Matukar Ina Raye 10
by @mrsisham12
MATUƘAR INA RAYE
(As Long as i’m alive)
Writer — MRS ISHAM
WhatsApp: ***
Page 10
Ana kiran sallar Magrib lokacin da Waheeda ta shiga gida. Ta tarar da Zuwaira a cikin gida tana cin abinci.
Da mamaki Zuwaira ta ce,
“Waheeda, wa ya dawo da ke?”
Jin sunan Waheeda da Zuwaira ta kira ne ya sa Ummah da Salma suka fito, su ma suna kallonta cikin mamaki.
Ummah ce ta ƙaraso kusa da ita ta ce,
“Mamana, ke da wa kuka dawo? Domin yayanku yanzu ya fita da niyyar zuwa ya ɗauko ki.”
Zunbura baki ta yi sannan ta ce,
“Ni kaɗai mana Ummah, a mashin mai ƙafa biyu.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku. Yanzu ke kaɗai kika dawo tun daga can anguwar Waheeda? Me yasa ba ki da lissafi ne? Ba kya ganin dare ya yi?”
“Ummah, cewa fa ta yi in kwana, ni kuma na ƙi.”
Cikin ƙasa da murya Salma ta ce,
“Ki yi haƙuri Ummah, ba za ta ƙara ba.”
Girgiza kai kawai Ummah ta yi sannan ta shige ɗakinta, ta barsu a waje.
Salma ta kalli Waheeda cikin tausasawa sannan ta ce,
“Autar Ummah, kar ki sake irin haka kin ji? Kin san duniya ta lalace. Ki kula da kanki sosai.”
Waheeda ta fahimci cewa tahowar da ta yi ita kaɗai bai dace ba, hakan ya sa ta ce,
“Toh.”
Muryarta cike da sanyin jiki.
Zuwaira ta tabe baki sannan ta furta,
“Ni sam ban ga laifin Waheedatu ba. Ita Anti Labiba ma me ya sa za ta barta ta taho ita kaɗai?”
“Hmmm.”
Shi ne kawai abin da Salma ta faɗa. Daga nan ta zauna ta dubi Waheeda.
“Za mu fita tallan dare?”
Waheeda ta marairaice fuska. Ganin yadda ran Ummah ya ɓaci ya sa ba ta tunanin za a bar ta ta fita yau.
“Ummah za ta bar ni?”
Salma ta haɗiye shinkafar da ke bakinta sannan ta furta,
“In kin ba ta haƙuri ba.”
Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, Waheeda ta juya ta nufi cikin gida, ta barsu a wurin.
Ciki ta wuce ta barsu a wurin. Ummah ta samu tana gyara gado. Ta tsaya daga bayanta tana mutsu-mutsu. Ummah ta share ta tamkar ba ta san da wanzuwarta a ɗakin ba, ta ci gaba da aikinta.
“Ummah, dan Allah...” ta kira sunanta a sanyaye kamar za ta yi kuka.
Ba tare da ta juyo ba ta ce,
“Kar ki ce min komai. Tattara ki fice min a ɗaki kar in miki abin da ba zan so ba.”
“Ke fa ba yarinya ba ce, Waheedatu. Nan da ’yan kwanaki za ki cika shekara goma sha huɗu. Duk abin da kike yi da hankalinki kike yi. Kawai son saka ni magana ne, ba komai ba. Ki ci gaba.”
Sosai Waheeda ta shiga yi mata magiya amma Ummah ta yi banza da ita. Da ta gaji ne kawai ta ce mata,
“Fi ta ki je ku fara haɗa kayan tallanku.”
Ba yadda ta iya, haka ta fita duk ranta babu daɗi.
Bayan sun yi sallar Isha’i suka fita kamar yadda suka saba. Tuwan madarar da Labiba ta ba ta kuwa, ta ci gaba da ɓoyewa a hijabinta, ta ƙi yarda kowa ya gani balle har a roƙe ta.
Zuwaira ce ta zuba doya mai zafi a baƙar leda sannan ta ba Waheeda.
“Autar Ummah, dan Allah ki miƙawa mai gadin sabon gidan nan doyar nan mana.”
Karɓa ta yi sannan ta nufi gidan. Ta kwankwasa ƙaramar ƙofar, yaron mai gadin ne ya buɗe yana tambayar waye.
Bayan ta sanar da shi aikan da ta kawo ne ya buɗe mata gate ta shiga. Tsaye ta yi daga bakin gate ɗin tana karewa gidan kallo kamar idonta zai faɗo ƙasa. Kamar sakiyar ƙauye haka ta tsaya tana kallon ƙayataccen gidan.
“Sannu yarinya.”
Ta ji muryar mai gadin.
Gaishe shi ta yi sannan ta miƙa masa ledar.
“Na gode. Za ki iya tafiya.”
Ya faɗa yana shiga sashensa, tare da kiran wanda ya buɗe mata ƙofar ya tabbatar ya rufe bayan ta fita.
Da ta ga ya shige, ga shi wanda ya kira bai fito ba, sannan babu kowa a harabar gidan, sai ta ce a ranta,
“Ai wallahi sai na kalli ko’ina a gidan nan saboda in ba wa su Safara’u labari.”
Tana gama faɗin haka ta miki ta wata hanya da ta ga ta yi straight.
Haka ta dinga tafiya tana kalle-kalle.
“Hey!”
Dakatawa ta yi da tafiya. Jin muryar da ta yi a bayanta ya sa ta juyo.
Kyakyawar yarinya ce tsaye a gabanta, sanye da riga da skirt masu kyau da tsada. Kamar talabijin haka Waheeda ta zuba mata ido tana kallon kayan jikinta. Har hasaso kanta take a cikin kayan.
Ganin ta zuba mata ido yasa yarinyar ta ce,
“Kin zo ganin wani ne?”
Ta tambaye ta tana sakar mata murmushi.
Kamar sokuwa Waheeda ta gyada kai.
“Eh. Mai gadinku ya siya doya a wajenmu, shi ne na kawo masa.”
“Na gane.”
Ta faɗa tana miƙa mata hannu, har yanzu fuskarta ɗauke da murmushi mai jan hankali.
“Sunana Nini, ke fa?”
Waheeda ma ta miƙa mata hannu tana mayar mata da murmushi.
“Ni kuma sunana Waheedat. Muna siyar da kosai mai bala’in daɗi da safe, da rana kuma awara, da dare kuma muna yin doya da awara.”
Waro ido Nini ta yi.
“Da gaske kuna yin kosai? Mamie ɗinmu tana son kosai, amma masu aikinmu ba su iya yi ba. Zan gaya mata, watakila ta dinga saye a wajanku.”
Har ranta Waheeda ta ji daɗin maganar. Ta samu customer kenan, tunda yanzu ita ce za ta dinga sayarwa a ƙofar gida.
Nini za ta sake magana kenan ta ji ana kiranta.
Kallan Waheeda ta yi ta ce,
“Mamie na kirana. Ki jira ni a nan kin ji?”
Kai kawai Waheeda ta gyada mata.
Nini ta bar wurin da gudu.
Ajiyar zuciya Waheeda ta sauke. Ta fara tunanin ta tafi ne ko kuma ta jira ta dawo.
Da ta ga har yanzu ba ta dawo ba kuma ita ta gaji da jira, sai ta fara tafiya domin barin wajen.
Yana kwance a kan gadonsa na alfarma, idanunsa a lumshe kamar mai barci.
Wani motsi ya ji a bayan window ɗinsa. Ya kasa kunne domin ya tabbatar da abin da ya ji. Da motsin ya sake yawa ne ya miƙe a hankali ya leka ta window.
Inuwar mutum ya gani.
Nan take ya fita daga ɗakin, ya zagaya har ya fito inda window ɗin yake.
Ganin mace ta ba shi baya ne ya sa ya furta,
“Waye a wurin?”
Da sauri ta juyo.
Hasken fitilar wajen ya haskaka farar fuskarta. Nan ya samu ganin fuskarta sosai.
Da mamaki yake kallonta yana tambayar kansa me ya kawo ta gidan a wannan lokacin.
Ita kuwa, tsoro ne ƙwarai ya bayyana a fuskarta.
A hankali ya fara takowa gare ta yana cewa,
“Me kike nema a bayan window ɗina?”
Yana sake taku, Waheeda ta zura a casa’in ta ranta da gudu, ta bar shi tsaye yana bin bayanta da kallo.
Tabe baki ya yi ya juya zai tafi, sai kuma ya tuna kamar ya ga ta yasar da wani abu.
Da farko ya yi niyyar ya kyale shi, amma sai ya ji yana son ganin me ta bari.
Daidai inda abin yake ya tsaya. Ya sunkuya ya ɗauki robar yana juyawa a hannunsa.
A hankali ya furta,
“Alawar madara?”
Ya yi maganar cikin tsigar tambayar kansa.
Yana tsaye yana juya robar, sai Nini ta iso gurin tana kalle-kalle.
“Ya BK, ka ga sabuwar kawata a nan?”
Ya zuba mata ido kamar bai gane abin da take faɗa ba. Sai da ta sake maimaita masa tambayar kafin ya ce,
“Wace kawarki?”
Cikin shagwaɓa ta ce,
“Wata fara kyakkyawa tana tsaye a nan, tsayinmu ɗaya da ita. Sunanta Waheedat.”
Ya girgiza mata kai.
“Ah ah, ban ganta ba.”
Yana faɗin haka ya shige ciki, ita ma ta bi bayansa har bedroom ɗinsa.
Tana ta surutai,
“Allah sarki! Ta gaji da jirana ne shi ya sa ta tafi. Gobe idan na je siyo wa Mamie kosai zan ba ta haƙuri, kar ta ga kamar na yi mata wulaƙanci. Ko Ya BK?”
Ya gyada mata kai yana tuna haɗuwarsa da Waheeda da kuma yadda ta danganta fuskarsa da kosan Ummanta.
Ya ɗago robar da ta yasar ya kalla, sannan ya ajiye ta a kan table, shi kuma ya zauna a kujera.
“Laaah, Ya BK?”
“Naam, Nini.”
Ya amsa mata yana danna wayarsa.
Har gaban table ɗin ta iso.
Ta sa hannu ta ɗauki robar tana murmushi, sannan ta dubi BK da ya maida hankalinsa kan wayarsa.
“Ka samu alawar madarar da kake so kenan. Bari in buɗe in ji taste ɗinta.”
Ya ɗan ɗago idanunsa ya kalleta.
“Kar ki buɗe.”
Ta shagwaɓe.
“But why? Please, in ɗauki ɗaya? Please… please, Ya BK.”
Ya girgiza kai alamar a’a, sannan ya ce,
“Ba tawa ba ce, Nini. Ta kawarki ce.”
“Wai Waheedat?”
Ya gyada kai.
Ta buɗe robar, ta ɗauki guda ɗaya.
“Gobe zan ce mata na ɗauki ɗaya. Na san ba za ta ji haushi ba. I want to taste it. Daga gani ma zai yi daɗi.”
Ganin ta buɗe har ta ɗauka ne ya sa ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Amma yana jin yadda ita kaɗai take santin alawar madarar.
Tsabar daɗi har jujjuya kai Nini take tana fitar da sautin,
“Uhmmmmmmmmm…”
“Tun da nake ban taɓa shan irin wannan alawar ba, I promise. Ya BK, ka taɓa shan irinta kuwa? Na san ma ba ka taɓa sha ba.”
Ta yi maganar tana ƙoƙarin sa masa a baki.
Ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai alamar baya so.
Ta sake shagwaɓe masa.
“Don Allah… don Allah ka ɗan ɗanɗana. Tunda kafi son alawar madara, za ka ji daɗin wannan sosai.”
Ganin idan bai ɗanɗana ba Nini ba za ta bar shi ba, ya karɓi wadda ke hannunta ya kai bakinsa.
Ta tsura masa ido tana son ganin reaction ɗinsa kan alawar.
Amma sam expression ɗinsa bai sauya ba, har ya gama cin wadda ya karɓa.
Ya dubeta a tausashe ya ce,
“Na ɗanɗana. It’s getting late. Go and sleep, Nini.”
Ta yi murmushi.
“Okay, Ya BK. Good night.”
Ta faɗa tana rungume shi, sannan ta fita.
Sai da ya ga ta rufe masa ƙofar kirif, sannan ya miƙe da sauri ya isa gaban table ɗin da robar take. Ya ɗauka yana jefa guda ɗaya a bakinsa. Wani irin lumshe ido ya yi yana jin daɗin ɗanɗanon alawar har cikin ransa. Ya zauna yana ci gaba da sha a hankali.
“Me yasa wannan alawar ta fi kowace alawa da na taɓa sha daɗi?” ya tambayi kansa.
Ya ci gaba da sha har sai da ya shanye tass, sannan ya soma tunanin idan Nini ta buƙaci robar domin kai wa Waheeda fa? Shiru ya yi yana ɗan nadama, sai zuciyarsa ta raya masa cewa kawai ya bata kuɗin ta.
Jin an taɓa handle ɗin ƙofar ne ya sa ya ɗaga pillow ɗinsa ya ajiye robar a ƙarƙashinsa ya ɓoye ta.
Mamie ce ta shigo, fuskarta ɗauke da tsadadden murmushi, hannunta riƙe da glass tray.
“Ina ta addu’a Allah ya sa kar in shigo in same ka ka yi barci, and I’m so lucky.”
Ta faɗa tana zama a gefensa tare da ajiye tray ɗin a kan teburi.
Shiru ya yi yana kallon tray ɗin. Wani irin yanayi ne ya sauka masa duk lokacin da ya ga tray ɗin magungunansa. Tsoro da firgicin da yake ƙoƙarin ɓoyewa suna bayyana a idanunsa. Yana ƙoƙarin danne su ne saboda ba ya son a ga rauninsa. Kowa ya riga ya san shi mai rauni ne, amma ba wanda ya san irin yaƙin da yake yi a ransa.
“Son...” ta kira sunansa ganin yadda idanunsa suke sauyawa zuwa ja, ga kuma zufar da take tsatstsafowa a fuskarsa.
“Mamie...” ya kira sunanta da wata irin murya mai rauni.
“Ki taimaka min... bana so... bana son wannan maganin.”
Ya faɗa yana riƙe saitin zuciyarsa. Ya cije lips ɗinsa yana jin yadda bugun zuciyarsa ya ƙaru fiye da kima. Ga kuma wani irin raɗaɗi da yake ji kamar an saka hannu an matse tsokar zuciyarsa ana murɗata.
Cikin tashin hankali Mamie ta rungume shi tana kiran sunansa.
“Muhammad, ka taimaka mini. Ka taimaki rayuwata. Ka sha maganinka. Idan wani abu ya same ka, ba zan iya rayuwa ba. Ka dube ni, Mamie na gabanka Muhammad.”
Da ƙyar ya ɗaga idanunsa ya zuba mata su. Tausayin kansa da na Mamie suka lulluɓe shi lokaci guda.
A hankali cikin azaba ya furta,
“Zan sha Mamie... zan sha.”
Da ƙyar ya iya shan maganin. Bayan ya sha ya kwanta a gado.
Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawayenta. Ta rufe shi da blanket sannan ta tsuguna a gabansa tana kallon kyakkyawar fuskarsa cike da so da tausayinsa.
“Allah ya ba ka lafiya Muhammad. Ya ba ka ikon cinye jarabawarka.”
Kiss ta manna masa a kumatu sannan ta kashe wutar ɗakin ta fita.
Duk abin da yake faruwa tana labe a window ɗinsa tana gani. Har fitowar Mamie daga ɗakin tana kallonsu.
Sai da Mamie ta fita, ta zagayo ta shigo ɗakin. Duk da duhun da ya mamaye wurin, ta isa bakin gadon ta zube a gabansa tana fashewa da kuka mai ƙarfi.
Sosai take kuka tana kallon fuskar BK.
Ta shafe kusan mintuna goma tana kuka kafin ta iya rarrashin kanta.
“Ka jure Ya BK. Na san za ka iya. Kai ba mai rauni ba ne kamar yadda suke maka kallo. Kai jajirtaccen namiji ne. Kuma wata rana za ka rabu da wannan ciwon.”
Ta faɗa cikin kuka.
“Wani irin yanayi nake ji a zuciyata? Na rasa me yake faruwa da ni Ya BK. Ina ma zan iya faɗa maka halin da nake ciki. Ban san ya aka yi ba, amma wutar soyayyarka tana ƙara ruruwa a zuciyata. Sanka nake tamkar raina Ya BK...
Me yasa hakan yake faruwa da ni? Da kana cikin hayyacinka da tabbas kallon mahaukaciya za ka yi mini. Domin soyayyar da nake maka ta fi ƙarfin yan uwantaka,tamkar soyayya ce ta uwa da ɗanta.
Yanzu ni kaina na san ni mahaukaciya ce. Na sani.”
Ta ƙarasa cikin kuka mai tsuma zuciya.
Sannan ta fashe da wata irin dariya kamar zararriya.
“Na ɗauka soyayyar yan uwantaka ce. Ashe soyayya ce tsakanin kanwa da yayanta. Amma kullum al’amarin yana ƙara girma. Wannan zuciyar tawa ba ta mini adalci ba. Dole ne in gano me take nufi.”
Ta faɗa tana dukan ƙirjinta.
Domin zuwa yanzu ta soma tsanar kanta. Ta rasa inda za ta fara gyara rayuwarta, abubuwan da take ji sun soma fin ƙarfinta.
A wannan lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin tare da kunna switch. Haske ya mamaye ko’ina.
Da mamaki Zannor dake tsaye a bakin ƙofa yake kallonta. Sannan ya maida dubansa zuwa BK dake kwance. Kallo ɗaya za ka masa ka san wannan ba barci ba na dadi ba ne, barci ne bayan wahala da azaba.
“Zanaya...” ya kira sunanta.
Da sauri ta ɗago kumburarrun idanunta ta zuba masa su. Nan take ta nufe shi da gudu ta faɗa jikinsa tana fashewa da sabon kuka.
“Ya Zannor, sai yaushe wahalar Ya BK za ta kare? A ko da yaushe haka za mu zuba ido muna ganinsa cikin ciwo da azaba?”
Bubbuga bayanta yake yi a hankali, amma a zahiri shi kansa zuciyarsa tana zubar da jini ne. Ya haɗiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, sannan ya ɗago idanunsa zuwa kan BK da ke kwance a gadon.
Wani irin raɗaɗi ne ya soki ƙirjinsa.
Tun suna yara tare ya taso da BK. Ya san murmushinsa, ya san fushinsa, ya san shirunsa, har ma ya san lokacin da yake ɓoye damuwa. Amma abu ɗaya da bai taɓa sabawa ba shi ne ganinsa cikin azaba.
A duk lokacin da ya ga BK yana fama da ciwo, sai ya ji kamar shi ne yake jin zafin a jikinsa.
Ya sha kwanciya da dare yana addu’ar Allah ya ɗauke rabin wahalar BK ya ɗora masa, ko da hakan zai sa ya rayu cikin ciwo har ƙarshen rayuwarsa. Amma kullum idan ya wayi gari sai ya sake ganin ɗan uwansa cikin irin azabar da ta kasa ƙarewa.
Wani lokaci har yana jin haushin kansa. Kallon yadda ciwo yake cinye shi a hankali.
Kallon yadda murmushinsa yake ƙara raguwa kullum.
Kallon yadda rayuwarsa take zama kamar kurkuku.
Ya matse haɓarsa da ƙarfi, idanunsa suka yi ja.
“Kin san me yake mini ciwo fiye da komai, Zanaya?”
Ya faɗa da ƙyar, muryarsa na rawa.
“Ba ciwon BK ba ne…”
Ya yi shiru na ɗan lokaci yana kallon fuskar ɗan uwansa.
“Abinda yake kashe ni shi ne ganin yadda ya saba da ciwon.”
Hawaye suka cika idanunsa.
“Ya daina kuka, ya daina ƙorafi, ya daina tambayar yaushe zai warke. Kamar ya yarda cewa wannan ita ce rayuwarsa.”
Ya girgiza kai a hankali.
“Kuma duk lokacin da na ga haka, sai na ji tsoron cewa wata rana BK zai daina yaƙi gabaɗaya…”
Wani sabon kuka Zanaya ta fashe dashi tana sake rungume Zannor sosai a jikinta domin wayannan kalaman na sa sun kashe ta. Ya za ta yi in Bk ya karaya? rayuwarta a yanzu ji take tamkar yana a hannunsa kuma tabbas wani abu ya same sa ba ta tunanin za ta kara ko da daƙiƙa daya a wannan duniyar.