Chapter 18
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 18
Sayyada barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
Rayuwa me juyi² a kwan a tashi ba wuya, satin Dr Waahab 3 a Ghana, baya samun hutu kullum cikin zirga-zirga yake, suna fito workshop da kuma kai ziyara manyan asibiti don neman ilimi da kuma bada ilimin.
Sai dare suke dawowa hotel wani lokaci su saya cin abinci a ALAJA SPECIAL RESTAURANT, wani lokacin kuma su dawo hotel saboda gajiya. Hakan yasa ba kullum suke zuwa hotel ba.
Yau ma haka suna dawowa, suka fara biya restaurant cin abincin dare, sun tadda an shirya musu tebur kamar kullum. Abinci suka soma ci saboda gajiya da yunwa, Dr Waahab a nutse yake cin abinci yana shan shayin gargajiya da ake haɗa masa na musamman, yana jin daɗin yanayin.
Bilqees ganin shigowar su yasa ta haɗawa likita fruits salad ta kawo masa, a nutse ta ajiye tare da cewa
"Barka da cin abinci"
Ya ɗago cikin sakin fuska ya ce
"Yawwa special chef"
Ta yi murmushi, sunan da ake kiranta da shi, shi ne shi ma ya faɗa mata, ta ce
"Ƴar koya ce"
"A'a iya haka ma Alhamdulillah"
"Na gode"
"Uhm to ban san sunan gwanar iya girki ba"
"Sunana Bilqees"
"Bilqees!"
Ya furta a hankali, ya sake ɗagowa ya kalleta tare da cewa
"Bilkisu kenan?"
"Eh"
"Nice name"
"Thanks"
"Me gadon zinari"
Ta yi murmushi sosai tare da cewa
"Mu ƴaƴanta ne amma ina mu ka ga gadon zinari"
"Duk da haka Bilkisu me gadon zinari ce"
"Haka ne"
"Sunan Mamata ne"
"Oho! Ya yi kyau"
"Na samu Mama a wajen cin abinci"
Ta yi dariya wacce ta dace da kyakkyawar fuskar bata ce komai ba, ya sake cewa
"Daga yau zan kira ki Mommie nah"
"Zaka tsufar dani"
Ya ɗago ya sake kallon ta ya ce
"Ki zauna mana tun ɗazu kina tsaye"
"A'a"
"Me yasa?"
"Ba zayyu ba"
"Me zai hana?"
"Hakan ya saɓa wa dokar wannan restaurant ɗin"
"Ok na fahimta"
Ta yi masa sai an jima ta wuce. Suna kammala cin abinci suka fice daga cikin restaurant ɗin.
Bilqees ganin sun tafi yasa suma suka shirya suka koma gida.
***********************************
Kasancewar uncle baya zuwa yasa yaran suka mai da hankali kan kyakkyawar Aunty, a kullum sai ta zo ta kawo musu Alawa da biscuit. Duk da haka yaran suna tambayar ta uncle sai ta ce yana uzuri amma zai zo, haka suke hakura.
Yau ma haka suna zaune ta zo ta iske su, suna ganinta suka saka murna suna yi mata oyoyo, suna zagaye ta, ta ce
"Shi kenan kowa ya zauna"
"To kyakkyawar Aunty"
"Yawwa a fara da gaisuwa"
Nan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, haka ita ma ta din ga amsa musu ɗaya bayan ɗaya, sannan ta ce su yi layi, su ka yi ta raba musu Alawa da biscuit suna murna su ka fara sha, tana zaune tana kallon su ganin suna cikin farin ciki hakan yasa ta farin ciki tare da murmushi, wani abu ya ce ɗago ki gani.
Ta hango sa yana tsaye ya kafe ta da manya manyan idanunsa, da alamu ya jima a wajen, sanye yake da jar riga me doguwar hannu me links sa kuma buɗaɗɗen wondo baƙi, ƙirjinsa a buɗe yake kamar ya haka yake dressing nasa, wuyarsa maƙale da sarka kamar kullum.
Gabanta ya faɗi, me kuma ya kawo shi, ganin yana takowa zai iso inda take yasa ta sallami yaran suka bar wajen, ya iso ya zauna a suna facing juna ya ce
"Yanzu haka na koma a wajen ki, abin wulaƙanta wa, why Angel?"
"Abraham we have to leave this place"
"But why Angel, always bushing me away"
"Abraham kana shiga rayuwata da yawa, mun yi wannan maganar ta wuce"
"Ok na ji, to amma ki dinga sauraro na, in ba haka ba zan fallasa kowa ya sani"
"Kada ka soma, bana so, tashi ka tafi"
"I wouldn't go anywhere"
"Ok, to ni zan tafi"
Ta yi sauri ta mik'e da nufin barin wajen ya sha gabanta yana ƙoƙarin riƙe hannunta ta daka masa tsawa
"How dare you try to touch me?"
Ya sauke numfashi yana ji kamar ya janyo ta ya rungume ta, duk duniya ba wacce yake ƙauna kamarta bai san me ya yi mata ba, kwata kwata ta tsane shi yanzu saɓanin da..
"I'm really sorry"
"Ka bar nan wajen?"
"Ok to Amma ba zan hakura ba"
Yana faɗin haka ya bar wajen, ta sauke numfashi, ta rasa ya za ta yi da Abraham...
"Waye wannan guy da ya bar nan yanzu?"
Ta ji sauƙar muryar uncle kamar daga sama, ta ɗago ganin yanayinsa yasa hankalin ta tashi ta mik'e da sauri, tana ci gaba da kallon sa, jikinsa har wani rawa yake idanunsa sun kaɗa sun yi ja.
Tun tuni ya iso a lokacin da yaran suke barin wajen, ganinta zaune ita kaɗai yasa ya yi sauri zai iso wajen kawai yaga wani ya riga sa isowa ya zauna, ya yi turu da kuma mamaki me ya haɗa kyakkyawar Aunty da wannan mutumin da alamu sun nuna ba musulmi bane!
"Uncle....
"Just answered my question Angel"
"Did you asked about my life before? Why should I answer your question now?"
"Who are you?"
"It's not easy to tell you about my life for now"
"Look angel ina da abin yi amma na bari na taho don na ganki, to me yasa za ki yi min haka?"
"Ban fahimce ka ba uncle, ka damu dani ne"
"Wannan wane irin banzar tambaya ne, ban damu dake ba zan zo nan"
Shiru ta yi idanunta suka ciko da ƙwalla ko dai ya faɗa a soyayyar ta ne? Amma ai bai taɓa ganin fuskarta ba!
"Angel we need to talk"
"Not now uncle"
"To yaushe?"
"Ka damu da rayuwata ne?"
Shiru ya yi yana kallonta, a hankali ya fara dawowa cikin hayyacinsa, me yasa ya tashi hankalin shi don ya ganta da wani? Me yasa zai damu? Ina ruwan shi da rayuwar ta? Bai taɓa ganin fuskarta iya sunanta ya sani, amma me yasa ya damu da ita?..
A hankali ya ja da baya, ya dafe goshinsa yana jin kansa na juya masa, but why?....
Yana kallo ta bar wajen ta iso bakin titi ta hau mashin ta bar wajen...
Ya sauke numfashi da ƙyar ya zauna kan dakali, me yasa yake jin wani abu cikin ransa a kanta, shi bai taɓa jin haka ba a kan wata ƴa mace, a hankali ya furta
"Who are you Angel?"
Shin ya hakura da son sanin wacece ita? Ko ya bincika yasan wacece ita? To me yasa zai yi haka? Akan wane dalili?....
"Special doctor"
Ya ɗago ganin Dr Faisal ne yasa ya sauke numfashi ya mik'e tare da cewa
"Ina za ka je?"
"Tafiya za mu yi"
"Ina za mu tafi?"
"Ka baro taro ba ba tare da wani dalili ba, shi yasa OG ya ce na nemo ka"
Ya sauke ajiyar zuciya, me yake faruwa dashi ne? A hankali ya ce
"Mu je"
Suka bar wajen....
***********************************
Bilqees ta kammala shirinta cikin uniform na wajen aiki, ta zauna suna breakfast da Mamanta ta ce
"Mama"
"Na'am Bilqees, ba ki rabo da labari"
Ta yi dariya, tare da cewa
"To Mama da waye zan yi hira in ba dake ba"
"UHM to ina jinki"
"Ina likita da ya bani 20k na maida masa 10k yaƙi karɓa"
"Eh"
"To shi ne ya tambaye ni sunana, na ce Bilqees ya ce ai sunan Maman shi ne"
"To ikon Allah"
"Eh har ya ce Mommy zai na kira na da shi"
"Ah to ya samu mommy me surutu"
Dariya tayi tana kai abinci bakinta sai da ta haɗiye ta ce
"Ai a ranan da ya maida kuɗin cewa ma ya yi na gaishe ki"
"To ina amsawa"
Suna cin abinci suna hira, ALAJA ta bankaɗo labule tana cewa
"To Bilqees sai ki fito mu wuce, in kin saka uwar taki a gaba ba ki son tashi, sai ka ce nono ki ke sha"
Daga Maman Bilqees har ita kanta Bilqees basu ce uffan ba, daman ta kammala ci ta mik'e, Maman Bilqees ta ce
"ALAJA an fito ko? To Allah ya bada sa'a"
"Amin, yawwa yaushe ne watan ƙarin shekara Bilqees?"
"Ai sabon wata da kwana biyu ne"
"Ah to abin ya zo ai"
"ALAJA za ki haɗa min birthday party ne?"
"To uwar taki da ta auri zaman ɗaki me zata yi miki in bani ba, a RESTAURANT zan saka a yi miki cake"
"UHM"
Shine abin da maman Bilqees ta faɗa, ALAJA ba bakuwarta bane, abin da ya fi haka ma zata faɗa. Bilqees ta maƙala jakarta a baya ta sanya takalmi ta fito suka wuce restaurant.
Tun da suka iso suke aiki, babu hutu, kasancewar Alaja restaurant akwai farin jinin customers ba a rabo dasu, wasu na fita wasu za su shigo, har yamma suna tarɓan baƙi, amma da Alaja ta sanar dasu ɓakin international hotel za su zo cin abinci yasa suka maida hankalinsu wajen shirya musu abinci, basu huta ba har sai da suka shirya dining.
Sun iso kamar yadda suka saba, bayan sun zauna ne Bilqees ta kawo wa likita shayin gargajiya, ta ajiye tare da cewa
"Barka da hutawa"
A hankali ya dago duk jikinsa babu kuzari, cikin kulawa ya ce
"Mommie nah sannu, ya aiki?"
"Da godiya"
Ganin yau baya yanayi yasa ta bar wajen, ta koma ciki, ta jima a zaune taga an turo ƙofa aka shigo ganin likita ne yasa ta tashi ta tsaya cikin nutsuwa ya ce
"Ki zauna kada ki damu"
Ta zauna, ya ɗan kishingiɗa da jikin bango, hannunsa na cikin aljihun jacket nasa, yana kallonta ta yi sauri ta sudda kai ƙasa, ya sauke numfashi tare da cewa
"Taimako na za ki yi?"
Ta ɗago kanta suka haɗa ido ta ɗan kawar da idanunta, a hankali ta ce
"Wane irin taimako?"
"Za ki dinga zuwa ɗakina na hotel...
Sai kuma ya yi shiru, ta kura masa idanu tana son ƙarin bayani, me za ta yi a ɗakinsa na hotel?...
Kamar ya san tambayar da ke cikin zuciyarta yasa ya ci gaba da cewa
"Aiki za ki yi min na wata biyu, ni kuma zan biya ki"
Da mamaki ta waro fararen idanunta tana kallon shi, ya sauke numfashi tare da ci gaba da magana
"Bana samun lokacin gyare-gyaren ɗakina ina fita tun safe sai dare nake dawowa, so nake ki kula min da komai na, ki dinga zuwa kina share min da goge²"
"Ba sai ka biya ni ba amma ka yi magana da Alaja"
Ta matuƙar burge shi, ya ɗan yi murmushi tare da cewa
"Wacece Alaja? Ne wannan restaurant ɗin ce?"
"Eh tun da ina aiki a ƙarƙashinta dole sai ta amince zan yi"
"Daman zan sanar mata, amma na fi so na fara ji ta bakin ki, don kada a tilasta yin abin da ba ki so"
Ta yi shiru tana auna kalaman sa, a hankali ta ce
"To ba damuwa ku yi magana"
"Sai kuma ba zan samu lokacin zuwa cin abinci ba, za ki dinga kai min na safe da dare"
"To ba damuwa"
"Amma ki din ga haɗa min da shayin gargajiyar nan"
Ta yi murmushi ta ce
"To"
Ya miƙa mata key na ɗakin bata ansa ba, ta ce
"Ku yi magana tukuna"
"Ki karɓa na san zata amince"
"To in bata amince ba fa?"
"Sai na zo na karɓi mukullina"
Ta sanya hannu ta karɓa, ya ce
"Ki yi sanar mata, ki ce ina so na yi magana da ita"
"To"
Ta ce, sannan ta sanya key cikin jakarta ta fice zuwa ɗakin ALAJA ta samata a zaune ɗauke da takarda da biro tana lissafi, ta nemi izinin shigowa sai da ta bata sannan ta shigo, ta zauna ba ta katse ta ba sai da ta dakatar don kanta ta ce
"Mene ne?"
"Maa ɗaya daga cikin baƙin da suka sauƙa a international hotel ne yake son magana dake"
"To ya jira ni a Corido"
"To"
Ta ce sannan ta fito zuwa ɗakin su ta tadda yana nan yadda ta bar shi, a hankali ta ce
"Zan nuna maka inda za ka jira ta"
"To na gode"
Ta yi gaba ya bi bayan ta zuwa Corido ta ce
"Ka zauna yanzu zata fito"
Tana magana idanunta a ƙasa, ya fahimci tana da kunya, tana ƙoƙarin barin wajen ya ce
"Mommie na gode"
"Ba komai"
Ta ce sannan ta dawo ɗakin ta, ALAJA ta fito ta tadda shi zaune ta fahimci wannan miskilin mutumin nan ne da ranar su ka yi gwagwarmaya, jikinta ya yi sanyi a ranta ta ce ko kashedin da ya yi mata ne yau yazo ya idda, ta zauna.
"Sannun ki"
"Yawwa sannu lafiya ka ke nema na?"
"Ita ta kawo ni"
Ganin bai bata fuskar wasa ba yasa ta ƙame bakinta, ta rasa me yasa take shakkar sa, ita manyan mutane ma ba su isa su ɗaga mata murya ba balantana wannan....
"Wacce na tura ta kira ki nake so ta yi min aiki"
ALAJA ta gyara zama zuciyar ta fal farin ciki, wato ya dawo kan hanya, daman ta san fulako ne, ta ce
"Wane irin aiki?"
"Za ta din ga kai min abincina hotel, sannan zata gyara min ɗakina"
A ranta ta ce, an zo wajen wa ya faɗa masa Borno gabas take, in zai saki ransa ai zai ga tattali sai dai Bilqees bata waye ba har yanzu...
"Ita kaɗai bana so a tura min kowa"
"Ai an gama, zuwa wane lokaci"
"Har mu koma ƙasar mu"
"To ba damuwa, amma tana mun amfani sosai anan"
"Zan biya ki kuɗaɗe"
ALAJA ta washe baki tana
"Ah yanzu na ji batu, daga gobe ma sai ta fara"
"Ba damuwa, kuma...
Sai ya yi shiru ya ɗago ta kalleta, ya fuzdar da iska sannan ya ci gaba da typing
"Ban amince ta yi wa kowa aiki ba"
"Ah ba damuwa Yallaɓai"
Ya mik'e ya bar wajen, cikin farin ciki ALAJA ta koma ɗakinta, sai da lokacin tashi ya yi suka taho gida dukkanin su kamar yadda suka saba.
Comment and share fisabilillah