HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Hs 44

by @legendspen

"senate karka zama mai saurin fushi! Shin baka san cewa makiya na iya shirya komai ba?"
"Mom, please... zan dawo idan na samu natsuwa. Amma yanzu, bar ni in kaɗai Bhatool kuma na haƙura da ita har Abada." Ya faɗa  tare da kashe wayar cikin halinsa na rashin son yawan magana idan ransa ya ɓaci. Ya kashe wayar ya bar Mom cikin damuwa.

"Na haƙura dake Bhatool... na haƙura dake har abada Bhatool, ki je ki yi duk abinda kike so, duk abinda kika ga dama."

Amrah ta fito daga gidan Anty (Maman Anas) tana wani irin kuka mai cin zuciya, wanda ya sa har mutanen dake wucewa a kan titi suke kallonta. Zuciyarta tana mata wani irin zafi, kalaman Anty dake nuna cewa an yi amfani da ita ne kawai don biyan bukatar wata daban suna ta kai-kawo a kanta. "Ashe ni ma yaudarata aka yi? Ashe ba don ni aka yi wannan shirin ba?" Ta faɗa a cikin ranta tana goge hawayen dake bin kuncinta.
Ba ta tsaya ko'ina ba sai gidansu Jannah. Tana shiga ta iske Jannah a tsakar gida tana gyara wasu littattafai. Jannah ta tashi da sauri ganin halin da Amrah take ciki. "Lafiya Amrah? Me ya faru kike kuka haka?" Jannah ta tambaya cikin firgici.
Durƙusawa Amrah ta yi a ƙasa, ta rufe fuskarta da hannu biyu tana sheshsheƙar kuka. "Jannah na cuci kaina, na cuci Bhatool, na ruguza auren da ba ni da tabbacin zan iya maye gurbinsa. Jannah ashe Anty amfani da ni ta yi, ashe kishina ne aka yi amfani da shi aka raba auren Senate da Bhatool ba don ni ba."
Jannah ta zaro ido, ta jawo Amrah ta zaunar da ita a kan kujera. "Amrah me kike cewa haka? Kina nufin duk abubuwan da suke faruwa ke kika kitsa su?"
Cikin kuka da nadama, Amrah ta kwashe dukkan abin da ya faru ta faɗawa Jannah. Ta faɗa mata yadda suka shirya hotunan da aka liƙa fuskokin Bhatool ta hanyar amfani da fasahar zamani (AI), da yadda ta ari lace ɗin Bhatool aka yi amfani da shi aka ɗauki hoton wata daban. "Jannah ina son in wanke Bhatool, ina son in gyara kuskurena ko da hakan zai sa kowa ya tsane ni. Zuciyata ba ta ba ni damar yin bacci ba tun bayan da na ji an sake ta." Amrah ta faɗa muryarta tana rawa.
Jannah ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalli Amrah cikin tausayawa da kuma fushi. "Amrah, gaskiya kin tafi wurin da ya wuce tunaninki. Amma tunda Allah ya sa kin yi nadama, to tashi mu tafi gidan Yaya Karima yanzu. Dole ne kowa ya san gaskiyar abin da ya faru kafin lokaci ya ƙure." Jannah ta faɗa tana miƙewa don ɗauko mayafinta.
A can gidan Yaya Karima kuwa, falon ya cika makil. Mom ce zaune a kan kujera, fuskarta ɗauke da damuwa tana ta kallon Bhatool dake kwance a jikin Yaya Karima. Abdul yana zaune a ƙasa riƙe da wayar Bhatool dake gyare, yayin da Mijin Yaya Karima, Barrister Al-Amin, yake zaune yana duba wasu takardu, amma hankalinsa duka yana kan maganar da ake yi.
"Mom, gaskiya wannan lamari akwai duhu a cikinsa. Usman ya yi gaggawa wajen yanke hukunci ba tare da ya bincika ba," Barrister Al-Amin ya faɗa yana kallon Mom.
"Haka ne Al-Amin. Ni kaina kiran da na yi masa ɗazu na ga cewa ya rufe kunnensa daga jin gaskiya. Amma ina tabbatar muku, muddin muka sami shaidar cewa wannan sharrin wani ne, to ni kaina zan sa ya dawo ya ba ta haƙuri," Mom ta ba shi amsa cikin murya mai natsuwa.
Bhatool dai tana can tana saurarensu, hawaye kawai yake zarya a idonta. Tana tunanin yadda Amrah ta iya aikata mata haka, kawai sai ta ji an turo ƙofar falon.
Amrah ce ta shigo, idanunta sun yi luhu-luhu saboda kuka, Jannah tana biye da ita a baya. Ganin Amrah ya sa Bhatool jin wani irin zafi ya taso mata daga ƙasan zuciya. Wani irin ƙarfi ne ya zo mata, ta miƙe tsaye da kyar tana nuna Amrah da yatsa, muryarta tana rawa saboda tsananin fushi.
"Amrah! Me kika zo yi a nan? Kina son ki zo ki ƙarasa abin da kika fara ne? Kin cuce ni Amrah! Kin raba ni da mijina, kin zubar mini da mutuncina a idon duniya! Don Allah ki fita mana daga gida, muguwa kawai! Ba na son sake ganin fuskarki a rayuwata!" Bhatool ta faɗa tana rushewa da kuka mai ban tausayi, yayin da jikinta yake wani irin rawa.
Mom da Yaya Karima duka suka miƙe tsaye cikin mamakin ganin Amrah a wannan lokacin. Abdul ya daka wa Amrah wani irin kallo na tsana, yayin da Barrister Al-Amin ya gyara zamansa yana jiran jin abin da zai biyo baya.
Amrah ta kasa cewa uffan, sai kuka da take yi tana ƙoƙarin durƙusawa a ƙasan ƙafafun Bhatool. Jannah ce ta matso kusa da Bhatool, ta riƙe hannunta cikin lallashi. "Bhatool, don Allah ki yi haƙuri. Na san abin da Amrah ta yi miki ya wuce misali, amma don Allah ki saurare ta. Ta zo ne don ta gyara, ta zo ne don ta faɗi gaskiyar da za ta wanke ki a idon kowa." Jannah ta faɗa cikin muryar roƙo.
Anan duka falon ya yi tsit, kowa yana jiran jin wane irin asiri ne Amrah za ta tona wanda zai iya canja akalar wannan babban al'amari.

Falon ya yi tsit, har ana iya jin numfashin kowa dake wurin. Amrah ta durƙusa a ƙasa, kanta a duƙe, yayin da take sheshsheƙar kuka mai ban tausayi. Ta ɗago idanunta da suka yi jawur ta kalli Bhatool, sannan ta kalli Mom da Yaya Karima.
"Bhatool, na san ba za ki taɓa yafe mini ba, amma don Allah ki saurari abin da zan faɗa. Ni ce na kulla miki dukkan abubuwan da suka faru, tun daga ranar farko da kika tare a gidan miji," Amrah ta faɗa muryarta tana rawa.
Bhatool ta rufe fuskarta tana kuka, yayin da Barrister Al-Amin ya gyara zama ya ce, "Ci gaba Amrah, muna jinki. Faɗi komai filla-filla."
Amrah ta ja numfashi, ta fara bayani cikin muryar nadama. "Ranar farko da na zo ganin gidanki Bhatool, ba ta yaki murna na zo ba. Na zo ne don in dasa miki abin da zai raba ki da Senate. Lokacin da kika kai ni zagaya gida, na yi amfani da damar da kika ba ni na shiga ɗakin baccinku, na ɗauki wani magani na fesa a ƙarƙashin gadonku, wanda nake tsammanin zai sa ku dinga jin ƙyamar juna. Kuma ranar da kika ga Senate ya dawo yana ciwon kai, ni ce na sanya hakan  turaren da fesa ne ya sanya mai ɓacin rai lokacin da yake waje."
Mom ta zaro ido, ta dafe ƙirji tana faɗin, "Subhanallahi! Amrah ashe dukkan wannan abin ke kika yi?"
Amrah ba ta tsaya ba, ta ci gaba. "Sannan ranar  dazo gidanki  na ja ki kika rakani waje duk shiri ne. Shi ma Ahamd mune muka shirya masa zuwa amma bai san da zuwan ki ba, mun yaudareshi ne kuma mine mu ka yi miki hoto, haka hoton nan na ari lace dinki nasa akayi hoton, shi ya sa na matsa miki lallai sai kin sanya wannan lace ɗin naki mai kyau. Na ce mikk na ari lace ɗin a wajenki da sunan zan tafi biki, amma ba inda naje nasanya ne, aka ɗauke ta hoto tana rungume da wani namiji a wani gida, sannan aka yi amfani da hoton fuskarki aka liƙa a jikinta."
Yaya Karima ta girgiza kai cikin takaici. "Lallai Amrah kin yi nisa. Amma wacece ta ba ki wannan shawarar? Domin na san ba za ki iya yin wannan duka ke kaɗai ba."
Amrah ta kalli Mom cikin tsoro, sannan ta ɗauko wayarta ta kunna wani sauti (recording). Muryar Anty (Maman Anas) ce ta fito sarai tana faɗin: "Amrah kinyi mini aiki mai kyau. Kin san fa Senate ɗana ne, kuma ba na son ganinsa da wannan yarinyar tun farko. Ke kin yi amfani da kishinki, ni kuma na yi amfani da hikimata wajen ganin na raba su..."

Wani irin jiri ne ya kwashi Mom, ta koma ta zauna da sauri. "Anty? Maman Anas? Ƙanwata ce take son ruguza farin cikin ɗana?" Mom ta faɗa cikin wani irin murya mai ban tausayi, hawaye ya wanke mata fuska.

Abdul ya daka wa Amrah tsawa. "Muguwa! Kalli irin abin da kika aikata. Kin ruguza aure saboda kishin banza."

Bhatool ta miƙe tsaye, tana kallon Amrah cikin wani irin yanayi na tsana da tausayi lokaci guda. "Amrah, na gode da kika faɗi gaskiya. Amma ki sani, kin riga kin illata zuciyata. Kin raba ni da mutumin da na fi ƙauna a duniya."

Barrister Al-Amin ya miƙe ya karɓi wayar Amrah dake ɗauke da recording ɗin. "Wannan ita ce shaidar da muke buƙata. Yanzu saura abu ɗaya, dole ne Senate ya ji wannan muryar, kuma dole ne ya ga wannan gaskiyar."
Amrah ta rushe da kuka tana neman gafarar kowa dake wurin, amma kowa ya juya mata baya, domin abin da ta aikata ya wuce duk yadda ake tunani.

"A'a tunda har Senate bai sami yarda dani ba, ya yarda da wani abu daban, har ya iya sakina nima na hakura da Senate har Abada."

Legendspen
***