MATAR GIDA PAGE 30
MATAR GIDA 030
SHUUKRAN/022
P30
Bayan ta gama gyara ɗakin ne ta dauki wata doguwar riga materail brown da aka yiwa ado da pink flower ta zura bata sa komai a ciki ba iya rigar ce kawai jikinta,rigar ta sauko mata har ƙasa yadda ko yatsun ƙafafunta ba'a gani haka ma hannu rigar ta rufe mata har yatsun hannunta,wata bakar hula ta dauko ta sa daga haka ta nufi bakin gado tana tafiya tana yawo cikin rigar jikinta,tana ji ana kiran sallah amma sai ta yi zamanta bakin gado tare da daukar waya ta kunna data ba tare da ɓata lokaci ba ta shiga group ɗin su na matan gida,kamar yadda Ɗalha ya faɗawa Amirah hakan kuwa ya faru karfe huɗu daidai Hafsah matar Muhsin ta shigo parlour Amirah tare da wata mata ƴar kimanin shekaru arba'in da biyar da a duniya biye da ita da alama ita ce ƴar aikin da Ɗalha ya ce za su zo,tarɓar mai kyau Amirah ta yi masu ta kawo masu ruwa da lemo da abinci,Hafsah dake zaune kan kujera hannuta riƙe da kofin lemo ta ce ''to Maman Sudais ga Aina'u baban Sudais ya ce na yi mata rakiya zuwa nan yayar Talatu ce wacce ta ke taya ni aiyukan gida'' fuska dauke da murmushi Amirah ta ce ''masha Allah sannu da zuwa Aina'u da fatan kuna lafiya'' wacce aka kira da Aina'u ta amsa fuska sake ta ce ''lafiya ƙlau alhamdulillah''Hafsah bata dauki lokaci ba ta yiwa Amirah sallama,bayan tafiyarta ne Amirah ta mayar da dubanta ga Aina'u ta ce ''Malama Aina'u kin zo lafiya? ya hanya?" fuskar Aina'u dauke da fara'a ta amsa har cikin zuciyarta ta ji dadi yadda Amirah ke mata magana lokaci guda ta ji hankalinta ya kwanta da Amirah,cike da nitsuwa Amirah ta ce ''Hafsah ta faɗa maki abinda ya kawo ki nan?" cike da girmamawa Aina'u ta masa ta ce ''eh ta faɗa min'' Amirah ta ce ''masha Allah ina da ɗakuna huɗu a bangarena in kin shiga ta waccan ƙofar zai sada ki da bangarena'' Amirah ta yi magana tana nuna site ɗinta ta daura da ''ɗakuna biyu za ki riƙa gyarawa kullum shine ɗakin yara ɗaya yaran maza ne a ciki ɗaya ɗakin kuma yaran mata za ki gyara masu ɗaki za kuma ki riƙa wanke bayinsu kullum,sai gyaran parlour da kitchen,kitchen biyu ne a gidan gaba ɗaya akwai kuma wanda yake bangare na,duka biyu za ki riƙa gyara su kullum sai kuma shara mopping da wanke wanke ,ɗakina da na mijina ba hurumin ki bane da kaina zan riƙa gyara su, sai girki shima zan rinƙa yi amma za ki riƙa ɗan taimaka min wasu lokuta,ina da injin wanki da shi nake wanke suturana da na yarana zan koya maki yadda ake amfani da shi za ki riƙa wanke kayan makaranta da na zaman gidan na yaran,da kaina nake wanke sutura na''shiru Amirah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''Allah yasa kin gane'' da sauri Aina'u da ta yi nisa cikin tunani ta ce ''na gane'' mamakin halaiyar Amirah take tunda ta fara sana'ar aikatau bata taɓa haduwa da irin Amirah ba,da yawa yawan mata da miji ke dauko masu ƴar aiki sake jiki suke su bar ma ƴar aiki ragamar gida baka ɗaya wasu har girki basa iya yiwa mazajen su sai dai ƴar aiki,muryar Amirah ne ya dawo da ita da dogon tunani da ta faɗa inda Amirah ta ce ''bismillah tashi mu shiga na nuna maki ɗakunan yara'' babu musu ta tashi ta bi bayan Amirah,bayan Amirah ta gama nuna Aina'u gidan ne ta dawo parlour Aina'u na biye da ita kasancewar Lahadi ne babu makaranta yasa tun sha ɗaya Amirah ta gama aiyukan gidan sai abubuwan da ba'a rasa ba bayan sallar la'asar Aina'u ta share ko ina ta yi mopping kamar yadda Amirah ta faɗa mata ta gyara kitchen bayan sallar magrib ta yiwa Amirah sallama
Ɗalha bai shigo gidan ba saida ya yi sallar isha'i kafin ya shiga nan parlour ya ga basket ɗin abinci abinci da alama Ammi ce ta aiko masu da shi,dakin Unaisa ya nufa ya tura kofar bakinsa dauke da sallama,bayan shigar sa ɗakin yaga Unaisa zaune bakin gado tana danna waya tana murmushi,amsa masa sallamar ta yi ba tare da ta kalle inda ya ke ba idon kan wayar ta ce ''sannu da dawowa'' Ɗalha ya amsa yana bin rigar jikinta kallo ''ya ce yauwa sannu'' ya dauki a ƙalla mintina shidda zaune wajen Unaisa bata ajiye wayar hannuta ba sai faman chating take tana murmushi ganin bata da niyyar ajiye wayar ne yasa Ɗalha faɗin ''kin ci abinci?" idonta kan waya ta ce ''a'a sai zuwa anjima'' Ɗalha bai ji dadin yadda Unaisa ke amsa masa magana ba, ya shiga gida amma baza ta ajiye waya ta yi masa sannu da zuwa yadda ya kamata ba,bai ji dadi ba sam amma sai ya danna zuciyarsa ya ce ''ya kamata ki ajiye wayar haka muje mu ci abinci,da wuri nake son kwanta yau'' a takaice Unaisa ta ce ''ok'' ta faɗa tare da tashi tsaye bayan ta ajiye wayar ta nufi hanyar bathroom da ido Ɗallah ya bita ganin yadda rigan ke binta kamar wacce tasa alƙiɓɓa ga hunnu rigar ta yi mata yawa sosai,ƙare mata kallo ya yi tsaf tana daf da shiga bathroom ya ce ''haka ki ka zaune babu bra'' a takaice ta bashi amsa ta ce ''a tsaye suke aiy inma tsayuwar su bai maka ba to rankwafawa suka yi ba kwanciya ba''tana gama faɗin haka ta yi wucewar ta bathroom ta dauro alwala bayan fitarta daga bathroom ne taga Ɗalha zaune nan inda ta barshi kallo ɗaya ta yi masa ta kawar da kai ganin yadda ya ƙorawa kirginta ido,darduma dake daure kan bed site drower ta dauko ta shimfiɗa ta zura hijab tana shirin tayar da iƙama Ɗalha ya jefo mata tambaya inda ya ce ''me kuma za ki yi?" a takaice ta bashi amsa ta ce ''sallah'' cike da mamaki Ɗalha ya maimaita kalmar sallah da ta faɗa ya ce ''sallah? sallar me karfe tara saura fa yanzu'' Unaisa ta taɓe baki kafin ta ce ''sallar magriba da isha mana'' Ɗalha da ya gama cika da mamaki ya ce ''magriba da isha? me ki ke tun ɗazu ba ki yi sallah ba?" cikin nuna halin ko in kula Unaisa ta ce ''wallahi chating nake ban san lokaci ya tafi ba,amma ba gashi yanzu zan yi ba bafa wani abu bane yanzu zan idar'' wata doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke yayin da Unaisa ta tayar da iƙama ta fara sallah tunda ta fara sallah Ɗalha ke binta da ido ya fahimci bayan ƙazanta Unaisa bata da isasshen ilimin addini,yana nan zaune har ta idar tare suka je parlour suka ci abinci bayan Unaisa ta yi sarving ɗinsu,farar shinkafa ce da miya tumatir da aka sa namar kaza har rabi bayan an yi yanyanketa,bayan sun gama cin abinci ne Unaisa ta tashi ta nufi hanyar ɗakinta tana tafe rigar ta na biye da ita da ido Ɗalha ya bita har ta ɓacewa ganinsa,da kansa ya kwashe plate ɗinda suka ci abinci ya wuce da su kitchen ya wanke kafin ya kwashe wormer's ɗin Ammi ya shigar dasu kitchen,tea ya haɗawa kansa ya zauna nan cikin parlour ya fara sha wayarsa riƙe a hannusa,karfe goma daidai ya tashi hannusa riƙe da mug cup ɗinda ya sha tea ya wuce kitchen ya wanke kofin daga nan ya wuce ɗakinsa inda ya shiga bathroom ya yi wanka kafin ya shirya kansa cikin wata baƙar riga da wando nigth wear bayan ya kwanta ne ya dauki wayarsa ya kira layin Amirah,Amirah da take kwance cikin ɗakin ta ji wayarta ta fara ƙara alamar shigar kira tun ɗazu take jiran kiransa amma taga bai kira ba har ta cire rai a tunaninta ya manta da su ne yau amsa kiran tayi ta gaishi shi cike da girmamawa ya amsa mata ya tambaye ta lafiyar yara ta ce masa duk suna lafiya daga haka ya tambaye ta ko Hafsah ta kawo ƴar aikin Amirah ta ce ''eh sun zo'' daga haka sun buge da hirar soyayya sosai Amirah ke mamakin Ɗalha ace saida ya yi mata kishiya ya fara nuna mata soyayya da rabon ya nuna mata irin wannan soyayyar tun sanda take amarya sun dauki aƙalla mintina ashirin suna hira kafin ya yi mata sallama,duk wani haushi da tsanar da Amirah ke yiwa Ɗalha daga ranar da saki ta,ta ji tsanar ya fara raguwa saboda yadda yake nuna mata kulawa da soyayya a yanzu alhali ya yi mata kishiya
SHUUKRAN