Chapter 21
Da wani irin mugun sauri ta tashi zaune a kan gadon tana tunanin a ina ma ta yar da wayar.
Tunawa da ta yi a mota ta yasar yasa ta miƙe da sauri, ta sa takalminta ta nufi ƙofa. Ba ta tsaya ko ina ba sai parking space ɗin da ke can har kusa da bakin gate.
Duk da dare ne sosai, amma tsakiyar ƙaton gidan kewaye yake da hasken wutan solar tamkar da rana ne.
Ita da kanta ta san yanzu dare ne sosai, but saboda sanin dalilin da yasa take son lallai-lallai sai ta ga wayarsa a wannan daren kafin safiyar gobe, yasa ta manta da hakan. Ta shiga tafiya da sauri kamar ba ita ba ce wannan yar gayu mai tafiya ɗaiɗai ɗin nan ba.
A gaban parking space ɗin ta tsaya tana bin motocin da ke jere kusan goma a wajen da kallo.
Sai dai ta yi iya dubawar da za ta yi, ba ta ga motar da suka fita da shi din ba.
Cike da tsananin jin takaicin rashin ganin motar, ta hau yin huci kamar wacce ta yi dambe.
Tana tsaye cikin rashin sanin yadda za ta yi, ta kama jan tsakin takaici kamar wata tsaka.
Cike da takaici ta juya zata koma sai kuma ta tsaya cak kamar wacce aka dakawa tsawa, saboda ganin farar motar a can ƙarshen motocin gidan, ashe su Japhat ne suka gyara masa parking.
Nan take wani kyakkyawan murmushin jin daɗi ya subuce a kan fuskarta ba tare da ta shiryawa hakan ba.
''Ta hanyar wayarka zan gane ko wane ne kai, sannan na hukunta ka.''
Ta ƙarasa wajen motar da sauri ba tare da jin tsoron dare ne ba, ko don gidan da haske ne ohoo.
Ta sa hannu za ta buɗe, amma me sai ji ta yi motar a rufe gam. Cikin azama ta sake jan marfin motar da ƙarfinta kamar za ta balla shi, sai da ko gezau wai an tsikari kakkaura.
''Kaiiiiiiii! Wayyooo! Damn it!''
Ta faɗa da ƙarfi tare da buga ƙafarta a ƙasa kamar wacce za ta fashe da kuka.
''Welcome, Madam. How can I help you?''
Japhat, da jin muryarta yasa ya zo ya faɗa cikin girmamawa.
Cikin sauri ta kalle shi kamar wacce ta ga abin da take fatan gani ta ce,
''Where is that car key? I want you to open it for me right now.''
Babu musu ya je ya ɗauko key ɗin tare da zagayawa ya buɗe mata motar, yana tambayar mene ne ta manta ya ɗauko mata, amma ta yi banza da shi ta je ta shiga motar, tun tana neman wayar cikin daɗin rai har ta fara hawaye, saboda dama can ita mutum ce mai saurin kuka.
''How can I help you, Madam?''
Japhat dake tsaye a bayanta yana kallonta ya sake faɗa a karo na biyu.
A zafafe ta ɗago ta kalle shi cikin fusatar da ya risketa yanzu ta ce,
''I told you, it's none of your business. Leave this place.''
Cike da bin umarnin oganniyar tasa ya ce,
''Yes, ma'am.''
Ya juya ya koma wajen da ya fito ya barta ita kaɗai a wajen, saboda yana da tabbacin babu abin da zai same ta.
Ita kuwa ko tsoro babu, ta sake kutsa kai cikin motar tana laluɓe-laluɓe.
''Idan har na gane kana ɓoye wani abu akan family na, sai ka yi daga sani ɗan kauye kawai.''
"Hey, future wife."
Da mutum sauri ta ɗago daga cikin motar a tsorace, tamkar wacce aka kama tana sata.
Sai dai ganin wanda ke a tsayen yasa ta tamke fuska sosai tare da kawar da kai gefe tamkar wacce ta ga kashi.
Shi kuma cike da iya barikanci ya matsa kusa daf da ita tamkar zai rungume ta, ya tsaya yana bin fuskarta da kallo, yayinda zuciyarsa ke ta zugasa ya taɓa ta.
Da sauri ta matsa baya tare da ɗagowa fuska a haɗe tana kallon cikin idanunsa kamar wacce ke shirin kai masa duka.
Cikin iyayi ya ɗaga mata girarsa ɗaya tare da riƙe kwankwaso ya ce,
''Me kika yi a nan ke kaɗai ne, future wife? Ko dai ni kika fito jira ne iyee?''
Ya karasa maganar yana lasar harshensa kamar wani maye.
Jin abin da ya faɗa yasa ta ɗago tana kallonsa tare da balla masa harara kamar idanunta za su fado saboda tsananin tsanar da take ji yana ratsa zuciyarta haka kawai ba dalili.
Cikin sauri ta sake matsawa baya tana yatsina fuska saboda ganin daga shi sai farin vest da ƙaramin wandon da iya kacinsa cinya.
''Ya wannan rubabbiyar wayar dake hannunki fa? Mu gani, na waye.''
Ya yi maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa kan wayar.
Da sauri ta ja wayar baya. Ya tsaya suna kallon-kallo ba tare da ta ce masa komai ba, ta manna wayar a kirjinta.
Tare da yin baya tana neman hanyar da za ta wuce.
Shi kuwa kamar wani maye ya sake takawo wajenta yana bin kayan baccin jikinta da wani irin kallo dake nuna tsananin soyayyarta da shaukinta.
Cikin jin takaicin yadda yake kallonta ta juya za ta bar wajen.
Ya yi saurin riƙe hannunta tare da jawo ta jikinsa duk a lokaci ɗaya, ya riƙe hannun sosai ta yadda ba za ta iya kwacewa ba, yana bin fuskanta da kallo a hankali cikin murya kamar na masu shaye-shaye ya ce,
''Haka kika ƙara kyau, baby girl?
Kin canja sosai, kin yi kyau kin ƙara ƙiba, everything look so good. Ke wato ko missing ɗina baki yi? I'm your husband fa.''
Ya sake matsowa jikinta sosai.
A maimakon ta ji kamar yadda take ji a duk lokacin da suka samu kusanci da Abdul ko yaya ne, sai ta ji kamar wani ƙaton dutse ne ya tsaya a gabanta tana ta mutsu-mutsun kwacewa amma ya ƙi saketa.
Ya ɗaga hannunsa zai taɓa fuskanta. Cikin tsananin takaici da tsanarsa ta sa dukkan hannayenta ta tura shi baya. Kamar ledar fiyawata haka ya tafi luu zai faɗi, sai kuma ya tsaya.
A fusace ta wurga masa harara kafin cikin ɗaga murya ta ce,
"Kada wannan kazamin hannun nan naka ya sake ya yi gigin taɓani, Aliyu. I'm warning you a karo na ƙarshe.
A kan wani dalili zan yi kewar ka? I think tun ba yau ba muka kawo ƙarshen maganar nan. So me yasa kake son a yi ta maimaita abu ɗaya? Bana son ka, I hate you. I hate to see you a gabana Aliyu, a wani lokaci ina ƙwale ka so ne saboda ummi saboda haka please and please ka kama kanka, if not zan faɗawa Daddy Wallahi."
Ta juya ta nufi cikin gidan da gudu.
Shi kuwa tunda ya ji ta ambaci sunan Daddy ya kama kansa, saboda ya san haɗuwar ba zai masa daɗi ba. Ya bita da kallo har ta ɓace.
Yatsu biyu ya ɗaga mata yana murmushi. A hankali ya sauke wani buyayyen ajiyar zuciya.
''Ki gama gujegujenki, ki dawo. Ina nan jiranki, Mammy. Dole ki so ni Wallahi.''
Ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya shige shashin su.
Tana shiga ɗakinta, a saman katafaren gadonta ta zube tana mai sauke numfashi, lamo ta yi cikin lallausan bedsheet da duvet ɗin gadon masu taushin tsiya da ƙamshi, sai sauke ajiyar zuciya take yi kamar wacce ta yi gudu sosai.
A hankali ta lumshe idonta tare da buɗe su ta yi shuru tana jin zuciyarta babu dadi. A maimakon ta yi tunanin Hydar da ya takurawa rayuwarta a yanzu, sai akasin hakan ya faru, haka kawai Abdul ke ta faɗo mata kuma duk lokacin da ta tuna shi sai gabanta ya faɗi.
Duk da yadda taso ta hana kanta yin tunaninsa hakan ya gagara. Cikin takaici ta yi tsaki tare da miƙewa ta zauna.
Ta riƙe wayarsa da ta ɗauko tana kallo fuska a haɗe tamkar shi ne a gabanta.
Ganin wayar sabo ne bai wani ji jiki ba yasa ta taɓa baki.
''Ko ma menene kake ɓoyewa a cikin ranka duk zan gane yanzu.''
Ta furta maganar a hankali, kafin ta danna wajen kunnawa. Wayar ya kawo haske, nan take hotonsa dake gaban wayar ya bayyana. Ganin hoton sai da yasa ta ji zuciyarta ya buga da ƙarfi.
Ganin ba password a wayar yasa ta shiga ciki. Wajen numbers ta fara shiga, sai dai ga mamakinta Numbers ɗin ciki ba su wuce biyar ba.
Daga Adamu, Baffa, Habu, Salim, sai na ƙarshe da aka saka harafin F kawai.
''F...''
Ta furta a hankali.
''Waye kuma wannan..? Budurwarsa''
sanin babu mai bata amsar tambayarta yasa ta faɗin,
''Duk zan gane.''
Ta gyara zamanta akan gadon sannan ta fita daga wajen number's din ta shiga photos. Tana shiga wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, nan ma sai da ta ji zuciyarta ya buga, ta lumshe ido da sauri, duk da idanta a rufe hakan bai hana ta ganin hoton da ƙwaƙwalwanta da zuciyarta haddace shi ba.
Sanye yake cikin fararen shadda da hula baki sai sallaya a hannun, yana tsaye a kan kwalta ga mutane a bayansa, kowa na harkansa. Alhamur ranar idi aka yi hoton.
Duk da a hoton ma fuskarsa a haɗe, amma hakan bai hana shi yin kyau ba.
Shagala ta yi da kallon hoton ba ko kiftawa. Ta daɗe tana kallon kafin ta sake taɓa screen ɗin zuwa na gaba.
Dummmm!
Kirjin ta ya wani buga kamar zai tarwatse. Ta zaro idanunta waje kamar wacce ta ga abun tsoro.
Cikin shakku ta sake tsurawa hoton ido. Nan kuwa ta tabbatar da ita ɗin ce dai ba wata ba. Hoton ta ne a ɗazu lokacin da take zubawa Japhat kashedi a company, yana riƙe da wayarsa ashe, hoto yake yi mata kenan?
Ta yi zooming na screen ɗin tana kallon hoton sosai. Duk da cewa unexpected ne hoton but ya yi kyau sosai.
''Shin mene ne dalilin da yasa ka ɗauke ni hoto menene dalilin yin hakan''
Ta tambaye kanta yayinda mamaki da ruɗani suka kasa barin kan fuskanta, ta yi shuru na ɗan lokaci, sannan ta sake yin magana a hankali,
'' Me yasa hotona? Me yasa ya ke kallon hoton su Daddy haka? Sannan me yasa na ƙasa korarsa tun a lokacin?''
Ta ƙarasa maganar jiki a sanyaye kamar ba ita ba.
A yanzu tambayoyin sun fi yawa a kanta fiye da amsoshin da take ganin tana da su. Haka kawai ta ke jin kamar akwai wani abu da Abdul ya sani, wani abu da ya kamata ace ta sani. Haka ta ci gaba da
tunane tunane da zarge zargensa sai dai har ta gama bata samu amsar da ta yadda da shi ba, wannan dalilin yasa ranta ya sake ɓaci sosai.
Cikin jin haushi ta ja tsakin takaicinsa tare da buɗe drawer ɗin dake gefenta, ta cilla wayar ciki. Sannan ta kwanta tana ta tunane-tunane, sai kawai cewa bacci barawo ya sace ta.
Washegari.
Tun da ta tashi ta dauki wayan nashi ta saka a jakanta, kafin ta shiga wanka
Tsaf ta fito cikin shirinta kamar mai zuwa aikin da gaske. Yau ɗin ma abaya ta saka kalar toka, ga takalminta shima kalar kayan. Ta yi kyau sosai sai ƙamshi take yi. Cikin takun nan nata na isa da gadara ta fito.
Gaba ɗayan su ta samu a dining suna breakfast, Ammi ne kawai ke tsaye a tsakiyarsu, da alama abincin take haɗa musu. Tana isa wajen.
Mayen nata dake zaune kusa da Umar ya tsayar da cin abincinsa ya kafeta da wannan yan iskan idanunsa babu ko kiftawa. Ganin hakan yasa ta haɗa fuska ta ɓata rai sosai. Tana harararsa kamar babu kowa a wajen.
Duk abin da ke faruwa a kan idanun Ummi tana lura da motsin ko wannensu. Sai dai ta kawar da kanta kamar ba ta ga komai ba.
''Good morning Daddy, Ummi, Ammi and brothers,'' ta faɗa a shagwabe kamar wacce za ta yi kuka.
Gaba ɗayan su fuskarsu da murmushi suka juyo suna kallonta.
''Morning sweet heart. Kin tashi lafiya? Har an yi shirin fita?''
''Eh Daddy.''
Ta faɗa tana ɗaukar shayin dake gabansa ta kurɓa daga tsayen da take. Da kallo ya bita har yanzu da murmushi a fuskarsa, murmushin da ita kaɗai ke da alfarmarsa.
''Mammy na, zauna mana ki yi breakfast ɗin da kyau kafin ki tafi. Naga da sauran lokaci tun da shima Fahad ɗin yanzu ya wuce.''
Lallai kam ita da ba ta ƙi ace ta rufe idanunta ta buɗe su ta ganta a gabansa ba ne za a ce ta zauna? Inaaa.
Ta girgiza kai da sauri ta ce
''No Daddy, sauri nake yi idan na je naci a can bye''
''Okay bye sweet heart, take care and if you see anything ba daidai ba immediately let me know kinji.''
Tana tafiya ta ce,
''Okay my lovely Daddy, bye.''
''Bye. Don't forget su Japhat na bakin mota suna jiranki.''
Ummi tana murmushi ta ce
''Wai nikam aikin menene Mammy ta samu take yi a kamfani? Daga dawowarta haka na ganta cikin zumudi da sauri kamar wacce ake jira meeting mai mahimmanci? Na yi zaton companyn nata a hannun Fahad yake?''
Aysha dake kusa da mijinta ta haɗiye abincin dake bakinta kafin ta ce
''eh shi ke kula dashi amma tunda ta dawo ta sa rigima zata ke zuwa''
Ummi ta girgiza kai
'' rigimar mammy dewa yake''
Ohoo ita dai Mammy ba ta ma san me ake cewa ba, dan tuni ta wuce saboda Allah-Allah ma take yi ta isa company ta ji dalilin zaman hotonta a wayarsa.
Kamar yadda su Japhat suka kai ta jiya haka yau ma. Mota biyu, ɗaya ita da shi Japhat ɗin, sai dayan kuma na sauran biyun. Haka suka wuce.
Mammy na tafiya suma duk suka watsa, kowa ya tafi wajen aikinsa har Haidar da ba a garin yake aiki ba shima ya fita. Aka bar iya Ammi da Ummi a gidan, duk da suma sun kammala cin abincin amma sai ba su tashi a wajen ba.
A hankali Ummi ta nisa tana kallon Ammi ta ce
''Aminiya dama so nake mu yi magana, dama idan sun watse.''
''To akan me?''
''Akan abubuwan da ya faru jiya''
Ammi ta ce'' to kin san hali ai ba'a rabasa da jaraba kullum ''
''Ni ba wai ina magana ne akan fadan da ya yi ba ma Fahad ba ne, magana nake akan tambayar da Safiyya ta yi masa.''
Shuru tana kallon fuskar aminiyar tata da ya canja zuwa na damuwa.
A hankali ta ɗan nisa sannan ta ci gaba.
''Mene ne kike ganin ya jawo ta yi masa wannan tambayar?''
Ammi ta yi shuru na ɗan lokaci kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
''Ban sani ba. Abin da na sani kawai shi ne, ko ya yi ne ba zai taɓa cewa komai ba''
Ummi ta daɗe tana kallonta kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce
''Amma, idan har Safiyya ta fara irin waɗannan tambayoyin, bai kamata mu ci gaba da ɗaukar komai kamar ba komai ba saboda haka a shawarce idan ta dawo kafin ta sake tambayar, ki sameta ki mata wani bayanin shikenan a wuce wajen,''
Ammi ta ɗago ido ta kalleta, sai kuma ta geɗa kai cike da gamsuwa da maganar ummin.
Da wannan shawarar suka samu matsaya Suka bar maganar suka ci gaba da hirarsu, kuma duk hirar game da Mammy ne, akan aurenta da Hydar.
Ammi da ta gama sauraran maganar da Ummi ke yi ta nisa jiki a sanyaye ta ce
''Har yanzu dai bai mayar da hankali akan maganar ba, kuma duk mun sani shi da kansa ya daure mata gindi ta ƙi aure. Ni na kasa ganewa ma, shi ne baya so ya ba da aurenta, ko ita ne bata son yin auren ne ohoo Duk na kasa gane musu.''
With so much confusion, Ummi ta ce,
''Wane irin kin kasa ganewa, aminiya? Ke da yarki amma ki zuba ido kina kallo. Yanzu shekarun Mammy nawa a duniya, balle ace auren ne bata isa yinsa ba? Sa'anninta gaba ɗaya, daga masu yara biyu sai masu uku. Ohoo Allah ka dube mu! Ni na rasa wani irin ƙaddara ne muka siyawa kanmu.''
Cikin tsananin rauni da rashin madafa Ammin ta yi shuru,
''Yanzu ya koma halayyarsa na da kenan?''
Jiki a sanyaye Ammi ta ce,
'' to me za'a fasa''
Sai Ummi ta yi shiru, kamar tana tunanin abin da ya kamata su yi.
Can kuma ta ɗago tana kallonta ta ce,
''To ko zamu koma wajen na kan dutsene game da batun auren nan, don naga alamun idan ba da taimakonsa ba Sa'ad ba zai taɓa sanjawa ba. Amma dai yana da kyau kafin mu je ɗin ku fara yin magana, mu ga yadda zai ɗauki maganar. Idan ya ƙi sai mu ɗauki mataki.''
Ita dai Ammi ''uhmm'' kawai ta iya faɗa saboda ta san halin kayanta, abun tashin hankali baya masa wuya, musamman idan ita ce ma. Amma haka nan Ummi ta yi ta bata ƙarfin gwiwa akan ta yi masa magana saboda idan ta yi shuru haka zai yi shima, kuma idan ya yi shuru Mammy ba za ta yi aure ba.
Ita kuma ta matsu a yi auren nan ko Aliyun zai samu ya nutsu ya rage wannan rawar kan nasa. Sai dai abu yaƙi yiwa ita, kuma bata tafan ace ba Mammy ya aura ba saboda wani dalilin nata da ba wanda ya sani. Haka dai ta ci gaba da zuga Ammin ta tare da tsara mata yadda idan ya dawo da daddare za ta tinkarasa har Ammin ta amince, sai dai a can ƙarƙashin zuciyarta wani irin tsoro ne da fargaba ke ta dawainiya da ita.
Ta san Sa'ad, ta kuma san yadda suke ita da shi. Abin ma da ta fi tsoro shi ne kar maganar ya ƙara tayar da wani sabon rikici.
---
Abdul
Misalin ƙarfe takwas na safe, tsaye yake a kusa da bishiyar goron biri da ke bayan ɗakin su, da ƙaramar waya a kunne, yana magana ƙasa ƙasa murya ciki-ciki tamkar wanda aka saka yin maganar dole.
''Wai da waye kake ta waya ne tun ɗazu? Ina jiran ka gama ka ɗaura min net ɗin nan, amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai ka ce cin ƙwan makauniya haba...''
Habu ya ƙarasa maganar daidai lokacin da ya iso gaban Abdul dake tsaye da waya a kunnensa.
A nutsu ya dakata da maganar da yake yi tare da zare wayar daga kunnensa.
A hankali ya juyo yana kallon Habu dake tsaye a gabansa, hannunsa riƙe da igiyar net, yana maimaita tambayar da wa yake magana.
A dakile murya ciki-ciki ya ce
''Da wacce kuke waya tsakiyar dare?''
Dariya Habu ya yi ya ce,
''To shikenan, don zaka yi waya da budurwarka sai ka ɓuya sai ka ce mara gaskiya? Wannan wayar fa ina naka babbar?''
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin zare ƙaramar wayar dake hannunsa da nufin ya gani.
Sai dai Abdul ɗin yaƙi sake masa wayar kuma bai amsa ba. Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa, ba tare da ya kalleshi ba ya ɗura wayar cikin aljihu ya karɓi nectait ɗin ya shiga naɗa masa, yayin da shi kuma ke ta tambayar ina babbar wayarsa, shi kuma ya yi shuru ya ƙi faɗar cewa his boss ta kwace.
Habu ya sake kallonsa na ɗan lokaci, kamar zai yi magana sai kuma ya basar.
Yana gama naɗa masa ya ce su fara tafiya, shi sai ya fara zuwa gidan Baffa kafin nan. Haka kuwa suka tafi suka barsa.
---
Su Inna dake tsakiyar gidan babu wanda ya ji shigowarsa sai sallamarsa da suka ji ciki-ciki a tsakiyar gidan.
Da ƙarfi kirjinta ya shiga buguwa kamar zai fito waje, saboda jin muryarsa.
Tana tsugunne cikin shirinta na kayan aiki, hannunta riƙe da ƙullin garin kokon da Inna ke siyarwa. Ta zo siya ne saboda ta dama tashi kafin ta wuce wajen aiki, sai kuma ta tsaya tana ba Inna labarin duk abun da ya faru a company.
A hankali ta ɗago kanta kamar mai jin shakkar abun da za ta gani ta sauke su a kansa. Ta yi sa'a ba ita yake gani ba, hakan ya bata damar more kallonsa.
Tun daga kan lafiyayyen fatan hannunsa mai ɗaukar hankali ga kamala da cikar halittar da duk wanda ya kalleshi sau ɗaya sai ya ƙara. Ga rashin yawan magana, shiru-shirun dake sake fito masa kwarjini ga duk wanda zai dubesa ko zama da shi.
Cikin ɗan sarkewar harshe ta shiga gaishesa cike da shakkar ko zai amsa, saboda tun da ya yi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa.
Sai dai ga mamakinta taga ya juyo yana kallonta, fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Cikin deep voice ɗin nan nashi wanda ke mata daɗi a duk lokacin da Allah yasa ta saurara ya ce
''Lafiya lau, ya su Mama?''
cak numshinta ya tsaya Saboda Wallahi ita sam bata yi tunanin ma zai amsa mata ba, balle har ya tambayi lafiyar Mama.
Amsawar da ya yin yasa ta ji kamar za ta mutu saboda daɗi. Cikin jin daɗi ta nufi gidan su tana tafe tana murna, ya yinda take ji kamar ta yi tsalle dan murna, a zuciyarta kuwa sai kiran sunayen Allah take yi tana masa godiya saboda alamun da ta gani na addu'o'inta a kan Abdul sun fara cika Allah ya fara karkato mata da hankalinsa gareta.
Dama kullum idan ta yi salla sai ta yi ta addu'a Allah ya karkato da hankalinsa gareta. Shi yasa wannan ɗan ƙaramin kusancin da taji yanzu a tsakanin su yasa take ganin kamar wani babban alama ne da Allah ke nuna mata akan ya karɓa.
A haka ta isa gida saboda murna, ko kokon bata tsaya ta sha ba ta wuce Company, don ta san za ta sake ganinsa a can.