MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 29

by @maimunabala209

MATAR GIDA 029



SHUUKRAN/022




P29




A hankali Ɗalha ya samu waje ya zauna a bakin gado yana ƙarewa Unaisa kallo ganin bacci take hankali kwance,ga nononta ɗaya a waje ɗaya kuma rufe da daurin ƙirji,ƙara kallon ɗakin ya yi a karo na biyu kafin a hankali ya kai hannu ya fara tashinta daga barcin da take,a firgice Unaisa ta tashi zaune tana ƙarewa Ɗalha kallo da shima ita yake kallo fuskarsa babu alamar wasa,buɗar baki Unaisa ta yi da niyyar masa sannu da dawowa,wani mugun wari ya dake hancin sa babu shiri ya ja baya ƙadan yana kallonta fuskarta dauke da murmushi ta ce ''beb ka dawo sannu da dawowa'' ta faɗa tana gyara dauren kirji ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin ya ce ''tun safe ki ke bacci Unaisa?'' Unaisa bata kawo komai cikin zuciyarta ba kawai ta ce ''a'a na tashi fa har na ci abinci na yi sallah,bayan na idar da sallah ne bacci ya kwashe ni''numfasawa Ɗalha ya yi tare da jinjina kai ya ce ''ok na fahimta''shiru ya yi na wasu ƴan sakkani kafin ya ce ''amma wormer's dake parlour ba ki kwashe  kin kai su kitchen ba bayan kin gama cin abinci,in baza ki iya wanke su ba at least sai ki shigar da su kitchen'' taɓe baki ta yi kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta ce ''na yi tunanin za ka dawo ka yi breakfast ne shi yasa ban kwashe ba'' cike da mamaki Ɗalha ya ce ''wani breakfast ɗin?" ya jefo mata tambaya yana ƙare mata kallo ita ma shi take kallo har sannan idonsa a kanta ya ce ''da ban dawo ba aiy ya kamata ki kwashe su tunda kin ga rana ta yi,ga kuma wormer's da aka sa maki lunch plate ɗinda ki ka ci lunch shima ya bushe''shiru Ɗalha ya yi yana mayar da numfashi saboda zuwa yanzu ransa ya fara ɓaci gashi baya son nuna mata ɓacin ransa kar daga aure su fara samun saɓanin wani iska ya fesar daga bakinsa kafin ya sunkuyar da kai ƙasa ya ƙure tiles dake shimfiɗe kasar ɗakin da ido ya fara magana cikin kwantar da murya ya ce ''a gaskiya bani son ƙazanta,komai ƙanƙantarta bana so''shiru ya yi na wasu ƴan sakkani kafin ya ce ''ya kamata ki san wannan Unaisa bana son ƙazanta ko ƙadan bana son mu fara samun issue da ke a kan ƙazanta,gaba ɗaya aure na da ke yau kwana shidda da daura mana aure kar ki bari na fara maki ƙorafi tun yanzu ɗan girman Allah ki gyara halaiyyarki da ɗabi'unki dan mu zauna lafiya komai ƙanƙantar datti ɗaga min hankali yake'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan saƙanni kafin ya gyara zama tare da mayar da dubansa gareta ya ce ''yanzu na tambaye ki mana kin yi wanka kuwa yau?" banza Unaisa ta yi masa saboda ranta ya fara ɓaci har cikin zuciyarta bata ji daɗin maganganun da ya yi mata ba har ta fara tunanin anya kuwa Ɗalha da ta sani ne wannnan ya za'ayi daga aure ya fara mata ƙorafi kan abinda bai kai ya kawo ba ko dai saboda ya samu abinda yake so ne kenan bata da wata amfani a wajensa tunda ya karɓi budurcin ta shi kenan ta zama banza har ita zai ƙalla ya kira ƙazama yanzu ta yarda da abinda ake faɗa cewa maza basu da amana da sun samu abinda suke so wajen mace shikenan ta zama abin wulaƙantawa




















Ɗalha da har sannan idonsa a kanta ya ƙara jefo mata tambaya ya ce ''tambayar ki na ke na ce kin yi wanka?" da wani irin sauri ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta fara masa magana cike da rashin kunya tana ɗaga murya ta ce ''wani wanka? wani wanka ka ke magana a kai?bayan wanka da muka yi daren jiya wani kuma zan yi?" lokaci guda jikin Ɗalha ya yi sanyi tun ba yau ba yake mugun tsoron Unaisa da ta fara masa magana cikin ɗaga murya sai ya ji gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi hakan yasa ya kwantar da murya ya ce ''ina nufin wanka ta soso da sabulu'' a takaice Unaisa ta basa amsa cikin ɗaga murya ta ce ''ban yi ba'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya yi gyara murya ya ce ''to gaskiya ya kamata ki tashi ki yi wanka ki kuma gyara ɗakin ki,wadan nan kayayyakin dake suke watse ƙasan ɗaki pls ki samo waje ki zuba su dan Allah ga pant ɗin ki a can ga brazzier can, kayan da ki ka uni da shi jiya gashi can,pls ki ware masu datti a gefi guda marasa datti ma haka,dan Allah ki gyara su and ki duba kayan ki in da turaren wuta pls ki kunna in kuma babu ki faɗa min,wormer's ɗin Ammi zan tura ƴar aikinta ta kwashe su sannan duk sanda Ammi ta aiko mana abinci pls da kin ci ki riƙa wanke kwanuka in da hali ki haɗa har wormer's ɗin wanke ki mayar da su'' shiru Ɗalha ya yi yana kallon Unaisa ta rabka uban tagumi kamar wacce aka zaga kamar ba zai ci mata komai ba sai kuma ya ce ''kin ji abinda na faɗa'' banza ta yi masa bata ce komai ba Ɗalha ya sake tambayar ta ya ce ''kin jin abinda na faɗa''nan ma ta yi masa shiru sai da ya tambaye ta sau uku kafin ta amsa a takaice ta ce ''na ji''  Ɗalha ya sauki ajiyar zuciya kafin ya ce ''yanzu kafin ki yi komai tashi ki je ki yi wanka ki yi brush'' wani mugun kallo Unaisa ta yiwa Ɗalha kafin ta ce ''wai sau nawa zan faɗa maka ba kullum nake wanka da brush ba na faɗa maka ɗazu da safe sai jibi zan wanke baki wanka kuma aiy daren jiya na yi Allah yasa da kanka ka taimake min na yi wanka'' shiru ta yi na wasu ƴan sakkani yayin da Ɗalha na binta da kallon mamaki ta ce ''me yasa ka ke son canza min tsari ne?"zuwa yanzu ran Ɗalha ya fara ɓaci hakan yasa haɗa girar sama da ƙasa fuskarsa babu alamar wasa ya ce ''tun da ki ka aure ni dole za ki canza tsarin rayuwar ki kar fa ki manta ɗazu na faɗa maki cewar bana son ƙazanta,in har kina son cigaba da zama da ni mu zauna lafiya dolen ki ajiye wannan ɗabi'ar ta kazantar'' cike da masifa Unaisa ta tashi tsaye tana jijjiga jiki ta ce ''me ka ke nufi da kazanta rashi wanke baki kwana sha biyu shi ne ƙazanta?" ta kafe Ɗalha da ido tana jiran amsa shiru Ɗalha ya yi yana ƙare mata kallo ta daura da ''wallahi ba ƙazanta bane ra'ayi ne da kuma tsari,kowanne bil'adam yana da tsari da ra'ayi a rayuwarsa saboda haka ni bazan taɓa wanke baki kullum kamar yadda mutane ki yi ba saboda hakan shine tsari na,wanka ma ba kullum na ke yi ba'' 
















cike da ɓacin rai Ɗalha ya mike yana nuna Unaisa da ɗan yatsa ya fara magana cikin kakkausar murya ya ce ''a gaskiya zamu samun matsala da ke in har ba za ki yi abinda na ke so ba,kamar yadda na faɗa maki ɗazu in har kina son cigaba da zama da ni dole ki yi abinda na ke so,saboda haka daga yau dolenki ki wanke baki kullum sau biyu safe da yamma haka ma wanka sau biyu za ki riƙa yi safe da yamma'' tun sanda ya fara magana ta shiga nitsuwarta ganin yadda yake magana cike da ɓacin rai tunda take da Ɗalha bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba sai yau hakan yasa ta fahimci lallai ransa ya ɓaci tuni ta shiga rigar nitsuwa,lokacin da ta ji Ɗalha ya ce dole ne tayi wanka sau biyu a rana ta kuma wanke baki sau biyu nan take ta rasa nitsuwarta hakan yasa ta daka tsalle haɗe da buga kirji ta ce ''wanka sau biyu a rana?brush sau biyu? sai ka ce wacce bata da imani ko wacce Allah ya halitta dan brush da wanka haka kawai na wanke baki sau biyu na yi wanka sau biyu to wallahi bazan iya ba,sai dai na riƙa wanke baki duk bayan kwanaki tara ina dalili'' ta kare magana tana gyara daurin ƙirji a hankali Ɗalha ya tako har inda take tsaye ya tsaya dab da ita idonta cikin nasa kafin ya fara magana ba tare da alamar wasa ba ya ce ''maganar za ki yi brush bayan kwanaki tara ko kwanaki goma ko shidda babu wannan zancen dolenki ki wanke baki kullum'' wani murmushi mai sauti Unaisa ta yi tana jijja kai ta ce ''wallahi bazan yi brush kullum ba bazai taɓa yiwuwa ba,cikin kwanaki sha biyu na cire kwana biyar,zan riƙa wanke baki duk sati ko wacce juma'a kaga kwana bakwai kenan'' ta ƙare magana tana sosa kai murmushin gefin baki Ɗalha ya yi ya ce ''ba ki isa ba kullum za ki wanke baki kin dai ji na faɗa maki'' ganin yadda Ɗalha ke mata magana yasa ta fahimci lallai ransa a ɓace yake gudun abinda zai je ya dawo yasa Unaisa yin shiru bata tanka sa ba,abinda ta sani dai shi ne baza taɓa wanke baki kullum ba in ta yi masa adalci ta wanke duk bayan kwanaki biyar ina dalili kullum ta yi ta goge baki sai ka ce wacce bata da aikin yi,wallahi baza ta iya ba ita ba bayahudiya ce ni baƙar fata ce'' ta kare magana tana murguɗa baƙi ita kaɗai cikin zuciyarta,Ɗalha ya ce ''kin ji abinda na faɗa maki?" ji ta yi gaba ɗaya ta gaji da zancen kawai ta ce ''na ji na yarda kullum zan wanke" a hankali Ɗalha ya koma ya zauna ya ce ''kin yi la'asar'' har sannan ranta ɓace ta ce ''na yi'' Ɗalha ya ce ''ok to abinda nake so da ke yanzu ki shiga bathroom ki haɗa ruwa ki yi wanka ki wanke baki'' ba dan son ranta ba ta wuce bathroom tana buɗa kafa kamar ƴar shayi daga shigarta bathroom ta haɗa ruwan wanka,ba tare ta ɓada lokaci ba ta fara wanka,bata wani goge jiki da kyau ba a ganinta ta yi wanka daren jiya ba dalilin sake yin wanka yanzu bayan ta gama wanka ne ta yi brush,sama sama ta wanke baki haka ma harshe wankesu ta yi sama sama,bayan ta gama wanka kamar ɗazu ta cika ruwan ɗumi cikin buta lamba shidda ta yi tsarki duk yadda ta yi tasa hannu ta wanke wajen tsoro ya hanata haka dai ta zuba ruwan kamar yadda ta yi ɗazu,Ɗalha dake zaune cikin ɗakinta ya tashi ya fita daga ɗakin wormer's ɗin Ammi ya kwashe ya kai su can part ɗin Ammi,amma bai bari wani ya ganshi ba,ta kofar baya ya bi ya shiga kitchen ya ajiye basket ɗin wormer's kafin ya fita daga kitchen,daga haka ya wuce part ɗinsa da Unaisa bayan komawarsa part ɗin ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya shirya kansa cikin ƙananan kaya blue jeans da shirt fari,daga nan ya wuce masallaci dan gabatar da sallar magrib saboda a lokacin har an fara kiran sallah a masallatai anguwa,kamar yadda Ɗalha ya faɗa mata bayan fitarta daga bathroom bata tsaya sa kaya ba ta shiga gyaran ɗaki gaba ɗaya kayayyakin dake baje ƙasa ɗakin ta kwashe su ba tare da ta linke su ba ta buɗe kofar saif da babu kaya sosai a cikin ta watsa kayan daga haka ta gyara gado ba wani gyaran arziƙi ta yi ma gadon ma kakkaɓa katifa ta yi,kafin ta shirya pillow duk wani abinda take daurewa kawai take amma har cikin zuciyarta bata son yi,kamar ta mutu haka take ji tsabar ƙiwa








SHUUKRAN