FreeArewaPen original
DUHU BAYAN MURMUSHI
- 1views
- 29chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciyar littafin hausa
Sample · 1
*DUHU BAYAN MURMUSHI*Na©®Rahma Kabir MrsMG.Page 1.Sarac Stars R Pen...✍️MARUBUCIYAR...'Yar Shugaba. / Mai Hakuri.Dan amana. / So sanadi.Kadaici. / Baki shike yanka wuya.Hantsi. / So sartse.Da wata a kasa. / Ƙarshen makirci.Ƙaddararren Al'amari. / Akan idona.Ƙazamin tabo / Rayuwar suhailat.Lubabatu. / Zamani.Gashin ƙuma. / Alhaki.Abun da ciwo. / Kazamar amarya.Amaryar Zayyad. / Ƙangin talauci.Mijin aro. / So da Manufa.Komai yayi farko. / Bayan Aure. Gargaɗi*Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a bar mini sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye.**BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*MUJAHEED.Da gudu ya faɗo cikin gidansu ya tsaya daga jikin bango yana haki tare da ɓoye hannunsa a baya, sai ya shiga zare ido yana harare-harare, yanayinsa gabaɗaya a zabure yake tamkar da an taɓa shi zai ari na kare ya ruga a guje. Daga can ƙofar gida kuma ihun yara ne suna ta hayaniya wanda jin haka yasa mama fitowa daga ɗaki, amma sai ta tsaya turus sa'ilin data ga Mujaheed a tsorace tare da karewa yanayinsa kallo, ta riƙe haɓa da niyyar yi masa magana sai ga wani matashin yaro ya faɗo gidan babu ko sallama yana tare da wasu yara su uku da suke biye da shi, ya tsaya yana cewa mama.Ki faɗa masa ya bamu burodin da ya sata yanzu a shagon babanmu.Innaillahi wa inna ilaihi raji'un.! sata kuma.? Mujaheed muga hannunka.Mama tayi maganar cikin mamaki tare da ɗaure fuska alamar babu wasa a lamarinta, sai Mujaheed ya ƙara yin baya da hannunsa yana sunne kai ƙasa fuskarsa fayau mai cike da tsoro da kuma ruɗani, domin a takaice ma bai gama sanin me ya aikata ba shi dai yasan burodin ya bashi sha'awa ne shiyasa ya ɗauka. Ganin ba yi da niyyar bayarwa sai Mama ta sausauta murya tace cikin yanayin tausayi. Mujaheed ka basu mana, idan yunwa kake ji sai na haɗa maka custard kasha kafin na kammala girki. Mujaheed ya turo baki sannan ya shiga ja da baya idanunsa suna kawo ruwan kwalla yana girgiza kai alamar ba zai bada ba.Yanzu Mujaheed menene ribar abunda ka aikata.? Bayan kuma ina iya ƙoƙarina akan ka, mu muna yi maka kallon mara wayo ashe kasan me kake yi tunda har tunanin ka ya baka ka ɗauki abunda ba naka ba, zaka bada burodin ko sai na saɓa maka. Ka basu na ce.!Ta ƙare maganar a fusace kamar zata rufe shi da duka wanda hakan ya ƙara tsananta tsoronsa, sai ya jefar da burodin a ƙasa yana ƙara nutsar da kansa baya son haɗa ido da kowa kuma ba um ba um-um, mama tayi kwafa ta cewa wannan matashin ya ɗauki burodin tare da basu haƙuri, ba musu ya ɗauka sai dai yadda yaga burodin ya laƙume ya saka shi cewa cikin ɓacin rai. Gaskiya baaba, ya lalata burodin, ji ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.