DUHU BAYAN MURMUSHI

1

by @rahmakabir13

*DUHU BAYAN MURMUSHI*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 1.

Sarac Stars R Pen...✍️

MARUBUCIYAR...
'Yar Shugaba. / Mai Hakuri.
Dan amana. / So sanadi.
Kadaici. / Baki shike yanka wuya.
Hantsi. / So sartse.
Da wata a kasa. / Ƙarshen makirci.
Ƙaddararren Al'amari. / Akan idona.
Ƙazamin tabo / Rayuwar suhailat.
Lubabatu. / Zamani.
Gashin ƙuma. / Alhaki.
Abun da ciwo. / Kazamar amarya.
Amaryar Zayyad. / Ƙangin talauci.
Mijin aro. / So da Manufa.
Komai yayi farko. / Bayan Aure. 

Gargaɗi

*Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a bar mini sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

MUJAHEED.

Da gudu ya faɗo cikin gidansu ya tsaya daga jikin bango yana haki tare da ɓoye hannunsa a baya, sai ya shiga zare ido yana harare-harare, yanayinsa gabaɗaya a zabure yake tamkar da an taɓa shi zai ari na kare ya ruga a guje. Daga can ƙofar gida kuma ihun yara ne suna ta hayaniya wanda jin haka yasa mama fitowa daga ɗaki, amma sai ta tsaya turus sa'ilin data ga Mujaheed a tsorace tare da karewa yanayinsa kallo, ta riƙe haɓa da niyyar yi masa magana sai ga wani matashin yaro ya faɗo gidan babu ko sallama yana tare da wasu yara su uku da suke biye da shi, ya tsaya yana cewa mama.

Ki faɗa masa ya bamu burodin da ya sata yanzu a shagon babanmu.

Innaillahi wa inna ilaihi raji'un.! sata kuma.? Mujaheed muga hannunka.

Mama tayi maganar cikin mamaki tare da ɗaure fuska alamar babu wasa a lamarinta, sai Mujaheed ya ƙara yin baya da hannunsa yana sunne kai ƙasa fuskarsa fayau mai cike da tsoro da kuma ruɗani, domin a takaice ma bai gama sanin me ya aikata ba shi dai yasan burodin ya bashi sha'awa ne shiyasa ya ɗauka. Ganin ba yi da niyyar bayarwa sai Mama ta sausauta murya tace cikin yanayin tausayi. 

Mujaheed ka basu mana, idan yunwa kake ji sai na haɗa maka custard kasha kafin na kammala girki. 

Mujaheed ya turo baki sannan ya shiga ja da baya idanunsa suna kawo ruwan kwalla yana girgiza kai alamar ba zai bada ba.

Yanzu Mujaheed menene ribar abunda ka aikata.? Bayan kuma ina iya ƙoƙarina akan ka, mu muna yi maka kallon mara wayo ashe kasan me kake yi tunda har tunanin ka ya baka ka ɗauki abunda ba naka ba, zaka bada burodin ko sai na saɓa maka. Ka basu na ce.!

Ta ƙare maganar a fusace kamar zata rufe shi da duka wanda hakan ya ƙara tsananta tsoronsa, sai ya jefar da burodin a ƙasa yana ƙara nutsar da kansa baya son haɗa ido da kowa kuma ba um ba um-um, mama tayi kwafa ta cewa wannan matashin ya ɗauki burodin tare da basu haƙuri, ba musu ya ɗauka sai dai yadda yaga burodin ya laƙume ya saka shi cewa cikin ɓacin rai. 

Gaskiya baaba, ya lalata burodin, ji yadda yayi masa kamar an matse gwangwani. a biya mu kuɗinsa kawai.

Haba ɗan nan, baka ganin Muhajeed bayi da cikakken Lafiya, kuyi haƙuri mana.

Haba dai, haƙuri kuma.?

Matashin ya faɗa tare da yin wasu ƙananun maganganu da mama bata ji me yake cewa ba yana turo baki.

Rashin kunya zaka yi min akan burodin ɗari biyar.?

To a biyamu mana kawai sai mu tafi, dan ba zamu ɗauki asara ba yasin.

Yaron ya faɗa cikin gatsali yana cije-cije, Mama bata sake magana ba ganin in ta cigaba da jan maganar yaron zai iya zaginta dan yanayinsa a tsaitsaiye yake, sai ta koma ɗaki ta dauko kuɗin ta dawo ta miƙa masa ya amsa yana juya kuɗin. 

Aha baaba ai gwara da kika biya dan asara kota kobo ce ba tada daɗi.

Ya ƙare maganar yana aje burodin a ƙasa ya tasa kan yaran da suka shigo suka fice cikin sauri, sai a lokacin mama ta juyo gurin Mujaheed fuska a dagule.

Amma Fisabilillahi Mujaheed yau da burodin muka karya ba, ban san meya baka sha'awar ɗaukar na mutane ba, gashi ka saka nayi asarar ɗari biyar a banza, to tabbas kaci bashi dan sai na faɗawa babanku yayi wa tufkar hanci. Haba.! ka barmu mu ji da lalurar da kake fama da ita mana, kar ka zo ka rakito mana wata damuwar, ai sai abun yayi maka yawa ga hauka ga sata.

Ta ƙare maganar kamar zata zub da kwalla kafin ta koma ɗaki rai babu daɗi, Mujaheed ya yi kamar zai fashe da kuka kansa yana ƙara sara masa, ya daɗe a gurin yana saƙar zuci wanda shi kanshi ya rasa me ya kai zuciyarsa ɗaukar abunda yasan ba nashi bane, yasan yana jin yunwa amma bai kai irin wacce zata yi masa lahani ba, jiki a sanyaye ya duƙa ya ɗauki burodin ya wuce ɗankinsa da yake farkon shigowa gidan ya tura ƙofa ya shiga ciki ya zauna a ƙasa ya tankwashe ƙafa, ɗakin nasa wani irin warin datti yake yi da hamamin balaga, sai dai shi baya jin warin kwata-kwata domin ya saba da shi dan tamkar ƙamshi ne a gurinsa. Ɗakin falle ɗaya ne babu bayi a ciki sai katifa da take shimfiɗe a ƙasa ga kuma shirgin kayansa da suke zube a ƙasa duk da akwai akwati da gana mazgo amma sun koma empty babu komai a cikinsa ya gama fitar dasu, kasantuwar bayi da cikakken hankali a tare da shi balle ya gyara ɗakin, baya iya yin wanka da wanki haka yake rayuwa cikin ƙazanta, sai in warin ɗakin ya fara fitowa tsakar gida shi ne Mama take faɗawa baba sai a saka almajirai su shiga ɗakin su gyara masa tare da yi masa wanki a biya su, gashi da girmansa ma bai daina fitsarin kwance ba saboda tun yana ƙarami bayi da control akansa, cikin dare in ya kama shi sai ya kasa fitowa saboda tsoro shiyasa yake sakinsa a inda ya kwanta dan so tari ji yake kamar mafarki ne, sai gari ya waye yake tabbatar da cewar da gaske yayi fitsari a zahiri, duk da yasan haka amma ba shi ne zai sa ya gyara jikinsa ko ɗakin ba, yafi gane ya yi ta yawo da wannan kayan a jikinsa sam bai damu ba. 

Bayan ya zauna a tiles sai ya yaga ledar burodin ya soma ci yana ƙuzan masa wuya, bai damu ba dan yadda yake ci tamkar cikin matsananin yunwa yake, a haka ya cinye tas kafin ya tuna da ruwa ya miƙe ya fito. Har lokacin ba kowa a tsakar gidan dan Ƙannensa suna makarantar Islamiyya, ya shiga kitchen da yake nan tsakar gida ya buɗe fridge, sai yaga mama ta yi zaɓo har yayi sanyi sosai, ya saki guntun murmushi kafin ya ɗauki gora ɗaya ya buɗe ya shanye tas, sai ya aje mata gorar a ƙasa ya ɗauki pure water ya fita zuwa zaure, anan ƙasa ya samu guri ya zauna ya buɗe ruwan yana sha a hankali saboda yana da sanyi sosai, kiran sallar La'asar daga masallacin kusa dasu shi ne ya saka shi yin tsam ya miƙe tare da lumshe ido ya buɗe domin abu na farko da ya ke faranta zuciyarsa shi ne Sallah, saboda tun yana ɗan shekara biyu mamansu ta fara koya masa yin sallah a duk sadda zata gabatar da farali, har kawo lokacin da ya yi wayo tana tunatar dashi Sallah shi ne farkon aikin da za a fara dubawa a cikin aikin mutum a ranar Lahira, sannan Sallah tana hana alfasha da abun ƙi, duk mai yin sallah da kyau zai kasance cikin nagartattun mutane, ire iren wannan bayanin yasa Muhajeed bai wasa da Sallah duk kuwa da halin da yake ciki na rashin wadataccen lafiyar kwakwalwa, tabbas karatun yaro ƙarami tamkar Rubutu ne akan dutse shiyasa Mujaheed ya kasa mance abubuwan da suka faru a lokatan ƙuruciyarsa wanda ya gudanar da mafi soyuwa a gareshi mahaifiyarsa, sai ya tuna da lokacin da ta taɓa ce masa. 

Dan Abbansa idan ka tafi masallaci banda wasa ka tsaya kayi Sallah mai kyau, kaga duk mai wasa da Sallah to Allah zai ƙona shi a wuta, kayi sauri ka dawo zan baka naira biyar ka siyo alawar madara. 

Sai ya saki yalwataccen murmushi wanda yake bayyana tsantsar kyawunsa dan duk abunda zai tuna na yarinyarsa da mamansu yana saka shi farin ciki, daga bisani kuma ya haɗe fuska kamar baƙin hadari, kabbarar da Liman ya tayar shi ne ya saka shi zabura ya fita cikin sauri kwakwalwarta tana gaya masa kar ya rasa jam'i, sai dai koda ya kama hanya ya manta shaf da satar da ya yi ɗazun kuma dama yaran layin suna ta dakonsa ya fito, nan take wasu suka shiga yi masa ihu da sha tara ya zama ɓarawo, sai ya tsaya ya dafe kunnensa yana runtse ido jikinsa ya shiga rawa, daga bisani ya ja jikinsa ya raɓe a jikin bango, wani yaro ya ɗauko dutse da niyyar zai buga masa yana cewa.

Ya sunansa.? Sha tara, sunan Mujaheed sha tara ɓarawon biredi.

Kai dan babanka idan ka buga masa dutse sai dai uwarka ta haifi wani, wannan halittar meya sani.? Yaron da ba shi da lafiya, to yasin ku ware a gurin nan kafin in baza yaro a ƙasa.

Cewar wani dan shaye-shaye da yayo kan yaran, wanda tuni suka dare kowa ya ari na kare, hakan yasa Mujaheed shima ya tsorata ya ruga da gudu yana kama kansa, sai da yayi nisa kafin ya tsaya da gudun ya isa gefen wani gida ya zauna yana takurewa guri ɗaya ya saka hannunsa a tsakanin cinyoyinsa tamkar mai jin sanyi, kabbarar Liman shi ne ya saka shi miƙewa da sauri wanda nan take ya tuna da asalin abunda ya fito da shi daga gida wato masallaci zai je, sai ya tsaya yana duba tsakaninsa da masallacin babu nisa, dan haka cikin sassarfa ya fara tafiya sai dai a tsoroce yake dan kar mutane su hantare shi, dan ya fahimci sam ba yi da farin jini a gurin mutane abu kaɗan zai yi su fara kyararsa suna zaginsa da Sha tara, shi dai ya san bayi da damuwa da duk yadda yake rayuwa yana jin daɗin kansa a haka saboda baya son mu'amala da kowa kwata-kwata domin suna yi masa kallon mara amfani, shiyasa a koda yaushe yake jaye jikinsa ga shiga jama'a dan kar ya ɓatawa kowa rai. Kuma wannan hantarar da mutane ke yi masa shi ke ƙara susuta masa kwakwalwa yake ƙara saka matsa tsananin tsoro. A wannan yanayin ya isa masallaci ya wuce famfo ya buɗe ya zauna ya soma alwala wanda ko za a ci shi gyara kaɗan ne, sannan da ya kammala alwalar nan take yaji iska mai sanyi yana tsara ƙofofin gashin jikinsa inda ya jika da ruwa, wannan ya saka shi sakin murmushi da jin daɗin yanayin, sai ya wuce cikin azama zai shiga masallaci fuskarsa ɗauke da annuri, amma yana saka ƙafa yaji an daka masa tsawa daga bayansa.

Kai sha tara maza fita, ai masallaci ba wajen wasa bane, idan kana so ka yi sallah to ka koma gida kayi wanka ka sauya kaya sai ka zo kayi.

Cewar wani Dattijo daya shigo cikin sauri, Mujaheed tuni ya ƙanƙame jikinsa tsoro ya bayyana a cikin kwayar idanunsa ya juya da sauri ya bar masallacin kamar zai kifa, ya tsaya daga wajen masallacin yana leƙen mutumin ko ya biyo shi amma ganin bai ganshi ba, sai hakan ya bashi damar komawa harabar masallacin ya kalli gabas ya shiga yin Sallah yana bin Liman har aka idar kana yayi sallama ya miƙe ya fito da sauri, daga nan ya miƙa hanya yana cin ƙumbar hannunsa da suka yi zara-zara da tarin datti a ciki.

Bayan mutane sun fito daga masallacin Malam Bashir ya miƙawa wannan Dattijon hannu suka yi musabaha yana cewa.

Baba ɗazun na shigo naji kana korar wannan yaron mara lafiya, ai da ka kyale shi kayi masa uzuri tunda ga yanayinsa, dan an gode Allah ma tunda har kwakwalwarsa tana tunatar da shi yayi sallah, kuma a yanayinsa yana buƙatar a riƙa jansa a jiki ta hakane kwakwalwarsa zai riƙa setuwa, amma kyara da hantara ƙara ruɗar da shi zai yi.

Malam Bashir banƙi ta taka ba amma ƙazantar dake jikin yaron yayi yawa, kuma haka ubansa ya zuba masa ido yana gararamba, sanan su kansu sun shaida bayi da lafiyar kwakwalwa balle mu mutanen unguwa.

To Allah ya kyauta.

Malam Bashir ya faɗa kafin ya fice daga masallacin cike da tausayin yaron, sai ya shiga yi masa fatan Allah ya bashi lafiya. Haka ya wuce babban Islamiyyar dake can saman titi wanda yake mallakinsa. 

A ɓangaren Mujaheed koda ya isa bakin titi karatun Alqur'anin da yaji ana yi shi ne ya saukar masa da farin ciki, sai ya soma bin hanyar da sautin karatun yake zuwa har ya cim ma ƙofar babbar makarantar Tarbiyyatul Islam da yake nan kan babban hanya, ya tsaya nesa da ƙofar shiga yayi shuru kamar mai nazari, yana so ya ƙarasa amma yana tsoron kar a yi masa ihu a koreshi, a haka malam Bashir ya ƙaraso kuma koda ya ga Mujaheed sai ya ƙarasa inda ya tsaya ya ɗaga hannu da niyyar dafashi amma sai Mujaheed ya ja da baya yana waro ido waje.

Karatu kake so.? 

Malam Bashir ya faɗa cikin yalwar murmushi a fuskarsa, Mujaheed ya gyaɗa masa kai cikin wannan zare idon wanda yake fal tsoro.

Zo muje ciki na koya maka.

Malam Bashir ya ƙare maganar yana miƙa hannu da niyyar kama nasa hannun, sai Mujaheed yaja baya yana girgiza kai daga bisani kuma ya juya cikin sauri ya fara tafiya yana yi yana waigensa, malam ya girgiza kai yana yi masa murmushi ya shige cikin makarantar, Mujaheed ya cigaba da tafiya har ya isa wajen wata mai sayar da abinci, yaje ya tsaya a ƙofar rumfar mai abinci yana taunar hannun rigarsa.

Kai.! ɓace min da gani kafin ka korar min customers, haba sai uban wari kake yi kana hamami.!

Ta ƙare maganar tana tsirtar da yawu, sum-sum Mujaheed ya yi gaba a zuciyarsa yana jin ba daɗi tare da jin kwaɗayin son cin abincin da mutanen rumfar ke ci, sai da ya yi nisa kafin ya soma tsince-tsince yana tarawa a cikin rigarsa, a haka har yayi nisan kiwo daga unguwarsu zuwa wata, sai da magariba tayi yaga gari ya fara duhu kafin tunaninsa ya dawo jikinsa ya juya dan ya koma gida cike da tsantsar damuwa, yanzu babban tashin hankalinsa shi ne kar duhu yayi bai koma gida ba saboda yana matuƙar tsoron duhun dare, sai dai a kullun tunaninsa baya hasko masa duhun daren har sai ya cim masa.

Mujaheed bai shigo gida ba sai wajen tara da mintuna na dare, dan ba ƙaramin nisa yayi da gida ba ga babu wutar lantarki gari yayi duhu, duk yadda yaso ya dawo gida akan kari ya kasa duba da fargabar daya cika masa zuciya da jin kamar wani zai cutar da shi a cikin ransa. Haka ya dawo da tarin kayan daya tsinto ya wuce ɗakinsa ya zubesu a tsakar ɗaki, ya saba kullun sai Aina'u ta kawo masa abun haske ɗakinsa dan tasan baya son duhu, ya zauna ya shiga ɗaukar abubuwan ɗaya bayan ɗaya, ciki har da karamar tocila daya kunna amma taƙi kawowa alamar ta lalace sannan ga wani a gogo da shima babu hannu a jikinsa kuma baya aiki, sai sauran kayan batirin Radio da tarkace, nan take ya shiga kurawa agogon ido ya buɗe bayansa ya shiga tattaɓawa yana nazarinsa, turo ƙofar da aka yi ya saka shi zabura ya ɓoye agogon a ƙarƙashin rigarsa yana waro ido ya juya yana duban ƙofar.

*Labari ne da ban taɓa rubuta irinsa ba, nayi ƙoƙarin duba rayuwar wasu da ake yi musu kallon marasa amfani, na shiga ciki dan na haskowa Al'umma cewar akwai wata ɓoyayyen abu a tare dasu. Sannan suma 'ya'yane wataƙila da za a tsaya a fuskanci halin da suke ciki da kyau tabbas za a iya magance matsalarsu domin ko wata cuta Allah ya saukar da maganinta. Dan haka ga rayuwar Mujaheed sai mu nutsa a ciki tare da ku dan jin yadda zata kaya.*

Alƙalamin Rahma Kabir.