SOYAYYAR ZUCI

Chapter 5&6

by @hadizah10

đź’–đź’– SOYAYYAR ZUCI đź’–đź’–
       (Love and Romantic story)
                        
     Written 
      by

  Deeyamerh 

07070647236
Page 5&6
Cikin É—akin ta buÉ—e ta shiga,abayan kofar ta tsaya a hankali take sulalewa har ta kai kasan carpet din har ta zauna,Da Ć™yar take iya É—aga kanta, hawaye sun riga sun cika idanuwanta kafin wani irin kuka ya kwace mata, kuka da tadade tana rike wa, daga can cikin zuciyarta yake, kamar an buÉ—e wani tsohon ciwo da ta daÉ—e tana Ć™oĆ™arin binne shi.
‎Ta ɗaura hannayenta a kan fuskarta, tana ƙoƙarin dakatar da kukan, amma abin ya gagara.
‎Tunaninta ya koma can baya...
‎Ta tuna da zaman da sauki Da Ammey lokacin da ita da mahaifiyarta suke kuka da  juna, akwai wani irin farinciki da ke ciken gidan mahaifinta cikin jin dadi da walwala,bame share mata hawaye idan tai kuka,Amma yanzu babu Ammey cikin duniyar ta,Babu wannan muryar da kullum take mata Addu'ar samun ci gaba a rayuwarta,Babu wannan rungumar da ake mata idan takawo daga school,Babu hannun da zai shafa mata kanta idan ta ji duniya idan tayi abin kirki.
‎lumshe idananu tayi wasu hawaye Masu dumi suka ziraro mata har kan kumatunta
‎“Ammey” ta furta a hankali, muryarta cike da rauni.
‎Sai ta tuna irin daren da mahaifiyarta kan zauna kusa da ita, suna hira har barci ya kwasheta,Kuka ne ya ƙara kubuce mata
‎“Da ace kina nan...” ta furta a hankali tana kallon wurin da babu kowa“Da ace kina nan, Ammey da ban ji kamar ni kaɗai ce a duniyar ba.”Ta sunkuyar da kanta, jikinta yana rawa saboda tsananin kuka.
‎A lokacin ne duk abubuwan da suka faru  a kwanakin da Ammey zata bata  suka dawo mata lokaci guda—kalaman da suka tsaya mata a rai kallon da take mata kamar na bankwana,duk inda tai da ido take binta tace"suhaima dawo kusa dani ji nake kamar zakiyi mun nisa".
‎Ta daɗe tana ƙoƙarin nuna cewa tana da ƙarfi,Amma a wannan daren, ƙarfinta ya ƙare,Sai kuka kawai kukan mai tsuma zuciya, wanda babu wanda ya san irin girman radadin da ke cikinsa.
‎Cikin sanyi jikinta ta shiga toilet, alwala tayo domin gabatar da Nafila, shimfiɗa dadduma tayi, ta kalli gabas ta kabbara sallah cikin nutsuwa take sallah. duk lokacin da ta kai goshinta kasa sai ta daɗe a kafin ta dago, Hawaye ne ko zubi mata ahankali, yayin da zuciyarta ke ɗauke da addu'o'i masu yawa.
‎Ko da ta idar da sallar,ba ta tashi ga kan sallayar ba, ɗaga hannuwanta sama tayi, idanunta cike da hawaye.
‎“Ya Allah… duk inda Ammey take Ka sanya ta cikin hannun mutanen kirki,Ka kare ta daga duk wani sharrin da ba za ta iya kare kanta daga gare shi ba.
‎Ya Allah, Ka kullube ta ta da rahamarka, Ka sanya duk wanda yake da hannun cikin Batan Ammey,Ka sanya shi cikin kwatan kwacin maraicin da nake ciki,kada Ka bar zalunci ya yi nasara a kanta.
‎Ya Allah… Ka dawo min da Ammey na cikin aminci,Kada Ka bar zuciyata ta saba da rashin ta,"Ya Allah, ni ba ni da ikon yin komai, Kai ne Mai ji rokan bawansa, Kai ne Mai iya canza komai cikin ƙiftawar ido,Ka dawo min da Ammey kafin zuciyata ta kasa ɗaukar wannan rashi.”
‎“Ya Allah… kar Ka bar ni ni kaɗai da wannan ciwon. Ka taimake ni… Ka taimaki Ammey.”
‎Ta runtse idanunta, hawaye suka sake zubo mata, sunkuyar da kanta tayi, kuka take kamar ƙaramar yarinya da aka kwace wa abin da ta fi so a duniya.
kwanciya tai anan inda tai sallah,wanna addu'ar da tayi sai taji wata nutsuwar tazo mata,sai a jiyar zuciya take saukewa,
‎Bom bom taji  bugun kofar dakinta kafin tace waye sai jin Muryar Mommy tai"dan uwar fito kizo kiyi aikin gidan kin shige daki kin nade ai ke da hutu kunyi hannun riga dan wllh ke da shi sai dai a lahira idan kina samu,maza fito ga wanke-wanke can da kika yawan kwana gun kwartonki yana jiranki danni ban haifi 'ya'yan da zasuyi aiki kina zaune ba, eh".
‎cikin daga murya duk da Muryar da duk ta  dushe gun kuka haka ta dagata tace "To Mommy ganin inshallah".
‎da sauri ta mike ta shiga Toilet furkata ta wanke har da sa kwalli dan karsu gane tayi kuka ko abinda sukai mata ya dameta,
‎fitowa tayi ta nufi hanyar kitchen inda Allah ya temake su Mubeenah basa gun,da sauri tashige kitchen har da sa key gudun kar Sabeer ya biyo ta,ai tana jiyuwa tai arrba da yadda kitchen din yayi kaca-kaca.
‎Tukwane da faranti marasa wanki sun cika sink, wasu kuma an jera su a kan tebur, man girki ya zube a ko’ina, ya bar wuraren da aka taɓa da shi da wani irin datti,Tarkacen kayan miya, bawon albasa, tumatir da ladar Indomie sun bazu a ƙasa,kusurwar kitchen ɗin kuwa, an jefar da ledoji da kwalaben lemuka wasu sun cika waje.
‎taka wa tai a hankali ta fara tsince abubuwan da ke ƙasa ɗaya bayan ɗaya,Cikin kasa da rabin hours tagama da kitchen har ta dawo parlon shima ta share tayi mopping ta saka Turan wuta ko ina tashin kamshi yake yi,koma watayi kitchen ta dura ruwan tuwo da miyya,cikik ikon Allah shima tagama,domin duk rashin sauri ta a tafiya Allah ya bata sauri gun iya aikin gidan...
‎Dakin ta shiga tai sallah tai wani wanka sannan ta shiga kitchen debu abin da tadafa tahau jeresu akan dinner table,nata tazubs ta wuce dakinta dan tasan halin Mommy zata iya cewa sai su haseenah sun gama ci sanan zata ci.
hayaniyarsu taji tasan sunzo cin banza,wllh abinda zai hanata batai musu mugunta dan kawai Abba yana zuwa cin abinci ne Amma da wlh duk sun gane basu da wayo,kakar da wayar ta tayi ne ya katse nata tunani ta, Message na shigo, dauka tai dan ta duba dan tayi zaman ko Fatima ce Amma sai dai me message  ne amma ba number alamun wanda ya Turo shi.
‎Bin message din tayi da kallo kamar me koyan Hausa sai kuma ta fara karantawa a fili"Uhmm sbd ina son ji daga gareki hakan na mun dadi sosai wallahi basan iya shekarun da zan dauka ina dakon samunki  a matsayin abokiyar rayuwa ba. bani da aiki sai kallon hotonki da yana mgana to shi kadai ne zai  iya kayyade addin kallonsa ina masa murmushi sai kace wani mahaukaci,ko dayake mahaukacine kan suhaima,duk yadda na zauto akan sonki kece sila tauraruwata keta musamman ce idan kika so tarwatsa taro kike 🥰 SECRET LOVER 
‎ta kalli message din nan yafi sai goma to waye wannan shi kuwa da bashi da aikin yi haka,to da alama mahaukacine.
‎jin an kira sallar i'sha yasa ta ajiye wayar tai sallah domin da wuri take so ta kwanta,karfe 4:00am take so ta tashi tai musu abin karya sannan ta shiga makaranta suna da lectures sir Rogo shima taji nace rade radin bashi da wasa to Gara komai a yishi akan idonta da a bata labari.
07070647236
🤔🤔Tofa anya suhaima ba da wani abu da ke boyewa ba kuwa?