Chapter 1&2
by @hadizah10
đź’–đź’–SOYAYYAR ZUCIđź’–đź’–
‎ (love and Romantic)
Written
By
Deeyamerh
‎Page 1&2
‎" Hey plz ki kula" taji saukar murya a bayanta .
‎Cikin sauri ta juyo saboda " Hey " da taji an sake ce mata .
‎kyakkyawan saurayi ne sanye da bakar jallabiya,wacce ta amshi fatar jikinsa, matashin saurayin fari ne sosai , me dauke da bakin saje da lallausar gashin kai.
‎meko mata wayarta yayi,da sauri ta kalli jakar ta domin tasan ta sakata a jakarta,hannun da ya Miko mun wayar nake kalla,shin a ina ya samu wata?ko me yankan Aljihu ne?duk wannan tambayar a xuciyarta takeyi.
‎“Ta faɗo daga jakarki ne” ya ce ganin yadda fuskanta ta nuna alamar tambaya
‎A hankali tasa hannun ta karba, Domin abin yabata mamaki, yadda rayuwar nan ta lalace waye zai tsinci waya, ya baka sai me tsoran Allah.
‎“Thank you.”ta fada cikin siririyan muryanta
‎Ya yi murmushi kawai.
‎"Suhaima" ya anbaci sunanta .
‎ cikin mamaki ta daga idanuwanta,ta kall kalle shi ganin yadda ya ambaci sunanta kai tsaye
‎sai kuma kawai taiyi murmushi ba tare da tace masa komai ba.
‎gira daya ya dage yana kallon ta, kallo ne da takasa gane me yake nufi.
‎“Eh.” ya furta da murmushi akan labbansa
‎“Daga ina" ta sake tambayarsa"
‎"hmmm idan lokaci yayi zaki sani,domin nasanki Fiye da yadda kike zato.”
‎kallonsa tai na yan mintuna , kamar ba zatayi magana ba sai kawai ta furta " Okay ," Sannan ta juya ta bar wajan. batare da ta bari ya sake magana ba
‎" Hey bakiji ba." yayi kokarin dakatar da ita .
‎" Please, jira na ake a gida , bazan iya tsayawa a hanya ba, ina magana da kai ba sabida za'a mun fada a gida ."
‎"Haka ne na fahimta , amma idan ba damuwa anjima zan iya zuwa gidan ku? Saboda akwai maganar da nake so mu yi."
‎" No Please " ta fada cikin sauri , sannan ta bar wajan ba tare da ta bari ya sake magana ba .
‎dan tsayawa yayi jim , yana kallan wucewar ta , kafin ya sosa kansa kadan yana murmushi shi kadai.
‎Suhaima kuwa har sauri sauri ta dinga yi saboda karya tsayar da ita ga xuciyarta da take faman bugu ba tare da tasan dalilin hakan ba .
‎--------------------------
‎Wa shegari da safe, da wauri suka shigo makaranta,domin suna da lecture kuma gashi malamin har in dai kabari ya shigo cikin class din, to sai ka jirashi a wajen har ya gama.
‎tana zaune a aji tana duba Assignment din da akaba su,sai taji Muryar kawarta Fatima akan ta tana fadinq"Ahh Suhaima da wuri haka? ko da yake wanda yace bayaji,ai Sir Ridwan shine maganinsu.."
‎"wllh Fatima baki da mutunci ko banza ai na rigaki zuwa , Kinga idan an tashi kece a ruwa tunda Ni har na riga na zo "
‎"oho dai " Fatima ta fada tana zama a kusa da suhaiman.
‎"yawwa suhaima Ni kuwa wani guy ne jiya akace kun tsaya da shi bayan mun gama lecture?
‎“Wane guy?”Suhaima ta tambaye ta domin har ga Allah ta manta da wani mutum da ta hadu da shi jiya,abinda yake gabanta shi kawai take mai da hankali akansa.
‎"kai Suhaima kar ki mai dani mara hankali mana,jiya naganki da idona sannan na tambayeki amma ki mai Dani wata yar Air".
‎dan dago da idanuwanta Suhaima tayi ta duka mata hararata.
‎cikin sauri Fatima tace "To ai gaskiya na fada Miki idan kuma baki yadda ba to kisamun Gas".
‎"Suhaima tana buɗe baki za tai magana yan class suka fara shigowa kamar an kuro dan wasu har da gudu suke haɗawa Domin 1:30am Sir Ridwan yace zai shigo".
‎da yawan students sun shigo wanda hakan yayi daidai da shigowar Sir Ridwan cikin class,lecture ya fara wanda hakan yasa duk wani students mai da hankali domin jin abinda ya kawo su,sun dau tsawon lokaci suna yi har lokacin fitarsa yayi,a haka duk wani lectures da zai shigo suka shigo domin yau karfe 5:00pm zasu gama.
‎harabar makaranta cike da Students masu tafiya gida nayi,masu tsaya Captain yayi musu karin bayani sunyi gefe,wanda zasuyi sallah na tafiya masallaci,masu tafiya gida sun nufi get.
‎suna tafe suna hira akan karatun da sir Maheer yayi musu,"Hmm nifa Suhaima kwat-kwata ban gane bayaninsa ba dan Allah zanzo bayan i'sha ki sake mun bayani kinji".
‎"To ni ce Miki akai nagane?naga ina kallon ku, ke da saudat kuna kallon picture a waya?,to kije saudat din tai Miki bayani eh".
‎dariya Fatima tayi tace"haba Besty karki mun haka mana kar aji kanmu mana"..
‎Suhaima ba ta sake cewa komai ba har suka isa bakin titi, inda suka tsaya suna jiran NAPEP.
‎Fatima ta kalli gefen titi, sannan ta juya ta kalli Suhaima. “Ki yi haƙuri, yanzu zai zo nasan wannan shirun naki.”
‎Suhaima ta yi shiru, idanunta na bin motocin da suke wucewa,Zuciyarta cike take da wani irin tunani da ita kanta ba ta fahimci dalilinsa ba.
‎Bayan wasu mintuna, sai ga NAPEP ta nufo inda suke,Fatima ta ɗaga hannu,me Nepep din ya rage gudun da yake ya tsaya a gabansu.
‎“ina zaku?ya tambayesu.
‎"Hotoro zaka kai mu".
‎"kushiga muje".me Nepep din yace.
‎Fatima ce ta fara shiga ta zauna, Suhaima kuma ta biyo bayanta,suna gama shiga me Napep din ya jasu sai hororo.
‎a hankali Fatima ta kallon Suhaima, "Yanzu dan Allah bazaki fadamun damuwarki ba? Suhaima ashe Ni kadai nake jin mun zama daya? shike nan tunda bayan iya jin damuwarki ba har na baki shawarar da ta dace dake".
‎Suhaima ta ɗan yi murmushi, amma ba tace komai ba,kawar da kanta gefe tai tana kallon tagar Nape din,a zahiri zaka ce titi take kalla, amma a cikin zuciyar ta ta lula duniyar tunani
Yawwa, idan ka zo, dai-dai layin Lamido street 002 a nan zan sauka, Ita kuma idan ka je gaba, layin Lamido Street 004 a nan za ta sauka,” Fatima ta faɗa, tana kallon fuskar Suhaima dan tasan yadda taja bakin tai gummm dashi bazata ce komai ba,tarasa me ke damun ta da har yake sata cikin wannan tunanin..
Gidan Fatima ya kasance cikin sababbin gidajen da kagana gani kasan meshi yana ji da ya'yan banking,layi mai kyau,dan tunga bakin Get din gidan zaka gane , Duk da ba su daÉ—e da komawa gidan ba, ya riga ya zama É—aya daga cikin gidajen da ke É—aukar hankali a layin.
Suna zuwa dai dai kofar get din tace"idan kasamu guri".fakawa yayi a gefen get din. Hannu tasa a jakarta ta dauko 2k ta bashi Sannan ya dago ta kalli Suhaima wanda a lokacin itama take kallo irin kallon nan na au yauma sai da kika kuma ko?.
Gwalo tai mata tace"Kinga Ni matsa na wuce tun biki kai mun duka ba,dan Allah ladan yau Ni zan sameshi fa".
Murmushi suhaima tai Amma a ranta tayi alkawarin idan ta kama Fatima me kwatarta sai Allah.
Matsa mata tai ta sauka"Nagode ba dan halinki ba ,tunda ke aikin ki shinshigi".ta fada tana mai dalla mata harara.
"Oh dai kome zakici dai nariga da na riga kike yawwa sai kiyi hakuri kawai".Fatima ta fada,tana mai dago mata hannu alamun byee" sai munyi waya".
Cigaba da tafiya sukai inada ana zuwa bakin layin da suhaima zata sauka tace"Malam idan kasamu guri".
A hankali ya tsayar da Nepep din a dai dai Lamido street 004,sauka tai a hankali tace" Nagode".
Kallonta me Nepep din yayi yace"Badamuwa Madam wanna Aikina ne,idan ba damuwa ko ko zan rinka zuwa ina kai ku sabado naga masu Nepep basu fiya wuce ba may be Kuma wata rana ku samu shiga makaranta da wuri Amma bansani ba ko hakan da nafada laifine".
Dan jimmm suhaima tai yi domin kuwa abin da yafada dai dai ne dan sunsha makara wllh,saboda ita Fatima taki yadda da diver gidansu ta gwammace su hau ta haya alhalin su na da yadda zasu yi."To kabari muyi shawara da ita duk abinda tace inshallah sai mu fada maka gobe kamar lokacin da ka É—auke mu to kazo wanna lokacin".
"Tom shikenan Madam Allah ya nuna mana inshallah zan zo din kafin ma lokacin".
Juyawa tai a hankali tana tafiya kamar bata son taka kasa,shiyasa da yawan samari sukan ce mata mai tafiyar wahainiya,takan rasa yazatayi da ranta dan ita bata iya sauri a tafiya ba,kanta a kasa har ta iso bakin Get din gidan,tun daga kan flowers din da suke zagaye da gidan zaka gane gida ne da yayi tashan kyau domin har yanzu da kyannasa,babban gida ne duk da a shekarun baya gidan ya fi nasu Fatima kyau da tsada,wanda a hakan ma yanzu yafi sabon gidan nasu girma,domin mahaifin Suhaima ya taɓa yin tashen kuɗi sosai,wanda duniya ta sa Ni,daga baya kuma karayar arziki ta same shi,wanda a yanzu ta sauya musu abubuwa da yawa.
wacce Suhaima?
Waye Sha'ayan wanda ya san Suhaima fiye da kanta?
Shin kawance suke da Fatima ko kuwa da akwai wata manufa a tare da ita?
Ko biyoni domin jin Amsar ku
07070647236