2
*HUDU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 2.
Sarac Stars R Pen...✍️
Gargaɗi
*Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a bar mini sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Baba ne ya tsaya a ƙofar yana leƙensa dan lokacin daya dawo mama ta faɗa masa duk abunda ya faru ɗazun, yace cikin sakin fuska.
Babban mutum ka dawo kenan.
Shuru Mujaheed bai ce komai ba sai dai ya miƙe, baba kuwa ya saki labulen ya koma da baya ya tsaya a tsakar gida saboda warin dake ziyartansa ba zai jure masa ba, cikin sauri Mujaheed ya biyo bayansa ya tsaya nesa da shi, baba ya ce.
Yau ance ka ɗauko min magana ko, meyasa haka Mujaheed.? Ko baka cin abincin da baya isarka ne da zaka fara ɗaukar kayan mutane.? Anya kana so mu shirya ni da kai kuwa.?
Ya ƙare maganar yana tsura masa ido cikin tausayinsa, Mujaheed ya sunne kai ƙasa yana matsa yatsun hannunsa yaƙi cewa komai, mama ce da ta fito take cewa cikin jimami.
Ai Mujaheed ba zai baka amsa ba dan wlh zan iya cewa kamar ya daina magana gabaɗaya, kusan sati biyu kenan da naji muryarsa a lokacin yana magana da Aina'u akan tace zata samo masa icen dalbejiya ya riƙa asuwaki tunda yaƙi yin brush.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Salamatu lamarin yaron nan kamar ƙara gaba yake yi, Ina Sha Allah zan sake amso masa maganin jinnu da muka taɓa karɓo masa kwanaki.
To malam banƙi ta taka ba amma da aljanu ne da tuntuni sun nuna, kawai dai kasan wani bagalar baya zuwa wa yaro cikin sauƙi ne, shi dai nashi da ƙazanta tazo da kuma mislikanci, kuma magani ai munyi shi sosai a baya, kawai mu dage da addu'a Allah ya kawo ƙarshen lamarin.
Ameen ya rabbi. Yauwa juye min ruwan zafin na tsawa dan a gajiye nake yau.
To mama ta faɗa ta wuce Kitchen sai Mujaheed ya juya zai shiga ɗaki.
Kai wuce ka amsa abincinka ka ci, ko kaci wani abun a waje ne.?
Baba ya faɗa yana nuna masa ƙofar kitchen, Mujaheed dai yaƙi tanka masa sai dai ya juya ya tafi ya tsaya har mama ta juyewa baba ruwa a bokiti kafin ta miƙa masa, sai ta koma ta ɗibowa Mujaheed tuwo ya amsa ya wuce ya zauna anan tsakar gidan ya ci, daya gama ya bar robar a gurin ya koma ɗaki yana goge miyar hannunsa a jikin riga, ya isa wajen karikitansa yana cigaba da auna wannan agogon yana tattaɓa injin bayansa, sai kuma ya kai shi jikin kunnensa yayi kasaƙe kamar yana ɗaukar darasi, daga bisani ya kawo shi gabda idonsa ya ƙanƙance yana auna abunda yake buƙata a cikin kansa, ya jima yana wannan aikin da babu wanda ya saka shi, daya gaji ne ya ɓingire a gurin ya fara bacci.
Da safe Mujaheed ya farka yana mai ƙanƙance ido saboda hasken gari daya so kashe masa shi, Aina'u ce ta shigo tana cewa.
Yayanmu tun ɗazu nake tashinka amma kaƙi motsawa. Kazo in ji baba yanzu.
Guntun Murmushi yayi mata kafin ta wuce zuwa ɗaki dan tayi shirin tafiya wajen koyan ɗinkin da mama ta sakata, Mujaheed ya miƙe sai ya cire kayan jikinsa ya ɗauko wasu manyan kaya masu datti ya mayar sai ya ɗauki wannan agogon da tochlight ya saka a aljihu ya fice daga gidan ba tare da yaje kiran baban ba, yana fita wani yaro ya fara tsokanarsa da sha tara yana yi yana rawa.
Ya sunanka.? sha tara, sunan babanka sha tara, sunan mamanka sha tara.
Mujaheed da ya ji haushin ambaton sunan iyayensa sai ya zabura zai kaiwa karon duka shi kuma sai ya ruga yana kyakyalewa da dariya, ya cigaba da yi masa wannan waƙar yana ƙara tunzura shi, Mujaheed daya samu sa'a ya tsafki yaron ya soma kifa masa mari, a lokacin kuma yayan yaron ya fito daga gida yaga abunda ke faruwa, sai yazo cikin sauri ya soma kaiwa Mujaheed duka yana zaginsa, Mujaheed da yake kan ba daɗi yaji wani sabon ƙarfi ya zo masa sai ya saki yaron da ya fara duka ya juya kan yayan suka soma dambe, nan da nan mutane suka fara taruwa aka shiga rabon faɗa. Baba ya fito kenan da niyyar wucewa kasuwa ya tadda wannan taƙaddamar, cikin azama ya isa gurin ya damƙo wuyar rigar Mujaheed ta baya, yasa dayan hannun ya ɓamɓare hannunsa daya kama wuyan rigar wannan yaron ya jashi baya, sauran mutane da suke rabo suka ja Anas shima, Mujaheed ya fashe da kuka yana huci domin ya kai ƙololuwar ɓacin rai musamman da Anas ya dinga zagin uwarsa, baba ya shiga tambayar ba'asi sai Anas ya sanar da baba cewar ai Mujaheed ne ya fara dukan ƙaninsa shi ne ya rama masa, cikin fusata baba ya juya ga Mujaheed.
Me yayi maka da zaka duke shi.? meyasa zaka fara tsiro da halin da banaka ba Mujaheed.?
Ai jiya ma burodi ya ɗauko a shagon malam Hamisu, gaskiya malam Musa idan matsalar yaron nan zai riƙa haifar da damuwa a cikin unguwa gwara a kai shi can asibiti mahaukata a tirkeshi in da rabon ya samu sauƙi sai kaga ya natsu. Ba zai yiwu ya riƙa sakawa yaranmu hannu ba mu zuba ido mu kyale, dan tunda ya fara haka to nan gaba ba za a kwashe ta daɗi ba.
Cewar babansu Anas ransa a ɓace, jikin baba ne yayi sanyi zuciyarsa tayi masa nauyi da jin furucin baban Anas, yanzu mutane sun lalace da son 'ya'yansu ƙiri-ƙiri suke nuna son kai babu kara, saɓanin mutanen da da suke da kawaici da kara.
Ayi haƙuri In Sha Allah ba zai sake taɓa ɗan kowa ba, amma kuma ku jawa 'ya'yanku kune su daina tsokanarsa saboda Muhajeed ba zai daki yaro hakanan ba, dan rashin hankalinsa bai kai haka ba, kuma In Sha Allah zai samu lafiya.
Ya ƙare magana yana kama hannun Mujaheed suka juya zuwa gida, mutanen dake wajen suka shiga mayar da magana wasu na bayan baban Anas wasu kuma suna bayan baba, haka dai taron ya watse rai babu daɗi. Baba yana shiga gida ya tadda mama a tsakar gida ya shiga bata labarin abunda ya faru, mama ta yi ƙwafa tace.
Ai wlh mutane basu da kirki, sannan shima Mujaheed waye yace ya fita ko karyawa bai yi ba salon yaje ya ɗauko abun wani azo ana wallahi tallahi, ni ko dai zamu gwada asubitin mahaukata ne muga ni ko zamu dace.
To gamu ga Allah, bari inna dawo sai muyi shawara akan lamarin, gashi nan ki bashi abinci ya ci ya ƙoshi.
To malam a dawo lafiya, amma ya batun maganar kayan katako na Aina'u nafi so fa mu fara shiri, dan da su yaya Tijjani sun zo za a tsayar da ranar aure bana so a sashi da nisa.
Salamatu wannan maganar da an jinkirta tukuna naje ƙauye na sanar da Innata kafin su zo ayi magana.
To duk yadda ka gani Malam, Allah ya nuna mana lafiya.
Ameen Ya Rabbi, baba ya faɗa kafin ya fice cikin sauri, Mama ta danƙarawa Mujaheed harara.
Babu wanka babu wanki balle Sallah da salati, yanzu shikenan rayuwarka Mujaheed ta koma baibai ka gama zama cikakken mara hankali, idan ma yaron ya zageka ne tabo zai fito a jikinka ne.? daga yau kar naji ka sake taɓa yaran mutane dan ba zaka saka mu yi shari'a da kowa ba wlh.
Tana gama faɗar haka ta wuce ɗaki tana kwalawa Aina'u kira, koda ta fito daga ɗakinsu tana ɗaura dankwali.
Kiyi maza ki shirya ki wuce kar ki ɓata lokaci dan zaki kai min kuɗin dashi gidan Baraka.
To mama, amma wai sai yaushe za a baki kwasa ne.?
Sai an saka bikin aurenki dan dasu zan yi miki siyayyar kayan kitchen na zamani.
Uhum Aina'u ta faɗa tana murmushi ta yi gaba mama tace.
Ja'ira naga kema kina son wannan auren sosai, wai ko kina waya da Idi ɗin a waya.
Kai mama wani irin Idi, Idris dai, kuma ko ɗazun da safe munyi magana yace in gaishe ki, yace cikin satin nan za a zo tambaya.
Eh lallai kice soyayya ta kankama, amma dai da gaske kina sonsa ko.? dan kar kisa mu zo muji kunya ki ɓata mana zumunci.
Mamanmu ai yaya Idris ɗan Uwana ne kuma kema kin tabbatar min da zai riƙe ni da mutunci, kuma kin ce zan zama fitila a garin tunda ina da ilimin addini ko.?
Sosai ma kuwa ai wlh Aina'u zaki farin ciki sosai dan na tabbatar Idi ba zai wulaƙantaki ba tunda da ubansa damu uwa ɗaya uba ɗaya, can ɗin ma gida ne a wajenki, ga ɗinki kina koya haka zaki samu taro da sisi dan in kin je ba zama zaki ba, babanku ma yace zai siya miki keken ɗinki sabo.
To Allah ya zaɓa mafi alkhairi, bari na ƙarasa shiri.
Yauwa ki je kitchen ki bawa yayanku tea ɗinsa ki kwashe masa sauran doyar data rage, idan kuma ba zai ci ba ki aje min anjima su Nasir zasu ci.
To Aina'u tace kafin ta fito tsakar gida ta samu Mujaheed a tsaye kamar rodi tun ɗazu bai matsa daga inda ya tsaya ba, yana ma jin hirar da suka gama yi, Aina'u ta zuba masa tea da yake a robar fenti har yayi sanyi dan tun ɗazu mama ta haɗa suka karya, ta kwashe masa doyar tana ƙirga sauran daya rage bai fi guda shida ba, ta tabbar wannan ba isar yayansu zai yi ba, ko da yake mama da kanta take taƙaita saka masa abincin a cewarta in ta zuba masa da yawa wulaƙanta wa yake yi, kuma akan tayi asara gwara a saka masa kaɗan in zai ƙara sai yayi magana, wanda shi kuma koda yana buƙatar ƙari ba zai taɓa yim magana ba, ɗan abunda aka bashi zai ci koda bai ƙoshi ba zai kakkaɓe riga ya wuce abunsa. Aina'u ta fito ta miƙa masa ya kalleta ta gefen ido zuwa abunda take miƙa masa, yayi matuƙar raina abunda ta bashi dan ko tea ɗin a ƙaramar kofi yake, sam abincin da ake bashi yanzu baya isarsa wanda hakan yasa shi jiya ya saci buredi dan ya cika cikinsa saboda bai yi karin arziki ba, kuma koda rana mama abinci kaɗan ta saka masa tana mitar ba zata saka da yawa ba dan in ya saka hannu ya zama haramiyarsu dan babu wanda zai ci saboda ƙazantarsa, yasan cewa hatta 'yan gidansu suna kyankyaminsa da kyararsa, Aina'u ce kawai bata yi masa komai dan sauran ƙannensa ma sun raina shi, basa shayin yi masa rashin kunya, Nasir da yake autansu har baban bola yake ce masa kuma mama bata hana ba dan ko ya nuna fushinsa cewa take ya gyara ya riƙa tsafta sai kowa ya ganshi da mutunci, shiyasa idan mutanen waje suka yi masa baya jin zafi domin a gidansu ma bai tsira ba.
Yayanmu ko ba zaka ci bane na dafa maka indomie.?
Ba zaki dafa komai ba in ba zai ci abunda kowa yaci ba ya barshi, sannan da kike maganar ki dafa masa indomie shagon waye zai je miki.? kuma kina sane da nace zan aikeki ki kai mini kuɗin adashe.
To mamanmu yaƙi amsa ne fa.
Dungure masa anan in ya gaji zai ɗauka.
Duk wannan maganganun mama tana yinsa ne daga cikin falo tana zaune, Aina'u bata yi abunda maman tace ba ta cigaba da riƙe masa kayan karin tare da rausayar da fuska kamar zata fasa kuka, Mujaheed yayi kwafa ba dan ita ba ba zai ci ba saboda faɗan mama ya ɓata masa rai, ya amsa ya koma can bangon dake kusa da ƙofar gida ya zauna a ƙasa ya fara ci, Aina'u har ta juya zata tafi taji maganar Mujaheed kamar a mafarki.
Kin yarda da auren da za a yi miki bayan a da nasan karatu kike so.?
Da sauri ta juya gurinsa taje gabansa ta tsuguna fuskarta ɗauke da yalwar mulmushi.
Yayanmu yaushe rabon daka yi magana.? dan Allah ka daina yawan shurun nan shima wani matsalar zai jawo maka.
Guntun murmushi yayi mata yana girgiza kai domin yasan ita ce kaɗai zata fahimce, shi shiyasa baya magana da kowa a gidan da ma a waje sai ita tilo, yana matuƙar jin tsoron yin magana tun lokacin da yanayin lalurarsa ta fara bayyana, saboda gwasale shi da ake yi da hantara, wannan ya saka masa mugun shakka da tsoron kar a kyare shi, wasu kuma suna ce masa mai muryar mata saboda a hankali yake magana, a nan gida kuma idan yayi magana mama cewa take ya riƙa buɗe baki ya faɗi abunda zai faɗa ya daina yi ciki-ciki, shi kuma akan ya buɗe murya gwara ya yi mata shuru, baba kuma cewa yake ai wannan sanyin maganar nasa dole ne ya jawo masa raini me yasa baya abu kamar namiji.? Aina'u ta katse masa tunanin da cewa.
Yayanmu ina son yaya Idris ko ka mance dangantakar dake tsakaninmu.? Mamanmu ta tabbatar min da can ma gida ne zan samu kulawa kamar ina gabansu, kuma baba yace zan cigaba da karatu har na ƙare secondary, ga sana'ar ɗinki ina koya wanda mama tace zan zama abar alfahari a garin, sannan wataƙila ma na samu koyarwa a Islamiyya.
Ina miki maganar Zamfara ne fa ƙaramar hukumar Anka ƙauyen Magami, kin tashi a birnin Kaduna ya rayuwa zata yi miki daɗi a kauye Aina'u.?
Yayi maganar yana katseta tare da ƙare zancensa cikin kafeta da ido yana taunar doya ga fegen bakinsa yana tara farin yawu. Aina'u ta ƙara sakin murmushi.
Shiyasa nayi maka wannan bayanin cewar idan nayi aure a can zan zama kamar wata tauraruwa ce, kuma da Baban Idrisa da Mamanmu uwa ɗaya uba ɗaya, sannan kuma kowa yana son auren kuma yaya Idris bai da makusa illa abunda nake ji matarsa ɗaya da yara biyar, amma Innarsu Idris ta tabbatar da matarsa ba tada matsala shiyasa mama ta ƙara yin na'am da haka.
Shikenan.
Cewar Mujaheed a taƙaice, Aina'u nayi jim ko zai kuma magana amma taji shuru dan haka cikin kwarin jiki ta miƙe da tunanin shima ya karɓi zancen aurenta, cikin yanayi na tausayinta ya bita da kallo wanda yake guje mata ta samu kanta a yanayin duhu bayan murmushi, ya tabbatar wannan ba shi ne mafarkin Aina'u ba sauya mata aka yi saboda ƙarancin shekarunta da kuma rashin wayo, dududu shekarunta sha biyar ta gama zana jarabar junior WAEC zata Shiga SS 1, kawai tun zuwan da suka yi wani biki da mama can Magami sai suka dawo da zancen Idrisa yaga Aina'u yana so, yayi zaton ko baba zai ce abari tukuna amma sai yayi na'am da batun musamman yadda mama tayi kane-kane akan maganar cewar auren dangi ne kamar tuwona maina ne, sannan zata cigaba da karatu kamar yadda kawu Tijjani ya faɗa, kuma ita tana tsoron zamani gwara ta kawar da ita tunda ta girma tana jinin al'ada, ko Zara itama tana ƙara tasawa kamar Aina'u zata yi mata auren wuri, shiyasa babansu ya amince da batun sannan yace ta koyi ɗinki hakan ma zai yi mata amfani, hakan yasa Aina'u ta fara zuwa shagon koyon ɗinki tana cigaba da zuwa Islamiyyar Hadda dan tuni tayi saukar Al-Qurani da Hadisai, yanzu haka tana da izu ashirin data haddace, shi kuma Mujaheed bai taɓa cewa komai akan batun auren ba sai yau, amma a nashi ganin kamar kashe rayuwar Aina'u za a yi ace daga binni a kaita ƙauyen Magami, duk da suna da wuta kuma akwai karatun boko na gomnati amma fa akwai bambanci a tsakanin rayuwar cikin binnin Kaduna da ƙauye, sai dai kuma guiwarsa ya sare tunda ita ma tana son auren bayi da bakin magana, ko da ma yayi to bayi da power tunda a kullun shi mutum ne mara amfani a gurinsu, shi kam a yadda yake rayuwa a haka yana yi masa daɗi ganin babu mai shiga harkarsa, sai yara da suke tsokanarsa wannan kuma ya saba, baya ganin wani aibu a halin da yake ciki kuma baya ganin ƙazantarsa, baya jin warin jikinsa, a wurinsa komai normal ne, shi dai gashi nan ne kawai.
Rahman ce.