MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 26

by @maimunabala209

MATAR GIDA 026



SHUUKRAN/022





P26






Wata karamar leda Rumaisa ta fitar daga jakarta ta hannu ta miƙawa Amirah ta ce ''wannan turaren wuta ne yana da kyau sosai sai tsada shi yasa na ba ki kaɗan in kin ji dadin sa sai ki yi min magana nasa matar ta kawo maki''Amirah ta hannu ta karɓar tana sauki ajiyar zuciya ta ce ''insha Allahu zan yi amfani da su nagode Allah ya saka da alkairi'' Rumaisa ta ce ''Ameen aiy yiwa kai ne'' yunƙurawa Amirah ta yi ta tashi tsaye tana faɗin ''bari na sa maki abinci'' Rumaisa ta ce ''me ki ka dafa?" Amirah ta bata amsa a takaici ta ce ''tuwo miyar kuka'' Rumaisa ta ƙada kai tare da faɗin ''a'a wallahi bazan ci tuwo ba ki dafa min indomie ina dalili'' Amirah ta yi murmushi tare da faɗin ''an gama ranki shi dade'' bayan Amirah ta gama dafawa Rumaisa indomie ne ta kwashi magungunan ta wuce pantry da su,gaba ɗaya tsumin ta zuba su cikin deep frizer dake cikin pantry wanda bata cika amfani da shi ba,namar rago ne da kifi sai kuma kaza cikin freezer,Amirah ta zuba magunguna gefi guda cikin freezer  daga haka ta wuce ɗakinta ta buɗe saif ta zuba gumba da garin magani tare da sabulan tsarki da turaren wuta daga haka ta rufe ƙofar saif ɗin ta koma parlour wajen Rumaisa sun cigaba da hira, Unaisa ce zaune kan kujerar turaren tsuguno inda Aisha ta lulluɓa ta da wata mayafi mai girma, hayaƙin turaren ya cika ɗakin,Unaisa ta dauki sama da mintina goma zaune kan kujerar bayan turaren ya gama ƙonewa ne Aisha ta dauki wata doguwar riga shara shara ta miƙawa Unaisa karɓar rigar Unaisa ta yi ta zura tana nan zaune kan kujerar bayan ta gama sa rigar ne Aisha ta cire mayafin tare da miƙawa Unaisa wata ƙwaryar cike da madarar nono danya karɓa kwaryar Unaisa ta yi Aisha ta ce shanye babu musu Unaisa ta kafa baki ta shanye madarar tas karɓar kwaryar Aisha ta yi ta fita daga ɗakin bayan wasu ƴan mintina Aisha ta dawo ɗakin Anty Lantana na biye da ita Aisha na riƙe da wata tire dauki da kofuna biyar kowanne kofi da kalar magani dake ciki waje Aisha ta samu ta ajiye tire ɗin yayinda Anty Lantana ta dauki wani kwaɓin magani ta fara shafawa Unaisa a suma,ko kaɗan Unaisa bata son maganin da ake shafa mata a kai sam warin maganin bai yi mata ba yau kimanin sati uku kenan ake mata amfani da maganin amma har yanzu ta ƙasa saba da shi,Anty Lantana ta dauki a ƙalla mintina talatin tana shafe sumar Unaisa da maganin kafin daga bisani ta wanke mata sumar da wata ruwar saiwar magunguna,bayan Anty Lantana ta gama wanke mata suma ne Aisha ta haɗo mata ruwan wanka da ya sha haɗin turaruka iri daban daban,bayan Unaisa ta fita daga wanka ta shafe jikinta da wata kwalacca mai khamshi,Unaisa na shirin barin ɗakin ne Aisha ta sa ta gaba saida ta shanye waɗacan magunguna da ta shigo da su ɗazu a tire,gaba ɗaya Unaisa ta gaji da wannan shaye shayen hakan yasa ta ce ''wai ni yayah yaushi zan gama shan magungunan nan gobe ne fa auren,sai nake gani kamar ya isa haka sama da sati huɗu ana abu ɗaya'' taɓe baki Aisha ta yi bata ce mata komai ba ta fita daga ɗakin















Karfe biyar na yamma kofar gidan Mallam Sa'adu mahaifin Unaisa cike yake fam da jama'a yan walima,an ƙawata wajen walimar da decoration mai kyau da tsari yadda a aka jera kujeru da kanopi amarya ta sha ƙwalliya ta yi kyau sosai,sai kamshi take kamar shagon turare,wajen ya yi shiru baka jin motsin komai sai muryar Malama Khadijah dake wa'azi cikin sipika,kowa ya nitsu yana sauraron wa'azi banda Unaisa da hankalinta na kan wayar hannuta tana charting tana murmushi ita kaɗai ƙawayenta su biyu yan islamiyyar su  dake zaune gefenta sai mamaki suke Yasmin ta kai bakinta daidai kunnen Unaisa ta fara magana cikin kwantar da murya inda ta ce ''ki yiwa Allah ki daina wannan charting walimar auren ki fa ake,dan Allah ki aji wayar haka'' idon Unaisa kan waya ta ce ''to Malama in na ƙi fa me za ki yi?" Yasmin ta taɓe baki tare da faɗin Allah ya ba ki hakuri'' cikin gatse Unaisa ta ce ''in ya bani ki kwace'' Yasmin ta ja bakinta ta yi shiru bata sake cewa komai Hindatu dake zaune gefen Yasmin ta ce ''sai da na ce maki kar ki mata magana amma kin ƙi ji,to ga irinta nan aiy'' Yasmin bata komai ba Hindatu ta daura da ''Allah ya sani ban yi niyyar zuwa ba ki kika nace mana sai munzo,tun shekaran jiya fa muke sintirin zuwa bikinta amma sai wulaƙanci take mana iri-iri,nai dai banga wasu ƙawayenta ba bayan mu amma ki duba ki ga irin wulaƙanci da take mana'' Yasmin ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce ''daga gobe aiy shikenan daga gobe baza ta ƙara ganinmu a gidansu ba'' Hindatu ta taɓe baki tare da faɗin ''ke dai za ki zo gobe ni dai na gama zuwa daga yau'' bayan tashi a walima Unaisa bata ko bi ta kan su Yasmin ba karshe Aisha ce ta sama masu abubuwa da aka raba wajen walima daga haka sun yiwa Aisha da Mama sallama suna shirin barin gidan ne Yasmin ta cewa Hindatu suje su sallami Unaisa tunda baza su samu daman zuwa gobe ba,Hindatu ta ce baza ta sallami Unaisa ba saidai Yasmin ta tafi ita kaɗai babu yadda Yasmin bata yi ba amma fir Hindatu ta ƙi hakan yasa Yasmin ta je ta sallame Unaisa ita kaɗai Yasmin na shirin barin ɗakin ne Unaisa ta jefo mata tambaya inda ta ce ''za ki je Kano kai amarya gobe?" fuskar Yasmin dauke da murmushi ta ce ''a'a baza a bari ba a gida'' Unaisa ta kalle Yasmin yayin da take cire doguwar rigar jikinta ta ce ''oky hakan ya yi daman so nake na ce maki ku yi zaman ku saboda ba lallai ku samu waje ba da mota biyu za'a tafi'' Yasmin ta yi murmushin da bai kai ciki ba ta ce ''masha Allah,Allah ya bada zama lafiya'' Unaisa ta amsa da ''Ameen'' tana kwance sumanta Yasmin ta sa kai ta fita daga ɗakin,bayan fitar Yasmin ta fadawa Hindatu yadda suka yi da Unaisa sosai ran Hindatu ya ɓaci ta yi ta masifah har sun samu abin hawa kowacce ta tafi gida 















Bayan tafiyar Yasmin gida tsabar ɓacin ta ƙasa danna zuciyarta nan ta shiga bawa Rumaisa labarin irin wulaƙanci da Unaisa ta yi masu,dake Rumaisa bata san Unaisa ce amaryar Ɗalha ba bata dauki maganar Yasmin da muhimmaci ba kawai ta bawa Yasmin hakuri ta ce sun yi daidai da suka ce baza su tafi gobe ba,karfe takwas na dare Amirah ce kwance cikin ɗakinta ta kashe gaba wutan ɗakin ya rige iya dim ligth,tana nan kwance Ɗalha ya shigo ɗakin bakinsa dauke da sallama Amirah ta yi shiru kamar mai bacci alhali idonta biyu a hankali ya tako ya shiga ɗakin nan bakin bed ya zauna ya kafe fuskarta da ido a hankali ya shiga kiran sunanta sarai Amirah na jinsa amma ta yi masa banza Ɗalha ya cigaba da kiran sunanta,ganin baida niyyar daina kiran yasa Amirah buɗe ido a hankali,har sannan idonsa a kanta ya miƙo mata wata doguwa farar takarda mai dauke da rubutun larabci wasu ayoyi ne ciki,a hankali Amirah ta tashi zaune ta sa hannu ta karɓi takardar tana bin rubutun cikin da ido cikin kwantar da murya Ɗalha ya ce ''addu'ar da liman ya bani ne,na su Sudais kowanne za ki ga an rubutu suna'' idon Amirah na kan takardar ta ce ''eh na gani Allah ya saka da alkairi'' ta faɗa tare da naɗe takardar ta buɗe bed side drower ta sa takardar bayan ta ajiye takardar ne tana shirin kwanciya duk wani motsin da take idon Ɗalha a kanta daidai lokacin da ta kwanta ne Ɗalha ya ce ''insha Allah gobe daga wajen daurin aure zan wuce Kano ko da akwai abinda kuke buƙata?" ajiyar zuciya Amirah ta sauke kafin ta ce ''babu komai inda akwai zan faɗa maka ko a waya ne'' ta kare magana tare da ƙirƙirar murmushi da iyakar sa baki wani irin nitsuwa hade da kwanciyar hankali ne ya ziyarci Ɗalha ganin murmushi fuskar Amirah hakan yasa ya gyara zama kan bed tare da janyo Amirah jikinsa ya kai bakinsa daidai kunnen ta ya ce ''nagode Allah ya yi maki albarka'' Amirah ta yi shiru bata ce masa komai ba a hankali ya kai hannusa cikin rigar bacci dake jikinta ya dauki lokaci a haka kafin daga bisani ya kwantar da ita kan gado ganin yana niman wuce gona da iri yasa Amirah saurin dakatar dashi ta hanyar riƙe masa hannu murya can ƙasa ta ce ''l'm on my period'' da mamaki Ɗalha ke kallon fuskarta da idonsa da suka fara canza launi da kyar ya iya furta ''sati uku da yaye Fauziyya shine jinin ya dawo? Amirah ta yi shiru bata ce masa komai ba Ɗalha ya daura da ''ba yanzu ya kamata ya dawo ba sai nan da watanni huɗu kamar yadda ya saba zuwa'' Amirah ta ce ''ya canza lokaci'' jiki babu kwari Ɗalha ya sauka daga kan bed ɗin ya wuce ɗakinsa,washe gari  karfe sha ɗaya daidai na safiyar asabar aka daura auren Unaisa da Ɗalha kan sadaki Naira dubu ɗari biyu daidai,sosai gidan Mallam Sa'adu ya cika da jama'a ƴan biki kowa ka gani za ka ga farin ciki shimfiɗe fuskarsa,amarya ta sha kyau har ta gode Allah bayan daura aure Ɗalha ya shigo tare da Muhsin da sauran abokansu aka sha hotuna,ana shirin kai amarya gidanta wasu motoci biyu na alfarma suka yi fakin kofar gidan Mallam Sa'adu wasu mata ne cikin motar kowacce cikin shiga ta alfarma,suturar jikinsu masu tsada ne sosai ga gwala-gwalai a kun uwansu da wuyar su,wata babbar mace ce mai kimanin shekaru hamsin ta fito daga mota yadda sauran matan na biye da ita gaba ɗaya mutanen dake wajen hankalinsu ya koma kan wa'inan matan kowa sai binsu yake da ido cike da mamaki,daga cikin ƴan biki ne wata ta yi magana inda ta yi magana cike da tsantsan mamaki ta ce ''Matan Gida? me ya haɗa Unaisa da Matan Gida?" ''innalillahi wa inna ilaihi raji'un'' Matan Gida wata kungiya ce da Hajiya Bilkisu ta kafa da sunan taimakon mata da tallafa masu da kuma wayar da kansu kamar yadda take faɗa saidai wannan kungiya kungiya ce da ta shahara wajen kashewa mata aure,kungiya ce da matan ciki ke cike da burika ƙala kala so suke su zama tauraro duk inda suka shiga ya zama su ake ji kuma su ake gani so suke su fi kowa hakan yasa kullum cikin canza motar hawa da sutura suke,duk bayan watanni shidda suke canza furniture ɗin gidansu wasu daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne wasu kuma ƴan kasuwa wasun su kuma ƴan zaman jiran miji ne,duk sanda matar kungiya ta tashi canza mota ko kayan furniture gaba ɗaya kudaɗenta take haɗawa ciki harda bashi kuɗaɗen mutane,wannan dalilin yasa zaka ga ana bin mace bashin miliyan uku miliyan hudu,da yawa daga cikinsu daga mai aure uku sai mai aure hudu wasu kuma zaurawa ne,gaba ɗaya matan ƙungiyar ƴaƴan talakawa ne wanda basu dauki rayuwa da sauƙi ba









SHUUKRAN