CHAPTER 13
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
SHAFI NA SHA UKU
Duk yowa kansa suka kai ana tambayar sa me ya faru, amma Sufyan bai kula da kowa ba. Lalumar wandonsa yake yi, yana duba jikinsa ko zai ga wani abu, amma bai ga wata alama ta komai a cikin wandonsa ba. Hakan ya sa ya fara tunanin ko wani abu ne ya cijesa.
Ya karkade jikinsa yana cewa, “Ina ga kwaro ne. Mu je ka…”
Bai karasa maganar ba ya ji wani irin zafi mai tsanani yana tashi daga cikin wandonsa. Bai san lokacin da ya fara ƙoƙarin zame wandonsa daga jikinsa ba. Abokan wasansa kuwa suka riƙe shi suna jan wandonsa sama, shi kuma yana ja ƙasa.
Cikin yanayin ruɗani ya ce, “Ku! Zafi ne fa! Wuta ce a ciki! Kai, ku bar ni in cire, na shiga uku!”
Yana magana yana hura baki tare da bige hannayensu.
Daga ƙarshe ya samu ya zame wandonsa, sai rigar Jessy kawai ta rage masa a jiki. Nan take ya fara tsalle-tsalle saboda zafin.
Suka riƙe shi, amma shi yana ci gaba da sambatu.
“Na mutu! Zan mutu! Shikenan, duwawuna ya mutu! Zafin azaba! Zafin mutuwa!”
Yana karkade wajen da zafin yake.
Ɗaya daga cikin ’yan wasan ya ɗauki wandonsa yana dubawa, sannan ya ce, Kai! Sufy, wannan ai kamar wani abu ne na kayan miya ya manne a jikin wandon. Ga shi nan, ƙanana-ƙanana kamar an yi jajjage!”
Da jin haka, sai suka runtuma da dariya.
Shi kuwa Sufyan tuni ya baje a ƙasa. Abu ɗaya yake ta faman yi fifita don kawar da zafin, ga baki a wangale.
Habib ne ya je ya nemo masa wani wando, ya dawo da shi.
“Ga wannan, saka. Kai, ko kunya ba ka ji? Tsirara kake fa.”
Sufyan ya ɗago da jajayen idanunsa da suka cika da azaba ya ce, “Na bi kunyar da gudu! Kai, ka san irin azabar da nake ji ne wai? dallah Malam hani guri.”
Habib zai yi dariya, sai ya kimtse bakinsa.
“Sorry. Taimaka dai ka karɓa ka saka, don wallahi yanayinka ba kyan gani.”
Sufyan na ci gaba da fifita ya ce, “In saka, in ƙara shiga wata ukubar ko?”
“A’a fa, saka kawai mu je ka wanke. Don wannan fifitar da kake yi ba mafita ba ce.”
Habib ya faɗa yana ƙoƙarin danne dariyarsa.
Da ƙyar suka tasa Sufyan ya sanya wandon, sannan suka kama hanya. Yana tafiya a gwale kamar wanda aka yi wa kaciya, yana ta fifita zafin da yake ji, har suka isa wani public toilet.
Shiga ya yi, ya sake yin wanka sosai, ya wanke wajen da kyau har ya ji sauƙi kafin daga bisani ya fito.
Ranar training ɗin ball ɗin da ba a yi ba kenan, kowa ya kama gabansa. Habib da Sufyan suna zaune cikin mota, sam fuskar Sufyan babu annuri ko kaɗan.
Habib ya ce, “Sufy, wai garin ya ne? Me ya ji ya shiga maka cikin wando haka?”
Sufyan ya ce, “Sharrin Farida kuma wallahi! Sai ta yi da-na-sanin yi min wannan tozarci. Jiya na sa ta yi min wanki ne da dare, shi ne wato bara ta shirya min mugunta. Kuma dama fa da zan fito sai kallona take tana dariya, ni ban gane ba. Ashe abin da ta shirya kenan. Hmm.”
Ya ƙarasa maganar yana kwafa.
“Wai yanzu ku aiki ya same ku kenan? Kullum burin kowa ya baƙantawa ɗaya? Kuma ita da ta tashi tata muguntar ma sai a wando?”
Habib ya ƙarasa maganar yana kyalkyala dariya.
Sufyan ya bishi da kallo, “Ka ga kai matsalata da kai kenan ko? Abun komai dariya ne wai?”
Habib ya girgiza kai, “Sorry Sir. Oh ango! Don har yanzu ango ne kai tunda ba a ci amarci ba. Angon gado! Yah Ahmad ya mutu ya bar maka gado mai girma. Kai kam, yanzu ya za ka yi da ita ne? Batun ya ji a wando fa, kar wata rana a bika da cinnaka kuma.” Ya fada yana kunshe baki kar dariya ta fito.
Cije baki Sufyan ya yi yana cewa, “Ka bar ni da ita ai, in tasan wata, bata san wata ba. Yanzu ya ina za ka je? Ni gida zan nufa saboda har yanzu ban gama dawowa daidai ba.”
Habib ya ce, “Ah, ya ci kam ka koma ka huta ai. Muje kawai, nima ka sauke ni a family house dinmu.”
Tafiya suka fara yi. Suna cikin tafiyar sai ga kiran Inno ya shigo wayar Sufyan. Ta shaida masa cewa lallai ya zo, tana binsa.
Hakan ya sa bayan ya sauke Habib, ba inda ya nufa sai gidan Inno.
Da yake har dare ya yi, ya tarar da Baba Haruna, Abba Shuaibu da Kawu Hamza suna zaune suna hira da Inno.
Yana shiga bayan sun gama gaisawa, Inno ta ɗauko kwandon zogale ta miƙa masa.
“Gashi nan, ka kai wa matar taka. Kasan ciki sai an tashi tsaye an kula da shi. Ina fatan dai ba ka takura mata ko? A dunga binta a hankali, sannan duk abin da ta ce tana da buƙata, kar ka yi garaje wajen siyowa. Yanzu ita abar tarairaya ce.”
Girgiza kai kawai Sufyan ya yi, domin ba shi da damar magana ko musawa Inno, tunda ga iyayensa nan zaune. Ya ɗauki kwandon, yana shirin tashi, sai Inno ta dakatar da shi.
“A’a, fa! Dakata. Dama tun tuni kai nake jira. Akwai kayan wankan jariri da muka saya ni da Hansai. Ɗauka za ka yi ka tafi da su can ku ajiye, saboda kar haihuwa ta zo ranga-ranga kayan ba su nan. Akwai na sawa ma suna gun Kulu, idan ta gama wanke su zan sa ta aika muku.”
Sufyan ya bi tulin kayan da ke cikin buhun da kallo. Takaici ya turniƙe shi. Ba yadda zai yi, dole ya ɗauka.
Amma babban abin da ya fi damunsa shi ne yadda kowa yake kallon cikin da ke jikin Farida a matsayin nasa.
Shi yaushe ma zai bari ya haɗa jikinsa da ita, bayan ta gama yawo ta sakar wa wasu? Bare ma kuma ko da wasa ɓaya jin cewa akwai ranar da zata birgisa.
Haka ya ja buhun ya fito da shi daga ɗakin, rai a ɓace. Ya jefa shi cikin motarsa sannan ya shiga.
Yana isa gidan, bayan ya yi parking, ya fito ya ɗauko buhun tare da kwandon zogalen ya shiga cikin gidan. Ganin Farida ba ta falo sai ya afka cikin ɗakinta.
Tarar da ita ya yi zaune a kan sallaya tana jan carbi. Ganinsa kawai ta yi a gabanta kamar an jefoshi, hakan yasa gabanta faɗuwa.
Wurgar mata buhun ya yi a jikinta, flask ɗin zogalen ma ya tura mata da ƙafa.
Kallon rashin fahimta Farida ta fara binsa da shi, sai ya ce,
“Ga tarin kayan ki nan, Inno ta ce. Ina ga kin manta da batun da na miki kan cewa ki zubar da cikin shegen nan, ko? Ba zan taɓa karɓarsa ba ke. Ko da ace tsautsayi ya sa cikin nan nawa ne, sai kin zubar, bare kuma na wani can ɗan iska. Na yi miki gargaɗi na ƙarshe kenan.”
Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin cikin fushi.
Ita kuwa Farida, duk a tunaninta zai yi mata maganar attarihun da ta sanya masa cikin wando ne, amma sai ta ji saɓanin haka.
Da ya fita, ta taɓe baki ta ja flask ɗin zogalen kusa da ita ta fara ci. Har cikin ranta tana matuƙar son zogale, fil azal, hakan yasa ta zauna tana cin abunta. Sai da ta cinye tas kafin ta tashi ta kalli buhun da Inno ta aiko mata da shi.
Buɗewa ta fara yi.
Ƙaton baho, kujerar yara, bokiti, da kuma poo guda biyu—ɗaya babba irin na manya, ɗayan kuma na yara.
Farida ba ta san lokacin da ta fashe da dariya ba. Ta tsaya tana kallon kayan ɗaya bayan ɗaya, tana girgiza kai.
“Lallai Inno…”
Sai ta sake shekewa da dariya,”Cikin da babu shi babu ranarsa duk ake yiwa wannan tanadin kamar gobe za a haifeshi.”
Idon Sufyan biyu har ƙarfe ɗaya na dare yana buga ball a waya. Da ya duba lokaci ya ga dare ya yi sosai, sai ya tashi ya leƙa ɗakin Farida.
Ganinta ya yi kamar kullum, ta yi shame-shame, gwarƙarinta na tashi tana ta zabga barcinta cikin kwanciyar hankali. Ɗan gajeren murmushi ya yi ta gefe sannan ya fita.
Shiga kitchen ya yi, ya ɗauko almakashi.
A hankali, da saɗa, ya koma ɗakin. Ya tsaya daidai saitin kanta, yana ɗaga almakashin sama.
“Yanzu fa aka fara wasan. Yadda kika tanadi salo kala-kala, haka nima na tanada.”
Ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi na mugunta. Ya damƙi gashin kanta, ya fara yanke shi a hankali. Duk lokacin da ta fara ƙoƙarin juyawa sai ya dakata, yana jiran ta sake komawa bacci.
A haka har ya gama yanke gashin gaba ɗaya, ya ciro reza daga aljihunsa ya kara kwashe sauran gashin, har sai da kanta ya koma tamkar ƙwallon goriba, daga nan ya koma kan gashin girarta shi ma ya kwashe tas kamar wani abu bai taba tsirowa a wajen ba.
Yana gamawa ya tattara gashin wuri guda ya kwashe, sannan ya tsaya yana kallonta.
“Cab! Sunan wani gari wai shi nan… Sumaila.”
Ya zaro wayarsa ya ɗauke ta hoto kafin ya fita daga ɗakin yana dariyar mugunta.
Ya koma ɗakinsa ya kwanta cikin farin ciki. Duk lokacin da ya tuna abin da ya yi ko ya kalli hoton, sai ya kyalkyale da dariya. Daga haka har barci ya yi awon gaba da shi.
Sanyin asuba da ke ratsa jiki tare da kiran sallar da aka fara ne suka farkar da Farida.
Jinta ta yi wani iri, musamman kanta. Kamar ana hura mata iska mai sanyi daga ko’ina.
Da sauri ta ɗora hannu a kanta.
Wayam!
Ta tsaya cak.
Hannunta ta sake kaiwa kan kanta, tana shafawa kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba. Nan take ta firgice ta miƙe daga kan gadon, ta nufi gaban mirror.
Da ta ɗaga kai ta kalli kanta…
Ba ta san lokacin da ta sake wata irin gigitacciyar ƙara ba.
“AAAAAAAAAAAAA!!!”