BABI NA TARA
Ko da suka zo kamar yadda ta saba har d'akin Maman su Zaliha Ramlat ta je ta gaisheta.
Hansatu ta yamutsa fuska tana amsa gaisuwar tana binta da kallon kwarilla.
tana fita a d'akin ta ciza baki
tana fad'in
"Ai ke da kwanciyar hankali sai dai ki gani a gidan wasu, tun da uwar ku ta aure min miji, mu zuba mu gani."
Mama ta rungume jikokin ta tana musu oyoyo, yaran suna ta tsalle jikinta.
Ramlat na zaune a gefe tana binsu da murmushi.
ganin yadda Mama ta maida hankalin ta sosai ta biyewa yaran, suna na ta zuba mata surutu.
Mama ta gyara zama ta Mai da hankali kan Ramlat da kyau ta dube ta, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, duk ta rame bata cikin walwalarta ga kuma ciki.
Mama taji ba dad'i duk da bata nuna mata ba a fuska,
Ramlat akwai hakuri da zurfin ciki ba kamar Rubaah ba.
Mama ta kuma mai da hankali kanta tana fad'in
"Ramlat ki na dai shan maganin da ake baku gurin awu ko?."
"Eh ina sha Mama."
"Yauwa, domin yana taimakawa matuka ga mace mai ciki,
musamman rashin jini da masu ciki suke yawan fama da shi yanzu,
gashi nan duk kin farance kamar babu wadataccen jini a jikin ki,
idan zaku tafi zamu biya ta gidan malam barau, a amso miki madubiya, ki had'a duk kirika sha zai taimaka miki,
kuma ki rage yawan aje damuwa cikin ranki, a gab'ar da kike ciki yanzu hawan jinin zai sami damar shiga da sauri."
numfashi ta d'an ja sannan ta ce
"Mama Mustapha ya sauya yanzu kamar ba shi ba."
sai Kuma tayi shiru tana wasa da 'yan 'yatsunta maganar da ke zuci ne ya fito fili, iya nan ta sai da batun dan bazata iya sanar mata abin da ya wuce wannan ba, shima wannan ɗin kuɓucewa ya yi a bakinta.
Mama ta jinjina kai tana karantar yanayin ta, tabbas tana cikin damuwa ko da bata fad'i ba.
gashi a jikinta ya nuna ta rame duk ta farance.
Mama ta ce
"Kiyi hakuri ki kara karfin addu'a. babu abun da yafi karfin Allah, amma ki kula da kyau kina da ciki kada ki bari damuwa ya yi tasiri a kanki.
ni ma kuma bazan gushe ba zan cigaba da tayaki da addu'a."
Ramlat ta jinjina kai, tare da yin murmushi.
"In sha Allah Mama."
Mama ta dubi su Muhsin da suke kan cinyarta ta ce
"Ku zauna bari na samo muku abinci."
ta zaunar da su a gefe kana ta mike.
ido ta kurawa labule ganin gilmawar mutum da sauri.
ta girgiza kai kana ta yi waje.
Hansatu data ta gama musu lab'e jin Mama zata fito ta wuce da sauri ta shige d'akin ta.
shewa tayi tana buga cinya ta tauna baki cike da keta ta ce
"Ai kadan ma kuga ni, sai ya sakota ta rasa mafaka."
ko da Rubaah ta dawo daga makaranta ta same su tayi farincikin ganin su sosai.
har yamma kafin Ramlat ta fara shirin komawa gida, sai take ji kamar Kar ta koma gidan gaba d'aya ya isheta.
ta ce wa Rubaah ta zo su tafi tare ta ce ita babu in da zata,
in ma zataje sai a weekend.
sanin halin ta yasata kyaleta, bayan tayi ta lallab'a ta kan tazo a weekend d'in..
Mama ta fito musu rakiya ta tanbayi malam Musa zasuje ta amso mata magani, gidan Malam Barau. ya ce sai ta dawo,
Rubaah na rike da hannun Mashkur da Muhsin suka tafi har da ita...
Hansatu ce zaune ita da kawar ta Ladiyo a d'aki.
Ladiyo tayi shewa tana fad'in
"Sai da ke kawata, duk wanda yaci tuwo da ke miya ya sha."
Hansatu ta mika hannu suka tafa
"Ai ni warki ce dai-dai da kugun kowa, ina gaya miki ai tun da na sami labarin,
yaron yana niman aure, na bazama bincike har na gano in da gidan iyayen yarinyar suke,
naje na gaya musu su tashi tsaye tun da wuri,su san gidan da za su kai 'yarsu, zata shiga kan wad'an da basu zauna ba. gara suma su mike da kafafinsu, tun maza kafin su kai 'yar su ta fito a wata d'aya;
ba sai ga ita Ramlat ɗin ranar ta zo duk a birkice ba.
na laɓe ina ji tana gayawa uwar tata yanzu mijin azaba yake bata, wulaƙancin duniyar nan a kanta yake sauke wa."
Ladiyo ta rike baki
"Umm Hansatu, uwar jaraba, ke fa halinki bai sauya ba tun na kuruciya, kin iya shirya magana daram ya zauna kamar haka a ka halitto shi."
suka Kuma shekewa da dariya suna tafawa.
Mama baiwar Allah tana ɗaki bata san me ake ciki ba, bata san Hansatu ce tayi kutun-kutun ta ba da babban gudummawa wajen rushe farin cikin ɗiyar ta ba.
sai dai sam bata yi sake da addu'a ba, dan tasan shine babban kariya ga dukkan bawa.
Yau Nafisat ta kuma kawo wa Ramlat ziyara kamar yadda tayi mata alkawarin zata kuma zuwa.
wannan karon ita da wata kawar ta mai suna Nadiya suka zo,
ta cika su da abin sha da na motsa baki.
suna cikin hira.
Nafisat ta nisa nata tambayar Ramlat ya suke ciki yanzu, tayi amfani da shawarin da ta bata?.
Ramlat ta ɗan sauke numfashi tare da kallon gefen Nadiya, dake zaune tana danna waya gami da taunar cingam.
da alama bata son yin maganar a gabanta, dan yau ta taɓa haɗuwa da ita, kawar Nafisat ɗin ce ita bata santa ba.
Nafisat ta nuna mata babu wata matsala tayi maganar ta.
ta kuma sauke numfashi tare da cewa
"Babu abinda ya sauya, yanzu kam na barwa Allah ikonsa, ina ta addu'a Allah ya yaye min, kuma Mama tana tayani."
"An sani addu'a shine maganin komai, to amma fa ki sani, a wannan gaɓar dole ne biyan bukata ya zamo itace maganin naki, duk yadda kika kai da daurewa fa bazai yiwu ba.
amma ina sammanin watakila sha'awar ki bata kai lokacin da na shiga nawa ba.
wlh ina gaya miki ko gurin aiki Kabir ya tafi sai na kira shi ya dawo, babu dare babu rana kowani lokaci a cikin bukata nake, har sai da na haihu kafin na huta.
Mustapha baiyi adalci ba a matsayin sa na miji shine suturar ki, a wannan gaɓar kina da damar kai karansa gurin magabatan ku, idan kuma kin ga zaki iya cigaba da daurewa to shikenan."
Nadiya da duk maganar da suke a cikin kunnen ta. bata sa musu baki ba, sai yanzu ta gyara zama tare da aje wayarta a gefe ta ce
"Hmm namiji ke nan, wutan kirya sai kin gama wahalar rurashi ya kama yana ci kamar abin arziki daga bisani ya mutu ya barki da sabon fifita.
da baki da tabbacin ruruwan sa cikin sauƙi, shi yasa ban ɗaurawa kaina damuwar ɗana miji ba wlh."
Nafisat ta katse ta
"Ba wannan ba Nadiya mafita yanzu a ke nima, mafita ke nan Ramlat ki kai karar sa.
idan ba haka ba ke zaki cutu shi kam yana da wata matar."
Ramlat ta jinjina kai
"Nima da nayi wannan tunanin amma se nake ga kamar ba zan iyaba, ina jin nauyi."
"Kin ji ki da wani batu, to sai kiyi ta zama ai kunya zata kai ki ta baro."
cewar Nafisat tana hararar ta, Nadiya dai tun da ta suke baki bata kuma cewa komai ba...
sun ɗan jima kafin suka tafi, suka bar Ramlat da tunani fal ranta da shawarwarin da Nafisat ta kuma bata...
Yau ta kama ranar juma'a babu makarantar islamiya boko kuwa da karfe 12 dai-dai Rubaah ta dawo gida.
tana dawowa daga makaranta kamar ko da yaushe ta tadda ruwan wankanta Mama ta d'uma mata yana ajiye a cikin boket. ta d'auka ta nufi bayi tayi wanka ta fito.
tun jiya ta kwana da shirin tafiya gidan Adda'n ta Ramlat, dan haka karfe 2 ta gama shirin tafiya.
ta d'au jakarta data saka kaya kala biyu kamar yadda tayi niyyar yi mata kwanaki biyu, zata kashe islamiyar ta na kwana biyu ke nan.
tayi wa Mama sallama bayan ta bata kud'in adaidaita har ta kai kofa Mama ta kira sunan ta,
"Rubaah."
ta juyo tare da amsawa daga in da take tsaye a bakin kofa.
Mama ta dube ta da kyau da idanu masu cike da nasiha ta ce
"Ziyarar 'yar'uwar ki kikaje kar naji wata magana kiyi abin da ya kai ki kawai, babu ruwanki da kowa da komai."
baki ta turo cikin shagwab'e fuska ta ce
"To ni Mama me zanyi dama."
"Ni dai na gaya miki bana son niman magana."
tayi waje tana fad'in
"Allah baki hakuri Mama gurin Adda Ramlat naje ba gurin kowa ba, dan ma tayi ta matsa min naje ne zan je, kuma dan na jima ban ganta ba ina so na ganta, ni ma bason zuwa gidan nake yanzu ba, tun da Yaya Mustapha ya auro waccan muciya da d'aurin zanin."
ta karashe maganar cikin yin kasa da murya tana ficewa daga dakin.
"Me kika ce Rubaah?."
"Ban ce komai ba Mama na ce kiyi min addu'a na dawo lafiya."
Mama tayi shiru dan bataji maganar nata na karshe ba, sai dai ta so ta fahimci wani abun take fad'a.
tabi 'yar tata da fatan shiriya dan ta san halin kayan ta sarai.
Tana isa bakin kofar gida ta tsaya tare da yin addua'r fita daga gida, sannan ta fice da kafar dama.
hakan na daga cikin d'abi'arta ko mi saurin ta sam bata mance wa da yin addu'a.
Habu da abokan sa suna zaune a tacan gefen gidan suna ganin fitowar ta wani daga cikin abokan nasa ya ce
"Kai Habu ga kayan alatun gidan ku ta fito,
yarinyar nan zazzafa ce dan ma bata gama kosawa ba."
duk suka juyo gare ta, Habu ya ce
"Ainihin zazzafa makuwa, dan bakuga ainahin surar a bayyane bane,
kana ganin ta 'yar karama amma wlh haɗeɗɗeya ce.
yarinyar ta had'u ciki da waje.
kai kad'an ya rage ranar na shiga dakin su na mammatse ta, Mamar ta ta ganni.
tana cikin cire uniform na lab'ab'a na leka ina kokarin shiga d'akin tsohuwar ta ta dakatar da ni."
ya wani ja numfashi yana hard'e kafafunsa tare da matse abin cikin wandon sa a sakanin cinyoyinsa.
ya wani tand'e baki yana piki-piki da ido tare da cigaba da fad'in
"Kai kaga rufaida yogurt d'in ta kuwa, duk da ta bawa kofa baya amma ina hango gefen su ta sakankanin hannayenta data d'aga tana cire rigar uniform ɗin.
kana ganin ta ƴar karamar nan suna nan a cikin riga kaɗan ya rage su gama kosawa.
wayyo Allah ji nayi kamar nayi sufa na juyo da ita na kallesu sannan na cafkesu na matse su na shanye su."
ya kuma narkewa cike da rashin ɗa'a.
abokin sa mai suna Nafi'u ya ce
"Yar karama da kayan aiki, ai dama da gani yadda take a had'e ta waje ta ciki ma haka take."
Duk sukayi shiru ganin ta zo zata wuce su, Nafi'u ya gyara zama tare da washe baki yana fad'in
"Aa kanwarmu ina zuwa haka?."
ko in da suke bata kalla ba ta cigaba da tafiyarta.
"Kanwarmu babu magana ne."
a dakile ta ce
"Unguwa."
da sauri ya ce "Ko na zo nayi miki rakiya ne?."
sai sannan ta juya ta dalla masa harara.
ya saki dariya yana fad'in
"Wannan kallo haka aa to a dawo lafiya."
tayi gaba tana yin kwafa.
ta haura titi da babu nisa sakani ta tari me adaidaita zuwa gidan Ramlat dake unguwar Fadamar mada.
a dai-dai layin babayo garba gamawa, aka sauketa. kasancewar gidan a nan titin yake.
unguwar shiru babu hayaniya dan unguwar manya ne. ta karasa bakin get d'in gidan ta kwankwasa.
Ramlat dake shanya a farfakijiyar gidan ta karaso bakin get d'in ta ce
"Wane ne?."
"Ni ce Adda Ramlat ni kam bud'e min."
da sauri ta bud'e mata karamar kofa jin muryar ta, tana fad'in
"Oyoyo Autar Mama."
sai kuma ta b'ata fuska
"Sai yau kika ga damar zuwa ko?."
Ramlat ta fad'a tana dad'a wangale mata kofar.
fuska Rubaah ta yamutsa ta ce
"Ai ki gode ma dan naji kwad'ayin ganin yarana ne ma da bazan zo ba."
"Um to ai dai na gode tun da naci albarkacin su, taho mu kara ciki."
ta janyo hannunta tana tambayan ta ya Mama tana nan lafiya dai ko.
har zasu shige kofar da zai sada su da ainihin cikin gidan Rubaah ta ja ta tsaya ta dubi Ramlat tana fad'in
"Yanzu wannan muciya da d'aurin zanin tana nan a cikin gidan nan?
ni fa shiyasa tun da tazo gidan nan naji zuwa gidan ya fice min a rai."
Ramlat ta girgiza kai cikin sanyi halinta daya sha bambam dana Rubaah ta ce
"To meye ruwan ki da ita tsare miki guri tayi ko ta shiga rayuwar ki? babu ruwanki da ita taho muje."
Rubaah ta kwaɓe baki tare da kaɗa kwayar idanunta ta ce
"Ni ta shiga rayuwar tawa ma tagani."
"Bama zata shiga ba muje dai."
Ramlat ta janyo ta suka shige ciki.
Mashkur da Muhsin dake wasa sakar gida suna ganin Rubaah suka mike da gudu sukayi gurinta,
ta bud'e hannu suka fad'o jikinta ta rungume su,
"Oyoyo 'yan yarana wlh nayi kewarku."
ta janyo su sukayi cikin d'aki.
Ramlat tana ta binsu da murmushi ganin yadda ta dage tana hira da yaran, har ta kawo mata abinci sukaci tare.
suna gamawa ta kwashi kwanukan ta kaisu kichin ta wanke ta dawo ta zauna idon ta a kan cikin Ramlat.
"Wai Adda Ramlat sai yaushe ne zaki haihu kam."
Ramlat ta shafi cikinta daya fara tsufa tayi murmushi sannan ta ce
"Uhum Rubaah in ban da abinki cikin wata bakwai ai da saura."
"Wannan karon ki haifo mana mace."
Ramlat tayi dariya
"To Allah yasa macen ce."
"Amin." ta faɗa tana mikawa tsaye
"Ni bari na yi sallah."
ta ruko hannun yaran suka shige ɗakin yaran, wan da idan tazo a nan take sauka......!
Mommyn Twins ce