, haka yake so da ma don ba ya so Mommy ta tsare shi da tambayoyi ko ta hana shi fitar, shi kuma a yanzu ba shi da ƙwarin yi mata magiyar da za ta saka ta amince ta bar shi da ƙyar kamar kullum. Gudun da ya saba yake kwararawa kamar don shi kaɗai aka yi titin, bai ankara ba ya kwashe wasu yara maza guda biyu, wanda robobin da ya gani a hannunsa ya sa ya gane almajirai ne, kamar zai tsaya sai kuma ya ja tsaki ya tsallake su ya wuce, a fili ya furta. "Su suka janyo wa kansu ai talakawan banza, ban da hauka da jaraba wacce bara ce a wannan tsakiyar daren?" Ya ƙara jan tsakin da ya zame masa jiki, tuno motarsa ta taɓa jikin yaran ya saka ya fara jin ƙyaƙyamin ta, ba dan ya yi nisa da gida ba kuma ba ya son ya haɗu da Mommy da sai ya koma ya canzo wata.

Huɗu saura na asuba ya koma gida, ya tarar da mug ɗin da ya bari a parlour da ledar da ya sha choculate har lokacin, takaici ne ya kama shi, ya san da yana da mai aiki da tuni ta kwashe su, Mommy ta samo masa har biyu bayan maganar da suka yi amma duk ba su yi masa ba, saboda ba kowacce kucaka zai yarda ta dinga taɓa masa kaya ba, ƙyamar talakawa yake yi sosai, gani yake kamar suna da wani ciwo da za su shafa masa, wannan ya sa ko mai aiki sai wadda take fes yake yarda da ita, ita ma sai ta sha sharuɗa da ƙa'idodi. 

***** ******

Sai da gari ya yi haske sannan Juraij ya farka, mamaki ne ya cika shi don ya manta rabon da ya yi missing sallar asuba, ya manta rabon da ya yi bacci mai yawan wannan. A hankali ya juya kansa da bai gama sakewa daga nauyin da ya yi masa ba ya dubi Ramlah, ita ma baccin take sosai, ga dukkan alamu ita ma ba ta tashi ta yi sallar ba, tashin ta ya yi, ta farka da ƙyar tana hamma haɗe da miƙa. 

A gurguje ya yo alwala ya yi sallah, bayan ya yi azkar da addu'oi ya miƙe ya fice daga ɗakin ya tafi sama gurin Daddy. Ya daɗe yana kallon shi tare da yi masa addu'a, sai da ya ɗura masa rubutun da ake ba shi kullum sannan ya fice daga ɗakin bayan ya gyara masa kwanciya cikin ƙuncin zuciya. Idan ya tuna yadda Daddy yake da kazar-kazar amma yau shi ne a haka sai ya ji tsoron Allah ya ƙara kama shi, zuciyarsa ta ƙara karyewa. 

Ramlah tana hango shi ta fito daga kitchen, bai kula ta ba ya shige bedroom ɗinsa da sauri ya rufo ƙofar. A gaggauce ya yi wanka ya shirya ya fito, tana bakin ƙofar har lokacin ta yi kalar tausayi da fuskarta, a raunane ta ce. "Yau ma ba za ka yi breakfast ɗin ba?" 

"Me kika saka mini jiya a coffee?" 

Yadda ya yi maganar ya sa ta ba shi amsa ba shiri.

"Maganin bacci ne, ina son ka huta, bana son kana stressing kanka, bana son wani abin ya same ka saboda rashin hutu, amma ka yi haƙuri Please." Ta ƙarashe maganar ƙwalla na cika mata ido. 

"Na ce miki ba zan yi baccin ba ne?" 

Ta girgiza kai hawayen idonta na zubowa.

Numfashi ya fesar ya janyo ta jikinsa, sassauta murya ya yi ya ce. "Kin san ina zuwa duba jikin Daddy duk dare, and akwai wani important thing da na so yi a jiyan, amma duk kin ja ban yi ba, shi ya sa raina ya ɓaci." Ƙara shigewa jikinsa ta yi ta ce. "I'm sorry Mine, ni kawai ina son ka huta ne, ka samu bacci ishashshe." Hancinta ya ja ya ce. "Kar ki kuma amma, ba ki sani ba ko na yi da wasu za mu yi aikin tare, kin ga za su ji ni shiru, na zama mai karya alƙawari." 

"In sha Allah." Ta faɗa tana bin shi da wani mayen kallo.

Raba ta da jikinsa ya yi tare da duban agogon hannunsa.

"Yau ne ranar komawa gurin mai maganin Daddy, ni ma ina son na je gida, na jima ban je ba, jiya ka dawo late kuma kana wannan aikin shi ya sa ban faɗa maka ba." 

"Ok, Mukhtar zai zo ku tafi tare, da yamma sai na biyo Flight mu dawo tare." 

"Allah ya kai mu lafiya, sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya ya kare mini kai." 

"Amin, thank you." 


Daga haka ya fice bayan ya gama jaddada mata abin da da karatu da sai sama da A a cikinsa saboda haddacewa, ta bi shi da kallo tana jin yadda a kullum son shi yake ƙaruwa a cikin ranta, murmushi ta saki ta rufe ƙofar parloun ta koma kitchen, Marka ta umarta ta ƙarasa abincin karin ita kuma ta haura sama.


***** *****


Ɗaki ne ƙarami irin na hostel, a hankali matashin da yake kwance akan ɗaya daga cikin katifun ɗakin na ƴan makaranta ya yi juyi tare da ajiye littafin hannunsa, yana yamutse fuska ya tashi zaune.

"Ƙwaro namu ya da cilli da littafi kuma?" 

Wani matashi kamar shi da ya shigo ɗakin ya faɗa yana duban shi. 

Keɓe fuska ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce. "Yunwa ce, ta hana ni sukuni Auwal, na daina gane komai." Auwal yana zama a kan katifar da ke fuskantar tasa ya ce. "Ni ma nan ita take sakaɗa ta, ga Harun tunda ya fita shi ma shiru bai dawo ba, bare mu san halin da muke ciki." Shiru ALIYU ya yi yana nazari, a sanyaye ya ce. "Muna da shinkafa ko?" Auwal ya ce. "E, amma gas ya ƙare, da ma da ko da ruwa ne mun dafa mun hanbuɗa kafin mu ga abin da anjima za ta yi." 

"Dole sai na je gida yau, I'm missing My Mum, ga ba kuɗi a hannunmu, komai ya ƙare mana, ba zai yiwu mu yi ta zama haka ba gaskiya." 

Murmushi Auwal ya yi ya ce. "Yaron Mumy, wallahi Mama tana shagwaɓa ka da yawa, ƙato da kai amma a ce ita za ta dinga yi maka shopping, komai da an taɓa ka sai ka ce bari ka kira ta."

"Ni ma ba son hakan nake ba Auwal, ita ta dage sai na yi karatun nan tunda ta fahimci ina so tun ina ƙarami, na yi na yi ta bar ni na ci gaba da yin ɗinkin da na koya amma ta ƙi, ta ce ilimi shi ne farko, shi ya sa nake dagewa don na yi abin da za ta yi alfahari da ni, ina kuma roƙon Allah kar ya ɗauki raina ko nata sai na jiyar da ita daɗi da farincikin duniya, domin ta sadaukar da nata don ganin ta inganta rayuwarmu, yanzu haka fa da muka yi waya jiya take sanar mini an kawo keke ɗinki da ta siya mini, industrial sewing machine sabo fil." 

"Ma sha Allah, ka ce daga mun yi graduation sai ci gaba da ɗinki?"

"In sha Allah, haka ta alƙawarta da ma, kuma ta cika, duk abin da ta faɗa za ta mun lokacin yana yi sai ta yi, bana manta bajintar da ta yi lokacin da na yi saukar alƙur'ani." Ya yi shiru yana kallon guri ɗaya, idanunsa cike da wani irin rauni, wani murmushi ya saki ya ce. "Allah ka ara mini dama na mayar da mahaifiyata Sarauniya." Auwal ya ce. "Amin bro, wallahi yadda kake ji da Mama ba ƙaramin burge ni yake ba, rayuwarku tana saka na ji kewar mahaifiyata sosai, Allah ya cika maka burinka a kanta ya sa ku rabu lafiya." Cikin jin daɗin Aliyu ya amsa da "Amin." 

"Na daɗe ina son ganin ta, yau dai sai na bi ka mun je tare."

"Da gaske?"

"E mana." 

"Ai kuwa surprise zan yi mata sai dai kawai ta gan mu." 

Daga haka suka miƙe suka shirya suka nufi department ɗinsu, test ce da su karfe takwas, kasancewar saura kwanaki su fara exam ya sa abubuwa suka ƙara ɗaukar zafi, semester ta zo ƙarshe kuma ita ce final daga ita sun yi graduation. 

Malama Hajara wadda aka fi sani da DR DUBIYA ita ce za ta yi musu test ɗin, mace ce mai kafaffen ra'ayi da rashin wasa akan lamuranta, hakan ya sa ɗalibai kowa ke shakkar ta, hatta da malamai girmama ta suke, saboda mece ce mai arziƙin da ya bayyana kansa a manyan motocin da take zuwa da su da kuma siturunta, ga mijinta sanannen ɗan siya ne da kowa ya san shi. 

Ƙarfe tara daidai kamar yadda ta faɗa ta ƙaraso department ɗin nasu, da gudu ɗaliba suka fara ɗiba zuwa cikin class, don ƙa'idarta ne idan ta shiga aji babu wanda yake kuma shiga, test ɗaya take yi kuma ba ta make up daga baya, sai assignment da take bayarwa da kuma attendence da su take haɗawa ta yi C.A ɗinta, course ɗinta mai three credit unit ne, shi ya sa kowa yake son wucewa, ga C.O a course ɗinta azaba ne, ta iya riƙe mutum sai ya yi ta gyarawa kafin ya samu ya yi passing idan ba Allah ne ya taimake shi ba. 

Ba ta shiga class ɗin ba ta saka aka kira mata Monitor, tana daga cikin motarta ta dube shi a kame ta ce. "Ku koma theater a can za mu yi." Da rawar jiki ya ce. "Ok Ma."

Rarraba su ta yi ɗaiɗai sannan ta gayyato wasu malaman suka taya ta invigilating, questions masu zafi ta ba su kamar yadda suka yi tsammani, duk da karatun da Aliyu ya yi amma sai da ya ji jiki, ga yunwa sai nuƙurƙusar hanjin cikinsa take yi, haka dai ya nutsu ya amsa ya yi submitted ya fito yana share gumi. Sai da suka taɓa abincin da Harun ya samo musu sannan suka shirya shi da Auwal suka nufo gida, don da ma wannan test ɗin ce kawai da su yau, duk yawanci malaman sun yi covering sai jiran exam kawai. 


****** *****

Amma tana tsakar gida tana tsintar waken abincin ranar siyarwa, Hasina kuma tana ɗaki tana ta ƙunci da saƙa zaren da ba ta gajiya a kullum, Tasneem ce ta matsa mata akan tana son zuwa gidansu, ta fahimci kuma so take ta ƙure ta, ita kuma ba dagargajewar gidan nasu ce ma babbar matsalarta ba, Amma ce, tana mugun kunyar nunata a matsayin mahaifiyarta, saboda abubuwa da dama, rashin kyau da rashin gayu da wayewa, da Amman ta yi boko ne ma ko tana kwalliya to da abin zai zo mata da ɗan sauƙi, ba ta manta ranar da suka je dubo wata ƙawarsu ta school da ba ta da lafiya, suka tarar Mamansu an yi mata ƙananun kitso ta zubo da su a kafaɗarta, ga ta fara tas mai kyau, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, suna fitowa kowa ya dinga yaba ta suna cewa kyakkyawa ce, to haka ta so a ce mahaifiyarta ta kasance, wadda duk ya kalle ta sai ya kuma.

Amma tana ta zuci-zucin kammala ayyukan gabanta da suka cakuɗe mata ta ji muryar Aliyu yana rangaɗa sallama, da sauri ta ɗago cikin murna tana faɗin. "Muryar wa nake ji kamar ta Zakina?" 

"Ni ne Mummm." Ya faɗa yana dariya tare da jan sunan.

Gyara kwanciya Hasina ta yi tare da jan tsaki, ita ba ta ga ta inda Amma ta dace da sunan Mum ba, amma Aliyu ya bi ya ƙaƙaba mata, ko kunya ba ya ji wani ya ga Amma ya ji yana ce mata Mum, ita fa da ita take da kyan shi zaman gidan nan ma ba za ta yi shi ba, don shi fari ne mai kyau kamar Baffansu, ita kuma baƙa ce mai kama da Amma. 

"Sannu da zuwa, amma Gadanga wannan bazata haka? Da ka kira ni ka faɗa mini ai da na yi maka mutumin naka ɗanwake." Amma ta faɗa tana tura masa kujerar da take kai, bai zauna ba ya tsugunna ya saka hannu ya fara taya ta tsintar waken, fuskarsa na fitar da yalwataccen murmushi.

"Daga zuwanka za ka fara ko? Kai da ba ka son ka ga ina motsi."

"Na fi son na gan ki a kwance ko a zaune kawai kina lazimi, Allah dai ya kai damo ga harawa, yadda zan mayar da ke Amma ko sarauniya sai ta duƙa miki." 

Dariya ta yi mai cike da farinciki da nishaɗi ta ce. "Allah ya nuna mini lokacin nan ɗan albarkana, ni iya furtawar ma da kake yi ba ƙaramin sanyaya mini rai take yi ba, ka je ka zauna ka huta ka shawo hanya, bari na kawo maka ruwa, ga shi ƙosai ya ƙare tas, ban kuma ɗaura girki ba bare ka ci, amma bari na yi sauri na dafa maka ko taliya ce. " 

"Kai Mum sai ka ce wani baƙo? Ba ni kaɗai ba ne ba ma fa, tare da Auwal muke ya zo gaishe ki." 

Da sauri Amma ta miƙe tsaye tana faɗin. "Kuma shi ne ka bar shi a waje? Je ka shigo da shi maza, amma ba ka kyauta mini ba gaskiya Zaki, da ka kira ni na tanadar muku abinci ai, ko don shi abokin naka." Kansa ya shafa ya ce. "Kar ki damu Mum shi ma ba baƙo ba ne, bari na shigo da shi, kuma mu ma ai haka muka zo miki hannu rabbana." Murmushi kawai Amma ta yi, ta shiga ɗakinta da sauri ta ɗauko hijabi ta saka, ta fito da darduma ta shimfiɗa musu a inuwa. Bayan sun shigo sun gaisa da Auwal cikin girmamawa ta kawo musu ruwa, sannan ta fara kiciniyar ɗora girki. Aliyu bai zauna ba, wanke-wanken da ya gani na kayan ƙosan safe ya wanke, Amma tana ya bari za ta yi Amma ya ce shi zai yi, ya gama ya wanke gurin tas cikin ƙwarewa, sannan ya ƙarasa yi mata tsintar waken, ya leƙa kitchen inda take kwaɓan ɗanwake yana faɗin. "Lokacin Sallah ya yi Amma za mu je mu yi, don Allah kar ki daka yaji ki bar mini zan daka, har na shinkafa da waken ma." Murmushi Amma ta yi ta ce. "Ai shi kaiwa nake a doko mini da yawa saboda rage aiki, amma na ɗanwaken da za ku ci dai yanzu ni zan daka muku, har wanda za ku koma da shi ma, irin dakan da kake so zan yi maka." Langwaɓar da kai ya yi ya ce. "Don Allah ki bar mini na daka Mum, kina da aiki da yawa a gabanki fa, ga shi mun zo mun tashe ki tsaye."

"Ba wani aiki, wake da shinkafar nan kawai zan dafa, sai yankan salak." 

Bai kuma magana ba sai ƙasan rigarsa da ya kama ya goge mata gumin fuskarta, sannan ya ɗauki mafificin da ta rura wuta ya sake hura mata, sai da ya yi mata fiffita ita ma sannan ya baro kitchen ɗin, ta bi shi da kallo tana murmushi, shi kaɗai take kalla a duniya ta ji ta manta dukkanin damuwoyinta, baƙincikin da Baffansu yake cusa mata shi take kallo a matsayin ribar haƙurin da ta yi a zaman aurenta. 

Auwal dai sai bin su yake da ido cikin sha'awa, a ransa yana ayyana dace da Iyaye na gari ma babbar ni'ima ce, kuma babu abin da ya kai kasancewa da su da faranta musu rai daɗi, Addu'a ya dinga yi wa tasa mahaifiyar da bai rayu da ita ba.

Bayan sun dawo daga Masallaci Aliyu ya dubi Amma ya ce. "Wai ina Hasina ne?" 

"Tana ɗaki a kwance kanta na yi mata ciwo." 

"Ɗaki?" Ya maimaita cikin mamaki da ɓacin rai, don ya san zai yi matuƙar wahala ciwon kan gaske Hasinan take, ya san ta sarai da rashin tausayin Amman, ga shegen son jiki."

Ita kuwa tana kwance sai tsaki take ja na yadda Aliyu yake ta nan nan da Amma, a ganin ta son gwaninta ne kawai da iyayi. 

"Don iskanci kina kallon aiki ya rincaɓe wa Amma amma ke kina nan a kwance ko?" Ya faɗa a fusace bayan ya ɗaga labulen ɗakin da take. 

Baki ta cuna ta tashi ta ɗauki wayarta da mayafinta, ta raɓa ta gefensa ta fice, ba don tana tsoron ya kwakkwaɗe ta ba da sai ta faɗa masa magana akan ya daina shiga rayuwarta tunda ita ma ba ta shiga tasa, ya yi zaton aikin za ta kama, amma sai ya ga ta saka takalmi ta yi waje da sauri. Zai bi ta Amma ta dakatar da shi da faɗin. "Rabu da ita, ai na faɗa maka ta ce kanta ne yake yi mata ciwo, ai tana taya nin aikin ba wai ba ta yi ba." 

A zuciye ya ce. "Da ƙyar ba, wallahi Amma da kin bar ni sai na bi ta na tattaka ta, ji fa yadda kike kai kawo a ranar nan? Kuma na san tun kafin asuba da kika farka ba ki huta ba, a haka za ki dafa ki ba ta ta ci ta ƙara miƙe ƙafa, me yake damun yarinyar nan ne, wato har yanzu ba ta bar wannan baƙin halin ba?"

Murmushin takaici Amma ta yi ta ce. "Sai haƙuri, da kuma addu'ar fatan shiriya." 

"Da kuma duka ba, ai na kusa dawowa gidan gabaɗaya, wallahi sai na saita mata zama, don ba zai yiwu ki dinga aiki tana kwance ba, ko me take ji da shi sai na sauke mata." Ya ƙarashe zancen yana jan ƙwafa. 

Shi ya taya Amman suka ƙarasa ayyukan, suna yi suna hira, Auwal da ma daga Masallaci bai shigo ba, ya zauna a ƙofar gida don ya ba su guri su gana, ko abinci ma sai a soro suka ci. 

Aliyu ya yi zaton Amma za ta zauna ta huta ne, amma sai ya ga ta janyo waken suya ta hau tsincewa, za ta jiƙa a kai mata markaɗe saboda awarar yamma, shinkafa da waken da ma wani yaro ne yake fitar mata da ita titi yake siyarwa. Wani abu ya ji ya soki zuciyarsa, a duk lokacin da ya tuna wannan faɗi tashin take yi ta biya musu kuɗin makaranta da duk sauran buƙatun rayuwa sai ya ji kamar ya fashe da kuka, wani irin tausayi da soyayyar ta su ƙara ninke masa zuciya. 

Hannu ya zira a cikin waken tare da faɗin. "Zan nemo mai aiki gaskiya Mum ta dinga taya ki, tunda na buɗi ido a duniya da wannan rashin hutun na san ki, zuwa yanzu ya ci ki huta, tunda ba zai yiwu a daina sana'ar ba don ita ce suturarmu sai a samu masu tayaki ana biyan su." Kansa ta shafa ta ce. "Ba ƙi nake ba Zaki, ni ma zan so hakan, amma ba zan iya gayyato wani gidan nan ba, ka san halin mahaifinku, ko a gaban waye ba zai fasa yi mini cin kashin da ya saba ba, ni kuma ba zan so hakan ba." Numfashi ya sauke cikin damuwa bai ce komai ba, abin da ta faɗa gaskiya ne, don ya fi kowa sanin tijarar Baffa da yadda yake treating Amma, ba darajawa ba komai sai cin mutunci, ga ɗawainiyar ragamar gidan da ya sakar mata. 

'Allah ka ba ni arziƙin da Amma za ta ji daɗi, ka ba ni lafiya wadatacciya da zan kula da ita da jikina da dukkan ƙarfina.' 

Ya faɗi haka a cikin ransa.

Da ƙyar Amma ta kora shi gurin Auwal ta ce ba zai bar shi a waje shi kaɗai ba, tunda an yi an yi ya dawo cikin gidan ya zauna ya ƙi. 


Hasina kuwa direct layin da gidan nan da suka gani ita da Saudat ta nufa, ta tsaya daga nesa ganin Security guards a ƙofar gidan tana ƙare masa kallo zuciyarta cike da burika kala-kala, sai a yanzu take ƙara ganin yadda aka danƙara shi, tana nan a tsaye Sauban ya fito ta ƙaramar kofar gidan yana latsa wayar hannunsa, yana sanye cikin ƙananun kaya, fuskarsa a cuzgune kamar koyaushe, yadda ya kame gami da taku cikin izza ba mai cewa yaro ne ɗan shekara ashirin da biyar. 

Shagala Hasina ta yi da kallon shi cikin burgewa, a fili ta furta. "Wow!" Tare da fara wani hasashe a cikin ranta, har ya yi magana da Security guards ɗin ya koma ba ta ɗauke idonta daga kan shi ba. Jiki na rawa ta nufi gidansu Saudat don labarta mata yau ta ga wani daga cikin ƴan wannan dandatsetsen gidan. 

Sai da Aliyu ya kai wa Amma markaɗen awara ya taya ta yayyankawa sannan suka tafi, tana ta kwarara masa addu'a da sanya masa tarin albarka, har lokacin kuma Hasina ba ta dawo ba, abin da ya rage masa farincikin kasancewa da Amma da yake ciki kenan, don sai cikiyarta take cikin damuwar jin ta shiru har yamma, ya san ita kuma tana can yawan gantalin gidan ƙawaye hankalinta kwance, ba don exam da ke tunkaro su ba da ba zai koma a yau ba, sai ya zauna don ya dinga taya Amma ayyuka da deɓe mata kewar zaman kaɗaici.




*#Zeey Kumurya* 
*#****