BABI NA GOMA
Da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare 12, jin motsi sosai ta bayan window ɗakin su Mashkur inda Rubaah ke kwance tare da su, ya sa ta miƙe tana murza idanunta. da Barci bai jima da ɗaukar ta ba, domin kallo suke yi aka ɗauke wutar nepa, hakan ya sa suka kwanta kuma ba su jima da kwanciyar ba.
Ta taka a hankali zuwa jikin window
da ke a buɗe, wadda kafin ta kwanta ta buɗe ta saboda yanayin zafi irin na garin Bauchi.
Da mamaki ta zuba wa Ramlat ido, wadda ta gani zaune tana faman fiffita wutar gawayi.
Ta duba agogo, ta ga ƙarfe 12 na dare ya gota.
Ta fito tsakar gidan tana mamakin me take son girkawa a cikin tsohon daren nan, wanda ta manta ba ta yi shi tun da wuri ba.
"Adda Ramlat, me za ki yi da wuta yanzu?"
ta yi maganar tana ƙarasowa inda take.
Ramlat ta dube ta tana ci gaba da fiffita wutar da gawayi guda ɗaya ya kama,
sai ƙoƙari take sauran ma su kama. "Rubaah, ba ki yi barci ba ne?."
"Na yi, motsinki ne ya tayar da ni."
Ramlat ta yi murmushi, ta san sam Rubaah ba ta da nauyin barci.
"Kin ganni nan ina ta faman wutar nan ya kama, da alama sai na sha fiffita da yawa. Gawayin ne ruwa ya taɓa shi, tunda na kwana biyu ban yi amfani da shi ba. Dama sai idan gas ɗina ya ƙare, kokuma babu wutar nepa idan ina sauri nake amfani da shi. Gaba ɗaya na manta cewa gas ɗin ya ƙare tun safe. Da wutar nepa nake ta amfani, gashi tunda suka ɗauke ɗazu ba su dawo da ita ba har yanzu."
"To wai me za ki yi da wutar ne Adda Ramlat? Yanzu fa ƙarfe ɗaya na dare ake nema."
"Zan girka indomie ne wa Abban Mashkur. Ya kwanta bai ci abinci ba, shi yasa ya kasa barci."
Cikin mamaki Rubaah ta ce,
"Amma dai kamar na ga ba ke ce da girki ba yau?."
Ramlat ba ta ba ta amsa ba, sai cewa da ta yi, "Je ki kwanta Rubaah, yanzu zan gama nima."
Rubaah ta ji takaici ya kawo mata har maƙoshi.
Ta kalli ƙofar ɗakin Amina wanda Mustapha ke ciki, kana ta dawo da kallonta kan Adda Ramlat ta ce,
"Yanzu su suna cikin ɗaki suna kwance, saboda tsabar rashin imani a tsohon daren nan ga tsohon ciki a jikinki, ke ce za ki fito ki yi musu girki? Wallahi ke kika ga dama ma! Ai wallahi ke ma dai..."
Ta yi ƙwafa tana taune laɓɓanta cike da jin haushinsu duka, har da ita Ramlat ɗin da take ganin ita ce babban mai laifin da ta zauna ana raina mata hankali.
Ta juya tana ƙananan maganganu ta koma ciki.
Sai da ta sha wahala sosai kafin wutar ta kama.
Bayan ta gama girkawa, ta je ta buga musu ƙofa. Tana tsaye gurin na tsawon mintuna biyar kafin Mustapha ya fito.
Yana sanye da gajeren wando kacal, babu riga a jikinsa,
ya haɗa gumi sharaf.Kallo guda ta yi masa ta ɗauke kanta,
tana miƙa masa plate da ta zuba indomin a ciki.
"Sannu fa, na gode," ya faɗa yana amsar plt ɗin ya koma ciki.
Ta juya itama ta koma ɗakinta tana jin zuciyarta na mata nauyi.
Auren da ya ce ya yi shi ne don ta samu mai taya ta ɗawainiyar gida, amma ko sau ɗaya ba ta taɓa ganin wani taimako da za ta ce Amina ta yi mata ba.
Girki ma sai Amina ta ga dama take yi, dan haka Ramlat ba ta damu da sai ta jira ta ta yi ba,
take girkawa kanta da ƴaƴanta abinci.
Yau ma Aminar ce da girki, amma ta fake da cewa ba ta da lafiya kamar kowane lokaci.
Ko a daren nan ma tana barci ya kirata a waya ya kwantar da murya wai yana jin yunwa, idan tana da abinci a gefenta ya zo ya karɓa.
Ta ce masa babu, sun cinye, sai dai ta girka masa wani abu.
Sai da taje kicin ta tuna gas ɗinta ya ƙare,
gashi kuma an ɗauke wutar nepa.
Washegari
Kamar yadda Rubaah ta saba yi idan ta zo gidan, za ta yi shara, wanke-wanke, har ma da girki.
Tana cikin shara ta ji an waso datti ta bayanta.
Ta juyo tana kallon Amina riƙe da ƙugu, da alamun dai ita ta watso dattin a wurin da ta riga ta share.
Wani kallo ta wasa wa Rubaah, ta koma ɗakinta tana yamutsa fuska.
Rubaah ta jinjina kai tana ciza baki, ta ce a ranta, "Ni ba Adda Ramlat ba ce, sai na koya miki hankali!."
Ta haɗiye maganar a zuciyarta ta ci gaba da sharan,
ba tare da ta share wurin da Amina ta waso dattin ba.
Sai da ta gama tsaf, kafin ta dawo ta tura daukacin sharan har zuwa bakin ƙofar Amina.
Daf da bakin ƙofar sosai ta tara mata shi a gurin,
ta faffansala wani dattin har cikin falon Amina, sannan ta wuce gefen ƴar'uwar tata.
Ta haɗa wanke-wanke a kicin ta wanke su, sannan ta ɗaura breakfast.
Sai da ta gama tsaf ta fito da abin karin falo,
kafin ta shige ɗakin su Mashkur.
Ta tayar da su, ta yi musu wanka a toilet ɗin ɗakin,
ta shirya su suka fito falo.
A lokacin Ramlat take fitowa itama. Ta yi murmushi ganin ko'ina a gyare tsaf, ga yaranta sun yi wanka cikin kaya masu kyau.
Rubaah duk da rashin haƙurinta da tsiwarta, amma sam ba ta da ƙyiuya, shi yasa Ramlat take son ta riƙa zuwa gurin ta domin tana taimaka mata sosai.
Ramlat ta ƙaraso da murmushi tana faɗin,
"Iye, Ruby autar Mama, Gaba kaɗan za ki ƙara, Mama ta aurar da ke.
To ai ba abin da ba ki iya ba na aikin gida."
Baki Rubaah ta taɓe ta ce,
"Chafɗi! Ai ni ba zan yi aure ba ma, balle a zauna ana raina mini hankali."
Ramlat ta yi dariya ƙawai tana girgiza kai.
Amina tana fitowa daga ɗakinta ta yi karo da sharan da Rubaah ta tara mata har zuwa cikin falonta.
Gaba ɗaya ta waro idanunta , fuskarta ta sha murtuk.
Ta juya fuuu ta nufi ɗakin Ramlat,
ta bankaɗo labulen da ƙarfi.
Ƙaraf idanunsu ya haɗu da na Rubaah.
Amina ta tsaya a bakin ƙofar tana huci, ta nuna Rubaah da yatsa ta ce,
"Ke! Fito ki je ki kwashe kazantar da kika tara mini a bakin ƙofa yanzu nan! Wace irin fitsararriyar yarinya ce ke da za ki kawo mini rashin mutunci har cikin gida na?!"
Rubaah ta ɗago fuskarta cikin zallan tsiwa,
ta ajiye kofin shayin hannunta cikin natsuwa, ta kalli Amina ido-cikin-ido ta ce,
"Haba Adda Amina, ai tunda kika koya mini yadda ake zubar da datti ta baya, ni kuma na ɗauki hadda na mai-maita har da ƙari na dawo miki da shi ta gaba.
Kuma ba zan kwashe ba, sai dai idan ke da kanki za ki kwashe."
Amina ta waro ido cikin matsananciyar fushi,
ta tako cikin ɗakin ta kai hannu zata janyo Rubaah, tana faɗin
"Ke kizo har gida na kina gaya min magana, tashi kije ki kwashe ko kuma na nuna miki cewa nan gidan mijina ne."
Rubaah ta buge hannunta tare da mike wa tsaye ta rike kugu tana binta da kallon sama da kasa.
"Ashe ma gidan ki ne bana Yaya Mustapha ba."
Amina
ta ce
"Ke, idan ba'a koya miki tarbiyya ba Ni zan ladaftar da ke,
dama naji labarin tashen rashin kunyar ki, sai na saita miki nutsuwa kafin ki bar gidan nan."
Rubaah ta kaɗa kwayar idanunta da babu tsoro cikin su ta ce,
"Kada ki kuskura Amina! Ni ba Adda Ramlat ba ce da za ki riƙa gallaza mata tana kallo.
Idan kika sake taɓa jiki na, yau sai na nuna miki ainihin farashin rashin mutunci a gidan nan!."
Ramlat ta zabura ta miƙe tsaye ganin Amina ta shako wuyan rigar Rubaah.
ai kuwa da karfi Rubaah ta ruko hannu nata tare da mussuke shi.
Ramlat ta ce
"Me kuyi yi haka? Amina ke da girman ki ai sai ki sa ta raina ki.
ke Rubaah sake mata hanu."
Rubaah ta saki hannun Amina cikin taƙama,
Amina ta banka mata harara har da Ramlat ɗin, sannan
ta juya ta nufi kofa tana faɗin
"Kafin ki bar gidan nan zan baki tarbiyyar da aka gaza baki."
"Ga kinan babban mara tarbiyya,
Ni zan koya miki tarbiyyar bari ki gani."
Rubaah ta faɗa cikin tsiwa tana huci.
Ramlat ta ce "Ke Rubaah dan Allah ki rabani da fitina, ina ruwan ki da shiga tsafgarta."
"Ita ta fara shiga tsafgata idan kuma ta sake shiga, kafin jibi tayi na bar gidan nan sai na saita mata hankali."
Ramlat ta rungume hannu tana kallon Rubaah, wata rana yarinyar mamaki mai haɗe da tsoro take bata,
shekara goma sha biyar gareta, har yanzu bata gama ciki sha biyar ɗin bama,
Amma halin ta ya girmi na ɗan shekaru ashirin da ɗoriya.
Har ta kare kwanaki biyun da zatayi Adda Ramlat bata kara bari wani abu ya kuma shiga sakanin ta da Amina ba,
ta toshe hanyoyin da zata bi su haɗu ma,
dama sharar tsakar gidan ne abu na farko wajen fitar ta tsakar gidan, washegari kuwa ta hana sharar ta ce ta bari ai gidan beyi datti ba tun sharar da tayi jiya.
da zata koma gida kuwa sai da ta rakata ta har waje,
ta tare mata abin hawa har taga tashin su kafin ta koma.
koda Adda Ramlat ta komo gidan da ta kalli kofar Amina sai tayi murmushi tana girgiza kai.
tuno da kalar hararar da Rubaah tayi tayi wa kofar kamar Amina'r ce a gurin.
ta shige ɗaki tana kuma girgiza kai gami da yin dariya da faɗin
"Allah ka shiryi Rubaah."
Bayan Sati Guda
Kamar yadda ta saba a kowace rana, ta fito sanye da uniform ɗin islamiyya,
fuskarta ɗauke da annuri.
bayan dawowarta daga makarantar boko.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ta isa ga mahaifiyarta ta yi mata sallama tare da sanar mata zata je islamiyya. Mama ta ce adawo lafiya, ta juya da sauri ta fice domin kada ta makara a rukunin karatun na yamma.
Lokaci ya tafi da sauri, hakan ya sa dai-dai ƙarfe shida na yamma saura 'yan mintuna kaɗan aka tashi daukacin ɗaliban makarantar ta Islama.
Rubaah ta taho gida cikin hanzari, tana mai addu'ar samun mahaifiyarta cikin koshin lafiya da farin ciki.
Ta tura tsohuwar ƙofar gidan nasu, sannan ta shigo cikin tsakar gidan da siriruwar sallama fuskarta wasai.
Hansatu, wacce ke zaune a tsakar gidan tana gudanar da wasu ayyukan gida na yau da kullum, tana jin sallamar Rubaah sai ta watsa mata wani tsinannan kallo mai cike da tsana da kyama.
Ta taɓe baki cikin gadara, ta kawar da kanta gefe guda tamkar ba ta ga mutum ba,
sannan ta ci gaba da juya ayyukanta cikin nuna halin ko-in-kula.
Rubaah, wacce ta saba da irin wannan halin Hansatu,
ita ma ta ɗauke nata idanun tare da taɓe baki a ranta.
Ba ta ce uffan ba, ta nufi ɗakin Mama kai tsaye,
ta tura labulen ƙofar ɗakin tare da yin sallama cikin sanyayyar muryata.
Mama na zaune a gefen tsohon gadon ta da ya riga ya gama kwanakinsa na alfarma.
Ta daka uban tagumi da hannuwanta guda biyu, idanunta sunq kallon ƙasa amma hankalinta ya yi nisa sosai a cikin kogin tunani.
Tana can tana nazarin makomar rayuwar tilon ɗiyarta guda ɗaya data rage a gabanta.
A kullum, babu abin da Mama ke yi face yi wa Rubaah addu'ar samun kyakkyawan ƙarshe, da buɗin rayuwa, da kuma samun kariya daga sharrin makiya.
Zaman gidan nasu ya zama abin tsoro da fargaba;
babu digon kwanciyar hankali ko ta fannin daƙiƙa ɗaya,
saboda kullum cikin bala'i, masifa, da hargagin Hansatu da 'ya'yanta suke jurewa.
Wannan uban damuwa ya taru ya yi mata katutu a tsakar zuciya,
har ya soma bayyana a fili a jikinta.
Ganin yanayin da mahaifiyarta ke ciki ya sanya Rubaah jin wani abu mai zafi ya soki tsokar zuciyarta.
Ta ji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, faararen idanunta masu kyau suka canza launi saboda tausayin mahaifiyarta.
Ta ƙaraso cikin sauri gami da nuna tsananin fargaba da damuwa ta zauna a kan doguwar kujera ta katako dake gefe guda.
Kujerar ita kaɗai ce a cikin ɗakin, kuma ta tsufa sosai har katakon jikinta ya soma macewa saboda tsawon lokaci.
Rubaah ta dubi mahaifiyarta cikin sanyin murya mai cike da bacin rai ta ce,
"Mama, me ya same ki haka? Don Allah ki gaya mini, ba dai wannan matar, mamar su Zaliha'n ba ce ta sake miki wani abun ba?."
Ta yi maganar ne cikin dacin rai da jin haushin Hansatu, domin ta sani sarai babu abin da zai sa mahaifiyarta ta shiga damuwa gami da daka uban tagumi a cikin daki idan ba fitina da masifar Hansatu ba.
Ta cije laɓɓanta na ƙasa cikin fushi, ta sake yin ƙwafa da ƙarfi sannan ta girgiza kanta ta ce,
"Wallahi wannan matar, akwai ranar da zan koya mata hankali a gidan nan! Ba za ta ci gaba da cutar da ke muna kallo ba."
Mama ta firgita da jin kalaman ɗiyar tata, wan da tasan idan ta furta sai ta aikata.
ta yi saurin daidaita zaman ta sannan ta yi ƙoƙari ta goge alamun damuwa da ke fuskarta. ta hanyar ƙirƙirar wani ɗan gajeren murmushi na ƙarfin hali.
Ta dubi Rubaah cikin tsawatarwa ta ce, "Kada na sake jin irin wadannan kalaman daga bakinki! Babu ruwanki da ita, ki fita harkan ta gaba ɗaya. Wa ya gaya miki cewa damuwarta ce ta sa na zauna a nan? Hutawa kawai nake yi saboda na ɗan gaji, ki daina tunanin komai."
Rubaah ta jinjina kanta kawai don kawar da zancen, amma a ranta ta sani sarai cewa ba haka abun ya ke ba; tana daurewa ne kawai don kada hankalinta ya tashi.
Mama ta sake dubanta cikin kulawa ta ce, "Tashi maza ki je ki cire kayan makarantar nan dake jikinki, Ga abincinki can, maza kije ki ɗauko ki ci kafin ya yi sanyi."
Rubaah ta miƙe tana mai sake yin ƙwafa a cikin zuciyarta.
Tun lokacin da ta shigo gidan ta ga yadda Hansatu ta watsa mata mugun kallo, ta tabbatar da akwai wata makarkashiya ko masifa da aka ƙulla a ƙasa kafin ta dawo.
Sai dai ta sani sarai cewa ko da ta matsa wa, Mama ba za ta taɓa gaya mata gaskiyar abin da ya faru ba don gudun tashin hankali.
Hakan ya sa ta sha alwashin cewa muddin ta gano abin da ya faru, ba za ta taɓa ƙyalewa ko ɗaukar rangwame ga duk wanda zai sake yunƙurin musgunawa ko cin mutuncin mahaifiyarta ba.
Cikin wannan tunani da ƙuduri mai ƙarfi, ta cire kayan makarantar ta sanya na gida masu sauƙi, sannan ta nufi inda abincin yake ta ɗauko shi, ta dawo kusa da Mama ta zauna ta soma ci, koda yake zuciyarta gaba ɗaya tana can tana shawagin yadda za ta tunkari fitinar gidan, tayi masa iyaka dan bata jin zata cigaba da zuba ido a na cutar da mahaifiyarta.
tana gani ba bata ɗauki mataki kan koma waye ba........!
*Masu tambayar HAMDAH da FEERYAL KARSASHI dukan su 1500 ko wani ɗaya 500 kiyi min magana ta wannan number 👉🏻****
Mommyn Twins ce