Page 50
⚡MARYAM
50A⚡
Cikin kiftawar ido duk wadanda suka shiga daki da nufin daukar abin da suke bukata suka fito tsakar palon kowa ya rude, rumtse idanu Abdallah ya yi yana jin zuciyarshi na tseren gudu yayinda Maryama ta gama sake mashi gaba daya nauyinta wadda hakan ke tabbatar mishi cewa ta suma ne sakamakon karar harbin bindigar da taji....Sauran karfin da ya rage mishi ya tattaro da karfi jin karar harbin na kara tunkarosu yace, "HIDDEN ROOM".
Duk yaranshi dake wajen sun san abinda yake nufi dan haka a 160 suka durfafi inda ya fada din, John ne yayi karfin halin tsayawa yana fadin, "Oga kawota in karba maka kai kuma kaji da kanka".
Kai ya girgiza mashi idanunshi suna cigaba da rinewa, da idanu ya nuna mashi Chioma daata jike wandon jikinta da fitsari tsabar tsoratar da tayi,hannun Chioma John ya ja ya kwasa a guje shikuma Abdallah ya saba Maryama a kafada yana taune lebe da rufe idanu.
Wani dan corridor suka shige hadi da bude daya daga cikin dakuna biyun dake wajen, da sauri suka tura wani shirgegen wardrobe dake dakin, wajen sumul yake ko ina lufbace da tiles sai walkiya yake yi,bazaka taba tunanin cewa akwai wani abu a wajen ba, bisa mamaki na naga daya daga cikin yaran ya zaro wuka daga aljihunshi,tile daya ya saita da wukan sai gashi ya daga shi sama gefe ya mayar kana ya dago wani da haka saida ya cire tiles guda shida a wajen sai ga wani abu ya bayyana a wajen, da sauri sauri ya daga wani rami zururu ya bayyana torch light na wayarshi John ya kunna ya haska cikin sannan ya cewa Abdallah, "Jump oga", sanin irin hatsarin da suke ciki yasa shi mikawa John Maryama da har lokacin take kafadarshi ya kama bakin ramin ya shiga akwai wasu matattakala a ciki dan haka ya fara takawa saida yayi nisa sannan ya dakata John ya zuro Maryama Abdallah ya kama kafarta suka cigaba da tafiya har ya sauka cikin dakin karkashin kasar wanda ya kasance mai fadin gaske kamar dakin zahiri, sauran ma shigowa sukayi daya bayan daya harda Chioma, saida suka gama shiga sannan wannan da ya bude musu kofar ya mayar ya rufe rufff kamar yan adam basa cikin wajen wardrobe din ya tura ya koma daidai kana ya kwasa a guje ya shige bathroom, cikin sillin na bandakin ya shige sannan ya maida ta ciki ya rufe ya cigaba da nausawa can kololuwar sama.
Jami'an tsaron Dubai da suka samu red alert daga Singapore cewa wani mai safarar miyagun kwayoyi da yaranshi sun tsere daga gidan yarin birnin JAVA na kasar Singapore bayan watanni biyar da kamasu a can bisa zargin shigowa da hodar ibliss da sukayi da kuma sabawa dokar kasa da kasa,sunyi nasarar balla gidan yarin inda da dama daga fursunonin da suke ciki suka tsere anyi artabu dasu sosai har anjiwa wasu daga cikinsu rauni, sai dai tsabar shu'umanci irin na tantiran ba'ayi nasarar kamasu ba har suka shigo dubai, wannan ne ya sa jami'an tsaron dubai din suka kasance cikin shirin ko ta kwana da taimakon masu bincike na farar kaya suka gano gidan Abdallah....Abdallah da tun da suka shigo Dubai ta barauniyar hanya jikinshi ya bashi cewa something most happen yana shigowa ya samu yan matan nan da suka hana zuciyarshi sakewa da nutsuwa tunda aka kamasu wanda ya tabbata cune aka mishi kuma yasan wanda ya mashi din and bai barshi ba dole zai dau mummunan mataki a kanshi, tunda aka kamasu yake tunanin yaran bai samu nutsuwa ba saida suka kubuto suka dawo,yana shigowa ya same su kamar gawarwaki,umarnin daukar abinda suke bukata ya bayar kamar takardu, inda akayi rashin nasara suka fara jiyo karar harbe harbe dake nuna abin da suke gudun fa ya riskesu.
Duk wani bincike da aka san kwararrun yan sanda dashi jami'an sun gabatar amma wayam babu kowa cikin gidan sai tarin kayan da suka samu da su hodar iblis din kilo kilo da kuma bindigogi hade da kudade samfurin dalar amurka. tsawon awanni uku suna aiki a gidan amma basu samu kowa ba dan haka suka tattara abubuwan da suka samu suka koma headquarter bayan sun sanyawa gidan tsaro sosai hadi da zagayeshi da siririn igiya irin na jami'an tsaro wadda ke alamta akwai matsala kenan a gidan.
Rumtse idanu Abdallah yayi da masifan karfi lokacinda John ya yi nasarar kwakulo bullet din dake makale jikinshi da wani dogon karfe mai kama da wuka, a dai dai lokacin ne kuma na farka ido na zaro duk da juyawar da kaina ke yi hakan bai hanani ganin komai da suka aikata ba,damtsen hannunshi ya kuma kamowa ya zura wannan karfe ya kwakulo wani bullet din fiit ya fito waje jini ya biyo bayanshi, kasa jurewa na yi wannan karon na bude bakina iya karfina na saka wani irin kara mai karfin amo.Saidai amon karar bata fita ba sakamakon matse bakina da Chioma ta yi da iya karfinta tana girgiza min kai.
Dressing na wajen John ya yiwa Abdallah sannan ya taimaka mishi zuwa kan dan gadon dake dakin ya kwanta yana jin azaba yana ratsashi, amma kasancewarshi jarumi bazaka taba fahimtar hakan a fuskarshi ba, babban damuwarshi ma shine yasan matukar wadannan jami'an tsaro suka yi nasarar gano inda yayi ajiyar kayanshi to tabbas zasu karya mishi tattalin arzikin da zai iya kara shekaru talatin gaba bai farfado ba,addu'a kawai yake a ranshi na fatan kar Allah ya basu nasara, saidai kash addu'ar Abdallah bata karbu ba,dan a dai dai lokacin da yake wannan addu'ar a lokacinne kuma yan sandan suka yi nasarar fitar da kayan nashi daga dakin ajiyarsu suka tafi dashi...
Wasa wasa muna a dakin nan mai cike da abun tsoro da firgici,babu sallah babu salati har dare ya raba tsakiya, sannan kowa ya mike kamar yadda John ya bada umarni,duk yadda aka so Maryama ta tashi kasawa tayi dan gaba daya babu wani sauran karfi a tattare da ita.Daga sama muka jiyo ana kokarin bude wajen sannan aka dallaro toci, gabriel ne wanda ya shiga silin da hanzari yace, "Ku muzo mu wuce".
Chioma ce ta fara taka matakalar ta fice kana biyu daga cikin yaran suma suka fito, da kyar Abdallah ya tashi yana dingishi ya dokawa John wanda ke kokarin dagani harara,tare da kama hannuna muka fara takowa dukkaninmu muna galabaice,baya baya John ya koma gami da bude wani dirowa ya dauki pistol gun guda uku ya gyara masu saiti sannan ya hauro shima raba musu bindigun yayi daddaya su uku sannan muka fita daga dakin a hankali.
Zuwa yanzu na yi nadamar zuwata Dubai yafi sau cikin carbi, tun ina kuka da hawaye har hawayena suka bushe suka kare tas,shin haka masu zuwa wasu kasashe neman kudi ke shiga gararin rayuwa?ko dai ni kadai ce kaddarata tazo a haka?wayyo innarmu wayyo hamma jay kuzo ku ceceni!".
Kamar yadda kuka san ginin gidajen larabawa suna dauke da doggin katanga to haka muka tsallaka katangar ta baya gaba dayanmu bayan mun yi nasarar fitowa daga gidan, hanya muka dauka cikin sanda kamar barayi muka fara bin jikin gini nidai binsu kawai nake yi, tabbas badon hannun Abdallah dake rike da tawa hannun ba, da tuni na kai kasa.
"Freeze". Muka ji an fada da karfi daga bayanmu, kana muka ji alamar an ja kunamar bindiga.
A take su Abdallah suka rikice yayinda suka fara kokarin zaro nasu bindigar dake makale a aljihun wandunansu, suka fara artabu da wadannan yan sanda da aka barwa gadin gidan su biyu, bahaushe yace sarkin yawa yafi sarkin karfi, su Abdallah sunyi nasara akan yan sandan inda muka cigaba da gudu, a lokacin inda za'a tsaga jikina na tabbata baza'a samu kk digon jini ba,muna tsaka da gudun ceton rai muka jiyo ihun Chioma da karfin gaske saura kadan ta kai kasa John ya dagata ya saba a kafada kasancewar shi shima jibgegen mutum.
Da taimakon Allah muka bar anguwar da kowa ya kasa lekowa saboda tsaro. Sosai muka yi tafiya ga dare har wani hadadden anguwa wadda yafi na farko haduwa da tsari, anguwace mai kama da aljannar duniya babu ce kawai babu a anguwar. Cikin daya daga gidajen alfarma dake jere reras aka yi knocking a hankali mai gadi ya leko sai da ya gama kare mana kallo sannan ya bude kofar muka shiga, a tsararren palon gidan john ya shimfide Chioma wacce ta zama gawa tuni dan wani harbi ne ya sameta a tsakar kai tana tsaka da gudu. "Oga ta mutu fa" John ya fada yana kallon Abdallah, kamar a mafarki haka naji maganar wani irin sanyi ne ya fara ratsani daga kan babbar yatsar kafata zuwa tsakar kaina luuu na tafi baya na fadi sumammiya..............wai nikam sau nawa Maryama zata suma ne?haba baki da jarumta kuma kika zabi shiga duniya?.
Sannu kan hankali rayuwa ke kara tafiya a sabon gidan da muka koma, tun daga lokacin kuma su abdallah basu kara fita ba duk abin da suke so sai dai a kawo masu har gida wanda hakan ke nuna min cewa lallai suna da wani uban gida babba kenan, ban san ya suka yi da gawar Chioma ba na dai farka na ganni ana min karin ruwa tun daga lokacin kuma ban kara ganinta ba, likita na musamman ke zuwa duba Abdallah da mishi treating na ciwukan da yaji, nayi kuka, na yi nadama na yi istigfari har ban san iya adadin su ba, a haka muka kara kwashe wasu wattani hudu, yau ina zaune bansan yaushe su Abdallah suka fita ba sai ganinsu nayi sun fado palon wani dan karamin jaka ya mika min na bude paspo dina ne a ciki sai tarkacen su atm da ipad da kuma karamar wayata duka dama a waccan gida na barsu, jaye da akwatuna wani daban da ban sanshi cikin yaran abdallah ba ya shigo yana dire su a gabana, kayayyakin sawarmu ne nida Chioma da muka barsu a wancan gidan wasu kuka ne suka kwace min tunawa da nayi da ita, shikenan ta mutu a banza, ba tare da tayi achieving abin da ya fitar da ita daga gaban iyayenta ba, sosai na yi kuka babu wanda ya ce min ko uffan, Abdallah ma abin da ya dameshi daban, yanzu bashi da kudi gaba daya arzikin da ya ke dashi an kwashe, yanzu ya samu wani kaya amma babu yadda za'ayi ya fitar dan gaba daya system na na jami'an tsaro na duniya akwai hotonshi a ciki, wanted ake nemanshi babu yadda za'ayi ya fitar da kaya yanzu ba tare da an kamashi ba.
"Wane amfani yarinyar nan ke maka ne a yanzu?"zuciyar Abdallah ta tambayeshi a yayinda yake zaune yana kallonta tana ta faman kuka."Zaka iya hadata da kayan nan fa ta fitar dasu kuma a dace tunda macece" zuciyar shi ta kara fada mashi. Da sauri kamar wadda aka tsikara ya mike ya fice zuwa garden na gidan ya fara latsa waya da hanzari ya kai kunne.
"Hello oga, na samu mafita fa, ina yarinyar da nake fada maka tana wajena? ehh, to ita zata kai kayannan zuwa Nigeria din baza'a samu matsala ba".
"Ka tabbata Abdalla? wannan ba aikin wasa bane fa" daga daya bangaren aka fada.
"Karka damu oga komai zai tafi yadda ake so" daga haka ya yanke wayar ya dawi ciki yana jin kamar an tsundumashi a aljannah.
Bansan mai ke faruwa ba, na ga dai cikin yan kwanakin Abdallah na kula dani matuka, yana yawan bani kudi wanda a yanzu basa gabana, burina kawai in koma gida gaban iyayena, yana yawan sa wani balaraben mai taxi daukata zuwa wajen shakatawa kala kala tare da siya min abubuwan amfani na yau da kullum bansan mai yake shiryawa ba, amma nasan ba banza ba.
Sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba, yau nake cika shekara daya cifff da sayan mabudi na budewa kaina rayuwar dana sani da kaico na wanzuwata a hadaddiyar daular larabawa Dubai. kamar kullum ina zaune a dakin da yake mallakina, na yi kuka har idanuna sun kumbura sunyi jajur dasu Abdallah ya shigo, babu wata kwana kwana ya sanar min da kudurinshi na son yi mashi safarar koken zuwa Nigeria ta hanyar hadiyewa,..
"Karki daga hankalinki Maryama, abin bai da wani hatsari kuma hanya mai sauki ake bi wajen cirewa kamar dai yadda zakiyi kashi a saukake haka za'a cire shi daga cikinki" ya fada yana sakar min murmushi wanda na ji kamar wuka ya soka min,gardama na yi da tabbatar masa lallai bazan aikata wannan aikin ba,duk da makudan kudaden daya kwadaita min zan samu,hakan bai sa na amince ba.
Mikewa Abdallah yayi yana tattara fatar goshinsa waje daya gami da min wani kallon dake nuna baki da hankali, an fada maki zan yi asarar kudina na ne a kan ki ba tare da na fanshe ba?.
"John, ya fada da karfin da saida na toshe kunnuwata, kan kace me John ya shigo dakin yana ta muzurai, magana ya mishi da harshen igbo sannan ya juya zuwa gareni yace "Dole ne ma kiyi abin da nake so, an fada miki zaman kan ki kike a kasar nan, to zama na kike yi, ke din tamkar baiwata ce". Wani jibgegen sarka John ya shigo dashi kafun inyi aune suka cafko kafafuna suka daure cikin wannan sarkar kana Abdallah ya tsugguna gaban gadon ya fara daddaura hodar cikin leda nylon yayinda john yace, "Oga bari muje da sauran mu yi clearing hanya....
Lumshe kyawawan fararen idanu na nayi, na dade ina jin yadda ake yabon kyawun zubin hallitar idanuna mutane da dama idan sun tashi yabon kyan hallita ta su kan kirani da mai idon madara tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya bani, amma a halin da na ke ciki yanzu sabanin kasancewar su launin milk idanun sunyi jajur kai kace attaruhu aka daka aka watsa cikin su ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaita wa ba, saidai ba ko daya daga ciki tsabar tashin hankalin da na ke ciki ne ya haddasa min canzawar launin ido.
A hankali na juya na kuma kallon shi zuciya ta na bugawa da karfi karfi yayinda nauyin da kaina yayi ya haddasa min ganin dishi dishi,...yana durkushe gaban gadon da nake zaune ya bani baya yana ta daddaure hodar iblis (COC@!NE) cikin wasu kananan leda nylon, da sauri sauri yake aikin wanda duk bayan second daya sai ya daga kai ya kalli kofa.
Rumtse idanu na kuma yi, zuciya ta na tsananta bugu tuna cewa wai nice zan hadiye gaba daya wannan hodar iblis din a cikin cikina inyi safararta zuwa Nigeria.Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na furta cikin raina kana nabi dogayen kafafuna farare sol da kallo wanda su Abdallah suka daure da sarka sakamakon gardamar da nayi hakan.Zuwa yanzu na tabbatar roko da magiya bazai min amfani ba,.
"You have to be brave" zuciya ta ta fada min, tabbas dabara ne kawai zanyi da taimakon ubangiji inbar wurin nan, if not rayuwata ta kare, safarar cocaine ba karamar risky bane ga rayuwata, cikina ne ya hautsine gami da bada sautin kululululu sakamakon tunawa da nayi wai hadiyar wadannan ledodin zanyi cikin cikina. duk da ya sanar min da hanyoyin da za'abi a fitar dasu idan mun isa nigeria hakan bai rage koda kaso daya cikin dari na irin tsoratar da nayi ba.
A hankali na fara bin dakin da kallo ko zan dace, aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa dani ga kuma wani tangaran mai dauke da rose flower duk a wuri daya, cikin dabara nakai hannuna duk biyun na dau lamp din da kuma flower vase din,...ya dukufa sai aiki yake a gaggauce hakan yasa bai maida hankali kaina ba, rumtse idanu nayi ina tabbatar wa kaina abunda zan aikata shine daidai, baiyi aune ba yaji saukar tangaran a keyarsa ji kake garammm cikin azama ya juyo jin abin unexpected, yana juyowa na kuma rotsa masa bedside lamp din at the same point, take yayi baya baya ya kwala wani irin ihun kiran suna na "MARYAMAAAA" ya fadi kasa jini ya fara malala a wurin, da gaggawa na fara kokarin kwance chains din da suka daure min a kafata, sai a lokacin na kula da cewa tunda ya fadi bai kara motsi ba, ga jini dake tartsuwa ta keyanshi da baki harda hanci.Zuciya ta ce ta kuma bugawa da karfi dan matsowa nayi kusa da shi a hankali nace "ABDALLAH" amma shiru ko motsi baiyi ba, na daga hannunshi ina sakewa hannun ya dawo, mikewa nayi ina ja da baya baya yayinda wani irin jiri ke kwasata, "ya mutu!" na furta da karfi a lokaci daya kuma wani irin bell yayi ring cikin kwakwalwata na kashe shi, idan aka kamani shikenan ba mai kara jin labarina a duniyar nan,...without second though na janyo bedside drawer na cire passport nawa da kuma credit card sai wayata da kuma tab nawa wanda ya dawor min daga wancan gidan,da sauri sauri na kuma zuge wata doguwar durowa mai dauke da kayayyakina jere reras ba tare da na bi ta kansu ba na janyo wata yar akwati na bude American dollars ne shimfide dauri dauri,abdallah ne ya bani ajiyarsu kwanki biyu da suka wuce, duk kaunata ga kudi amma na kasa daukansu, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban wani,dauri biyu kawai na dauka, gyalen bakar abayata na yafa da hanzari kana na bi gefen abdallah na fice daga dakin,.
"Act smart maryama this is dubai not abuja nigeria" zuciyata ke bani shawara sai dai duk yadda naso bin shawaran na zuciyata na kasa jikina sai rawa yake, yayinda launin idanuna ke kara sauyawa zuwa tsananin tashin hankali,cikin sa'a na fita daga gidan ba tare da mai gadi ya tuhume ni ba sanin matsayina da yayi a gun mai gidan, cab na tsayar na shige hade da cemasa "Airport," ina daidaita zamana cikin cab din wani irin kuka mai masifar karfi ya taho min amma haka na dinga dannewa wanda ya haddasa min rawar jiki hadi da takurewar fuska.
ABU DHABI INTERNATIONAL AIRPORT UAE.
"I need ticket to nigeria" na fada muryata ta na rawa, dago kai mutumin yayi yana kallona jin yanayin muryata sannan ya mayar da kanshi yace "your passport ma'am" ciro dan karamin takardar paspo dina nayi jiki na rawa na mika mishi ya karba yadan dudduba kana ya miko min yace "ohk give me a moment to check ma'am" ya maida hankali kan computer dake gabanshi ya danyi danne danne na dan lokaci kana ya dago yace "The earliest flight is emirate airlines but the economy is full, would you like to opt for business class? ko zanyi schedulling naki zuwa gobe". "Gobe"? na maimata no bayadda za 'ayi inkai gobe a kasar nan wannan ba mai yiwuwa bane, pleadingly nace plss sir ka kara duba min economy din maybe a dace.
Kafun ya bani amsa kamar ance in juya na hango su suna ta baza ido cikin airport din, zaro ido nayi yayinda wani irin zufa ya karyo min har yana diga a kasa, jiki na na rawa na zaro credit card nawa na mika masa nace "a bani business class din" kallo na yayi da mamaki ganin yadda nake ta jan mayafi na don ya rufe min fuska, yayinda na ke jin rawar da kafafuna ke yi yana gab da kayar dani kasa...Kaina a sunkuye nake tafiya bayan na gama da batun ticket mutumin ya sanar min da naje na duba information panel domin sanin exact time da zamu tashi da kuma seat no dina, dan dago kai nayi kadan na kalli gefen da na hango su dazu, aiko karaf muka hada ido da John muna hada ido naga ya tunkaro inda nake, nasan bazaiyi gigin da za'a kamashi ba ganin a airport muke hakan yasa nima na dan saisaita nutsuwata amma deep down saura kadan zuciyata ta shige cikin cikina, tafiya nake amma gaba daya hankali na yana kansu ganin bina suke bil hakki, without thinking twice na kwasa a guje domin duk kokarina na ganin banyi gudun ba kasawa nayi,ga uban zufan da ya gama min wanka.
Gudu na dinga yi irin na ceton rai cikin ikon Allah ban hadu da security ba...,garapp naji na bugi wani abu mai kauri kuma mai laushi kana mai sanyayyen kamshi,a lokaci daya kuma wani irin zafi ya ziyarci hannuna hade da watsewar wasu takardu a kasa,jikina na mazari na sunkuya da sauri sauri na shiga tattare takardun da suka zube a kasa cikin second daya na mike na kamo tafin hannunshi ba tare da na daga kai naganshi ba na damka mishi takardun hadi da furta sorry sorry is not intentionally, ban yarda na hada ido dashi ba na ci gaba da gudu na.
Juyawa yayi yana kallona da madaukakin mamaki kafun yabi tsadadden suit nashi da na bata masa da coffeen dake hannunsa...wani dan lungu nabi na ga wani babban dustbin ba tare da dogon tunani ba na shige cikin dustbin din mai cike da tarkacen datti ina sauke numfashi da zare idanu kamar bera cikin bokitin gari, da addu'ar Allah ya tseratar dani,duk kuwa da nasan cewa hakkin wasu ke bibiyata a rayuwa wadanda ba lallai su yafe min ba.....