03
by @takwalam
TITLE: *JARABTA*
WRITER: *TA_KWALAM*
PAGE: *J_III*
Iyayen Juwairiyya sun manyanta, saboda idan kuka duba Juwairiyya ita ce auta, lokacin da suka haife ta sun bawa shekaru arabain baya, gwara ita Inna ce ma take a shekaru talatin da biyu zuwa da biyar, to yanzun Juwairiyya kanta shekarar ta ashirin da biyu, kunga iyayenta ba Yara bane ba, gidan su gidan gadon malumta ne, kakan ta malami ne, haka Wanda ya haife kakan ta ma.
Dan haka a cikin gidan addini da tarbiya ta tashi. Sede Hakan ba wai guarantee bane ba na tabbacin tsarkake rayuwar mutum, akwai shedan, Wanda idan ya Dan samu a bit of space se yaci galaba akan ka, kamar yadda yayi akan Juwairiyya.
Inna na zaune ta idar da sallar azahar, ta dauka casbaha ta ja abubuwan da take son ja kafin kuma ta mike dan zuwa kitchen, so take kawai ta Sha kunu, tana fitowa sukai karo da Ahmad da yake son shigowa dakin nata , bata Wani kalle shi da kyau ba, dan da ta kalle shi da tabbas zata fahimci akwai damuwa, damuwar ba Daya ba
"Inna ina zaki je?"
"Kunu zan dama"
Ta bashi amsa tana wucewa kitchen din, ya dan fara kokarin tsayar da ita tace
"Ko menene dan Jira ni a daki, zan same ka yanzun"
Ba yadda zaiyi se kawai ya nufi dakin nata ya zauna, kitchen ta shiga ta dauka tukunya, ta zuba ruwa a ciki ta daura saman 3kg camping gas da yaranta suka saya mata saboda irin wannan bukatar, sun Santa da son Shan kunu, to bazai yiwu dan kawai zata Sha kunu se ta hura itace ko coal ba. Zuciyar ta wasai ta daura kunun ta akan wuta, sannan ta dubi dattijuwar dake yi musu aiki tace
"Iya yau bamu gaisa ba, kin shigo nayi baki"
Iya tayi murmushi tare da gaida Inna, sannan suka cigaba da hira take tambayar ta
"Uwar daki na aure ya kusa kuma kenan?"
Inna tana murmushi tace
"Juwairiyya kam an kusa in shaaa Allah, wata biyu ya rage"
Iya tayi adddua sannan Inna ta juye kunun ta cikin wani katon mug sannan ta nufi daki inda Ahmad ke zaune yana jiran ta. Kafin ta shiga dakin se taji sallamaar mutane a tsakar gidan.
Juyawa tayi tana amsawa, mata ne guda uku suka shigo, bata san su ba, amma hakan bai hana ta sakin fuska ba, tace
"Sannun ku da zuwa, Bismillah"
ta fada tana aje mug din kunun a gefe, matan suka karaso tare da fadin
"Mahaifiyar Juwairiyya muke nema'
Daya daga cikin matan ta fada tana bin Inna da kallo, Inna ta saki murmushi tace
"Ni ce Mahaifiyar Juwairiyya! Ku karaso daki mana"
Wadda ke sanye da purple veil tace
"Allah sarki! ai ba zama muka zo yi ba, mun zo ne akan Juwairiyya da Yusuf..."
Bankade labulen da akai aka fito shi ne yasa matar yin shiru, Yaya Uwa ce ta fito, da alama ta jima tana jin maganganun su, babu wanda ta cewa uffan se kallon su da take,
"Da kun shigo munyi maganar a ciki zai fi akan a tsaye"
Inna ta fada bayan ta dauke kallon ta daga kan na Yaya Uwa, wadda ke tsaye har lokacin tana wani irin smirk. hannu tasa ta dauki kunun ta
"Mu fa ba zama ya kawo mu ba kamar yadda muka ce miki, mun zo muce miki, Yusuf ya fasa auren Juwairiyya!"
Idanu a warwaje Inna tace
"Saboda me? akan wanne dalili?"
"Yarinyar da ta gama tambele a titi kuka lullube da hijabi, ita ku ke tunanin dan mu zai aura?"
Da sauri Inna tace
"Haba kukuwa, idan zaku fasa auren se ayi cikin lumana, amma ba se ya kai da irin wannan kazafin ba..."
Suka kwashe da dariya baki daya mockingly, suka ce da alama dai Inna bata san halin yar ta ba, Ahmad ne ya fito tare da fadin
"Dan Allah kar kuyi haka, idan fasa auren zaku yi, its absolutely ok, amma se ku turo maza suyi magana tun da dama su suka zo suka tamabaya."
Se lokacin Yaya Uwa tace
"Kun yi kyan kai kam gaskiya, saboda babu wani dan uwa da zai ga abin da yarinyar tayi ya cigaba da barin dan uwan shi ya neman auren ta"
Da sauri Inna tace
"Me tayi? Me yasa kuke jifanta da kalamai marasa dadi, Ahmad..."
Cikin sauri Ahmad ya ruko mahaifiyar ta shi ganin yadda lokaci daya ta rikice, Yaya Uwa da ta karaso wajen, zaku rantse da Allah ku ce ai ita ce uwar Juwairiyya ko kuma matan da suka shigo gurin ta suka zo.
" Ke nan tuanani ki ke sharri akaiwa yar ki? hmmm Hannatu kenan. tantirancin da yar ki take zaki ce baki sani bane ba? amshi kalla"
Ta fada tare da mikawa Inna wayar da ke hannun ta, kafin Ahmad ya karba tuni Inna ta karba wayar, a daidai fitowar Juwairiyya tsirara daga toilet!.
Hannun Inna se ya fara rawa, mug din da ke cike da kunu ya kwace daga rukon da tayi masa ji kake tas ya hadu da terrazzo da ke malale a tsakar gidan!
Kai ta cigaba da girgizawa tana fadawa kanta, kuskure ne, idanun ta ne suke gizo amma wannan ba kamillaliyar Juwairiyyar ta bace ba, ta runtse idanun ta, ta sake budewa ta kalla wayar...
hannun Juwairiyya ta rike da karamin towel tana tsane kanta hade da sakin wani murmushi me kayatarwa!
wani irin abu ne ya caki zuciyar Inna, tamkar wadda aka sokawa wuka haka taji, Ahmad ya saka hannun shi ya tankwabe wayar daga hannun Inna, cikin sa'a kuwa wayar ta fadi ta hadu da terrazor da ke malale a tsakar gidan.
Inna bata sake magana ba, ta juya a hankali ta koma shige dakin ta, ba tare da tana ganin gaban ta ba ta karasa kan lazy sofa dake aje a gefen gadon ta ta fadi, idanun ta ta runtse saboda wani numfashi da take ja da karfin gaske, ji take kamar an saka abu an shake mata wuyan ta, Ahamd ya shigo da sauri, tare da karasawa in da take kwance ya tallafo ta yana fadin
"Inna! Inna!! Innalillahi wa inna ilaihil raji'un, Inna kalle ni, Inna menene yake damun ki? Inna ki fada min"
lokacin da ya birkito ta, ta koma tana facing din shi, da ya kalla fuskar ta se yaga as if bai taba ganin ta ba, tamkar ba Innar shi bace ba yanzun da suka gama magana, gaba daya fuskar ta ta canja, bakin ta yayi gefe guda, Ahmad yayi saurin fashewa da kuka yana fadin
"Inna, kar kiyi haka, Inna ki tsaya nayi miki bayani..."
Ya cigaba da fada yana kuma jijjiga ta, gaba daya kwakwalwar shi bata aiki, bata ma bashi ya kai ta asibiti ba.
"To kukan maganin me zaiyi maka, matsa akai ta asibiti mana"
Kamar wadda taji me ake cewa, se Allah ya bata ikon bude baki tace
"Mutuwa zanyi, tafiya zanyi na sani. ku kula da yar uwar ku, nasan KUSKURE ne tayi, Allah ya shirya ta"
Daga haka bata sake magana ba, kuma gurnanin da take ma sosai ya ragu, hakan yasa Hasher saka hannun shi ya dauke ta cilak yayi waje da ita.
Babu kowa tsakar gidan, Dan matan sun bi Yaya uwa dakin ta ana maida yaddaa akai, tana Kuma sake zuga su.
Ahmad ya biyo bayan shi fuska kace kace da hawaye. yana kokarin saka ta a mota Hashim ya karaso shima da motar shi a gigice, kilan dai duk yanzun suka ga scandal dinnan saboda yadda suke a gigice.
A zuciyarsa, Hashim ya kasa fahimtar yadda ƙanwarsa, wadda ya yi alfahari da ita tsawon shekaru, ta kai ga wannan hali, a ina suka kasa? Da har Wani zai hillace ta ta aikata Haka?
Shi Hasher matar shi ce ta nuna masa video, ya kuma hanzarta tahowa gida dan kada Inna ta gani,
"Ahmad me ya samu Inna? me ya faru?"
Ahmad da har lokacin hankalin shi yake a tashe yace
" She saw the video, taga video Juwairiyya"
Kai ya dafe yana nanata Innalillahi wa inna ilaihil rajiun, kusan tare suka fada motar dan tafiya asibiti, a hanya Hashim yana ta kallon fuskar Inna, yasan ta rasu amma ba zai iya fadawa yan uwan shi yace mahaifiyar su ba ta tada rai!
Zuciyar shi wani irin harbawa take, hannun shi na cikin na Inna Yana karanta addua nema mata gafara, shikenan Innar su ta tafi? Ahmad ya juyo ya kalle shi yace
"Ya naga kamar jikin ta ya saki?"
Hashim dai Bai ce musu komai ba, Hasher dake tuki Shima ya juyo ya Dan kalla Inna briefly kafin ya Maida hankalin shi kan tukin da yake yace
"Alhamdulillah! Inna ta samu bacci"
Hashim ya goge kwallar da ta taru gefen idanun shi, Bai ce musu ko uffan ba, saboda ba shi da courage din fada musu, ba dai daga bakin shi ba.
Suka karasa asibiti a emergency unit, kamar dai yadda muka san kowannen emergency na asibiti, yawanci ma'aikatan a tsaye suke kan kafafun su suna Kai kawo Dan taimakon marasa lafiya, ko da motar Hasher ta tsaya Hashim yace su Jira yayi musu magana kafin a shigo da ita.
Cikin sauri ya shiga sede kusan kowannen nurse da Doctor aiki suke a wannan lokacin, saboda wata trailer da ta Fadi ta jikkata mutane a gefen titi.
"Kamar Dr. Hashim! "
Ya ji an fada se Kuma can tace
"Hashim Dan Malam!"
Yaji wata murya tayi masa magana, cikin sauri ya juyo se idanun shi ya sauka akan na Maryam, Maryam abokiyar karatun shi ce lokacin medical school, dukda ba medicine tayi ba amma tare sukai preclinicals din su, ita din nurse ce, rabon da su hadu da ita tun bayan gama makaranta ba su Kara haduwa ba se yau.
"Nurse Maryam! Please ki taimaka kizo kiyi min certifying death dinnan"
Cikin sauri Nurse Maryam ta zaro stethoscope din dake makale akan teburin aikin su tabi bayan shi tana tambayar waye ne? Haka ya fada mata mahaifiyar shi ce!
Da sauri ta karasa ta bude seat din, hade Kuma da saka stethoscope din a daidai zuciyar Inna amma shiru, lub dub ya dauke, tamkar Inna bata taba rayuwa ba, ta gwale idanun ta ta haska amma pupils din ta ba suyi dilating ba, dagowa Maryam tayi ta kalla Hashim cikin Wani irin tausayawa tace
"Dr. Sede kuyi hakuri fa, amma Bata da Rai!"
Ahmad da sauri ya karaso gaban Nurse Maryam yace
"A'a! Inna bata mutu ba, Kara dubawa, Abu Huda ka duba Inna bata mutu ba, yanzun fa..."
Maganar shi se ta katse lokacin da Hasher ya daura hannun shi saman kafadar shi, a take kuwa hawaye ya ballewa Ahmad shi dama haka yake da saurin kuka tun Yana yaro, magana kadan se kuka, ba shi da dauriya irin ta Maza ko kadan. Hashim ya kalla Nurse Maryam yace
"Nagode sosae, nagode!"
Itama jikin ta duka yayi sanyi, rabon da ta Sanya shi a idanun ta tafi shekara bakwai zuwa takwas, yau Kuma ta hadu da shi, se komai yazo a baibai. Cike da tausayawa tace
"Allah ya jikan ta Dr, Allah ya gafarta mata!"
Ya gyada Kai ya karasa cikin motar, ya kalla Inna kamar me bacci, ya saka hannun shi ya tofa addu'a sannan ya rufe mata idanun ta, idanun shi sun kada sunyi jawur zuciyar shi kamar zata balla kirjin shi ta fito haka yake ji.
Cikin motar dukka sunyi shiru, a lokacin ko allura ka wullar akwai yiwuwar kaji karar faduwar ta saboda tsabar shirun da sukai, babu Wani Wanda yayi yunkurin Kiran waya, se can Hasher ya dubi Ahmad yace
"Ko zaka kira Malam da Kuma Abu Saif ka fada musu?"
Ahmad ya share hawayen shi ya ciro wayar ba tare da amsawa Hasher maganar ba ya fara Kiran Malam, shi Kuma Hashim ya fara neman layin Abu Saif, cikin sa'a ya dauka, abin da ya fara cewa Hashim
"Abu Huda, ka samu Juwairiyya a waya kuwa?"
Har Wani daci yaji cikin bakin shi, Jin sunan Juwairiyya, duk ita taja komai, ita ta saka su a cikin wannan tashin hankalin da suke ciki, ita ce baya ma son tuna sunan ta, yarinyar nan ta cuce su, ta zalunce su ta tona musu asiri
""Abu Saif, Inna ta rasu!"
"Wacece Inna Kuma?"
Muhammad ya fada daga dayan bangaren, gaba daya kan shi ya cushe ya ma manta wai Inna suke Kiran mahaifiyar su,
"Inna dai ta mu, ita ce ta rasu ka taho gida"
Tamkar an Sara masa adda a Kanshi haka yaji sakon Hashim cikin kan shi, runtse idanun shi yayi gam, ya Kuma rike wayar gam a kunnen shi, muryar Hashim na amsa kuwwa a kan shi.
Oum A'eesh