MASIFAFFAN NAMIJI

16

by @jamilaumarjanafty

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty💞*


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.


*016*

"Duka yanmata Hudun ajere suka Shigo Kowacce na Bin Bayan yar"uwanta Cikin Shiga ta alafarma da kece Raini na musamman kowacce tana Tashin kamshi da Gayunta na musamman wanda take ji Har acikin Ranta itace zatayi nasaran samun Zankadeden Miji irin Abokin yayansu Salisu.

Barkat Itace Babbansu Itace kan Gaba Doguwar mace ce mai Fadin Fuska da Dara Daran Idanuwana Farace tas kamar atabata Jini ya Fito Tana da Dirin Jiki na Mata Daidai gwargwardo,Itace ke Bin Salisu Duk da akwai wata tsakaninsu Sadiya Allah yayi mata Rasuwa,Barkat Tana aji uku ne a Abu Samaru inda take karantar Micro Biology,Tana kuma sanye ne da Wata Ubansu Doguwar Rigar leshi wacce aka mata Dinkin A Shape ya kama ajikinta Sosai sai Daurin Maryam babangida Datayi ta yane Jikinta da wani Siririn gyale Fuskarta yana Fitar da wani Annuri wanda Daga gani kasan Haka baiwarta Take ammh kuma Daga kallonta zaka Fahimci bata da yalwar Fara"a kamar Sauran kannenta,akallah a shekaru bazata wuce Shekaru 25 aduniya ba ammh Fuskarta da yanayin Tsarin Jikinta ya Boye Duka Shekarunta.

Sai Bahiya wacce ke Bimata Itama Farace sosai sai Doguwar Fuska gareta Mai Dauke da madaidaicin Hanci da kuma Karamin Bakinta,Idanuwanta basu kai na Barkat ba,Ita nata suna da kwarmin Sosai Sudan Shige kadan itama Tana sanye Cikin Riga da Sikat na Atamfa tayi Daurin Ture ta bazo gashin Dokin datayi kari Dashi ta baya Bayan ta saka wani Mayafi baki ta yane kanta Dashi,Bahiya tana Abu ne itama aji Biyu Tana karantar Computer Science ne akallah a shekaru zatayi Shekaru 23 aduniya,ita tana da Fara"a soaai Domin Duka Fararan Hakoranta Suna Washe ne,sabanin Barkat da Ko Burbushin Fara"a bashi a saman Fuskarta.

Sai Ta ukunsu Bahijjat,Itama Farace Kamar sauran ammh bata kaisu haske ba,sai dai bata da Diri Sosai Sirintantan ya Fito Sosai,tana da kyau Ammh kuma Fuskarta Doguwa ne,haka Karan Hancinta,itama karatu take a poli tana Nd2 tana karantar SLT,ashekaru bazata wuce 20 aduniya ba sai Karamarsu Aina ita kuma Yarinya Sosai Ammh bata da Haske kamarsu Black beauty ce,Tafi kyau ma sai dai Bata da Tsawo Gajera ce Sosai,tana Shekaran Karshe a makarantar Sakandiri ta yanmata Dake basawa Ashekaru bazata wuce 18 ba in ka kalleta ma zaka Fahimci yarinyartar sosai itama taci kwalliyarta Sosai Duk dama Hajiya ce ta matsa mata sai tabi Jerin yan"uwanta ammh ita sam Bata Ma Fatan tayi Aure yanzu Shiyasa ma bata damu kanta ba kuma Tana Fatan Insha Allahu ma baza"a zabeta ba Tunda ga Na sama da ita su Anty Bahiya.

Duk acikin Mintunan da basu gaza Goma ba Nazifi da Abdullahi Suka karesu musu kallo Dama already Salisu yayi musu Bayanin Sunayensu da kuma matakin karatun kowaccensu Shiyasa suna ganinsu suka Tantance kamannin kowaccensu,Su kuwa Dukkansu zama sukayi saman Kujeran Dake Fuskanta Abdullahi da Nazifin kansu na kasa kowacce da Abunda take sakawa acikin Zuciyarta,bayan sun Hada baki wajen gaishesu Cikin Girmamawa.

Abdullahi ya waiga ya kalli Nazifi Shima ya kallesa,Kana Abdullahi ya maida kallonsa kansu yana amsa gaisuwan nasu Cikin kulawa Da Sauri Barkat ta Dago Idanuwanta sama suka Hada Ido Hudu da Abdullahi Lokaci Daya taji gabanta ya yanke ya Fadi,Shi kuwa Kansa ya dauke sama yana Fadin"Sannun ku da Fitowa yan mata.."Yafada batare Daya Shirya Fadin Hakan ba ganin Nazifin yayi Shuru yaki Cewa komai.

Jin Muryansa yasa kowaccensu ta Dago kanta tana kalloshi a kallon Farko Dukkansu sun zata Abdullahin ne, wanda zai zabi Daya acikinsu ganinsa Cikin Farar Shadda Tazarce harda Hula sabanin Nazifi da bai ma Sanya Hular ba kuma Shi Tunda ya kare musu kallo Yaji ba wacce zatayi Daidai dashi Gwarama karamarsu sai dai kuma tayi Gajarta dayawa Shiyasa kawai ya Kara Hade Ransa kawai ya maida Hankalinsa wajen latsa wayarsa.

Su kuwa kowacce sai ta Fara gyarawa Barin ma Bahiya datafi kowa Rawan kai da kafa,Cikin yanga tace"Yauwa..Baku Ko sha Ruwa ba..? Tafada tana wani karya Murya Take mata kafa Bahijjat tayi Tana Hararanta ta kasan Ido yayin da Barkat Ta Lumshe ido Cikin Sanyi Jiki da Kasala kana Ta Bude tana Bin Abdullahi da wani irin kallo Wanda ita kanta ta kasa gane kanta Duk Jin kanta da Jan ajinta Sai gashi ta saki Idanuwanta gabadaya Tana kallon Kowani Motsi na Abdullahi Tana naji aranta yau Taga Namijin Data Dade Tana nema.

Abdullahi yayi Mirmishin yake yana Satan kallon Nazifi Lokaci Daya yana dan zakudan Kafadansa ganin haka yasa Nazifi ya Dago kansa yana kallon Abdullahin wanda ya Rausayamai kai Cikin Alamun kayi mgana mana,Kallonsa Nazifi yayi kafin ya maida hankalinsa kansu Ido Cikin Ido yake kare musu Kallo Kur kai kana ganin kallon kasan na Kurullila ne Shiyasa kowaccensu ta maida kanta kasa,Sai Barkat wanda dama Chan kanta na gefe ne Hankalinta da Numfashinta yana kan Duk wani Motsin Abdullahi ne.

Cikin Gadara Nazifi yace"Masha Allah...Lalle Hajiya ta iya Haihuwa..Sai dai gashi ba wacce ta gabatar mana da kanta Tun zuwanmu..."Yafada kai Tsaye yana kallonsu Bahiya ce tayi Mirmishi ta Dago Cikin Salo Tana Fadin"Ok..Ba matsala Ni Sunana Bahiya..'Bahijjat tayi karaf tace"Haba Bahi ki bari mana Anty Barkat ta Fara mgana mana.."

Baki Bahiya ta Tura bata kara mgana ba Abun sai ya kusa saka Abdullahi Dariya sai ya kanne ya koma gefe kawai yana kallon Ikon Allah ganin Nazifin yana kokarin Raina musu wayau Cikin Ladabi Bahijat tace"Anty Barkat ki Fara mgana Don Allah.."

Ta Fada Tana kallonta Ko Dago kanta batayi ba kanta na kasa Tana wasa da Zoben Hannunta ganin Taki mgana ne yasa Nazifi ya kalli Bahijjat yana Fadin"Ku ku Fadamana Sunayenku..Tunda Taki Fadi Kila ta cire kanta ne Ba Damuwa.."yafada kai Tsaye yana kallon Barkat din aransa yana Fadin"Allah raka taki gona Duk mun sanku irinsu Sakina ne masu Jin kai sai ka kwasa ka kai Gidanka ka kwasan ma kanka Bala"i.."

Jin Haka yasa Bahiya ta Fara gabatar da kanta sai Bahijjat sai Aina,Barkat ce ta karshe kamar Batazatayi mgana ba ta Bude Baki Cikin yangar da ya zamar mata Jiki tace"Barkat..."Daga haka ta Rausaya kanta gefe kawai Nazifi yaso ma ya saki Tsaki sai dai ya Fasa Abdullahi kuwa Ruwa ya Dauko ya tsiyaya a kofi ya Tsiyaya yasha Kadan,Ya ijiye Kofin kenan Ganin Falon ya Kara Daukan Shuru,sai wayarsa Dake gaban Aljihunsa ta Dauki Kara ya Zarota da Sauri Ganin Sunan mai kiran yasa ya Dafe kansa yana kallon Nazifi Lokaci Daya yana Fadin"Nayi ma Hafsatuna Laifi ban Kirata na gayamata zan Tsaya wani waje ba..'

Nazifi ya kada kai yana Fadin"kaima baka kyauta ba..Gata ita kadai agida su Amira na wajen Ammi.."Mikewa yayi yana Fadin"Bari na Lallasheta ina Jiranka awaje.."Yafada yana kama Hanyar barin Falon Lokaci Daya yana Daga Kiran da Fadin"Hafsatun Abdullahi..."Ya fada Cikin Wata Murya mai Cike da kauna da Muradi mai Girma ba Barkat ba Hatta su Bahiya sai da suka Raka Abdullahi da ido Suna Tunanin kowaye wannan gayen ya gama Haduwa acikin Ran Bahiya kuwa tana addu"ar Allah sa ya zabeta in shine wanda ke neman Matan.

Barkat kuwa Tuni Zuciyarta ta Fara Zafi Jin Crush dinta yana Kiran wata da Hafsatunsa Lumshe ido Tayi tana maimaita Sunan Abdullahi acikin Ranta Lokaci Daya ta saki Mirmishi,ita kadai Duk Nazifi na kula Da ita Tabe baki yayi kafin yayi mgana yaga Dukkansu sun mike Bahijjat Da Bahiya suka tsaya mai sallama Barkat kuwa Da Aina Gaba suka wuce suka Fice Daga Falon Nazifi yace ma su Bahiya suma Hajiya Amina mgana zasu wuce,Sun Fita ba Dadewa sai gata ta Shigo nan Nazifi yayi mata Sallama Ya bata 10k Taki karba sai da ya nuna bai ji Dadi ba Itama sai Fada take basu Ci wani abu ba,da zai mike tace ina Abokin nashi yace yana waje tace toh su gaida gida Sun gode kwarai.

Har Nazifi ya Fice Daga Falon Tana Zaune Aranta tana Fatan Ya ga wanda Tayi mai,Domin Tasan Nazifin Sosai tare suke zuwa da Salisu Abdullahi ne ma bata wayeshi, ba Cikin Gida ta koma Bahiya ta Fara Taranta da"Hajiya waya zaba?ya gaya miki.? Hararanta Hajiya tayi kafin tace"Bansani ba mai Shigen Rawan kafa..Wazai zabeki da wannan Azarbabin naki.."

Bahijjat tace"Haka taje tana yi Hajiya Ta bari ma Anty Barkat tayi mgana taki.."Hajiya ta kada kai Tana Fadi "Daman na sani..Ke kam Bahi Allah ya Shiryaki."Tura baki take yi tatashi ta Shige Dakinsu Nan Hajiya ta nuna musu kudin Da Nazifin ya bata Cikin Yarinyata Aina tace"hajiya waye Ya Nazifin aciki wai..?
Hajiya Amina tace"Mai Sky Blue din Shadda ne..".

Dukkansu Da mamaki sukabi Mahaifiyar nasu da kallo Cikin Mamaki Bahijjat tace"What Hajiya.?na zata mai Farar Shadda ne.."Hajiya tace"A"a bashi bane..Bansanshi ba ammh Shima Salisu yace Dukka Abokansa ne Shi Aminin Nazifin ne inaga Rakosa yayi.."Barkat ta Dago Kanta akaro na Farko Tun Bayan Shigowar Hajiya Falon Cikin Kasala tace"Abokinsa..? Tafada Cikin karya wuya da Mamaki Hajiya ta kalleta tana Fadin"Eh haka Salisun yace min..Ammh me neman matan Shi Nazifin ne."

Bahijjat tace"Tabdi..Allah Hajiya na Zata Dayan ne..Shi Nazifin ya Cika Nuna kamar ma ba wacce tayi mai acikinmu Dayan kuma yafi Shi Nuna aji da  suwas na manyan yara..."Hararanta Hajiya Tayi Tana Fadin"Kema sakarya ce...Tafi kibama Mutane waje,Duk Halinku Daya da Bahiya Din."Dariya tayi ta wuce Tana Fadin"Nifa Daman Bai min Ba Dama Dayan ne gwara gwara yafi kallon Mutumici Allah sa ma ba wacce tamai acikinmu..."Da Harara Hajiya ta Rakata Har ta Shige Dakinsu Barkat kuwa Jikinta neyayi sanyi Jin Abdullahi ma Rako yayi ganin Yanayinta yasa Hajiya tace"Barkat lafiyanki kuwa..? Dago Dara Daran idanuwanta tayi tana Fadin"Bakomai Hajiya.."Daga haka kawai ta mike tana Rangaji Zuwa Dakinsu kamar mara Lafiya Duk da Hajiya ta santa da Wani Irim Iko da sanyi kan komai sai da tayi mamakin Chanzawarta Kai kawai ta kada Ta Tashi da kudin Hannunta zuwa Cikin Bedroom dinta.

Abagaren su Abdullahi kuwa Basu cema Juna komai ba sai da suka Dauki Hanya kana Abdullahi ya kalli Nazifi yana Fadin"To ya Mutumina..? An dace..? Baki Nazifi ya Tabe yana Fadin"Ba"a dace ba...Kasan Allah Duk kwanwan Ja ce,In na kwasa wni Bala"in zan kara kaima kaina kawai.."Abdullahi yace"Meyasa..? kuma naga Dukkansu ba laifi Abokina.."Nazifi yace"Ban ce suna da Laifi ba Im nace zan kushesu bam ma kaina adalci ba kawai dai Abunda na Fahimta auran mace mai Ilimi Sosai wacce ta Fara girma matsala ne gwara ka auri karamar yarinya yar Sakandiri wacce zaka koyamata komai da kanka Wacce na Tabbata bazata Taba gardama ko Sa"insa da kai ba.."Abdullahi yayi Dariya yace"kuma fa Hakane kaima kayi Dabara toh ga karamarsu Mana.."

Nazifi ya Tabe baki Yana Fadin"Ita gaskiyan matsalanta bata da tsawo kuma kasanni ni Bana son Gajeran mace.."Abdullahi yace"kai..kenan ba wacce tayi maka kenan ko..? Nazifi yace"Kusan haka gaskiya.."Abdullahi ya Kada kai yana Fadin"Nifa na zata babbarsu zaka Zaba naga tafi su Aji da Kama kai.."Nazifi ya juyo yana kallonsa Lokaci Daya yace"Wa kenan..? Abdullahi ya Tabe baki yana Fadin"Wata ke ma da Suna Baraka ko wa..?

Nazifi ya Sheke da Dariya yana Fadin"Au Wai barkat ko..? Abdullahi yace"Oho ina jin Haka Sunan yake..Ita.."Nazifi yace"Allah ya Sauwake ai ni Irinsu basu Burgeni masu Shigen Girnman kai da Nuna isa Duk irinsu Sakina ne, sai ka kwasam ma kanka Ka kwashi Bala"i Ni Wlh sam Bata Burgeni ba.."Abdullahi yace"Allah ya kyauta yanzu me zaka ce ma Salisun..? Kasan fa Ba Dadi Kace mai Duk Cikinsu ba wacce tayi maka..?

Nazifi yace"Bayani zan koramai..Dama bance mai Dole wata Zatamin ba..Shima ya sani Cewa nayi zan Duba in naga wacce tamin Shikenan.."Abdullahi yace"Shikenan ammh kaki min ne..Da ko karamar kun Daidaita Gajartan ta bawani abu bane Tunda ai sakina tana Tsawo Shikenan ka Hada Both Side."Ya karishe Fada yana Dariya Nazifi ya Bankamai Harara yana Fadin"Kaima Ai Hafsah na da Tsawo In ni batamim a,kai sai ka Taimaka kaima ka Hada Duka Bangaren  Mr Shawara man.."Abdullahi yace"Ikon Allah miye yayi zafi shi fa Wuta Ba Mallam..Nazifi Wada? Ni kaji nace maka ina Son Auran yara kanana ne..? Wannan ra"ayinka ne Ni ba nawa ba.."Nazifi yace"Toh sai kowa ya bar Ra"ayinsa Fakat.."

Abdullahi yace"Miye Zafi..? Shikenan Chapter close daman Salisun nake ji Gaskiyan mgana zai Ji ba Dadi.."Ko kallonsa Nazifi bai karayi ba,ballatana ya kara mai Mgana har yayi parking kofar Gidansa Abdullahi ya Bude Murfin Mota ya Fice Lokaci Daya ya Rankwafo yana Fadin"Toh mutumina sai yaushe kenan..?

Nazifi yace"Sai gobe kenan ko..? Any way  muyi mgana ta waya Goben zan koma Kaduna Sakina Tamin waya zata Dawo Goben.."Abdullahi yace"Ah ba Haduwa kenan Amarya zata Dawo wajen Tsohon gauron angonta Hajj Nazifi.."Kafin ma Abdullahi ya matsa Nazifi ya Tada Motan kadan ya Rage ya kadashi yayi baya yana Dariya afili ya Furta"Ji bakinciki zai ma Hausina Asara Tunda Shi Sakina bata damu dashi ba.."Yana Tsaye a wajen har Motar Nazifi ta bace ma ganinsa,kana ya zo Zai Shiga Gida Jin Kofar gidan a kulle yasa ya Ciro dan makullin Dake Hannunsa ya Bude ya Shiga.

Hafsah har ta Fara Barci saman Kujaran Falon,Shi ya Tadata tana ganinsa Ta Mike ta Fada Jikinsa Tana sakarmai kukan Shagwaba tana Fadin"Ina ka Shiga ne Tundazu ina ta Jiranka Har Auwal yazo ya kawo ma Mashin Dinka ya tafi baka dawo ba.."?Yana Buga Bayanta Cikin Lallami yace"Am So Srry Hausina..Laifina ne da zamu Fita da Nazifi ban Kiraki na Fadamiki ba ammh ai na Fada miki da kika Kirani ko..? Tana kara Shigewa Jikinsa tace"Toh kuma Shine kace gakanan zuwa kaki dawowa da wuri ni kadai agida ina Jin Tsoro.."

Abdullahi ya Tarairayota yana Fadin"Oh my god...Am so sorry Hafsatuna Bazan kara ba kinji ko..? Yafada Lokaci Daya yana Yawo da Hannunsa abayanta Cikin Rada tace mai ga abinci yace mata Ammi ta cika musu Ciki Jin haka yasa ta washe baki Shikuma ya Shiga gayamata Diramar Ammi  dasu Amira Hafsah na Dariya ammh bai gayamata inda suka je da Nazifi ba yadai ce mata sun Biya wani waje ne,Bata damu da Tambayarsa ba sanin ko zata mutu bazai gayamata ba sanin Halinsa na Zurfin Ciki da Rike sirri koda banashi bane balle na Amininsa Nazifi.

Washegari kuma Su Abdullahi suka Tafi Danja Daurin Auran Diyar Mijin Goggo Habiba amotar Nazifi dashi da Abdullahin da Nazifin da Mama sai Inna Abu  da Baba wada sai Auwal sukaje sukayi samu Daurin Auren, wajen uku na Rana suka kamo Hanya suka Dawo Suna Dawowa Nazifi ya wuce Kaduna Bayan ya Kira Salisun ya mai Bayanin ba wacce tayimai Salisu bai nuna damuwarsa ba ammh acikin Ransa baiji Dadi ba sam Haka ya Kira Hajiya Amina ya gayamata Cewa Nazifin yace ba wacce tayi mai Hajiya ita kanta Bataji Dadi ba ammh sai ta nuna Allah yasa Hakan ya zama alheri,Da su Bahiya sukaji labari basu ji Dadi ba Musamman Bahiya,Bahijjat kuma ko ajikinta Ballatana ma Aina Da bata damu ba Barkat kuwa Bata bari kowa ya gane yanayinta ba ammh a zahirin gaskiya Jiya ta kwana da mafarkin Abdullahi wanda ya Shiga Cikin Zuciyarta Lokaci Daya batare data sani ba.

*******

Bayan Sati Biyu Tsakani Sai ga Waya Daga kano Cewa Anty Hadiza ta Haihu yan Biyu Duka Maza,ammh C.s akayi mata tana asibitin Murtala Aminu specialist Hop,Dake kano,Ammi ta Kira Hafsah Tana Fadamata Ihun Murna Hafsah ta saki Cikin Farinciki Dadi kamar ya kasheta Abdullahi na Office sai ga Kiran Hafsah tana gayamai Haihuwan Shima yayi murna Sosai Cikin Zolaya yace"Hafsatuna nima ko yau na Bada Himma na baki ajiya kwan Haihuwa guda Biyu ne..? Ina son Twice Sosai fa..".

Kunya ya kamata ta saki Dariya Tana Fadin"Allah ya bamu Masu albarka Yace Amin..Cikin Shagwaba tace"Abban Amira gobe zan Tafi ko..? Tunda ma su Amira na wajen su Ammi haryanzu.."Cikin mamaki Abdullahi yace"Ina zaki gobe..? Cikin Sauri Hafsah tace"Kano mana Abban Amira Kaga fa C.s akama Anty Hadizan yau Ammi tace Zata Tura Inna Asibi tatafi Chan wajenta Ni kuma ba sai gobe na tafi ba.."

Cikin Mamaki yace"Ki dawo yaushe kenan..? Hafsah tace"Wai da Bayan suna kaga nesa ne kada ayi Tafiya Rarrabe.."Baki kawai Abdullahi ya Rike yana Fadin"Hakane..Sannu Uwar Suna ko nace na Sha"ani..Allah kaimu.."Daga haka kawai ya yanke Kiran Ita kuma Hafsah jin Haka yasa ta Shiga Murna nan da nan Ta Hau Shirin kayanta bayan  ta gama ta Kira Subai ta Fadamata itama tayi murna Tace insha Allahu zata je suna Nan Hafsah ke gayamata gobe zata tafi sai bayan suna zata dawo Subai ta rike baki Tana Fadin"Ke don Allah shi ya Abdullahin ya barki..?

Hafsah tace'Nima nayi mamaki kila Don suna Shiri da Anty Hadizan ne..'Subai tace"Sai dai haka..Allah sarki Allah ya bata Yayanta nawa yanzu..? Hafsah tace"Uku ne,da wadanan Yan Biyu making 5 kenan..."Subai tace'Masha Allah Allah ya rayasu"Daganan suka yanke Kiran Daga ita Mama ta Kira ta gayamawa Mama tace Ammi ta kirata yanzu Umman Sadiq ta kira itama tace Ammi ta Kirata yanzu ta gayamata,Tace insha Allahu zata yi kokari tazo Zaria Allah barshi sai ta karisa kanon.

Duk wanda ya kamata yaji Haihuwan yaji Hafsah kuwa har Daddy ta Kira tana mai Barka,Ya Dinga Tsokananta yana Fadin Yana Jiranta wata Shekara Duk kunya sai ya kamata,Abdullahi ma Daya dawo ya Kira Daddy da Ammi yayi musu barka Harda Anty Hadizan wacce har ta Farfado Tun da Rana Tunda tun Cikin Daran Jiya ne akayi aikin,Inna Asibi har ta isa Tun safe,Abdullahi yana jin Hafsah na Fadama Anty Hadizan gobe tana Kan Hanya Har Anty Hadizan tana Cemata sai suzo tare da Matar Baba Mustapha Hajiya gaje Domin yanzu suka gama waya tace suna tafe gobe Marwan zai kawota Babban Danta.

Har jinta yayi tana Fadin sai ta Bisu suzo Tare,Abdullahi bai nuna mata komai ba adaran Ranar Haka suka Raya wannan Daran cikin Farinciki da Soyayyah Tun Safe,kuma Hafsah tatashi da Gyaran Gida tayi Breakfast da wuri Ta Shirya tayi wanka Babban akwatinta ta Cika da kaya Tun safe ta Kira Mama gaje ta gayamata zata Bisu tace tayi kokari ta Biyo su Tafi tare,Abdullahi bai ce mata komai ba sai da ya Shirya zai tafi Office kana Hafsah tace"Abban Amira baka ce min komai ba.."?

Yana Daura Tek tie dinsa yace"kamar name..? Cikin mamaki tace"Baka ce min komai kan Tafiyata kano yau ba kuma baka bani kudi a hannuna ba Haka zan tafi..?.
Kai tsaya yace"Haka zaki Tafi mana Tunda ke kika Tsara Tafiyar naki.."Tsuru Hafsah tayi mai da ido cikin Rawan Murya tace"Ban...ga..ne mganar ka...ba Abban Amira.."?

Bai bama Mganarta muhimmanci ba yace"Ni nace ki Shirya ki tafi kano kije ki tare sai bayan Suna..? Ke kika Tsarama ma kanki Tafiyar bazan hanaki ba Saboda yar"uwanki ce ta Jini in na Hanaki bazaki ji Dadi ba ammh in ni zan Tsara miki Tafiya sai nace ki bari sai ana gobe suna ki tafi In akayi suna ki Dawo yau kuma sai kibisu kije ki Dubata ki Biyosu ki Dawo duk wanda kika zaba bazan Hanaki ba."

Hafsah taji ta Raina kanta Cikin Wani Irin murya tace"Ammh ai Kaasan Anty Hadiza bata da wata Kanwa sai ni ko..? Bai kamata na Tafi ba tun yau..?

Yana Daukan key din Mashin dinsa da jakar Brief case dinsa yace"Wa kika ji yace bai kamata ba.? Ya kamata mana Sosai.."

Hafsah takada kai kafin tace"Toh kagani..."Yana yar dariya yace"Shikenan Allah ya kaiku lafiya kima Mai jego barka.."Daga haka yasaka kai zai Fice Cikim mamaki tace"Abban Amira.."

Cak ya tsaya Lokaci Daya ya waigo yana Fadin"Uhmm..Menene..?

Kanta na kasa tace"Baka bani komai ba...Kasan kuma bana yi Tafiya bani da kudi a Hannuna ba.."

Kai Tsaye Abdullahi yace"Bani da kudi yanzu a Hannuna...Tunda ke kika Shirya tafiyanki na zata kina da kudinki ne Shiyasa kikaga ban hanaki ba."Yafada yana Kafeta da idanuwansa Dago kanta tayi Cikin Rau rau tace"Abban Amira waya bani kudin.? Kai tsaye yace"Ina zan sani..Nifa nazata kina da kudi ne Tunda kika Shirya tafiya yau.."..

Idanuwanta suna kawo kwallah tace"Yanzu dai bazaka bani ba kake Nufi ko Abban Amira..?

Kai Tsaye yace"Gaskiyan mgana ayanzu dai bani dashi..Shiyasa nace ki bari Zuwa ana gobe suna Lokacin na samu albashina sai na baki Ishashen kudi ammh yanzu kam ko sisi bazan baki ba keda kika Shirya tafiyan Dama baki Tanadi kudin da zaki rike bane..? Yafada Cikin nuna mamaki yana yar dariya hawaye ya kawo idanuwan Hafsah tayi maza ta Share Lokaci Daya ta kada kai tana Fadin"Bakomai nagode..Bakomai yajamin ba sai Rashin sana"a

Dariya ta kaama Abdullahi sai ya kanne yana Fadin"Allah Madam..? To ko zaki Jira in kin Kafa sana"ar taki kin samu Riba sai ki Tattara ki tafi... ? Ya fada yana mata Dariyan mugunta Takaichi ya kama Hafsah ta kadai kawai ta juya zuwa Ciki Tana Fadin"Zan tafi..Insha Allahu Tunda dai ka amince bazan Rasa yadda zan yi ba..

Shima kai Tsayen yace"Shikenan Allah kiyaye Hanya ni ba bakon zafi bane na amince ki Tafi..Ammh kuma ban yarje miki kije kina Roko ko baran kudi ba Tunda ban ce ki Tafi Dole ba Fitinarki ce atoh.."Daga haka kawai ya saka kai ya fice yana mamakin Taurin kai da Rashin Hankalin Hafsah na wani Lokacin..



Littafin Masifaffan Namiji  free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai Completed document  1k ne biya ta wannan acct ɗin 5040273639 Moniepoint Jamila Umar.
Ko tuntuɓa ta wannan lambar ***

*Janafty*