THE SECRET BENEATH THE SCAR
by @zeeyluv
Page...............16
Da sauri Ummie ta kunna wutar ɗakin ta na faɗin, "Hayat lafiya?" Ta yi maganar ta na ƙarasawa gareta. Ganin duk ta rikice sai haki ta ke yi ya sa Ummie jawo ta jikinta ta shiga shafa mata kai tare da faɗin, "Relax dear, ki kwantar da hankalinki mu na tare da ke ba abin da zai same ki." Sannu a hankali bugun zuciyarta ya shiga daidaita. Ummie ta kalla Farhat tare da faɗin,
"Farhat kawo min ruwa."
Shi ko hamshaƙin ya na nan tsaye tamƙar ba ya cikin ɗakin ƙala bai ce ba. Ban da ido da ya zuba mata babu ko ƙyaftawa, a zuciyarsa ya na mamaki ashe akwai abin da zai iya tsoratata haka.
Farhat ta dawo ɗakin ɗauke da ruwa a hannu ta miƙa wa Ummien. Ummie ta amsa ta ɗago kan Hayat ta ce,
"Daure ki sha ruwa za ki samu relief." Ba ta musa ba ta kafa kai sai da ta shanye tas sannan Ummie ta janye Cup ɗin daga bakinta, nan ta ke ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya.
Ummie ta shiga jero mata sannu ta na ci gaba da tapping bayanta. Sai da ta ga ta samu nutsuwar da ya kamata sannan ta ce, "Tell me, me ya tsoratar da ke haka?"
Ɗan murmushin yaƙe ta yi ta ce,
"Nothing much Ummie karki damu i'm fine. Ku yi haƙuri na tayar da ku daga bacci." Ta ƙarasa maganar hawaye taf idonta.
Ganin haka ya sa Ummie ta mayar da kallonta kan su Asad ta yi musu signal da ido da su basu waje. Babu musu su ka juya su ka fice daga ɗakin.
Rarrashinta Ummie ta shiga yi cikin kalamai masu sanyi da tausasa zuciya har sai da ta tabbatar babu wani sauran tsoro tattare da ita sannan ta ce, kwanta. Bayan ta kwanta ta tofe ta da addu'a. Za ta ja blanket ta rufe ta kenan idonta ya sauka a kan wani ƙaton tabon da ke ta wajen gwiwar hannunta. Dakatawa Ummie ta yi da mamaki tana kallon tabon wanda yafi kama da tabon mummunar ƙunar wuta.
Ummie ta ce, "Hayat me ya sameki a hannu haka?" Da sauri Hayat ta ja hannun rigarta ta na rufe wajen cikin i'ina ta ce,
"Ummie ba wani abu bane, rauni na ji tun ina ƙarama shine taɓon bai ɓace ba har yanzu."
Ummie ta ce, "Alright good night. Ki yi ta nanata La'ilaha'illallah har bacci ya kwasheki kin ji babu abin da zai ƙara zuwa ya hanaki bacci In sha Allah."
Ta ɗaga wa Ummie kai haɗe da furta,
"Shukran Ummie." Ummie ta yi murmushi ta na faɗin, "Laaaaa.... La Shukra ala wajib."
Daga haka ta kashe mata wutar ɗakin ta fice a ɗakin zuciyarta cike da tambayoyi kan rayuwar Hayat ɗin, saboda ga dukkan alamu ta lura akwai wani ɓoyayyen damuwa a tattare da ita.
A parlour ta tarar da Asad tsaye kamar me tunanin wani abu. Ƙarasawa inda ya ke tsayen ta yi. Jin alamar motsi ya saka shi ya juyo.
"Ya ta ke yanzu?" Ya tambaye Ummie a taƙaice. Ummie ta ce, "Lafiya qalau na samu na rarrashe ta."
Ya ce, "Okay ya kamata ki samu ki je ki kwanta ki yi bacci dare ya yi already."
Ya nagama faɗin haka ya juya zai bar wajen ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa.
"Asad, ban san mene ne ra'ayinka game da yarinyar nan ba yanzu. Amma akwai abu guda ɗaya da na sani, shine tabbas yarinyar nan tana cikin damuwa tattare da zuciyarta. Na hango hakan ne ta cikin ƙwayar idonta mai ɗauke da wani irin tsantsar tsoro da na hango yau a idanunta."
"Ummie, ki daina tausayin yarinyar nan, saboda ba abin tausayi ba ce ita, ko da kuwa ta na cikin damuwar da kika faɗi ɗin. Barin ta wannan gidan shine mafi alkhairi a gare mu." Asad ya yi maganar cikin ko in kula.
"Asad ba ka ganin kana ƙara assasa wannan takun saƙar da ke tsakaninku ne ta hanyar rashin nuna kulawa a lamarin ta?" Ummie ta yi mishi tambayar ta na kafe shi da ido. Ƙin yarda ya yi su haɗa ido da Ummie sai cewa ya yi,
"Ummie don ba ki san halin irin waɗannan matan bane sosai." Ummie ta katse shi cikin ɗan ɗaga murya ta ce,
"Kamar ya kenan? Me kake nufi da halin irin waɗannan matan eh? Yaushe ka zama mai yanke wa mutane hukunci haka? Kasancewar yarinyar tana sanya ƙananun kaya da shigar turawa ai ba shi ya ke nufin ba ta da tarbiyya ba ko kuma mutuniyar banza ce ita.
Mutane nawa ne su ke shigan mutuncin kuma ka same su da munanan ɗabi'u, waɗanda kuma kake musu kallon su ne na banza ka same su da kyawawar ɗabi'u da tsabtatacciyar zuciya?"
"Ummie ki fahimce ni, ni ba batun shigar ta kaɗai ne matsalata ba. Yarinyar da ba ta mutunta al'adunta da kuma muhallin da take zaune a ciki. Irin waɗannan mutane kansu kawai suka sani. Ba na son ta yi dogon zaman da zai saka rinjayi Farhat ta sauya mata ɗabi'a. Shiyasa zai fi kyau ta bar gidan nan as soon as possible."
Yana gama faɗin haka ya rufe da faɗin, " Ki je ki kwanta Ummie dare ya yi sosai. Sai da safe." Daga haka ya juya ya nufa ɗakinsa....
Itama Ummie ta nufa nata ɗakin zuciyarta cike da saƙe-saƙe.......
*******
Washe gari da safe.
Ya na cikin shirinsa na zuwa office, wayarsa da ke kan mirro ya yi ƙara alamar shigowar message. Dakatawa ya yi da shirin ya kai hannun kan waya saboda dama akwai saƙon da yake sa ran shigowarsa. Amma ga mamakinsa sai ya ga saɓanin haka. Sunan Afeef ya gani ɓaro-ɓaro a kan allon wayar wanda ya ke nuni da shi ya turo da saƙon. Buɗe saƙon ya yi, ya ci karo da list ɗin kayayyaki na mata kala-kala ko wanne da adadin yadda ake son yawansu ya kasance. Tsaki ya yi haɗe da furta,
"Afeef! Yaushe zai fita daga sabgar mata ne wai." Ko cikakken minti ɗaya bai yi ba da buɗe saƙon sai ga kiran Afeef ɗin ya shigo. Ɗaga kiran ya yi tare da karawa a kunne.
"Assalamu'alaikum Akhy. Barka da safiya fatan ka tashi lfy?" Cewar Afeef ɗin ta cikin wayar.
Asad ya amsa da, "Alhamdulillah." A taƙaice.
Afeef ya ce, "Yauwa Akhy na san ka ga saƙona ko?"
"Na gani Afeef me zan yi da list ɗin siyayyar ƴan matanka?"
Cikin sauri Afeef ya ce, "Laaa ba yadda kake tunani bane fa. Wannan list ɗin kayayyakin da za'a kai wa sirikar Hamra ne. Tun jiya Abie ya bani na siyo tom ni kuma..."
"Kai kuma ka manta Afeef tun da ba sabgar da ya shafi yan mata bane ai dole ka manta." Cewar Asad.
Afeef ya ce, "Allah ba haka bane Akhy, abubuwa ne su ka yi min yawa ga shi yanzu ba damar na fita, kuma nan da awa biyu za'a je kai kayan. Na rasa yadda zan yi, na san duk duniya kai kaɗai na ke da shi wanda ya ke fitar da ni a matsala idan na shiga. Ka taimaka min don Allah...
"Afeef!"
Ammie ta hango shi daga inda ta ke ta ƙwala mishi kira. Da sauri ya ce, "Zan kiraka anjima Ammie na kira na." Ya na gama faɗin haka ya yanke ba tare da ya jira amsar Asad ɗin ba.
Dafa kansa Asad ya yi yana faɗin, "Afeef matsala." Sannan ya ci gaba da shirinsa cikin ɗan hanzari saboda tsayawa da ya yi magana da Afeef ya so ya makarar da shi.....
Ummie kam ganin bai fito breakfast da wuri ba ya sa ta san cewa da wuya ya tsaya ya yi breakfast ɗin tun da har ya kai wannan lokacin. Hakan ya sa ta haɗa mishi na shi a warmers tare da cika mishi tea flask da black tea wanda mafiya yawan lokuta yafi maida hankali a kan black tea ɗin fiye da abinci.
Kamar kuwa ta sani yana fitowa a gaggauce ya isa inda ta ke yana bata morning hug tare da faɗin,
"Barka da safiya kyakkyawar uwata."
Dungurinsa ta yi a kai cikin ɗan haɗe rai ta ce,
"Ka kiyaye ni da sanyin safiyar nan."
Sarai ya fahimci fushi ta ke yi da shi, kuma ya san a kan maganar jiya ne. Ɗan ɓata fuska ya yi ya ce,
"Ashe yau zuwa office bai ganni ba kenan, Ummie na fushi da ɗanta." Ya yi maganar ya na shirin kwance agogon da ke ɗaure a tsintsiya hannunsa. Ummie ta yi saurin riƙe hannun nasa ta ce,
"Me kake shirin yi?"
"Office ɗin na fasa zuwa yanzu zan kira a yi cancelling meeting ɗin da zamu zauna yau da MD na company ɗin ZEEVANA LUXE kan batun gina sabon branch ɗinsu da za su buɗe a nan Egypt.
Tun da Ummie na fushi da ni, ai ƙila ina iya fita trailer ya bi ta kai....." Da sauri Ummie ta yi saurin toshe bakinsa gabanta na wani irin faɗuwa, take idonta ya ciko da ƙwalla.
Ilahirin jikinta ya shiga kakkaura ta na faɗin, "Kul na sake jin makamancin wannan furucin daga bakinka Asad. Kasan me kake faɗi kuwa? Kasan girman abin da ka faɗi kuwa Asad? No ko da wasa kar na sake ji."
Jikin shi ne yayi sanyi qalau don shi har ga Allah da wasa ya ke yi bai san maganar zai raunata zuciyar Ummien har haka ba. Ganin yadda gaba ɗaya firgici da tsoro ya bayyana a kan fuskar Ummien ne ya ƙara sanyaya jikinsa, wani tausayin Ummien na su ya kama shi. Nan take ƙwalla ya soma cika idonsa ya yi saurin mayar da su haɗe da kwantar da kan Ummie a kan faffaɗan ƙirjinsa ya na faɗin,
"Relax Ummie babu abin da zai samu Muhammad Asad ɗinki. Har ta tattaɓa kunnen Asad da Farhat duk sai kin gani. Sannu hankali da taimakon daɗaɗan kalamansa nutsuwarta ya soma dawo mata, sai ajiyar zuciya ta ke saukewa a hankali. Sai da ya tabbatar ta dawo normal sannan ya leƙa fuskanta cikin marairaice ya ce,
"Tom yanzu Ummie ta yafe wa Asad?" Ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓar da sai yana gaban Ummie ne kawai ya ke yi.
Cikin murmushi da har sai da sautinsa ya bayyana ta dungure masa kai ta yi tana nufar inda ta ajiye basket ɗin da ta shirya mishi warmers a ciki ta na faɗin,
"Ban sani ba." Murmushin ya yi mai ƙayatarwa wanda ya yi sanadiyar bayyanar beauty point ɗinsa da ke gefe da gefen kumatu wanda ba ka taɓa sanin yana da su sai yayi ƙayataccen murmushi ya ce,
"Asad na godiya Ummien Asad."
Daidai tana dawowa wajen ɗauke basket ɗin ta ce,
"Point of correction Ummien Hayat da Farhat na ke." Sarai ya fahimci abin da ta ke nufi sai ya basar ya kai duban shi zuwa kan agogon hannunsa ya ce,
"Ummie yau na makara over. Wai ina Farhat ne ta zo ta kai min abincin mota."
Ummie ta ce, "Fitar sassafe ta yi yau su na da test." Daidai nan Hayat ta fito sanye da kayan bacci riga da wando mai tsansti, kanta sanye cikin hular mai gashi-gashi ka na ganinsa a ido kasan zai yi laushi don yadda jikin teddy yake haka hular ya ke. Fuskar nan fayau kamar wata mara lfy looking so cool da ita.
Ɗauke kansa ya yi gefe ya na wani shan kunu kamar ba shi ya gama taɓara a gaban Ummie ba yanzu.
Da fara'a Ummie ta ce, "Dear har kin tashi." Maimakon Hayat ta amsa mata sai ta mayar mata da,
"Sabahul khair ya Ummie." Ta ƙasan ido ya ke kallonta a fakaice tare da taɓe baki a ransa yana mamakin jin kalmar larabcin daga bakinta. Ummie ta yi murmushi haɗe da jawo ta jikinta ta amsa da,
"Sabahul Noor, habibty. Fatan kin tashi lafiya?" A kasalance ta ce, "Lafiya qalau Ummie."
Ganin ta yi kamar ba ta san da wanzuwarsa a wajen ba ya sa ya ce, "Ummie na fa yi latti fa."
Watsa mishi harara Ummie ta yi tare da faɗin, "To na riƙe ka ne?"
Ya ce, "Abincin tom." Sai da ta ƙara hararar shu sannan ta juya kalle Hayat cikin kwantar da murya ta ce,
"Ɗiyata taimaka ki kai mishi abincin nan motarsa kar ya cinye ni da mita." A ladabce ta ce,
"To Ummie." Ta saka hannu ta ɗauki abinci ba tare da ta yarda ko da wasa ta kalle inda ya ke tsaye ba. Sallama ya yi wa Ummie ya yi gaba ta bi shi a baya har wajen motar. Bayan motar ya buɗe mata ya na tsaye a wajen ƙiƙam ba tare da ya matsa daga wajen ba. Hannu ta saka ta ja ƙofar motar ya buɗe gaba ɗaya, hakan ya ba ta damar ajiye basket ɗin.
Ganin da gaske ta ke yi wato ba za ta gaishe shi ba. Ta juya za ta wuce ya saka hannu ya fincikota. Abinka da abin da ba ka yi zato ba kuma ta tashi yau jiki babu ƙwari, ta yi luuu kamar za ta faɗi ƙasa motar ya yi suporting ɗinta. Hannunsa ya saka tare da tallabo haɓarta kwatsam idonsu ya sarƙe da na juna..........
#ASecretWrittenInScars
#HayatsHiddenPast
#TheFireInHerDreams
#TurbayaNovel
#ZeeyluvWrites
#ShelelenYota
#Ecoth_Team_Of_Yota
GA WANI SANARWA MAI MUHIMMANCI. SAURA 4 PAGES FREE PAGE SU ƘARE WATO BOOK 1 KENAN SAI A SHIGA BOOK 2. TOH DON ALLAH MASU CE MIN SUNA SON ZA SU YI PAYMENT NA CE SU YI HAƘURI ZAN SANAR DA LOKACIN PAYMENT ƊIN. TOM YNZ ABIN YA SAUYA SAI KU YI HAƘURI KU KARƁI UZURINA A HAKA DON ALLAH🙏🏻BA ZAN YI PAID GROUP A WHATSAPP BA SBD WASU DALILAI NA MASU ƘARFI🥹A AREWAPEN ZAN CI GABA DA POSTING BOOK 2 IN SHA ALLAH...... NA GODE🥰
Shalelen Yotawa..........✍🏻