CHAPTER 12
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA BIYU
“Malama, ba zan iya wannan jiran ba, domin akwai kayan ƙwallo na, kuma gobe Muna da training da yamma. So in za ki yi wanki kawai ki yi, in kuma ba za ki iya ba, ki faɗa mini.”
Rasa abin faɗi Farida ta yi, domin har cikin ranta ba ta jin cewa za ta iya tsayawa ta yi wa Sufyan magiyar da har zai sa ya samu damar rainata ba. Zaɓi biyu kawai take da su a halin yanzu: ko ta yi wankin ya ji daɗin cewa ya isa da ita, ko kuma ta ƙi yi, in ya so ya kira ya shaida wa Baba Haruna cewa ya ba ta umarni amma ta ƙi bi.
Idan kuwa Baba Haruna ya ji, ta san za ta fuskanci mummunan hukunci. In kuma bai faɗa wa Baba Haruna ba, ba ƙaramin aikin Sufyan ba ne ya sake wannan bidiyon kamar yadda ya faɗa a farko, ga zancen cikin da bata san yadda zata bullowa lamarin ba.
Numfasawa ta yi, ta kalle shi cikin manyan idanuwanta. Ta durƙusa ta kwashe kayan da yake gabansa. Tana ɗaga kai suka haɗa ido, ta galla masa harara.
Dariyar mugunta Sufyan ya yi, ya ɗaga mata gira.
“Da kika ce ba kya ji, ai da kin bari, da kin ga aika-aika cikin daren nan.”
Wucewa toilet ɗinta ta yi ba tare da ta ce masa komai ba.
Shi kuwa, rai fal daɗi, yana daga bakin ƙofa cikin ɗaguwar murya ya ce, “Su fita fa, kin san ba na shiri da ƙazanta.”
Ya faɗa yana juyawa. Ya koma falo, ya je kan kujera ya baje, yana jiran barci ya ɗauke shi.
Shiga toilet ɗin ta yi ta fara yi masa wanki. Tana yi, zuciyarta na zafi, ga wani irin baƙin ciki da ya turniƙe mata ƙirji.
“Wai ni Sufyan ne ke ba ni umarni da ban isa na kauce masa ba? Ni ce nake yi wa Sufyan wanki? Cikin daren da kowa ke barci, amma ni ga ni a nan. Kamar yadda ka baƙanta mini, nima sai na baƙanta maka. Sai ka yi da-na-sanin sani yi maka wanki.”
Abin da take ta kitsawa a ranta kenan. Ga barci ya addabe ta, idanunta har rufewa suke ƙoƙarin yi da kansu. Haka ta daure ta ci gaba da aikin har wajen ƙarfe ukun dare, sannan ta kammala.
Da yake akwai gefen shanya a ciki, sai ta shanya masa kayan.
A daddafe ta fita daga toilet ɗin ta nufi kan gadonta. tana kwantaciya kuwa, barci ya yi awon gaba da ita.
Sai da aka kira Sallar Asuba Sufyan ya farka. Ganin kansa a falo ya yi, sai ya tashi ya je ya yi alwala. Har zai fita zuwa masallaci ya ji sautin gwartin barcin Farida na tashi.
Lekawa ɗakin ya yi, domin bata kulle ƙofar ba saboda gajiya. Da ya shiga sai ya ganta shame-shame a kan gado, ta baje tana ta sharɓan barci, bakinta a wage. Kanta ma dankwalin ya yi gefe, ga wani guntun gashi ya tsaya a tsefe. Karar gwartin nata kuwa kamar an kunna inji.
Tsaki ya yi yana kallonta, ganin yadda ta yi ba kyan gani. Sai muninta ya ƙara bayyana fiye da yadda ya saba gani.
“Wayyo! Ga biri a siffar mutum. Ga wani ɗan iskan gashi kamar hammatar ɗan iska.” Ya fada yana jan gashin.
“Ke dai kam ta ko ina ba sauki. Idan kina tare da wani a ɗakin nan, wannan gwartin naki ma ai ba zai bar mutum ya yi barci ba.”
Ya faɗa yana kallonta, sannan ya fice daga ɗakin.
Yana fita zuwa tsakar gida, har zai tafi masallaci, sai ya ci karo da wani kyankyaso, irin manyan nan.
Dariyar mugunta ya yi, ya sa hannu ya ɗauke shi.
“Yanzu kuwa zan yi maganin gwartin nan.”
Ya ƙara faɗa yana komawa cikin gidan.
A hankali ya shiga ɗakin. Sai da ya daidaici tsakiyar kumatunta, sannan ya jefa mata kyankyason a kai. Da ya tabbatar ya sauka, sai ya yi saurin ficewa daga ɗakin yana kunshe dariyar mugunta.
Kyankyason ne ya fara yawo a fuskarta, yana ta ƙoƙarin shiga mata baki. A firgice ta farka, ta kai hannu wajen, kawai sai ta ji ta danko wani abu.
Da ta ga kyankyaso ne, sai ta ƙara firgicewa. Nan take ta jefar da shi daga jikinta, jikinta yana rawa.
A rayuwarta babu abin da ta fi jin tsoro kamar kyankyaso, balle babba irin wannan. Ta tsani ganinsu ko da kuwa ba za su zo kusa da ita ba. Ina ga kuma yanzu ga shi a jikinta, yana ta yawo yana ƙoƙarin shiga mata baki!
“Wayyo Allah! Na shiga uku”
Ta ƙara ihu tana tsalle daga kan gadon, tana duba jikinta cikin tsananin tsoro.
Da ƙyar ta tashi ta ɗauki sandar mop tana jan kyankyason. Duk ta rude, tsikar jikinta har tashi take. Da ta samu ta fitar da shi waje, zama ta yi tana ta maida numfashi.
A haka Sufyan ya dawo ya tarar da ita a takure. Kau da kansa ya yi yana dariyar mugunta, ya wuce ɗakinsa.
Ta jima a haka kafin ta tashi ta je ta yi sallah. Ko da ta idar da sallarta, ta gagara komawa barci. Zaune ta yi tana ta tunani, can sai wani tunani ya faɗo mata.
Tashi kawai ta yi, ta sanya riga da wando, ta zumbula hijabi da nikabinta sannan ta fita.
Gudu ta fara tana motsa jiki. Da farko kamar wasa ta fara, nauyin jikinta na jan ta, amma haka ta daure ta dage ta ci gaba. Daga ƙarshe sai ta ji numfashinta na neman ɗaukewa, wanda hakan ya sa dole ta dakata da gudun.
Zama ta yi a kan wani dutse tana haki. Ganin gari ya fara wayewa kuma mutane za su fara fitowa, sai ta tashi. Tafiya take yi a hankali tana ci gaba da maida numfashi, kamar daga sama ta jiyo haushin kare. Juyawar da za ta yi kuwa, sai ta gan shi yana binta yana haushi. Take ta manta da gajiyar da nauyin jikinta, gudu ta kama kafa mai naci ban baki ba. Da ta ga karen na ƙoƙarin komota, bata san lokacin da ta cire takalmanta ta riƙe a hannu ba.ta ci gaba da falfalawa kutubur-kutubur jiki ko ina na rawa.
Tana kaiwa daidai gidan,hankaɗa gate ɗin ta yi ta shige a birkice. Sufyan na zaune kamar yana jiranta a farfajiyar gidan, take ya fara tuntsirewa da dariya, har yana riƙe da ciki.
Da har za ta wuce ba tare da ta ce komai ba, zafin da zuciyarta ke yi ya sa ta tsaya.
“Wai mahaukaciya ka gani ne da za ka tsaya kana kallona kana yi mini dariya?”
Sufyan ya nuna ta da hannu yana dariya.
“Gani na yi kamar an jefo dilar gwanjo?”
Ya ƙara dariya, yana kallon yadda take haki da takalmanta a hannu.
Farida ta cije leɓenta, tana ƙoƙarin haɗiye takaicin da ya cika mata zuciya. Binsa da fusataccen kallo kawai ta yi ta shige ciki abunta.
Tana shiga, ta cire kayan jikinta, ta shige wanka saboda gumi ya gama jiƙa mata jiki. Tana gamawa ta haye gado domin barcin da ba ta samu damar yin isasshe jiya ba har yanzu yana bibiyarta, ga shi kuma ta ƙara gajiyar da kanta.
Misalin ƙarfe huɗu ta shiga kitchen kenan tana ɗebo abinci, sai ta ji sallamar Inno kamar wadda ta diro daga sama. Da ta fito, sai ta tarar da Inno tsaye da katuwar gora a hannu.
“Yawwa, yar albarka! Abinci kike ci ko? Kar a yi wasa da ci fa saboda lafiyar jariri. Maza je ki ɗauko kofi ki dawo.”
Kallon rashin fahimta Farida ta yi wa Inno, tana cewa, “Kofi kuma? Mene ne wannan, Inno?”
Inno ta ɗaga gorar tana nuna mata.
“Ruwan adduar rubutu ne. Na sa Malam Habu ya yi miki na masu ciki. Kin san lamari na ciki, da wuri ake fara tarairaya. Ya ba da kariya, gudun bakin mutane. Kambun baka ba wasa ba ne, Faridatu. Dauko, kin ji?”
Farida ta haɗe rai tana cewa, “Ni fa, Inno, na faɗa miki ba wani—”
Kafin ta ƙarasa, Inno ta katse ta da dakuwa.
“Ungo nan, husumammiyar ɗiya! Ana ce miki ga Annabi, kina kifta wasu zaratan idanuwanki. Je ki ɗauko mini!”
Turo baki Farida ta yi, ta je ta ɗauko kofin ta miƙawa Inno.
Karɓa ta yi, ta zuba mata ruwan adduar, sannan ta miƙa mata.
“Karɓi nan. In kika zo nakuɗa kika ji ki subul, ki sambado lafiyayyar budurwa ko saurayi, ai kya tuna da ni ko? Waya sani ma ko tagwaye ne”
Farida ta karɓa rai a ɓace, tana kallon Inno.
“Ke sha mana! Ban son husuma fa. Gata na miki wanda uwar ki Kulu ba za ta iya ba. Yoo, ƙaunarki nake, Faridatu! Duk cikin jikoki ke kaɗai Ubangiji ya duba ya yowa halittar fuska irin tawa. Amma dai jiki kam ban san daga wacce duniyar kika kwaso ba. Kin ga kuwa, ai dole in so ki ko?” Inno ta faɗa tana dariya.
Farida na kaucewa tana yatsina fuska, haka Inno ta tasata a gaba, sai da ta shanye ruwan rubutun da ta zuba mata tas.
Inno ta yi murmushi tana cewa, “Yawwa, ko ke fa! Gaba ki tuna da taimakon da na miki ai. Kin ga sauran wannan ma ki aje, kullum kina ɗiba kina sha, kin ji ko?” Ta ƙarasa maganar tana ajiye gorar gefe.
Farida dai sai yatsina fuska kawai take yi.
Ta tashi har za ta fita, sai kuma ta tsaya tana cewa, “Yawwa, na sa an tsinko min ganyen zogale ma. Zan dafa in yi miki kwaɗo anjima, in mai gidan naki, Sufuyanu, ya zo sai ya tawo miki da shi. Kin san ku masu ciki akwai kwaɗayi, kuma ana so ma ku riƙa cin abu mai galmi-galmi.”
Inno ta ƙarasa maganar tana dariya, yayin da Farida ta girgiza mata kawai aranta tana faɗin, “ni dai na shiga uku da wannan tsohuwar.”
Inno na fita Sufyan na dawowa daga School,Da waƙarsa ya shiga gidan, yana tafiya yana bouncing. Ya shige ɗakinsa, ya saka jersey ɗin ball ɗinsa na training. A tsakiyar ɗakin ya tsaya yana saka takalmi, yana girgiza jiki tare da ci gaba da waƙarsa:
“Ba mu da abin kushewa sai dai kallo,
Indai za mu fito, ce mana hello!
A gurinmu ake ganin sabon salo,
Ya ya za ku yi, hasken rana ya billo!”
Ita kuwa Farida, me za ta yi ban da dariya? Kallonta ya tsaya yi yana cewa, “Ya ne wai?”
Cikin dariya ta ce, “Ya fa, kamar ya?”
Ta faɗa tana kawar da kanta.
Tsaki ya yi, ya ci gaba da waƙarsa yana rawa har ya fita.
Filin da suke buga ball ya tafi. Duk sauran ’yan wasan sun riga sun taru, shi kaɗai ake jira. Yana zuwa sun haɗu kenan za su fara bugawa, sai ya jin wani irin azaba a cikin wandonsa ya yi. Da sauri ya sa hannu cikin wandon yana ihu…
***