MATAR GIDA PAGE 25
MATAR GIDA025
SHUUKRAN/022
P25
Gyara zama Ɗalha ya yi kafin ya daura da ''na yi magana da limamin masallacin da nake zuwa sallar asuba kan batun Ummu Abiha,na yi masa bayani yadda take zama ta yi ta magana ita kadai,sai kuma Rayyan yawan faɗa da yake yi da Afef da kuma Sudais kan yawan mantuwa da yake,ya ce min insha Allah zai fidda ayoyin Allah da za'a rubuta masu suna sha kowanne da nasa za'a rubutu ko a tofa a ruwa,a karshe dai ya ce dole mu ƙara kula da yaran mu dage wajen yi masu addu'a'' kan Amirah ƙasa ta ce ''masha Allah,Allah ya taimake mu ya shirya mana su'' Ɗalha ya ce ''ameen'' shiru ne ya biyo baya bayan wasu ƴan sakanni Ɗalha ya cewa Amirah zai fita Amirah ta yi masa Allah kiyaye hanya,bayan Amirah ta tabbata Ɗalha baya gidan ta sake wani kuka mai sauti kuka take babu ji babu gani da za'a tambaye ta dalilin kukan a wannan lokacin ita kanta bata san dalilin kukan ba,tun ranar da Ɗalha ya miƙa mata takardar saki ta ji sonsa ya ragu sosai a zuciyarta daga kaso ɗari soyayyarsa ta koma kashi ashirin zuwa ashirin da biyar,abinda yasa Ɗalha ya ƙara fita ranta shine auren da zai yi aure,harda aure ba haramun bane amma gani take kamar ta gaza ta wani wajen ne,duk hidimarsa da na yara da take yi bai gani ba hasali ma bai taɓa yaba mata ba,hakan yasa zai auro wata wacce zata sauke duk wani nauyinsa a kanta,a yanzu haka dai babu wani so ko kaunar Ɗalha cikin zuciyarta in ma akwai to kaɗan ne,murya can ƙasa ta ce ''wai ita Unaisa'' ta furta ita kadai kamar wani take gayawa,ta dauki a ƙalla mintina goma tana kuka kafin daga bisani ta bawa kanta hakuri, bathroom ta faɗa ta yi wanka bayan fitarta ta shirya kanta cikin wata atamfa ɗinkin riga da sikit daidai lokacin da zata rufe ƙofar saif idonta ya sauka kan magungunan da Rumaisa ta bata taɓe baki ta yi ta rufe saif ɗin ta cigaba da sabgoginta tana cikin aiki a kitchen ta jiyo muryar Hafsah matar Muhsin cikin parlour tana sallama,Amirah ta rage wutan talgin tuwo dake tafasa kan wuta daga haka ta fita daga kitchen ɗin fuskarta dauke da murmushi ta fito ta tadda Hafsah zaune kan doguwar kujera,waje Amirah ta samu ta zauna cikin parlourn nan suka gaisa da Hafsah bayan sun gama gaisawa ne Amirah ta koma kitchen ta dauki ruwa da lemo a cikin firiji ta kawowa Hafsah
Hafsah ta dauki kofin ruwa ta kurɓi ruwa kaɗan tare da ajiye kofin,mayar da dubanta ta yi ga Amirah ta yi magana cikin kwantar da murya ta ce ''ya jikin Fauziyya?" Amirah ta bata amsa fuska sake ta ce ''jiki da sauki sosai alhamdulillah bakin ya fara warkewa''Hafsah ta ce ''masha Allah'' shiru ne ya biyo baya can Hafsah ta ce ''dan Allah Maman Sudais ki yi hakuri kan abinda ya faru,ranar a asibiti ban samu damar ba ki hakuri ba,wallahi ban san lokacin da ta shiga ta dauki hypo ba kawai sai jin ihunta na yi'' ta ƙare magana cikin kwantar da murya Amirah ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce ''babu komai wallahi haka Allah ya rubuta,aiy su yara ba'a iya masu,ita fa Fauziyya ko a gida haka take ko yaushe tana manne da ni duk inda zan shiga tana biye da ni ga ɓarna Allah dai ya shirya mana su'' Hafsah ta ce ''ameen'' daga haka sun cigaba da hira ganin hirar ba mai ƙarewa bane yasa Amirah cewa Hafsah zata kitchen ta duba talgin da ta yi ko ya nuna Hafsah ta ce babu damuwa ta faɗa tare da tashi tsaye ta ce ''muje na ɗan kama maki wani aikin'' Amirah ta ce ''kai haba dai ke da kike zo dubiya'' Hafsah ta yi murmushi ta ce ''aiy mutumiyar ce har yanzu bata farka ba bare mu gaisa'' Amirah ta ce ''haka ne kam'' daga haka sun wuce kitchen Amirah na gaba Hafsah na biye da ita, bayan shigar su Amirah ta tuƙa tuwon masara bayan ta tabbar da talgin ta nuna yadda Hafsah ta haɗa kwanukan da su Sudais suka yi breakfast da ta gani cikin sink ta fara wankewa Amirah kuma ta shiga pantry ta buɗe robar garin da ta ɗiba garin tuwo ɗazu ta mayar da sauran garin da ya rage cikin robar,suna aiki suna hira, cikin hirar nasu ne Hafsah ke tambayar Amirah ko zata tafi walimar Unaisa da za'a yi yau da la'asar,Amirah ta ji tambayar wani iri ita bata san da wani walima ba kawai sai ta ce ''a'a bazan samu damar zuwa ba saboda bana jin daɗi ga kuma jikin Fauziyya ba zan fita na barta da ƴanuwanta ba'' Hafsah ta ce ''haka ne kam,ni gaba ɗaya ma yarinyar bata yi min ba bata da kunya ko kaɗan rannan baban Sudais ya kawota gidana uni ya ce zai dawo bayan la'asar ya dauketa,ba ki ga rashin mutunci da yarinyar nan ta rinƙa masa ba a waya kamar wata uwarsa haka take masa magana shi kuma sai lallaɓa ta yake tun daga ranar na cewa baban Muneebah kar ta sake zuwa min gida,abinda ya fi ɓata min rai shine yadda baban Sudais ya rinƙa bata hakuri,kin san wasu mazan akan mata masu kyau wawaye suke zama'' Amirah ta yi shiru ta ƙi amsa Hafsah tsabar mamaki wai Ɗalha ne mace ta yi masa rashin kunya amma shi ya bata hakuri nan take Amirah ta ji zuciyarta yana mata wani zafi, bata yarda Hafsah taga yanayin da take ba kawai ta ce ''in kin gama wanke tukunyar ki bani zai shigar da shi ciki'' Hafsah ta dauki tukunya ta miƙawa Amirah tare da faɗin ''kin san mahaifin yarinyar bafulatani ne mahaifiyarta kuma shuwa ce ƴar kasar Niger,ba ki ga kyau wajen yarinyar ba amma sam bata da ɗa'a'' da wani irin sauri Amirah ta fita daga kitchen tana faɗin ''ina zuwa Maman Muneebah ana kirana a waya'' daga haka ta fita daga kitchen sosai Amirah ta shiga yanayin damuwa wata irin mace Ɗalha zai dauko mata ne haka innalillahi wa inna'ilahi raji'un haka ta yi ta maimaita kalmar cikin zuciyarta gaɓa ɗaya bata son sake jin komai game da Unaisa nan ta shiga tunanin dabarar da zata yiwa Hafsah ta samu ta tafi dan gaba ɗaya bata son jin zancen Unaisa,wata dabara ce ta faɗa mata da sauri ta shiga bathroom ɗinta ta wanke fuska bayan ta gama wanke fuska ne ta shafa mai da poda sama sama,ta dauki turare ta fesa kaɗan ba da yawa ba daga haka ta dauki gogaggen hijab kalar atamfar jikinta ta zura daga haka ta wuce inda take zuba takalmarta ta dauki baƙin takalmi marar tsawo ta sa,ƙaramin purse ta dauko ta sa wayarta tare da kuɗi naira dubu ɗaya,bata tsaya ɓata lokaci ba ta dauki Fauziyya dake barci ta sa ta a kafaɗa daga haka ta fita daga ɗakin
Kitchen ta wuce ta tadda Hafsah na ƙolla tuwa tana jera su cikin flask baki sake Hafsah ke kallon Amirah cike da mamaki ta ce ''fita za ki yi?" Amirah ta ce ''eh yanzu likita ya kirani gaba ɗaya na manta akwai allurar da za'a yiwa Fauziyya da sha ɗaya da rabi kinga yanzu sha ɗaya da talatin da takwas shi ne ya kirani yanzu kan allurar'' Hafsah bata kawo komai ba ta ce ''Allah sarki Allah ya ƙara lafiya Fauziyya'' ta faɗa tana leƙin fuskar Fauziyya dake kafaɗar Amirah,Amirah ta ce ''ameen'' tare suka ƙarasa kwashe tuwon Amirah sai faman sauri take ita dole zata kai yarinya allura haka ta tisa ƙiyar Hafsah tare suka fita Allah ya taimaka sun sami abin hawa lokaci ɗaya, Amirah ce ta fara shiga adaidaita bata ko tsaya sun yi ciniki ba ta cewa Hafsah ''nagode sosai Allah ya bar zumunci'' Hafsah ta amsa da ''ameen'' ta faɗa daidai lokacin da ta shiga adaidaita da ta tsare,adaidaitan Amirah ne ya fara yin gaba na Hafsah na biye da shi Amirah ta faɗawa mai adaidaita sunan asibitin da Fauziyya ta kwanta ta ce ya kaita can,bayan sun yi nisa Amirah ta cewa mai adaidaita ya mayar da ita gida ta yi mantuwa,bayan ya mayar da ita ta tambaye da kuɗinsa ya ce dubu ɗaya,dubu ɗaya dake cikin purse ɗinta ta cire ta miƙa masa,bayan shigar Amirah ta kwantar da Fauziyya cikin ɗakinta daman wankin tiolet ya rage mata cikin ayyukan gidan,da bathroom ɗinta ta fara kafin ta wuce na Ɗalha daga nan ta wanke na yara,bayan ta gama wanke bathroom ɗin duƙa wanka ta sake yi kafin ta dauro alwala lokacin ana kiran sallar azahar bayan ta idar da sallah ne Fauziyya ta farka daga bacci,Amirah ta dauki a ƙalla mintina ashirin wajen ba Fauziyya abinci harda abinci babu zafi sam amma da zarar ya taɓa mata liɓe komai kankantarsa sai ta yi kuka saboda zafi,bayan Amirah ta gama ba ta abinci ta wanke mata baki ta bata ruwar madara ta sha,zama Amirah ta yi nan cikin babban parlour tana hutawa tun karfe huɗu da ta tashi yiwa yara shirin makaranta sai yanzu ta samu hutu,Amirah na nan zaune Rumaisa ta shigo parlour bakinta dauke da sallama Amirah ta amsa mata sallama tana bin ta da wani kallo ganin wasu mayan ledoji a hannunta gaban Amirah Rumaisa ta dire ledojin kafin ta samu waje nan ƙasan parlour ta zauna tana mayar da numfashi gorar ruwa faro dake gefen Amirah Rumaisa ta dauko ta buɗe ba tare da ɓata lokaci ba ta kai baki saida ruwar ya kusa ƙare kafin ta cire baki daga gorar tana mayar da numfashi ita dai Amirah sai bin Rumaisa take da ido,bayan wasu ƴan sakanni Rumaisa ta ja ledojin da ta shigo da su ta fara fidda galan galan ɗin magunguna kowanne cike da magani bayan ta gama ne ta mayar da dubanta ga Amirah tare da daukan ɗaya daga cikin galan ɗin ta ce ''wannan tsumin rake ne a firiji za ki sa baya son zafi'' wani galan ɗin ta kuma dauka ta ce ''wannan kuma tsumin kananfari shima ki sa a firiji,sai wannan ai kin sa shi aiy tabaje ne,ga kuma wannan La shakkah ko shekara zai yi baya lalacewa,sai kuma wannan tsumi ne na kayan itatuwa ki sa shi a firiji,duk za ki iya ƙara masu madara da zuma in kuma baza ki iya ba sai ki sha su haka'' wani ledar Rumaisa ta buɗe ta fidda wata farar roba cike da gumba tare da wani garin magani sai sabulun tsarki ta ajiye su gaban Amirah kafin ta mayar da dubanta ga Amirah ta ce '' wannan gumba ce ita kuma wannan garin ci da kaza ne ko kifi ko nama,sai sabulun tsarki dan Allah ki dauri ki yi amfani da su,dan ba ƙaramin ƙudi na kashe ba''
SHUUKRAN