JARABTA

1

by @takwalam

TITLE;  *JARABTA*

WRITER; *TA_KWALAM*

PAGE; *J_I*



Shi social media algorithm baya tantance gaskiya ko karyar labari, kawai abin da yake iya tantancewa shi ne engagement ! Wato wannan like din, wannan reshare din, wannan dadewar da muke akan post.

Mamakin post din da ta gani akan FYP din TikTok din ta, a # tag din an saka #The cheating saga, kawar ta dake gefen ta wadda ta bada dukkan hankalin ta wajen saurarar lecture da ake yi cikin aji. Zungurar ta da Muniba tayi shi ne dalilin dauke hankalin ta daga kan Mr. Shlangs wanda yayi nisa a bada bayani akan yadda fitsari yake taruwa wato dai mechanism of urination, ta kalla Muniba wadda gaba daya take a firgice tace cikin rada saboda tsoron kada malamin yaji maganar da zata yi

"Menene?"

Wayar ta ta Mika mata tace

"Kalla!"

Abida ta saka hannunta ta karba wayar ta fara kallar abin da Muniban ke son ta gani, cikin sauri Wani gasp yayi escaping Leben ta, kifar da wayar tayi tana kallon Muniba a tsorace tace

"Mene wannan?"

Muniba ta tabe Baki tace

"Asirin wata ne ya tonu!"

Kafin Abida ta sake magana tuni Mr shlangs ya fara musu magana, dole ta aje wayar zuwa lokacin da class din ya kare, kafin Wani lokaci, Muniba ta nunawa mata da yawa dake cikin ajin, wasu su tsaya su kalla har karshe, wasu suna fara kalla su aje wayar su tafi, se Kuma magana wannan tace 

"Maganin su, basu dai iskanci ba to Allah ya Kara!"

Dayar me pink din hijab tace

"Wai da ku baku ga wannan videos din ba se yanzun? ai kusan kwana biyu kenan suna trending"

Abida ta sake baki tana kallon Rahma tace

"Bamu labari"

Ai Rahma se ta samu guri ta zauna ta fara kokarin Basu labari kamar haka

"Ni dai yadda naji ance wai mijin kawar yayar ta ne..."

Se kuma tayi shiru tana murmushi, Muniba da ta kagu taji karshen labarin tace

"Cigaba mana"

Rahma da ke murmushi tace

"Ku dai ku kalla kawai"

Muniba ta harare ta saboda taso taji komai na labarin yadda zata ji dadin zuwa ta bayar, a karo na biyu ta sake tambayar rahma da fadin

"To ta ina videos din sukai leaking?"

Rahma kamar wadda akai a gaban ta tace

"Ance matar ce tayi leaking video bayan ta gani"

Nan suka hadu suna ta Shima matar albarka, suna fadin ai gwara da tayi Hakan, ai wallahi idan su ne ma abin da zasuyi se yafi haka, suna tayi...

Lokaci guda #The cheating saga ya zama daya daga cikin most searched Abu akan TikTok da Instagram, wasu sunyi downloading sun kawo shi WhatsApp, wasu Kuma sun yi reposting, sunyi sharing, wasu sunyi downloading sunyi sabon voice over akai sunyi posting, idan ka shiga comment section kowa da nashi version of story da yake bayarwa.

  1k comments da zaka gani, zaiyi wuya ka samu hamsin da suka yiwa ta video din sahihiyar adduar shirya, mafi yawan su suna aibata ta, tare da Allah ya Kara akan abin da ya faru. Tuni suma bloggers suka fara magana akai, kafin Wani lokaci dai duniyar social media ta arewacin Nigeria ta kacame da Cece kuce akan wannan post da ya dungunzuma mutane.

Duk wannan abin da ake Bata sani ba, saboda ita ba ma'abociyar shiga social media bace ba, Kai ita Bata TikTok ma saboda tana ganin TikTok kawai na Yan iska ne.

Gwara gwara ma IG wato Instagram shi kam tana da account da shi saboda ganin girke girke, to shi dinma se tayi wata, sati uku bata shiga ba, to ta ina zata San abin da yake faruwa?

Misalin hudu na yamma ta kammalla Shirin ta tsaf na zuwa lecture, hijabin ta da yake ninke saman gadon ta ta saka hannun ta warware tare da sakawa sannan ta zura flat shoes din ta ta dauka jaka ta nufi hanyar fita, se ta tuna Bata zare key daga jikin Locker din ta ba, ta dawo ta zare sannan ta saka mask ta rufe fuskar ta kafin ta fita.

Dama dai ansan mata da hayaniya, so hostel dai ba'a raba shi da hayaniyar student, yau dai se taji hayaniyar ta dan banbanta da sauran ranakun, mutane da yawa ma suna tsatsaye a corridor, tun da ta fito se taji anyi shiru ta bangaren da take!

Ta cigaba da tafiyar ta a hankali kamar yadda ta saba a kowannen lokaci, in dai maganar nutsuwa ce to fa ba tada na biyu, kana kallon ta kaga nutsatsiya kuma ma'abociyar hankali da addini. 

Ko kadan bata kawo wannan whispers din ba da ita ake, ta cigaba da tafiya har ta sauka staircase, se taji ana cewa

"Eh ita ce! Wallahi ita ce!"

"Ina zaku ce zata aikata? Wallahi batayi kama da hakan ba'

"Musa a baki amma fir'auna a zuci! Ta bata wayon ta"

Ire iren maganganun da Juwairiyya ta cigaba da ji a yayinda take fita daga hostel, amma tunanin ta gulmar wata ake ba gulmar ta ba.

A ganin ta ba tada wani abu da za'ayi gulma akai. A haka ta karasa lecture hall din su, Nan ma hayaniyar ake, amma tana shiga ajin yayi tsit kamar idan an yasar da allura zaka ji karar faduwar ta!

A lokacin se ta danji a bit of nervousness, ta ayyana me yake faruwa? amma se ta karasa space din da ta samu a row na uku daga tsakiya, gefen wata budirwa ce da saurayin a zaune.

Ba zata iya cewa ga sunan su ba, amma dai tasan course mate din ta ne, sallama tayi sannan ta zauna. Se taji daga bayan su ana cewa

"Ai wallahi ba zata zauna kusa dani ba, tab mazinaciyar!"

Gaban Juwairiyya ya fadi, Amma se ba ta kawo da ita ake ba, har lecturer ya shigo ya fara abin da ya kawo shi, tana gama lecture ta nema hanyar fita se wani Dan class din su ya taso ya sha gabanta, ta kalle shi kamar yadda yake mata Wani kallo.

Se ta dauke Kai tare da kokarin rabe shi ta wuce, kawai se ya Kai hannun shi kan hijab din ta, kafin ta fahimci abin da yake kokarin yi, ya cire mata hijab din dake jikin ta

Lokaci ya tsaya cak! Wani irin sanyi ya shiga jikin ta idanun ta suka bude sosae saboda mamaki, zuciyar ta na bugawa da karfi kamar zata balla kirjin ta ta fito

Rabs ya katse da fadin

"Ai gwara ki dinga yawo tsirara akan kina fakewa da sunan hijab kina Zina"

Da farko dai bayan hijab din ya cire, kanta babu dankwali, gashin ta me yawan gaske da ta daure shi da ribbon in a bun ya bayyana, rigar jikin ta camisole ce wadda take sleeveless saboda zafin da ake yasa bata Wani saka kayan kirki ba, ta zumbula hijab akai, amma dai ta suturta jikin ta. 

Gaba Daya ajin ya rikice da ihu, se tafi ake masa irin ya kyauta dinnan, wasu tsirari a ajin har sun kafe camera suna video, wasu live ma sukai going a TikTok, yayin da Juwairiyya ta tsorata ta da abin da Rabs yayi mata.

To kowa yasan Rabs a school ma baki daya, ga ilimi ga rashin mutunci, shiyasa ita ma Juwairiyya ta San shi, dukda magana bata taba hada shi da ita ba, ta dago idanun ta da suka kada sukai jawur ta kalle shi, tare Kuma da kallon mutanen da suke tsaye.

  Wasu suna dariya, wasu na murmushi, taga mutane da yawa da take gaisawar mutunci da su amma har da su, humiliation, embarrassment duka sukai clouding Juwairiyya, ta kalla Rabs cikin sanyin murya da take rawa 

"Menene haka kake yi? Bani hijabi na"

Ta fada ranta a matukar bace, ya wulla hijab din can gefe sannan yace

"Ke da kika tsaya akai Miki video tsirara zancen yawo a haka cikin school ma ai privilege ne"

Bata fahimta ba, ba Kuma zata fahimci inda maganar shi ta dosa ba hakan yasa tana dagowa ta wanke shi da Mari.

Maimakon ihun da ake na cheering Rabs a ajin se ya koma gasps na mamaki dake escaping bakuna mutanen lecture hall din, ta karasa inda ya wulla hijab din ta tsugunna ta dauka ta mayar jikin ta sannan ta fice da sauri dan komawa hostel.

Sede tun da ta fita zuciyar ta, kwakwalwar ta suka addabe ta da tunanin me ya faru? Me Kuma yake faruwa? Waye zai bata wannan amsar? 

Se da ta tsaya masjid tayi sallar maghrib da Isha kafin ta koma hostel. Wannan zaman ma da take tana ganin yadda ake nuna ta, yadda ake mata Wani irin kallo da bata saba ganin ana mata irin shi ba, se ta dauka ai maganar cire hijab da Rabs yayi ne ya zagaya makaranta har ake zunden ta.

Tayi matukar kokari wurin ganin ba tayi kuka ba, dukda zuciyar ta ciwo take mata akan abin da Rabs yayi amma ta daure ta Kuma fadawa kanta duk abin da za'ayi a bari se ta koma inda take samun nutsuwa wato gadon dakin ta na hostel. Bayan an idar da sallah tana kokarin fitowa sukai karo da Hafiza tana kokarin shigowa masjid din, tana ganin Juwairiyya ta saki ajiyar zuciya tace

"Ina wayar ki?"

Ta tamabayi Juwairiyyan cike da damuwa, Juwairiyya ta karasa fitowa tare da saka flat shoes din ta a kafa kafin tace

"Tana hostel ban fito da ita ba"

Hafiza ta lumshe idanun ta cike da damuwa tace

"Tsakani da Allah handset aka ce ba landline ba fa, duk inda zaki je ya zamana tana hannun ki"

Wannan mitar in dai da sabo Juwairiyya ta saba Jin ta daga bakin Hafiza, se ta Bata hakuri hade da fadin

"Kiyi hakuri! Sauri nake ne shiyasa"

Hafiza ta goge karamar kwallar da ta sakko mata ba tare da ta bar Juwairiyya ta lura ba, 

"Naga abin da ya faru! Yaya ki ke jurewa, nasan duk inda kika wuce nuna ki ake ko?"

Juwairiyya ta rausayar da Kai gwanin tausayin 

"To ya zanyi? Dama nasan videon duk ya baza school"

A ranta tana jin dacin abin da Rabs yayi mata, Hafiza ta share kwalla wannan karon freely ma ta bar kwallar tana zuba, 

"To ke ko a IG Baki gani ba? Se trending yake kusan kwana hudu?"

Juwairiyya se ta tsaya daga tafiyar da take, ta kalla Hafiza dake kuka tana magana 

"Dazun fa akai abun, wanne video kike magana akai?"

Kukan Hafiza se ya tsaya tace da wata raunaniyar murya 

"Baki San abin da yake faruwa ba?"

Juwairiyya ta gyada kai 

"Ban sani ba Hafiza, menene?"

Se jikin Hafiza ya mutu murus 

"Muje hostel tukunna!"

Nanma tunda suka shigo ake leken su, Hafiza tace da Juwairiyya kada ta Kalli kowa a cikin su har suka karasa daki, zuwa lokacin jikin Juwairiyya ta mutu, ta rasa ma tunanin da zatayi? Ta rasa menene yake faruwa har haka. Se da ta kaita daki sannan 

"Ki kwanta kiyi searching #the cheating saga ki gani"

Daga haka Hafiza ta fice saboda tayi avoiding questions ko Kuma taga yadda kawarta zatayi breaking idan ta gani. Allah ya sani tana ma Juwairiyya kyakyawan zato, bata taba kawowa Juwairiyya zatayi haka ba, amma idan ta tuna shedancin namiji se ta yi shiru kawai.

Sannan ta tuna yadda rayuwa zata iya gwada kowa da kowa, babu Wani exception. Juwairiyya har tafsir din qurani ta iya, mutum ce me addini wadda a cikin addinin ta tashi, mahaifan ta sunyi namijin kokari wajen training din ta, kana kallon ta ba se ka tambaya ba, kaga wadda aka Haifa cikin tarbiyyar musulin ci, amma wannan video kadai ya isa humbling Hafiza, ya isa ya zame ma Hafiza darasin duniya, duk iliminka shedan zai iya cin galaba akan ka, wannan haka yake.

A karon farko a rayuwar ta taji tsoron abin da zata gani idan ta kunna data!






Oum Aeesh