Page 51
💫MARYAMA💫
51
Cike da mamaki da al'ajabi yake bin tsadadden suit nashi da tayiwa wanka da coffee da kallo,kana ya kai dubanshi kan takardunshi masu muhimmanci da suka yi ɗai ɗai a ƙasa, akan dogayen yatsunta farare sol ya sauƙe idanunshi da sauri sauri take haɗa takardun kana ta miƙe ba tare da ta kalleshi ba duk yadda yaso hakan kuwa,hannunshi ta kama ta damƙa mishi papers din gami da faɗin "Sorry it was not intentionally".
Daga haka bata jira jin abin da zai ce ba ta cigaba da gudunta bilhaƙƙi. With much interest ALQASEEM ya juya ya bita da kallo, wani irin ƙwalalo idanu ya yi waje ganin abin da wannan kyakkyawar yarinyar ta ke aikatawa, ruf ta rufe dustbin ɗin da ta shige bisa mamakinsa, bai fita daga shock ɗin da ta sanyashi na shigewa mazubin shara ba yaga wasu kattin maza masu ƙirar kisa sun yanko kwana a sukwane suna ta mazurai kamar saci babu, "hey young guy! Baka ga wata yarinya ba haka fara mai kyau da baƙar riga a jikinta?"
John ya tambayi Alqaseem dake tsaye ƙiƙam har lokacin..
Juya mishi kai yayi ba tare da ya ce komai ba, gajiya suka yi da dube dubensu suka bar wajen. Cike da takun kasaita ya nufi wajen dustbin É—in, dan duk yadda yaso sharewa kasawa yayi al'amarin yarinyar akwai ruÉ—arwa a ciki.
Hankerchief nashi fari sol ya É—auko cike da kyankayami ya daura saman marfin yana kwabe fuska kamar yaga kashi ya buÉ—e robar, da sauri na rufe idanu na tsam ina kara takure jikina waje É—aya yayinda rawar da jikin ke yi ya tsananta har ina jin yadda yake jijjiga abin da nake ciki.
Ya Ilahil Alamina, shikenan ƙarshena ya zo, shikenan sun gano ni, tabbas kasheni zasu yi ba tare da na nemi yafiyar iyayena da hamma jabeer ba, wasu hawaye masu ɗan karen zafi ne suka biyo saman kuncina yayinda na sadaƙar ina jiran jin irin damƙar da zasu min.
Cike da maÉ—aukakin mamaki yake bin kyakkyawar baby face nata da kallo gashin da ke kwance saman goshinta da ya kusa haÉ—ewa da girarta cikakku shi yafi komai É—aukar hankalinsa, "what's her story, she look so young da har waÉ—ancan mutane zasu bita, and da gani duk da kasancewarta farar fata sosai zaka fahimci daga african countrys ta fito kamar Nigeria ko niger. Menene labarinta?" ya tambayi kanshi dan haka kawai ya samu kanshi da son jin wani abu dangane da ita.
Cigaba da matse idanuna nayi ina jiran jin yadda za su wantsalar dani daga dustbin É—in,amma har tsawon shuÉ—ewar minti biyar babu alamar motsin su sai dai tabbas ina jin alamar idanu a kaina da kuma saukar numfashin dake tabbatar min akwai É—an adam a wajen.
A hankali na fara buÉ—e idanuna kaÉ—an ta wutsiyar idon na hangonshi yana tsaye ya harÉ—e hannuwa a kirji duk da tashin hankalin da na ke ciki, hakan bai hanani hango yanayinshi ba.
Cikakken namiji ne mai matsaikacin tsawo kalar fatarshi irinta majorityn mazan arewacin Nigeria ce wato shi ba baƙiƙƙirin ba ba kuma fari sol ba,."Manzon Allah S A W, ya sanar damu cewa 'annazafatu minal iman.' lallai tsafta tana daga cikin imani, So what are you doing inside this dirty thing?"
Kakkauran muryarshi ta ratsa dodon kunnena. Da sauri na ɗago kaina muka haɗa idanu, dage gira yayi haɗi da jinjina kai yana tabbatar min da tambayarshi. bani da amsar da zan bashi dan haka na cigaba da kallonshi kamar wawuya ko kuma wacce taga sabon hallita..."zaki fito ne, ko zaki cigaba da kallona sai kin ruɓe a ciki?" ya kuma watso min wata tambayar ganin ban bashi amsar farko ba.
Ƙoƙarin miƙewa na fara yi amma na kasa, sai abin ya bani mamaki lokacin da na shiga ban samu tangarɗa ba, amma fita yana neman gagarata lallai babu abun da tashin hankali ba ya sanyawa. Ganin ta kasa miƙewa ne yasa Alqaseem sanya hannunshi biyu cike da ƙyanƙyamin wajen ya ɗago shoulder dina na miƙe sannan na zuro dogayen ƙafafuna na sauƙo. Kafar tawa ya bi da kallo yana ɓata fuska ya nuna ƙafar gami da faɗin, "Ina shoes naki?" ƙafar nima na bi da kallo sannan na mayar da kallona cikin dustbin ɗin, babu su babu dalilinsu kallon da yake bina dashi ne ya sani buɗa hannuna duka biyu, a karon farko cikin wata iriyar murya mai bayyana halin da nake ciki na ce, "Ban sani ba,kilan ina gudu ne suka fadi".
"Mai ya saka ki gudun?" Ya watso min tambayar fuskarshi babu alamun wasa. Rawa muryata ta fara yi nace, "wllh ba da gangan na aikata mishi ba, wllh Allah kenan tsautsayi ne, ni ban taba aikata haka ba". Shaaaa hawaye suka biyo kuncina, bude baki yayi zaiyi magana muka jiyo an fara announcing tashin jirgi, "poor girl, zata sa na yi missing flight a banza" ya fada yana juyawa da sauri zai bar wajen dan akwai meeting mai muhimmancin da zai shiga da zarar ya iso naija, ko mai ya tuna kuma sai ya juyo ya ce, " ina kika nufa yanzu?".
Ina cigaba da share hawaye na na ce, "Gida zan je" "see you, dama na ce jeji zaki ne? i mean mai ya kawoki airport?".
"Zan tafi gida, amm zan tafi nigeria" na yi saurin gyara zance na ganin irin kallon da ya watso min.
"Ohk" kawai yace kana ya cigaba da tafiya, har yayi nisa ina tsaye ban motsa ba sai bugun tara tara da kirjina ke yi,ina tunanin haduwata da su john dan na tabbata basu fita daga airport dinnan ba,.
Jin ana kara tabbatar da tashin jirgi nan da wasu yan mintuna ne yasa ni bin bayanshi da sassarfa kafata babu takalama ban damu da kallon da jama'a ke min ba lokacin da na shigo cikinsu...Tabbas da hawaye suna karewa babu shakka da ni Maryama hawayena sun kare domin yadda suke zuba a ko wacce dakika ta bugawar agogo, saidai abin mamaki basa tsayawa. ko yanzu ma da nake zaune cikin Emirate flight dake kokarin tashi daga dubai ya yada zango a nigeria, wasu hawayen na share ina gyara daidaituwar zaman seatbelt dina.
Alqaseem na zaune a gefenta ta hagu, mutane uku ne kawai a tsakaninsu. duk wani motsinta akan idanunshi suke yana ankare da ita duk bayan minti kadan tana sanya gefen gyalen dake kanta ta share hawaye dashi. Tunda yake shi a rayuwarshi is hardly ya sa damuwar wani a ranshi musamman idan bai sanka ba, mutum ne shi mai kiyayewa da kuma tsantsani akan harkar mutane. amma wannan yarinyar is differ da sauran mutane da ya saba haduwa dasu.
Bai san mai ya sa ba ya damu a ranshi da yanayin da take ciki,
"me ke damunta?"
Yai wa kanshi tambayar sai dai babu mai bashi amsa dan haka ya cigaba da kallonta kawai da har zuwa lokacin bata daina share hawaye a kai a kai ba, ko da servant na cikin jirgin ta kawo mata abin motsa baki ma girgiza mata kai kawai tayi ba tare da ta amsa ba data iso kan Alqaseem ne ya tabbatar mata ta koma ta bata abu mai dan ruwa ruwa.
Batayi musu ba ta koma kan Maryama ta bata kamar yadda ya ce din, juyowa ta yi da idanunta wadanda suka koshi da kuka suka hada idanu babu musu ta amshi juice da cake din ta fara sipping kadan kadan.
Tafiyar direct ce babu tsayawa, tun Maryama na fahimtar wasu abubuwa har bacci ya fara rinjayarta wanda shine dalilin samun tsagaitar hawayenta.
Bayan awanni takwas cifff suna zurara gudu a sararin samaniya jirginnasu ya sauka a filin tashi da saukar jirage na kasa da kasa Nnamdi Azikwe dake babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.
A hankali fasinjojin ke saukowa kana kowa yana kama gabanshi, masu bin wani jirgi zuwa other states kuwa suna nufar wajen hutawa, cikin yanayi na tagaiyara na kai duba na gabas da yamma kudu da arewa bayan na fito daga jirgin babu inda na sani babu kuma wanda na sani, hawayen dai da suka riga suka zama aminaina sune suka kara gangarowa a karo na barkatai.
Yana tsaye a can gefe ya harde hannu a kirji yana kallonta pietifully, al'amarin yarinyar ya daina bashi mamaki yanzu sai tausayi, mai ya kaita Dubai? me ya hadata da wadancan mutanen marar sa kyan gani da kananan shekarunta? Me ta aikata musu suke binta?.
Wadannan sune tambayoyin dake cike fal a kwanyarsa, kuma a wajenta ne kawai yake da tabbacin samun amsarsu...,cike da kasaita ya nufo inda take tsaye tana ta rarraba jajayen idanunta cikin airport din dan a ko wani lokaci driver dinshi yana iya zuwa,
"Ina ne gidan naku yake?".
Kakkaurar muryarshi da zuwa yanzu na gama haddarta ta ziyarce ni. Da sauri na juyo ina kallonshi sai kawai na fashe da kuka mai tsanani har mutanen dake wucewa sun fara tsayawa.
A mugun fusace ya ce, "zaki bani amsa ne ko kuka zakiyi ki tara min mutane, idan bazakiyi magana ba sai in kama gabana dama ganin kamar you need help ne ya sani shiga sabgarki. Ina ne gidan naku?". ya fada babu wasa, "Nima ban sani ba, ina ne nan?" na bashi amsa hadi da kuma tambayarshi.
Baki a bude ya ke kallona kafin ya maimaita tambayar da nai mishi, " ina ne nan?".anya Alqaseem ko dai aljanah ka ke kulawa ne ko kuma mahaukaciya?
Zuciyarshi ta tambayeshi, da yadda ya so ne juyawa zaiyi yayi tafiyarshi, amma sai ya kasa hakan yana kallona da kyau yace, "Nan Abuja ne, ina wayarki da kayanki?"
Hannu na buda mishi gami da fadin babu kaya, wayar kuma kilan na yar da ita a can". Can ina?" ya tambayeni da kulewa a voice nashi, "Dubai" na bashi amsa a takaice.
To kin kyauta, shima ya fada a takaice ya juya zai bar wajen, da sauri na sha gabanshi na durkusa bisa guiwa ta na ce , "domin Allah ba dan ni ba ka taimaka ka kaini wajen Innarmu wllh Allah ban san ina ne nan ba, ban taba zuwa nan ba kuma bani da kudin da zai kaini gida".
"Waya biya maki kudin da kika zo daga dubai din". "Ni na biya, da credit card na biya kuma shima ya fadi tare da wayata" na katse shi ta hanyar bashi amsa gaba daya.
Wasu security ne suka iso wajenmu da tambayar me ke faruwa, Alqaseem ya ce, "you don't worry sir, family issue ne" isowar drivern shi ne yasa taron wajen watsewa ya sani a gaba har wajen wata dalleliyar mota kirar range rover baka wuluk sai maiko take yi, back seat drivern ya bude mishi ya shiga yana sanar dashi ya bude min gaban motar, da sauri na fada dan sai nake ganin tamkar zai tafi ne ya barni, ina mishi ganin dan uwana a yanzu bani da kowa bani da komai daga Allah sai wannan bawan nashi da ba dan shi ba bansan inda nake ba yanzu.
Hawayen dai still na share da gefen mayafina da har ya fara zama kanzo kanzo dan digar da ruwan hawayen ke yi bisa, bai ce mata ko uffan ba sai ma tab na shi da ya bude yana wasu aiyukka a ciki, tafiyar minti talatin muka yi daga filin jirgin zuwa wani tabkeken anguwa da bazan iya kwatanta haduwarshi ba dan halin da nake ciki, bakin wani wawakeken get driver din ya yi horn mai gadi da kamar jira yake ya wangale kofar muka shiga cikin gidan mai dauke da wani babban duplex building mai kyawun gaske a parking space yai parking kusa da wasu motoci guda biyu suma masu matukar kyau.
Duk da yanayin galabaitar da nake ciki, hakan bai hanani yaba tsaruwar wannan gida ba....fitowa muka yi daga motar a daidai lokacinne kuma aka zuge kogar glass na shiga ainahin palon gidan, wata kyakkyawar mata ce akalla bazata haura talatin ba ta fito, sanye cikin atamfa army green mai ratsin fari yellow da kuma orange, wuyarta da kunnenta sunsha wata dankareriyar sarkar gwal hakama hannunta da yatsunta duk gwal ne sanye sai walwali suke yi ga wani kamshi na musamman dake tashi a jikinta fuskarta dauke da murmushi mai kayatarwa,bakace kadan a kallo daya zaka fahimci cewa ta fito ne daga kabilar kanuri, turuss taja ta tsaya a tsakar gidan fara'ar dake saman fuskarta yana daukewa yayin da take kare min kallo daga sama har kasa, a tare zuciyar mu ya bada sautin dammmm nida ita.
Daga inda take tana nuna ni da yatsa tace, "Honey! wace wannan kuma mai kama da sadaka yallar ta shigo min gidana har tana da guts na jera kafada da kai?".
Dama yasan za'a rina amma sai ya dake gami da cewa, "Sameera is this how to welcomed your husband da kika yi two weeks baki ganshi ba, uhmyimm?".
"No honey! just to comfirm ko sadaka ta zo nema ne, amma kasan nayi kewarka ai, and gaba daya wannan adon is for you ta fada tana fari da idanu da tahowa gareshi zata rungumeshi, da sauri na matsa can gefe ina jin daci a cikin makwogorona wai yau nice ake kwatantawa da mai neman sadaka.?
"Not here Sameera! baki ga driver da mai gadi suna kallonmu ba?" yafada yana rike hannunta maimakon rungumarshi da tayi niyyan yi. Tafiya suka fara yi tana makale da shi gam da alama ma sun manta dani, rumtse idanu nayi da karfi ina tuna wani yanayi can baya.
"Muje mana malama kin tsaya" cewar driver dake jaye da trolley din mai gidan, "haaaan kuje ina musa? honey baka bata sadakar bane?" cewar wacce aka kira da Sameera tana kallon fuskar mijinta, "No ta biyo mu ciki zan maki bayani zuwa anjuma".
Badon ranta ya so ba suka shiga cikin palon da Maryama, lumshe idanu Alqaseem da Maryama sukayi a tare sakamakon wani daddadan turaren wuta na asalin yan borno da ya gauraya da sanyi ac ya bugo su,a bangaren tsafta kawai sameera tana da kaso casain cikin dari a zuciyarshi, dan haka ya kara riketa gam har suka shiga tsakar palon,"Honey abinci ko wanka? da wanne zaka fara"hango dining table din dake shake da kuloli yayi yana hadiyar yawu dan yasan ba karamin gara zai kwasa ba, sameera lamba daya ce wajen iya girki,.
"Let me freshen up kafun in ci abincin ki bata masauki", daga haka ya shige wani corridor da zai sadaka da dakunan baccinsu...Juyowa tayi tana kallon Maryama da ta rakube waje daya sannan ta dauki waya ta daddana ta kara a kunnenta, "ina bukatan ganinki a main palo yanzun nan," daga haka ta yanke wayar wata yar dattijuwa ce ta shigo tana kaiwa durkushe gaban sameera "gani nan uwar dakina" ta fada jikinta na dan rawa kadan,
"Ma'u! ki bawa wannan masauki a bangarenku a bata abinci kuma ki tabbatar tayi wanka dan bana son kazanta kin sani". Sabuwar mai aiki aka samu ne hajiya?".
"Wannan ba huruminki bane kawai kiyi abun da na sanya ki ma'u". Allah ya huci ran giwar mata sarauniya a gidan mijinta.
Karon farko wani tsadadden murmushi ya subuce mata.....Koda ta shigo dakin ta samu har ya fito daga wanka yana goge jikinshi da towel a gaban mirror. Rungumarshi tayi ta baya tana zuro kanta daidai wuyanshi ta harde hannayenta duka biyu a kirjinshi tace, "honey kuma baka jirani ba in tayaka wankan", "murmushi yayi ya ce ki tayani wanka ko ki min shiririta irin wadda kika saba" tana dariya ta karbi towel din ta kai bathroom sannan ta fito, ita ta shafa mishi mai gami da kimtsa shi saidai al'amarin yarinyar tsaye yake a ranta, dan haka tana tsaka da fesa mishi turare ta ce, " dan Allah wai wacece ne kazo da ita, hankalina ya kasa kwaciya fa".
"You can never change Sameera, ke dai baki son kiga kowa ya rabeki haka ake rayuwa?" to wannan dai.........Nan ya bata labarin iya abinda ya sani akan Maryama ya kare da cewa amma zuwa da safe zamu ji ta bakin...."
Katseshi ta yi ta hanyar fadin, "wane irin ta bakinta kuma honey? ai in Allah ya kaimu da safe da kaina zan kaita park in sanyata a motar garinsu basai ka wahalar da kan ka ba wajen jin ta bakinta,ince dai ta fada maka sunan garin nasu?..............