Bonus page
by @smauta
Baban Kawata bonus page
Satin su kaka daya da tafiya Germany kullum manar cikin kuka take gogan nata kuma ya kifa kasa bazataje ba yau kimanin kwana 4 tana gaba dashi ta rufe kanta a daki saita tabbatar da bata gidan take fitowa, yanzu haka tana daki kwance abin duniya ya taru yayi mata yawa ita koda kawu labaran dinne ma tabi tabar gidan kangin bautar nan ba abinda ta tsana a yanzu irin zaman gidan nan...........
Karfe 7 na dare khalil a tsaye bakin MANAR MANAR MANAR tanajin shi arzikin ansawa bai samu ba dakin shi kawai ya wuce direct ya dauko spare care,koda ya bude kofar dukunkune take a bargo gaban gadon ya tsaya yana kallon ta sarai yasan tanajin shi, manar ya kira sunanta a hankali tare da wata irin murya ta sigar lallashi nayi maki wani abu ne?kamar jira takeyi kuwa ta mike tambaya ta kakeyi ka rabani da farin cikina kayi camping dina a gidanka kasa kawuna ya tafi yabar ni dagani sai kai a cikin gidan nan wai in tambayeka me kkeso dani ne?????
Banison komai manar amma inason zama dake kina debeman kewa akan yadda zan shigo gidana na tarar da ba kowa koba komai nasan yanzu idan nadawo nasan nabar wani a gidan,banso ta sanadina damuwa ta dameki,kaka suna cikin koshin lafiya,kakar ka ce ko tawa duk abinda kika dauka dai-dai ne nidai nasan a wurin kaka ma nafiki power dama sakon gaisuwar ta ne zan baki tace a gaisheki kuma ki kwantar da hankalin ki tana cikin koshin lfy,mtswwwwwwwwwwwwwwww ta buga mashi tsaki tsammm ta fice ta bar masa dakin duk rashin kunyar nan samun kanshi yayi da dariya yace na yarda ba'a abota sai hali yazo daya idan tana wani abun kamar halim,sai lokacin ya tuno yau kusan 2 weeks baiyi mgn da ita ba hankalin shi ba'a kwance yake ba tanacan ta cika jiran kiranshi take kawai ta fashe😹🥱
Parlour ta zauna biyota parlour yayi kinci abinci banajin yunwa,rike cikinshi yayi kamr yaro nikuma inaji daria ma ya bata har bata san ta murmusa ba,in rokeki wata alfarma baby girl,bazanyi ba ma kowace alfarma ce ka rike abunka, dariya yayi yasan duk wannan rigimar shiya siya am very serious manar inajin yunwa kosan nan naki da kunu nake craving zan samu???????
Fuuuuu ta mike har taje gaban kitchen ta kalle shi wlh kawai naji tsoron Allah ne kar wani abu ya sameka amma da bazanyi ba🙄 remote ya dauka ball dinshi ya cigaba da kallo baayi hour ba ta fito yana kallonta tana hararar sa kamar wadda akaima dole ta dangwara tray din gabanshi bai kulata ba ya buda wani kamshin daya daki hancinsa ne yajashi kan cin abincin,kinsan dai banacin abinci idan dare yayi amma tunda naki ne zanci,s ranta tace ji rainin wayau kagama rokona yanzu kaceman haka.…..........
Ta maida kanta a TV kamar tana gane me akeyi a ball ɗin,ki shirya gobe zamuje kiyi shopping kayan back to school da kike needing,bana needing komai kuma ba zan koma wata school ba muddin kaka bata dawo ba😳😳😳zaro ido yayi waje kinsan yaushe zata dawo,bansani ba amma ko shekara zatayi bazan koma ba karma kayi asarar kuɗin ka dan wallahi bazan koma ba in tafi china bansan a wane hali take ciki ba, yanzu dakike abuja kinsan wane halin take ciki, bansani ba amma ina tareda dakai kome ya faru ma nice ta farko da zan fara sani yanzu ma zuciya ta takeso ta yarda da maganar kawu anya ba saida su kayi ba??????
Dariya yake harda hawaye in rasa suwa zan siyar sai kaka gaki mai jini a jika idan za'a bani miliyan dari akansu ke idan na badaki sai billions,indai saida su nayi banga amfanin zamana dake ba,tsamm ya mike tsaye ki shirya goben bansan dogon zance,ba inda zanje wallahi,gabanta yazo me kikeso ayi???kawai ka kaini wurin kaka, bakisan inda ake bi aje wurinsu bane nasani amma banida kudinda zankai kaina wurin su,zaki dade baki gansu ba kuwa dan a yanzu kudi ke magana, maganar daya gayamata taji ba dadi sosai dan yanada kudi ya taimaka masu shikenan yanzu tazama karen farautar shi zai saka mata ka'idoji wata zuciyar tace bai isa ba ni manar zanyi aiki tukuru koda zan rasa raina na nemi kuɗi a duniyar nan..........