HALINSA!

Page 01

by @salmaahmadisah

HALINSA!

© SALMA AHMAD ISAH

*SADAUKARWA*

Wannan littafin sadaukarwa ne zuwa ga Rabi’atu Abubakar (Pinky) A gift filled with love from your lilly, Thanks for your support prayers and love.

~Gaisuwa~

Gaisuwa ta musamman zuwa ga Khadeeja Abubakar Alkali (Khadeeja Candy) a.k.a Oum Namra, Fatima Yakubu, Fatima Ahmad Isah, Amina I. Ibrahim (Nanameera), Jamila Umar (Janafty). Allah ya bar tare.

بسم الله الر حمن الر حيم*

Page | 01

Aure! A 'yan kananan shekarun a take da su duniya, wanda basu wuce goma sha tara (19) ba, idan aka tambayeta menene aure? Za ta ce wata tarraya ce ta mutane guda biyu, bautar Allah shi ne kasudin wannan tarayya, zama ne da an an lokacin da a fara shi, amma sanin ranar da zai kare babu wanda ya sani, ta sani da cewa zaman aure ya gaji kalubale iri-iri. Za ta iya cewa gidan aure tamkar jami'a ce, kowa a fannin da yake karanta, dan haja jarrabawar ko wani fanninta banbanta da ta wani fannin. Ta kuma tabbatar da cewar duk yadda wasu suka kai ga fuskantar kalubale a rayuwar aurensu, wasu suna cikin farin ciki a nasu auren. Sannan akwai wani abu da ta yi imani da shi kan aure, cewar Aure kan sauya mutum!

A ɗan ƙaramin hankalin da take da shi, wannan ce ma'anar da ta bawa aure, shin da gaske haka auren yake? Ko ko kallon biri takewa rogo? Shin ita ma nata auren zai kasance cikin masu sa'a? Koko akasin haka ce za ta faru da ita? Duk da waɗannan tarin tambayoyin da suka cika kanta, irin wanda 'yan mata da yawa kan yi gabbanin aurensu, hankali kwance, sannan cike da zumuɗi Rahama take shirin aurenta.

RAHAMA POV.

"Assalamu alaikum!" ta yu sallama tana saka kai cikin dakin mahaifiyarta, Hajiya A'i da suka kiranta da Anti ta ɗaga kai ta kalleta, sannan idonta ya zarce kan ledojin da ta shigo da su.

"Har kun dawo?"

Anti ta tambaya yayin da take rufe kofar lokarta da take tsaye a jikinta, fuskar Rahama cike da annuri irin na sabuwar amarya da ɗaukin aurenta ba ya ɓoyuwa a fuskarta ta amsa da "Eh Anti, Mun dawo!" ta amsa tana ƙarasa shiga cikin ɗakin, ta zauna a bakin gado tana aje ledojin hannunta.

A tsanake Anti ta ci gaba da ƙare mata kallo, irin kallon da take binta da shi a kwanakin nan, Rahama yarinya ce da ba ta iya ɓoye farin cikinta, ko damuwarta, nan da nan fuskarta ke fallasa halin da take ciki. Kuma ba Anti kaɗai ba, duk wani wanda yake tare da ita ya san da hakan. Kasancewar Rahama 'yarta ta fari bai sabta mata goyon 'yan fari ba, domin a ganinta yanzu an wuce wannan zamanin, ta ja 'yarta a jiki sosai, ta yanda duk wata damuwatata ba ta iya ɓoye mata, hasali ma duk duniya ita take fara faɗawa.

Kuma idan ka gansu sai ka ce Rahaman ƙanwar Antin ce, domin ita ma Antin ba wani tsufa ta yi ba, kuma dama ba shekarun, sannan tana kula da kanta kuma ba ta shan wahala a gidan aurenta, babban abin da yasa jikinta ba ga nuna shekarunta ke nan.

Yaranta huɗu da mahaifin Rahama, Rahama ita ce babba, sai kuma ƙannenta maza guda uku, Mahmud, Ibrahim da kuma Amir. Ba su da dukiya, amma suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, domin ba su naimi komai sun rasa ba, kasancewar mahaifin Rahaman ƙaramin ɗan kasuwa ne.

"Kin ga ɗinkunan fa Anti"

Maganar Rahama ta katse dogon nazarin da Anti ta shiga kan makomar 'yarta a sabuwar rayuwar da za ta fara nan da sati ɗaya kacal. Kayan fitar bikin da Rahama ta karɓo a wurin ɗiki ta kalla, tana faɗin sun yi kyau, sai da ta nuna mata su dika, sannan ta shiga yi mata batun lalle.

"Rahama!"

Anti ta kira sunanta yayin da ta zauna a bakin gadonta, Rahama ta nutsu tana kallon Anti da ta lura tun wata ɗaya da ya wuce ta rasa walwalarta. Tun lokacin da Abbansu ya sanar musu da za a haɗa aurenta da ɗan uwanta Umar, wanda ya kasance cousin ɗinta ne ta ɓangaren mahaifinta. Idan za ta iya tunawa kowa a dangi barka yake da wannan haɗi, domin ko a ganinta Umar ya cika duk wata kamala da ya kamata ace an so aurenta. Shi yasa ake ta son haɗashi da yara a family'n nasu, da Allah yasa ita ce ta yi nasarar samunsa sai kowa yake mata murna da barka, banda Anti da dukkan alamu suka nuna cewar ba ta maraba da auren, tun da jimawa ta lura, kuma ta yi ta kokarin jin abin da ya sa Anti ta shiga wani hali tun bayan da aka saka ranar aurenta da Umar, amma Antin ta ce ba komai, shi yasa ita ma ta ture komai ta ci gaba da hidimar bikinta, domin a ganinta damuwar Antin ba za ta wuce rabuwa da ita ba kamar yanda wasu daga cikin ƙawayenta suka faɗa mata. Har ga Allah ita ma akwai wannan damuwar a ƙasan zuciyarta, amma farin ciki da ɗaukin auren da take shi ne ya danne damuwar. Domin ba ta yi ƙarya idan tace ba ta son Umar, duk da ba wani lokaci mai tsayi suka shafe tare ba, tun da su ba a Haɗejia suka ba, suna Yobe state asalin jahar su mahaifinta ke nan. Duk 'yan uwan mahaifinta a can suka da zama, mahaifin Umar na ɗaya daga cikinsu, ba wani sosai ta san shi ba, amma sukan haɗu lokaci zuwa lokaci a taron family ko aure, suna ko idan ta kai ziyara Yoben. Babban abin da za ta iya faɗa a kansa shi ne yana da kyau, abin da aka fi saninsa da shi ke nan, sai kuma kyauta da sakin fuska ga 'yan uwansa, domin a tsaye yake da ƙafafunsa kan kasuwancinsa, ta sanu cewa nesa va kusa ba haɗuwarta da shu tsintar dami ne a kala, idan ba rabo babu abin da zai sa ta samu Umar, shi yasa take godewa Allah da ya bata shi.

"Magana nake so mu yi!"

Anti ta Faɗi, Rahama ta gyaɗa mata kai alamun tana jinta.

"Kin tabbatar kina son Umar?"

Rahama ta yi shiru, domin tambayar ta zo a bazata, kanta a ƙasa tace.

"Anti su Abba fa sun riga sun gama magana, ni ai bani da ta cewa, ko zan ƙi shi ba a wannan gaɓar da komai ya kusa faruwa zan cs bana sonsa ba!"

Anti ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, duk da dama ta yi zaton amsar da za fa samu, ita ta fara gabe cewa Rahama tana son wannan auren, kafin kowa ya gane.

"Rahama! a wasu lokutan, abubuwan da muke gani ba su ne gaskiyar zahiri ba, ki zauna ki yi tunani, na san kin san cewa waɗannan mutanen da suka tayaku murna da dariya sun fi ki sanin waye Umar, saboda sun fiku kusa da shi, kuma su ɗin sai su ne suka yawo da shi a family cewar bai yi karatu ba, ba shi da addini da dai sauransu!"

Shiru Rahama ta yi, domin ba ta san cewa abin da ya hana Anti son wannan auren ke nan ba, wannan batun kam ta san da shi, kuma tana ji ana gulmar a family'nsu. amma ko sau ɗaya ba ta taɓa kawo hakan a kanta ba.

Har dare ya yi wannan tunanin yana cikin ranta, ta rasa ma wa za ta faɗawa, can wajen ƙarfe goma sha ɗaya lokacin da take shirin kwanciya, sabuwar wayarta da Umar ɗin ne ya siya mata ta fara ƙara alamun ƙira na shigowa, hannunta ta miƙa ta ɗauki wayar, ganin an rubuta "Zawjy" haɗe da heart emoji yasa da sauri ta ɗaga, sannan ta kara wayar a kunne, ba wai dan komai ba, sai dan tun a wayarta ta farko da shi ya faɗa mata cewar shi sau ɗaya yake kiran waya, idan ta katse ba a ɗaga ba zai sake kira ba, kuma ko an kira shi ba zai ɗaga ba, shi yasa ba ta wasa da wannan damar, daga ya ƙira jikinta na ɓati take ɗaga wayarsa.

"Hello!"

aka faɗi daga ɗayan ɓangaren.

"Assalamu alaikum"

ta ce, madadin maida masa abin da ya faɗa, kuma kullum haka suke yi, shi ba ya sallama idan ya kira, ko da ita ce ta fara masa sallamar da "hello" yake amsa mata. Gaida shi ta yi cikin ladabinta abin birgewa ga kowa, ya amsa, muryarsa ba yabo ba fallasa, ba ta yi mamaki ba, dan ko da yaushe a haka suke magana, wasu lokutan har ɗauka take ko dai ba Umar ɗin da ta sani ba ne, domin shi wancan yana da haba-haba, amma shi ko wannan babu wani emotion a tattare da maganarsa, kawai blank!

"Kika ce nawa ne zai isheki ki yi wancan party'n?"

ta ɗan yi shiru, zannan ta lissafa masa.

"Zan tura miki yanzu, sai ku siya, akwai wani abu kuma?"

a zahiri ta girgiza kanta, tana mamakin halinsa, domin tun da suka fara magana da shi, ba su taɓa yin wata hirar soyayya, ko tattauna abin da ya shafi goben aurensu ba, ko ya ji damuwarta ko shi ya faɗa mata tasa, ba ya yi, idan ya kirata to jawabi zai shaida mata, ko kuma ya tambayeta wani abu, yana gamawa zai kashe wayarsa, kuma ba ya sake kira sai wani abin ya taso, da fari ta ɗauka ko yana busy ne, domin ƙawayenta ma haka suka ce mata, amma sai ta fara tunanin duk busy'n da zai shiga ya kamata ace yana ɗan bata lokacinsa ko kaɗan ne, bayan kuɗi tana buƙatar wasu abubuwan da ban da suka shafi shawarawari da kuma tattaunawa kan gobensu, amma ta lura hakan bai dame shi ba, wani lokacin har tunani take ko ba ya son auren ne?.

"Ya Umar!"

ta ƙira da ƙarfin halin da ta ƙudire a zuciyarta cewar yau zai ta tambayeshi abin da yake ranta.

"Na'am"

Ya amsa daga ɗayan ɓangaren, sai sa ga haɗiyi miyau, cikin tsoron amsar da za a bata yayin da ta gama tambayarta sannan tace.

"Ya Umar ko dai ba ka son auren nan!"

shiru ya ɗan wuce na sakkani, kafin ya bata amsa da.

"Wannan wce irin tambaya ce?"

Sautin da ya yi amfani da shi wurin bata amsar sai da yasa ta yi nadamar tambayarsa.

"Ka yi haƙuri kawai na..."

An faɗa miki idan bana son auren akwai sh*gen da ya isa ya mini dole? Ni fa ba a tirsasani! abin da nake so shi nake yi!"

Cike da mamaki ta ƙame, da ma gata da saurin kuka, har hawaye sun fara zubo mata, da ta tuna cewa mahaifinsa fa na da rai, mahaifiyarsa ce ta rasu, wato mahaifinsa bai isa ya sa shi ba ke nan yake nufi ko me?

"Ka yi haƙuri, amma na ga kular da kake bani ta yi ƙaranci, shi yasa na tamabaya!"

wani dogon tsaki ta ji ya ja ta cikin wayar, sannan yace.

"Kuma kawai dan zam aureki sai na sakar miki fuska ki raina ni? Bana ɗaukan raini da kika ganni nan, yanzu sai na fasa auren, kuma ya fasu billahillazi!"

Hawayenta suka ƙara tsananta, ta sharesu tana sake ba shi haƙuri.

"Aikin banza kawai!"

Daga haka ya latse wayarsa, ta haɗa kai da guiwa tana sauƙe ajiyar zuciya haɗe da siraran hawayenta na damuwa. Ta shafe kusan minti goma tana hawayen ba tare da sanin abin yi ba, kafin ya sake ɗaukan wayarta, ta kira ƙawarta Hajeer.

"Hello Rahma!'

ta amsa a sanyaye.

"Lafiya? me ya faru da wannan daren?"

Cikin hawaye ta tsarawa Hajeer komai, sannan ta ƙara da tambayarta abin yi. Mamaki ta yi jin Hajeer ɗin na dariya.

"Yanzu ke dan kun ɗan samu wannan saɓanin ahi ne duk kika bi kika tada hankalinki? To albishirinki, ni da Jaan (Saurayin Hajeer ɗin) muna yin ya fi haka, kuma mu shirya abinmu kamar ba ayi ba!"

"Hajeer ba za ki gane ba, ba fa wannan ne kaɗai abin da ya tsoratani ba, Ya Umar fa bai yi karatu ba, ga saurin fushi da zuciya!"

Rahama ta faɗi cikin fatan Hajeer ɗin ta fahimceta.

"Mtsww! Kuma sai me? Yanzu fa ilimin ba wani amfani gare shi ba in dai ba ka da kuɗi, kuma shi Allah ya kashe ya ba shi, batun fushi kuma da sauransu za ki iya sauya abinki bayan kun yi aure!"

Kuskure na farko! Domin a lokacin ta ji fiye da rabi na damuwarta ya sirare ya bi iska, ƙwaƙwalwarta ta gama yarda da abin da Hajeer ta faɗi, har tana dasa mata fatan eh za ta iya sauya shi bayan aurensu.

"Allah ko Hajeer?" Ta tambaya cikin son tabbatarwa.

"Wallahi kuwa, ai tsaf za ki sauya abinki, kuma ki bar shi ya gama buga hard to get ɗinsa, daga ƙarshe dai ke za ki aure shi, yanzu ke sai ki bari ya suɓuce miki? Ai ko idan kika kuskura kika yi wannan ganganci kina ji kina gani za ki zama abar dariya."

A zahiri ta gyaɗa kai tana ɗora kanta a kan pillow, hankalinta ya kwanta har ta samu damar sauraron huɗubar cewa za ta iya sauya shi daga bakin Hajeer. Daga nan kuma suka shiga hirar ledies party'n da za su yi a jibi. Suna gamawa ta yi addu'a abinta sai bacci.

------

Assalamu alaikum Fam! Bayan dogon lokaci da na ɗauka ban yi rubutu ba yau gani tafe da sabo, mai taken HALINSA, da fatan za ayi hkrn bina sannu a hankali har zuwa ƙarshe, duk da tafiyar ba wata mai tsayi ba ce, na gode da so da ƙauna.

#SalmaAhmadIsah

#Halinsa

#Candy