Chapter 9&10
by @deeyamerh10
💖💖 SOYAYYAR ZUCI💖💖
(Love and Romantic story)
Written
By
Deeyamerh
07070647236
Page 9&10
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Duk abinda ya kama tayi a cikin gidan dai da tayi, Sannan ta zauna zaman jiran jiran Fatima,a cikin ranta take cewa yau ko Haseena na gidan ko kuwa an bi maciyin pussy part Din da,ita dai bata taba ganin wanna masifa ace agola yafi yar masu gida iko? ko da yake Abba ne mai fada aji to shima Mommy ta mai dashi kamar wani Robot abinda tace shi yake yi ba binkice,karar da wayar tayi ne yasa ta dawowa daga dogon tunanin da ta tafi.
'Hello" Tom gani nan.hijab din ta tasa ta fice abinta,cikin ikon Allah har taje bakin Get bata hadi da kowa ba,dan haka tai saurin ficewa dan taji alamun part din maza wani na shirin fita,
yau sai da tayi yar tafiya sannan ta same me Napep din a bakin get din layin,sallama tayi Sannan ta shiga ciki.
'Madam Barka da safiya" me Napep yace yana kallonta da madubin machine din.
brk kadai ya aiki ya kuma dawai niya da mu?.
"Alhmdulllah wannan aikina ne Madam"
ba sake bi ta kan zancan sa ba,mai da dubanta ga Fatima tayi, kintshi lfy ya su Umma?".
alhmullah jiya bayan munrabu tasani a gaba da metar yanzu bakison zuwa gidan? wai tun ranar da kika kwana, bata sake ganin kafafuwanki ba,
"Allah sarki My Umma zanzo da bari nayi sai mungama exam sai nazo hutu,tunda Kinga saura 1 week mu fara exam.
"ni kuwa suhaima ya presentations kuwa?Allah yasa kinyo masa dan daga ganin sa wllh ba mutunci".to ke me yakai ki fadar wani Woow sai kace kin finki kyau yayi"?
dariya suhaima tayi sanan ta ce"ke dallah turanci ne ya burge Ni, amma kuma kin san babu wani da namiji da yake rudata,dan haka kima kwantar da hankalinki Suhaima ba tunanin maza a cikin zuciyarsa".
kallonta kwai fatima Take ko dan batasan ya soyayya take ba dan tun da suke da ita bata taba ji suhaima tace ga saurayin ta shiyasa ko da taga kwanakin baya wani tsayar da ita wllh ta zata saurayi tayi.
da wanna tunani suka shiga cikin makaranta, inda New theater take cike da Students ana jiran sir Rayyan,wanda basa zuwa sai gasu domin labari yaje musu,
kamar yadda suka saba zaman gaba haka ma yau to kasance sai dai yau a me makon su biyu wanna karan su uku ne,suhaima Fatima saudat.
kamar kullum basu wuce 10mins da shiga cikin theater sai ga sir Rayyan kafin ya iso kamshinsa ya rigashi zuwa,yau fa shigar ta daban ce domin manyan yasa irin dinkin tazarce wanda samarin yanzu sukeyinsa,sai hullar colour din yard din,hannunsa daure da agogon Rolex,flat shoe ne a kafarsa.
direct gun blackboard yaje ya tsaya,maker ya dauka ya rubuta suna topic din zasuyi kafin daga bisani yace"where is Mrs gadanya"?.
cikin nutsuwar ta tace "sir gani".
Mrs. Gadanya, please come up on stage and give us your presentation. If you do well, you will all get your CA marks. But if you fail, then you will all fail.”
a hankali ta mike ta fara takawa zuwa inda yake,duk wani takun da ke zuciyarta na bugawa ne domin abin kamar sabo ne a gare ta,wllh da zai lura jikinta rawa yake domin haka kawai taji shakkarsa da gwarjininsa ya kamata.
dai-daita nutsuwarta tayi sannan ta sunkuyar da kanta,cikin muryar ta me sanyi ga wanda bai santa sai yace suhaima bata magana
a hankli ta fara da"My Name is suhaima Lamido Gafanya, and I'm her to present the MBBS (Bachelor of Medicine, Bachelor of Surgery
MBBS means Bachelor of Medicine and Bachelor of Surgery. It is a professional medical degree that prepares students to become qualified medical doctors.”
Human Anatomy and Its Importance in Medicine
Human Anatomy is the study of the structure of the human body. It involves learning about the different parts of the body, such as the bones, muscles, heart, brain, lungs, blood vessels, and other organs, and understanding where they are located and how they are connected.
yadda take bayani shi ya shagaltar da duk wani students domin kuwa bayani take daki bayan daki,shi akansa sir Rayyan yayi mamaki sosai da bayanin nata,
ahankali yace mata"stop Mrs gadanya". Students ya kalla yace"any questions".duk shiru sukai domin sun ji dadin bayani ta,
ganin kowa yayi shiru yasa yace to shi yana da question din,doka mata tambayar yayi ya zuba mata ido yaji irin amsar da zata bayar.
sai da runtsa ido dan wllh gaba daya muryarsa tana so tafi ƙarfin jarumtarta,Ba ta jin ta iya jure tsayuwa magana da shi ta 1hours batare da abinda yake boyewa ya fito fili ba.
kai ta sunkuyar da shi kasa sannan tabashi Amsa dai dai da abinda ya tambaya,ai kafin yayi magana kawai Captain ya hau tafi ji kike raf raf domin indai ana bada mark to wllh sun haye.
tsayawa sukai da tafin,domin shi kansa sir Rayyan ta burge amma duk da haka sai da ya tambaye su again"Are you all satisfied with her presentation, or does she need to make any corrections?
daya ga cikin yan class din ne yace"sir bamu da ja akan abinda ta fada,dan jimmm sir Rayyan yayi kafin yace"okay
I’m satisfied with the presentation she gave and with the explanation. Therefore, everyone will receive CA marks for this presentation.
I’m grateful to have such hardworking and brilliant students. May Allah bring us together again in our next lecture. Thank you, everyone.marke dinsa ya dauka ya kara gaba.
ai tunda yace sun haye ta kasa daga kafarta daga gun har sai da su saudat da Fatima sukazo suna rungume ta sannan tadawo cikin hankalinta
thank You suhaima Allah ya kara basira gaskiya munji dadi sosai.haka masu hankalin cikin su,sukai tai mata godiya banda yan groups din su Zee-zee domin har kuka sai da tayi dan kawai ya ce mata Mrs Gadanya o Ni Deeyamerh wannan bala'e har ina wa
haka ranar tai mata dadi sosai ashe wannan abu ya tsayawa zee-zee rai,ba irin alwashin da bata dauka akan suhaima ,domin ita a ganinta Sir Rayyan son suhaima yake.
A bangaran suhaima kuwa batasan wainar da ake toyawa,domin ita har kar gabanta take,a yanzu bata da buri face abu guda uku,na farko shin ta ina zata fara nemo Ammey,na biyu waye SECRET LOVER wanda a yanzu yake so ya debe meta kewa duk da har yanzu bata taɓa yi masa reply Amma yana debe mata kewar abubuwa da yawa,na uku shine tagama karatun Medicine,
_________________
Semester tayi nisa komai yayi zafi har Yanzu Suhaima bata Sami sakewa ba, idan ka ganta tana dariya to ita da Fatima saudat ne,duk da karatun Yana musu mugun wahala, ahankali suake bin su Captain yana nuna musu abinda bada ganewa domin ya lura basu da girman ka.
Saura kwana hudu su Fara jarabawa misalin karfe hudu na marece tana zaune wani class tana faman karatu Sir Rayyan yazo wucewa kunnensa like da Bluetooth har ya gitta sai yaga kamar ita, yayi jimmm Yana tunanin ita ce ko ba ita bace da baya yawo ya leka ta window class,kyakkyawan gani yayi domin ita ce kuwa,zai iya cewa ko ya shigo class din baya ganinta Amma idan ya bada Assignment yana ganin sunata,karamin bakinta yake kallo yadda yake miss miss da baki alamun karatu take,shi abin dariya ma yake bashi wllh.
sai a lokacin yake kare mata kallo kyakkyawa ce ajin farko,ga hasken ta dai dai wa dai da,a kallon farko zaka gane macce mai gashi ce domin gaban goshinta duk gashi ya kwanta.yadda take magana haka dimple din yake motsawa,duk da acikin hijab kullum yake ganinta Amma yasan macce mai dari,irin darin da sai sunyi tumbur zaka gane😋dan murmushi yayi wanda shi kadai ya barwa kansa dalilin yinsa.
wucewar ke da wuya sai ga gan din su zee-zee domin har labari yaje mata cewar ga sir Rayyan da suhaima can suna zance, wannan dalilin yasa ta tahu a fusace,bata tsaya lura da waye a tsaye gun kawai sai saukar mari suhaima ta ji,Tass"ke kin isa kiso abinda naso wllh baki iyasa Rayyan nawane Ni kadai,wllh wllh idan biki fita a harkar mijina ba.....ai bata karasa ba suhaima ta dauke ta da mari hagu da dama...nuna ta take da dan yatsa Sannan tace"idan kina haukarki kada ki sake ki tabo jikar gadanya dan Wllh tundaga kan kakan ko kanki zan iya sawa a batar da su,ke Rayyan yake ko Ridwan ke yake gabanki Amma suhaima baya gabanta,dan Haka kifita a harka ta bani da dadi.....karki ga ina miki shiru ba tsoranki nake ji ba kingane banza jaka...
Ai duk wani wanda yake kusa da class din nan sai da ya leko dan abun mamaki ne wai fadawa kan Lecturer,may be bema son sunayi ba...
Ai zee-zee bata bari suhaima tasake cewa komai ba kawai ta danko wuyanta. Ai kafin kace me Dambe ya kaure tsananinsu Daman suhaima najin haushinta ai kuwa ta zaune akan ruwan cikinta sai naushinta a fuskanta take,ga fuskar taci beaching....take kuwa wani gurin ya fara kwailewa,ai kafin aje a kira fatima, suhaima tayiwa fuskar zee-zee jaga-jaga da duka...idan banda ihu da neman dauki ba abinda zee-zee keyi,ai koda na juye ba kawayen zee-zee duk sun gudu....
HOD akaje aka kira Yazo yagansu ai kuwa yace su biyoshi officer,ita kuma Zee-zee akai ta clinic domin aduba ko hakuranta sun fita domin jini ne kawai yake fita.....