TURƁAYA

The Secret She Carries

by @zeeyluv

Page...............17




Ita ta fara ɗauke idonta daga cikin na sa ta yi gefe da idanunta ta na kallon wani direction ɗin daban. Duk da kasalar da yake tattare da ita, hakan bai hanata aro jarumta da ƙarfin hali ba. Nan da nan ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta na tsuke bakinta. 


Cikin tsare gida ya ɗago haɓarta da ya tallafe cikin hannunsa, ya ɗan matse haɓar ta yadda ya san za ta ji zafin hakan wanda sai da ta runtse ido don azaba. A daƙile ya ce, 


"Wato ke har kin yi growing wings a gidan nan da ba za ki iya gaida mutane ba ko? Saboda ba a koya miki tarbiya a gidanku ba." 


Sosai kalamansa na ƙarshe su ka dake zuciyarta har sai da idonta ya kawo ruwa, don jin furucin ta yi tamƙar cin fuska ne ga iyayenta. Amma ta share ba tare da ta ce komai ba ta shiga kici kicin fisge kanta daga gare shi saboda sam yau ba ta tashi ya niyyar rigima ba sai ta ci alwashin duk abin da zai mata ba za ta tanka shi ba. 


Ya na tsaye a wajen duk wannan kiciniyar da ta ke yi ko gezau bai yi ba saboda ba wani riƙon kirki ya yi mata ba, amma kasantuwar ƙarfin ba ɗaya ba ya sa ta gagara ƙwatar kanta. Sai kawai ta ɗan yi relax kamar ta haƙura wannan hanyar ba zai ɓille mata ba. 


Ganin ta yi relax ɗin ya sa yayi murmushin mugunta wanda iyakacinsa fatar baki, ya sakankance. Ai kuwa ta fake idonsa ta gantsara masa cizo a hannu babu zato babu tsammani. Tuni ya yi saurin sakinta ya na yarfe hannu saboda cizon ya shige shi ba kaɗan ba. 


Nan ta samu falle ta yi hanyar ciki da sauri. Sai da ta kai entrance ɗin da zai sada ta da ciki sannan ta dakata ta juya tana kallon shi daga inda ta ke yadda ya ke ta yarfen hannu. Abin ya so ba ta dariya amma ta gimtse saboda ba ta cikin yanayin nishaɗi. Daidai nan ya juyo karaf su ka haɗa ido ta yi saurin galla mishi harara tare da murguɗa mishi baki sannan ta nufa ciki. 


Haɗe rai ya yi daga inda ya ke yayi mata ƙwafa a kan za su haɗe ne......


Duk abin nan da ya faru a kan idon Ummie ya faru, daga inda ta ke ta na ganin komai ta makeken windon da ke facing ɗin parking slot na gidan. 


A parlour ta samu Ummie ta na ƙoƙarin kunna Tv. Hayat ta ce, 


"Ummie ina Farhat ne wai? Gaba ɗaya ban ji motsinta ba." 


Ummie ta ce, "Ai Farhat ta tsufa a makaranta yanzu, test ɗin safe su ke da shi, shiyasa ta fita da sassafe." 


Hayat ta ce, "Okay." Tare da nufar hanyar ɗakinta. Ummie ta yi saurin faɗin, "Hayat ina kuma za ki je? Ga breakfast can ya na jiranki?  Ta ɗan yatsina fuska ta ce, "Ummie not now. Ba na jin yunwa." Ta na gama faɗin haka ta shige ɗakinta. 


Har ɗakin Ummien ta bi ta da breakfast ɗin. Da sallama ta tura ƙofar ɗakin ta saka kai ciki.  A can tsakiyar gado ta hange ta. 


Hayat ta yi zurfi cikin tunani har ma ba ta san lokacin da Ummie ta shigo ba, sai da ta dire mata abincin a gabanta ne ta yi firgit ta dawo cikin tunaninta. Idon Ummie ne ya sauka a kan hotuna da ke gabanta.....




********


Shigowar Sheikh gidan ya yi daidai da dawowar Abie daga office. A parlour su ka yi kiciɓis. Cikin girmamawa Abie ya gaishar da Sheikh ɗin. Sheikh ya amsa tare da tambayar shi, "Lateef ina gift ɗin da na ce Arwa ta rubuta ka bata za a kai gidan iyayen ango?" 


Abie ya ce, "Afwan da yake yau ina da wasu ayyuka ne sosai a office ya saka na ba wa Afeef ya haɗa kayayyakin." 


"To yanzu ina Afeef ɗin ya ke?" Cewar Sheikh. 


Kafin Abie ya kai ga ba wa Sheikh ɗin amsa ya hango Afeef na zuwa. Ya ce, "Yauwa ai ga ma Afeef ɗin ai bari ya ƙaraso mu ji." 


Suna tsaye a wajen ya ƙaraso kanshi duƙe a ƙasa sam bai ma san su na wajen ba, don da ya sani da tabbas ya canza hanya. Sai ya gama shigowa cikin tsakiyar parlourn sannan ya ankara da su. Nan da nan ya ja burki ya tsaya gabanshi na faɗuwar rashin sani abin da zai ce. 


Da fara'a Abie ya ce, "Yauwa Afeef ina ka ajiye kayayyakin nan? Ga masu kai war har sun hallara." Daram dam dam zuciyarshi ta bada wani sauti mai ƙunshe da ban tsoro a cikinta. Cikin inda inda ya fara laluɓen aljihunsa ya na kame-kame. 


Kamar daga sama ya hango mutane niƙi-niƙi da kaya wanda ga dukkan alamu ma'aikata ne. Daidai nan saƙo ya shigo cikin wayarsa da ya ke riƙe a hannunsa. "Sent." Abin da ya gani kenan a rubuce. 


Abie ya ce, "Wai Afeef lafiyarka ƙalau kuwa ina tambayarka abu ka tsaya ka na mini inda-inda. Idan ba ka siyo ba ka fito ka faɗa min mana." 


Marairaice fuska ya yi ya ce, "Haba Abie ya za ka ce ban siyo ba! Kawai surprise na ke son na yi muku ne. Ku duba ku kalle can ku ga." Ya ƙarasa maganar ya na musu nuni da hannunsa zuwa ƙofar shigowa. 


Abie bai san lokacin da ya washe baki ba don murna, ganin yadda Afeef ya fitar da kunya a lokacin da ya ke gab da kunyata a idon jama'a bai bari ya kunyata ba. Abie ya shafa kan Afeef ɗin ya na faɗin, "Allah ya yi maka albarka Ibni, ya kareka daga sharrin mutum da aljan." Afeef sai amsawa ya ke yi da 


"Ameen." Daga haka Abie ya ce, "Bari na ƙarasa ciki kafin ku gama shiryasu. Shima Sheikh da ya ke tsaye tun ɗazu a wajen ya na jiran ya ji cewa Afeef bai siyo saƙon da aka bashi ba ya sauke mishi trailar tijara sai kuma Allah ya taimaka ya rufa wa Afeef da Abie ɗin asiri. 


Shi ma ya ja jikinsa ya yi ciki ba tare da ya furta komai ba, kuma tsaye ba za ka ce ya ji daɗin kawowar ko akasin haka ba. Kasancewarsa mutum ne shi mai murɗaɗɗan zuciya da aƙida na bala'i ya sa baka taɓa gane gabansa bare bayansa.


Sai a sannan Afeef ya samu damar sauke wata nauyayyen ajiyar zuciya. Ta ke kuma ya wani ƙaunar ɗan uwansa Asad da tausayinsa ya lulluɓe shi nan take. A ransa ya na ƙiyasta yadda ƙanwarsa za ta yi amfani da abin da yayanta ya siya mata ba tare da ta san cewa ɗan uwanta bane siya. A fili ya furta, "Allah ka nuna min ranar da zan ga duka ahalina a ƙarƙashin inuwa ɗaya...."




******


Da mamaki Ummie ke kallon hotunan, duk da ba ta ganin abin da dake cikinsu kasancewar tsoffin hotuna ne ba komai kake iya ganin sosai daga nesa ba. Ba abin da ya fi ɗaukar hankalinta illa ganin yadda gefen hotunar ya ke a ƙone, wanda da alama wuta ne ta taɓe su. 


Cikin dabara Hayat ta ja blanket ta rufe hotunar saboda ganin yadda hankalin Ummie ya koma kan su. Kuma sam ba ta son ta yi mata tambaya game da hotunar saboda ba ta san amsar da za ta bata game da su ba. 


Maimakon tambayar da ta ke jira ta ji ya fito daga bakin sai ta ji  Ummie ta ce, 


"Maza cinye ki ba ni plate ba na son jin wani excuse daga bakinki. Haba sai ka ce an canza mini ke, ina murna na samu me ɗebe min kewa da saka ni farin ciki a gida kuma lokaci ɗaya kuma za ki koma sauya. To sam ban lamunta da wannan halayar da kika aro ba duk sai ya sa ki muni kamar zombie." Ummie ta ƙarasa cikin ɗan haɗe rai. 


Babu shiri Hayat ɗin ta kwashe da dariya ta na faɗin,

"Allah ya ja da ran Ummie ta. Na tuba, na bi Allah na bi ki. Yanzu zan ci abincin tas kafin mu wuni ki na min lecture a gidan nan yau." 


Ta yi maganar cikin barkwance. Sai kuma ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce, "Amma Ummie don Allah ki daina cewa na koma zombie. Duk wannan kyaun fuskar tawa." Ta ƙarasa kamar za ta yi kuka. 


Ummie ta ce, "Ba ni dainawa matuƙar ki ka cigaba da wannan baƙin halin da sunan da zan koma kiranki da shi kenan."


"A'a Ummie ba ma zai kai ga haka ba in sha Allah. Zan fa dawo normal kamar yadda na ke na ci gaba da addabarku har sai na gundureku. Kawai mood swing ne ke damuna, amma yanzu haka ma ya kama kan shi tun da ya ji Ummie ta fara haɗa ni da zombie." Cewar Hayat ɗin ta ƙarasa ta na dariya. 


Ummie ta ce, "Better ki faɗa masa babu wajenshi a wannan gidan ya yi ta kansa kar na sake ganin ƙafarsa ah tom. Kuma minti biyar na baki ki cinye abincin nan kafin na dawo na zo na samu empty plates." 


Yadda kika ce haka za a Ummie ta, ni ko a minti ɗaya kika ce ma na cinye ai tsaf zan cinye yadda na ke jin yunwar nan, dama fulako ne saboda a zo a rarrashe na ci shiyasa na yi haka kuma gashi na samu." Ta yi maganar ta na dariya. 


Ummie ta dungure mata kai ta na faɗin, "Ja'ira wato kin mayar da ni kakanki ko? Akwai gaba ai za ki faɗo hannuna." 


Kafin ka ce me? Tuni Hayat ta wartsake ta ci gaba da sabgoginta kamar yadda ta saba. Ranar a gida ta wuni tare da Ummie babu inda ta je. A wuni ranar wata soyayya da shaƙuwa ya sake shiga tsakaninta da Ummie. Haka ta saka Ummie a gaba da hira. Ummie na kitchen ta na girki ita kuma ta na gefe ta na zuba. Dama ba girkin ta iya ba balle ta ce za ta taya Ummien. Haka itama Ummien ba ta buƙace da  ta yin ba. A haka har Farhat ta dawo............



*******************



Kamar yadda al'adar garin ya ke, gidan maza ne ke zuwa gidan mata karɓar kyaututtukar aure haka su ma ya kasance a ahalin SHAREEK KHAN. Musamman aka haɗa ɗan ƙwarya-ƙwaryar liyafa domin tarbar ango da iyayensa.


Anci an sha an yi wa dangin ango tarbar na ban girma daga nan dangin angon su ka shiga duba kyaututtuka su na ta sam barka. Yayin da ƙasan ran Kiswar(Ammu mahaifiyar Irfan) ke neman abin fakewa da shi domin tada husuma. 


Idonta ne ya sauka a kan wani haɗaɗɗen lafaya da wani label a jiki. Ɗago lafayar ta yi da sauri ta na zare ido...........





GA WANI SANARWA MAI MUHIMMANCI. SAURA 3 PAGES FREE PAGE SU ƘARE WATO BOOK 1 KENAN SAI A SHIGA BOOK 2. TOH DON ALLAH MASU CE MIN SUNA SON ZA SU YI PAYMENT NA CE SU YI HAƘURI ZAN SANAR DA LOKACIN PAYMENT ƊIN. TOM YNZ ABIN YA SAUYA SAI KU YI HAƘURI KU KARƁI UZURINA A HAKA DON ALLAH🙏🏻BA ZAN YI PAID GROUP A WHATSAPP BA SBD WASU DALILAI  NA MASU ƘARFI🥹A AREWAPEN ZAN CI GABA DA POSTING BOOK 2 IN SHA ALLAH...... NA GODE🥰



Shalelen Yotawa..........✍🏻