BARA A KUFAI

Page 9.

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*

*Zeey Kumurya*


9.

BRIGHT PENS 2026


YOTA ID 003



Sai daf da Magriba Hasina ta koma gida, lokacin Amma ta gama haɗa komai na awara, ta yi wanka da alwala tana jira a yi Magriba ta fita ƙofar gida ta soya. Rai a ɓace ta dubi Hasina ta ce. "Daga ina kike?" 

"Gidansu Saudat." Ta faɗa ba yabo ba fallasa. 

"Yanzu abin da kika yi daidai ne Hasina? Ki fita tun rana amma sai yanzu za ki dawo? Kuma ba ki faɗa mini inda za ki je ba? Kina ganin yayanki ya zo ki tsaya ku yi gaisuwar kirki ma ba ki yi ba saboda kawai ya faɗa miki gaskiya." 

Ɓata rai ta yi ta ce. "Amma dai kina ganin abin da ya yi mini, kawai sai ya zo ya rufe ni da masifa? Ina ruwansa da rayuwata." Haɓa Amma ta kama ta ce. "Yayan naki? Duk duniya bayan mu ba ki da kamar shi fa, idan ba ki nutsu kun daidaita kanku a yanzu ba sai yaushe? Duk abin da ya faɗa miki ai gaskiya ce, kuma ba don yana ƙin ki ba ne." 

"Tunda kin fi son shi ai dole ki faɗi haka da ma." 

"Ba son shi na fi yi ba, ke da shi duk ɗaya ne a gurina, halinku ne ba ɗaya ba, ke ma idan kika gyara kika koma kamar shi kowa sai ya so ki, amma ke ba abin da kika zaɓar wa rayuwarki sai ƙunci da rashin kunya, haka kawai ba a yi miki komai ba sai ki ƙule a ɗaki ki ɗauke wa kowa wuta, mene ne amfanin hakan Hasina? Don Allah ki bar wannan halin ki haɗa kai da ɗan'uwanki, ku kaɗai Allah ya ba ni, idan tun ina raye ban gan ku a inuwa ɗaya ba bayan raina sai yaushe kuma? Wacce irin ɗawainiya ce bai yi miki ba tun kina yarinya? Wacce soyayya ce bai nuna miki ba?" Cikin ƙunƙuni ta ce. "Ba ni na saka shi ba ai bare a mun gori, idan ana so mu haɗa kai shi ma a yi masa magana ya daina ɗaga mini murya tunda ba haifa ta ya yi ba." Jinjina kai Amma ta yi tare da bin ta da kallo. 

"Ga turare can ya kawo miki to ki shiga ɗakina ki ɗauka." 

Ba kunya kuma ta shiga ta ɗauka ta wuce ɗakinta ta adana tana ɓaɓɓata rai. Amma ta bi ta da addu'ar neman shiriya.

**** ***** 

Washegari tun daga sallar Asuba Ahayan ta fito ta fara gyaran gida, tana yi tana azkar ɗin safe, gidan ƙasa ce a ƙasa babu siminti, ko'ina kuma zubar da ruwa ake, sai ya haɗu ya cakwale, ga shirgi ko ta ina, ita kuma a kullum sai ta ce sai ta gyara shi ya yi fes. Bayan ta gama shara da wankin banɗanki ta ja ruwa ta ciccika botikan gidan ta janyo wankin da aka kawo jiya ta fara yi. Wani irin ciwon baya take ji da ba ta taɓa jin kamar shi ba, amma ba ta isa ta ce ba za ta yi wankin nan ba, da ta nemi hutu Umma za ta ce idan ba ta yi ba ƙasa za su dafa su ci? A zaune take a kan kujera ƴar tsugunno, duk da haka haki da numfarfashi kawai take yi. Tana nan zaune Umma Lantana da Baba suka fara cacar baki, akan sadakin Zeenat, tun daren jiya ta dage sai ya ba ta za ta yi wa Zeenat siyayya, shi kuma ya ƙi ya ce ai mijin ya ce ba sai an kai ta da ko cokali ba, tashin Umman Lantanan kenan ko sallah ba ta yi ba suka ɗora daga inda suka tsaya, ƙarshe sai da ta kai har marin ta Baba ya yi tare da faɗin. "Wallahi idan kika cika mini ciki a yau ba gobe ba zan warware ragowar igiyar auren da ta rage mana, idan kuma kin cika ƴar halak ki ci gaba, shashashar banza mahaukaciya da ba ta san inda yake yi mata ciwo ba." Wannan furuci nasa ne ya sa ta yi shiru ba ta ƙara cewa uffan ba, sai cika da batsewa kawai take yi.

Wajen ƙarfe takwas Ummi da Rauda suka shirya suka tafi School, Ahayan ta bi su da kallon burgewa, tana son makaranta da karatu sosai, amma rashin samun dama ya sa ta haƙura, Sabira ma fitowa ta yi tana kallon su kamar za ta yi kuka, su suna Secondary school ne, ita kuma Primary, su ba a cika matsa musu akan kuɗin makaranta ba kamar ita. A raunane ta ƙarasa kusa da Ahayan ta ce. "Aunty Ahayan ba ki samu kuɗin school fees ɗin ba?" Murmushin ƙarfin hali Ahayan ta yi mata ta ce. "Na kusa samu in sha Allah, ina samu zan biya miki kin ji?" Sabira ta gyaɗa mata kai a sanyaye sannan ta koma ɗaki. 

A lokacin Inno ta fito cikin tafiyar ƙasaita, ta ci kwalliya kamar kodayaushe, cillawa Ahayan ATM ɗin hannunta ta yi ta ce. "Ki je ki ciro mini kuɗi, a ciki ki ɗauki 5k kuɗin da Adam ya tura miki." Cikin azarɓaɓi Ahayan ta goge hannunta a jikin zaninta ta ɗauka tana faɗin. "Na gode! Na gode sosai! Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi." Tsaki Inno ta ja a wulaƙance ta faɗi adadin kuɗin da za ta ciro mata, da abubuwan da za ta siyo mata na cefane. 

Wankin da ba ta ƙarasa ba kenan saboda bautar Inno da ta shiga yi, ta siyo mata kayan miya, ta biya wani gida da ake kiwon kaji ta ba su sallahun su yanka guda uku, suka faɗa mata kuɗin ta ba su a cikin kuɗin da ta ciro, sai da ta jira aka gama komai sannan ta ɗauka ta kai gida ta yi aikinsu, wani ta soya wani ta yi farfesu wani ta saka a miya, sannan ta yi couscous da za a ci miyar da shi, taimakon da Allah ya yi mata yau Umma ta yi girki, ta yi tuwon gari an ba ta, ta ci ta ƙoshi, kuma da Umma ta gama girkin sai ta ci gaba da wankin da fara. Sai da ta gyara wa Inno gaban ɗakinta tas inda ta yi girkin ta wanke duk abin da ta ɓata ta ƙara gyara tsakar gidan sannan ta yi wanka ta yi sallar Azhar, yadda Inno take ta saka turare a gidan da umarta a kwashe duk wani kayan datti ya saka ta gane baƙi za ta yi, daga gani kuma tana ji da su da ba su girma. 

Duk yadda ta so ta koma Islamiyya yau tunda kuɗin wata ya samu amma ciwon da jikinta yake yi mata ya saka dole ta haƙura, ta fito tsakar gida ta saka tabarma ta kwanta ruf da ciki ko za ta samu sassauci a bayanta da take jin kamar zai ɓalle, gabaɗaya jikinta ma tsamin gajiya yake yi mata, ta tabbatar bayan hutu da jikin yake buƙata har da ganin likita, da ita wata mai gata ce ciwon da take ji ya ci ta je asibiti. 

Tun daga fitowa daga motar da ta yi da takun da take ɗaiɗai tana yamutsa fuska cikin ƙasaita ya saka mutanen ƙofar gidan bin ta da ido, a ƙyamace ta ƙetare soro ta ƙarasa ciki, sautin takalminta da ƙamshin turarenta ne ya saka Ahayan ta gane an shigo gidan, da sauri ta yunƙura ta tashi zaune tana cize baki na azabar ciwo. 

Cak Ramlah ta tsaya tana bin gidan da kallo kamar mai shawarar shiga ko fasawa, a kan Ahayan da ta sunkuyar da kanta ƙasa ta tsayar da idanunta tana bin ta da wani irin ƙasƙantaccen kallo, daidai lokacin Inno ta fito daga ɗakinta tana faɗin. "Laure ya kika tsaya daga nan kuma? Na ga shigowarki ai ta taga, maraba lale." Glass ɗin idonta ta ɗage ta mayar da shi kan goshinta, idonta akan Ahayan ta ce. "Wai har yanzu wannan agolar ba ta bar gidan nan ba?" Inno ta kama haɓa tana ƙanƙance ido ta ce. "Ina za ta bari? An samu jar miya da abin da aka rasa a gidan uba ana ci? Ai tana nan ba ranar tafiya, shegiya ga baƙinjini sai goga kafaɗa muke da ita ba mashinshini bare mu fara tunanin ranar yar da ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda." Ƙara yamutsa fuska Ramlah ta yi ta ce. "Wallahi na tsane ta! Bana son ganin ta, duk murna da zumuɗin zuwan da nake ina cin karo da ita na ji duk sun tafi, ke ma Inno na yi na yi kibar gidan nan amma kin ƙi, ban san me ya sa kika nace ba, ji bi datti fa, da wani uban cakwali ga wata shegiyar kwata can da ka shigo ita take fara yi maka Welcome, ga tsainanniyar shanya an cika igiya, ga..ga..ga.. haba! Wannan wanne irin abu ne, da ajina da arziƙina amma a ce nanne gidanmu?" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. 

"Ki yi haƙuri, shigo ki huta, daga zuwanki ko zama ba ki yi ba kin fara da mita, wannan uwar shanyar kuma yanzu zan saka su kwashe ta tunda ba kya so." 

Dogon tsaki Ramlah ta ja ta ɗage kayan jikinta ta ci gaba da tafiya tana ɗaɗɗage hanci. 

"Sannu da zuwa Aunty, ina wuni?" Ahayan ta faɗa kanta a ƙasa cikin ladabi. 

"Yana gidan uwarki, shegiya mayya!" Ta faɗa a harzuƙe tare da duban Inno ta ce. "Kin ga irinta ko? Ban da ƙaddara me zai haɗa ni da wannan yarinyar bare har ta yi mini magana? Ta ƙara jan tsaki sannan ta bi ta kan tabarmar da Ahayan take kai ta wuce fuu har tana datsewa Ahayan ɗanyatsan ƙafa da tsinin takalminta, Inno ta kama hannunta suka shige ɗaki tana lallamin ta.

Yarfe hannu Ahayan ta shiga yi cikin azaba, ƙiran da Inno ta ƙwalla mata ya sa ta miƙe a hanzarce, sai da ta yi sallama sannan ta shiga ɗakin.

"Kwaso kayan abincin can." Inno ta faɗa cikin ba da umarni. 

Da sauri Ramlah ta ce. "Abincin da zan ci?" Inno ta gyaɗa mata kai.

"To fara wanke hannunta, ta gurza shi da ƙasa sosai." Ta yi maganar tana latsa wayarta.

"Sai ki tashi ki ji abin da ta ce." 

Jiki a sanyaye ta miƙe ta koma ƙofar ɗakin ta dinga gurzar hannunta kamar mai wanke zunubi, sai da Ramlah ta ga dama sannan ta ce ta bar shi haka ta ɗauraye hannun da ruwa ta dawo. Ta yi duk yadda ta ce tana jin tafin hannun na yi mata wani irin zugi.

"Zauna a nan." 

Ramlah ta nuna mata gaban kujerar da take kai.

Gabanta na faɗuwa ta zauna don ta san irin tsanar da Ramlah ta yi mata da yadda take wahalar da ita a duk lokacin da ta zo gidan, da takalmi a mai tsini a ƙafar Ramlah ta ɗora ƙafafunta a kan kafaɗun Ahayan, Husna ta zuba abinci ta ɗauki plate ɗin ta ɗaura a kan cinyarta ta fara ci a gayance, tana yi tana karkaɗa ƙafafuwanta, ƙasar ƙasan takalmi na zuba a wuyan Ahayan, tsinin takalmin yana tsikarin ta a kumatu. 

Tsabar baƙinciki da muzanta jikin Ahayan har tsuma yake, wasu hawaye masu zafi suka shiga zubowa a kuncinta, ta yi ƙasa da kanta kawai tana jin yadda kanta ya fara sarawa mata.

"Mine zai zo fa, ina fatan akwai abincin da za a tarɓe shi da shi." 

"Inno ta ce. "Da akwai mana, har shi aka dafa, ai na san duk lokacin da kika zo shi yake zuwa ya ɗauke ki, yaron kirki ai yana ji da ke." 

Murmushi Ramlah ta yi bakinta cike da abinci ta ce. "Kamar yadda nake ji da shi fa, tattalinsa nake fiye da ƙwai, yadda nake jin shi a raina zan iya fansar da komai nawa saboda shi, ciki har da rayuwata." Dariyar shaƙiyanci Husnah ta yi ta ce. "Kai Aunty Ramlah zan ga yadda za ki yi idan Yaya Juraij ya ƙara au..."

Cokalin hannunta ta wurga mata tare da faɗin. "Sai dai uban ƙara aure, ji shegiyar yarinya da hauka, ana maganar hankali za ki sako abin da ba zai yiwu ba, to bari ki ji, yadda idan mutum ya mutu ba ya dawowa haka Mine ba zai taɓa ƙara aure ba." Ta ƙarashe maganar tana ƙwarewa. Da sauri Inno ta miƙa mata ruwa tana faɗin. "Mene na tayar da jijiyoyin wuya akan zancen waccan shashashar?" Hararar Husnah Ramlah ta yi ta ce. "Mugun fatanta ya ƙare a kanta." 

"In sha Allah ba mai zama da kishiya a cikinku, ku kaɗai za ku yi warkajami a gidajenku."

Ahayan dai tana ɗorare tana jin su, ta gaji da zaman tana so ta gyara amma tana tsoron ta yi laifi, haka ya daure ƙafafunta na ci gaba da sagewa kamar ba sa jikinta. 

Ramlah ta ci gaba da ba wa Inno labari. 


"Na kawo Daddy gurin magani ne, na baro shi a can tare da Mukhtar cousin ɗin Mine, nan da ƙarfe huɗu zai biyo Flight ya zo mu koma." 

"Ya jikin nasa kuwa? Ana samun ci gaba?"

Wani murmushi Ramlah ta yi ta ce. "Da sauƙi sosai, yana samun lafiya gaskiya." Inno ta ce. "Allah ya ba shi lafiya, in sha Allah zan saka rana na zo na sake duba shi." 

Daga nan suka shiga hirar yadda Daddy ya fara cuta, a kalaman Ramlah Ahayan ta gane ba ƙaramin so da ji da mijinta take yi ba. 

Sai da Ramlah ta gama cin abinci sannan ta sauke ƙafafuwanta, da ƙyar Ahayan ta iya miƙewa ta bar ɗakin bayan ta gama ci mata mutunci.

"Shegiya sai warin rana take, ni kar ma na shafi wani ciwon na manta na ɗora ƙafata a jikinta." 

Ita dai ta fice tana sauke ajiyar zuciya, kamar za ta faɗi haka take ji, da ƙyar ta ƙarasa ɗaki tana numfarfashi ta kwanta a wahalce, kallo ɗaya Umma ta yi mata ta watsar, ba tare da ta bi ba'asin ganin ta cikin wannan yanayin ba, ta ci gaba da baza kayan mutane da ta kwashe a igiya wanda ba su gama bushewa ba. 

Har ɗaki Umma ta je ta gaisar da Ramlah, ta amsa kamar an yi mata dole a wulaƙance, Umma Lantana kuwa da ma ba ta gidan, Baba yana fita ita ma ta fice. 


Bayan la'asar Inno ta azalzalo Ahayan da Umma ta saka su gyaran gidan.

"Ku yi sauri mana hana,  ku yi abu da jiki, baƙo mai daraja ne zai zo mini, a share ko'ina tas a kwashe duk wani shirgi." 

Haka take ta faɗa tana maimaita musu kamar ita ta yi naƙudar su ta kawo su duniya, da sun ɗan kuskure sai ta rufe su da faɗa, Umma ce ƙarfin aikin don Ahayan kwata-kwata babu ƙwari a jikinta, ƙarfin hali kawai take yi. 

Gabaɗaya gidan sun baɗe shi da ƙamshi, Inno ta sake kaya da kwalliya, har wani ƙaton carpet ja dogo suka shimfiɗa a tsakar gidan, don Ramlah ta ce mijinta ba zai taka wannan jar ƙasar ba. 

Bayan sun gama bautuwa ta kama kunnen Ahayan ta murɗe ta ce. "Kar na ƙara ganin gilmawarki a tsakar gidan nan har sai mijina ya zo ya tafi, don idan ya gan ki zuciyarsa za ta iya tashi." Kai kawai Ahayan ta ɗaga mata tana jin wani irin ɗaci a maƙoshinta, ta rasa me ta yi wa Ramlah da ta yi mata wannan tsanar, duk yadda Inno take gana mata izaya da nuna mata tsana Ramlah ta ninninka ta, duk yadda take ƙoƙarin kiyayewa don su rabu lafiya idan ta zo gidan amma ba ta tsira daga wulaƙanci da tozarcinta, tana jin fitsari amma haka ta daure ta koma ɗaki saboda gargaɗin Ramlah, tana kwanciya wani wahalallen bacci ya kwashe ta.



Misalin ƙarfe huɗu da rabi da wasu mintuna Mukhtar ya yi parking motar da ya ɗauko Juraij daga airport a ƙofar gidansu Ramlah, suna tafe Mukhtar yana ba shi labarin abubuwan da suka wakana a gurin mai magani, ta can suka fara biyawa, amma bai samu ganin Daddy ba, an saka shi a wani daki an rufe ana ta banka masa hayaƙi, sai ta ƙaramin windown ɗakin ya leƙa ya hango shi. 

A hankali ya ɗaga kansa da yake jin kamar zai yi bindiga saboda tarin abubuwan da suke cikinsa, Mammy ta kira shi za su zo dubiya ya sanar mata Daddyn yana wajen mai magani, hakan ya sa ta dinga faɗa na bar wa Ramlah ragamar komai da ya yi, haka ma Kawunnansa, har gurin aiki suka bi shi, yana fitowa ya gan su, kamar za su ari baki haka suka dinga caccake shi su ma, saboda sun ga lokacin da aka fita da Daddy, daga su har Mammyn babu wanda ya ce wa kanzul har suka yi suka gama. 

Numfashi ya sauke a hankali ya ɗaga ƙafarsa da yake jin nauyin damuwarsa har a cikinta ya fito daga motar, yana sanye cikin ƙananan kaya da suka haska farar fatarsa suka yi masa kyau sosai, fuskarsa babu walwala ya latsa wayarsa ya kira Ramlah.

"Ka shigo ciki." Abin da ta ce kenan ta katse wayar. 

Ahayan tana cikin bacci fitsari ya matso ta, duk yadda ta so ta daure amma ta kasa, don kamar zai faso mararta ya fito saboda matsuwa. Miƙewa ta yi ta lalubi ɗankwali ta ɗaura.

"Ba ki ji warning ɗin da aka yi miki ba kenan?" 

"Fitsari ne ya matse ni, kamar zai zubo haka nake ji." 

Taɓe baki kawai Umma ta yi, ita kuma ta saka kai ta fita. Daidai lokacin su Juraij suka shigo gidan, Ramlah kuma tana tsakar gida tana jiran su, gaban Ahayan ya faɗi, amma ta daure ta wuce toilet ɗin da sauri kanta a ƙasa, Ramlah ta raka ta da wani mugun kallo, Juraij kuma bayanta kawai ya gani tana tafiya, yadda take bin bango kamar mara lafiya shi ya ɗauki hankalinsa, farkon-farkon ciwon Daddy da yake tafiya da bin bango ne ya faɗo masa a rai. 

Kyakkyawar tarɓa ya samu daga Inno, ta dinga duƙa masa kamar ba mijin ƴarta ba, ya sha addu'oi da shi da Daddy, bai so cin abinci ba, amma matsawar Inno ta saka ya ci kaɗan, sai kuma ya ji abincin ya yi masa daɗi, Mukhtar ma zagewa ya yi ya ci yana ta santi, wani irin daɗi Ramlah ta ji, kanta ya fasu an yaba girkin mahaifiyarta, don ita ba ta san Ahayan ce ta yi ba. 

Biyar da mintuna suka tafi a gaggauce saboda Flight ɗin six za su bi, suna ƙofar gida suna jiran Ramlah su Ummi suka dawo daga Islamiyya, ba wani sanin shi suka yi ba, amma tunda sun dawo daga school sun tarar da Ramlah a gida sai suka gane mijinta ne, hakan ya sa suka gaishe su, Mukhtar ya ba su kuɗi, da rawar jiki Raudah ta saka hannu biyu ta karɓa, da murna fal ciki suka shigo gidan suna ƙirga kuɗin.

Ahayan tana kwance Ramlah ta shiga ɗakinsu tana toshe hanci, wuyanta ta damƙa ta wanka mata mari, a fusace ta ce. "Ke wacce irin daƙiƙiya ce ne? Bana ce kar ki fito ba? ko raini ya fara shiga tsakanina da ke ne? Mijina za ki bari ya gan ki? To wannan ya zama karo na ƙarshe da za ki sake bari ko farcenki mijina ya sake gani! Idiot!" Ta ƙarashe maganar tare da yin cilli da ita, goshinta ya bugu da ƙofa sannan ta faɗi ƙasa, Ramlah ta taka ta da takalmin ƙafarta ta fice fuuu. Ummi da shigowar su ɗakin kenan ta raka ta da harara sannan ta dubi Umma ta ce. "Me ta yi mata?" Umma ta ce. "Don ta fita fitsari lokacin ita kuma mijinta ya shigo gidan." Rai a ɓace Ummi ta ce. "To shi ne za ta yi mata wannan cin mutuncin? Wai ita Aunty Laure a kanta aka fara aure ne? Ta bi ta ishi mutane komai mijinta komai mijinta." Ta ja tsaki sannan ta ce. "Ko dacewa ma ba su yi da shi ba." Raudah ta ce. "Ai ba haɗi, shi kyakkyawa ɗan gayu, ita kuma kawai farin ne da iyayi." Tsawa Umma ta buga musu ta ce. "To ya isa haka, kar a jiyo ku ku janyo mini wani bala'in ban ji ba ban gani ba." Shiru suka yi Ummi na hucin ɓacin rai, Raudah ce ta taɓa Ahayan tare da kiran sunanta, amma shiru babu amsa, a rikice ta shiga jijjiga ta amma ko sirin gashi bai motsa ba a jikinta.


*#Zeey Kumurya*
*#****