BABI NA SHA BIYU
Duk da cewa yau daren kwananta ne a tsarin gidan,
kuma ranar tana da matukar daraja a gare ta, sakamakon lalurar da ta sinci kanta ciki, na yawan ƙarfin sha'awar da ya sami gurbin zama cikin rayuwar ta na sanadin cikin da ke jikinta.
amma har asuba ta gobe ta kusa, har karfe sha biyu na dare ya gota ba ta sanya idanunta a kan mijin nata Mustapha ba.
Ta sauke wani zafafan numfashi mai cike da ɗacin zuciya da takaici,
yayin da take duban 'ya'yanta, Mashkur da Muhsin, wadanda barci mai nauyi ya riga da ya sace su a gefenta a kan kujerar falon.
Ta zuba musu idanu gami da zayyana hoton rayuwarsu a fili, amma a zahiri tunaninta ya yi nisa sosai,
ya lula cikin kogin sanyaya gwuiwa na rayuwar aurensu.
karar buɗe kofar falon ne ya tsinka mata lissafi, ya kuma dawo da ita daga duniyar dogon tunanin da ta dade tana lulawa.
da sauri ta juya idanunta masu cike da gajiya zuwa ga kofar,
tana mai amsa sallamar da Mustapha ya yi cikin muryar hanzari Yana tura kofar, ya ɗan shigo ta ciki gami da janye labulen falon da sauri.
Hannunsa na hagu yana riƙe da tafukan hannun Amina, yayin da yake jera mata sannu cikin fargaba,
"Shigo da ƙafarki ta ta dama... Yi a hankali don Allah, sannu kin ji?."
Ya tallafo ta suna takowa cikin falon.
Ramlat ta zuba musu idanu cike da mamaki da fargaba.
Ta miƙe tsaye da kyar sakamakon nauyin tsohon cikin dake jikinta.
Fargaba da tsoron abin da ya faru ya sanya ta dafe katon cikin nata da sauri,
domin a tunaninta wani babban hatsari ne ko tashin hankali ya faru da su a waje.
Ganin yadda Mustapha ke ruko hannun Amina yana jera mata sannu, ita kuwa sai wani narkewa take tana faɗin "Wash-wash."
Cikin sauri da fargaba, Ramlat ta mike daga kan kujerar da take zaune ta nuna musu gurin tana fadin,
"Subhanallah! Abban Mashkur me ya faru kuma? Mene ne ya same ta haka? Yi sauri ka zaunar da ita a nan."
Mustapha ya matso ya zaunar da ita cikin kulawa yake cigaba da yi masa sannu.
Tana zama, Amina ta sake narkewa gami da zamewa ta kwanta kan doguwar kujerar.
Ta ci gaba da sauke nishi ɗaya bayan ɗaya cikin nuna wahala, tana juyar da kanta dama da hagu tamkar wacce ranta ke shirin fita saboda tsananin rashin lafiya.
Ita kuwa Ramlat, saboda tsabar karamci da sanyin rai, sai jera mata sannu take yi ba kakkautawa,
zuciyarta cike da tsantsan tausayin halin da kishiyar tata ke ciki.
Musamman ma da ta lura cewa Amina tana ta dafe ƙaramin cikin jikinta da ya soma fitowa fili; itama cikin wata uku ne a jikin ta.
Ta dubi Mustapha da fuskarta cike da fargaba ta ce,
"Abban Mashkur, tunda abin ya kai haka ai da asibiti kai tsaye aka wuce da ita! Gaskiya bai kamata a barta a gida a cikin irin wannan mawuyacin halin da take ciki ba."
Mustapha ya shafo fuskarsa cikin damuwa ya ce,
"Tun ɗazu nake ta ce mata mu tafi asibitin amma ta ƙi sam, wai na bari kawai da kansa zai lafa."
Ramlat ta girgiza kanta ta ce, "A'a gaskiya, zama a gida da ciwon ciki irin wannan ga mace mai juna biyu ba zai taɓa yuwuwa ba. Kamata ya yi ka fita ka tada mota kawai mu tafi asibitin yanzu nan."
Ganin cewa Mustapha ya amince da shawarar Ramlat kuma ya soma yunƙurin fitowar don ɗauko mota,
Amina ta sake narkewa sosai, cikin murya irin na mai jin jiki da fitar da wahalallun numfashi ta ce,
"Yaya... Don Allah ka bari kawai sai gobe da safe. Ni gaskiya ba zan iya zuwa asibiti a cikin wannan daren ba."
Ramlat ta zuba mata idanu na wasu daƙiƙoƙi,
tamkar mai son karanto wani abu a fuskarta ko kuma nazarin gaskiyar lamarin.
Daga nan ta mayar da dubanta ga Mustapha, wanda ya riga da ya fasa fitar, ya dawo ya zauna a gefen kujerar da Amina ke kwance.
Ya ɗago kanta da hannuwansa biyu ya ɗaura a kan cinyarsa,
sannan ya shiga shafa gashin kanta yana jera mata kalmomin rarrashi da nuna zallar kulawa.
Ramlat ta sauke idanunta akan Amina na ƴan dakiku. kana
ta nufi hannun kujerar da su Mashkur ke barci ta zauna a kai,
tana mai ci gaba da nazarin lamarin da ke shirin jefa ta cikin ruɗani da fargaba.
nan take, hankalinta ya ba ta cewa wannan ciwon na Amina ba na gaskiya ba ne; shiri ne kawai da kullalliya irin ta makircin mata domin a lalata mata daren kwananta.
Tana zaune shiru, ba ta sake cewa uffan ba, illa kawai ta zuba wa sarautar Ubangiji idanu tana kallon ikon Allah na yadda Mustapha ya gama ruɗewa tamkar bai taɓa ganin jinya ba.
Can da daɗewa, Mustapha ya ɗago kai ya dubi Ramlat sannan ya ce cikin sanyin murya,
"Ramlat, ki kwashe yaran nan ku shiga ciki ku kwanta abunku. Dare ya fara nisa. Zan zauna da ita a nan falon kafin gari ya waye, idan jikin nata bai yi sauƙi ba sai mu wuce asibitin kawai goben."
Ramlat ta sake sauke wani sabon numfashin na biyayya da juriya.
Ta miƙe tsaye da kyar tana fadin, "To shikenan Abban Mashkur, Allah Ya sawwaka, Ya ba da lafiya."
Ta daddaga yaran nata guda biyu ta kai su ɗakin baccinsu,
sannan ta wuce ta shige nata ɗakin ta rufe ƙofar.
Zuciyarta ta cika tap da mamaki, ɓacin rai, da al'ajabin wannan sabon salon na wulakanci.
Yau fa ranar kwananta ce amma Amina ta tada karyar ciwo, kuma Mustapha ya kawo ta har cikin sashenta yana ji yana gani, sannan kuma ya ce ta shiga ciki ta bar su a falo don su kwana tare!
Ta kwanta a kan gadonta tare da runtse idanunta sosai,
ƙoƙarin kuma gyara kwanciyar tata tayi. Amma abin takaicin, gaba ɗaya ji take tamkar a kan ƙaya ko duwatsu take kwance, ba a kan gado da katifarta ba.
Ta tsinci kanta a cikin wani irin daci na kishi.
Bacci ya ƙaurace wa idanunta gaba ɗaya, ta kasa ko da datsa idon.
Tana jiyo sautin muryoyinsu daga can tsakar falon;
yadda Amina ke ta zuba masa shagwaɓa ta tsiya da canza murya, shi kuma Mustapha duk ya riƙirkice ya fita a hayyacinsa tamkar bai taɓa ganin ciwo ko mace ba a rayuwarsa.
Dare ya tsala sosai, ko'ina na gidan ya yi tsit na natsuwa, har lokacin barci bai sami nasarar sace Ramlat ba,
saboda zafin dake ruruwa a ƙirjinta. Can cikin dare, ta jiyo muryar Amina daga falo tana fadin,
"Yaya... Don Allah fitsari nake ji, kazo ka taimaka min."
Ramlat ta yi juyi cikin ɓacin rai tana gyara kwanciyarta a kan gadon.
bada jima wa ba ta ji alamun shigowar Mustapha cikin ɗakin nata,
sanye da Amina a ƙirjinsa, ya ɗauko ta kamar jaririya ko 'yar tsana. Ya wuce da ita kai tsaye zuwa cikin bayin dake cikin ɗakin nata.
Yana tsaye a kanta har ta gama abin da take yi, sannan ya sake ɗauko ta a jikinsa ya fice da ita suka koma falon.
Tun da take a rayuwarta, ba ta taɓa sanin cewa haka girman kishi da zafinsa yake da daci ba.
Ta ji kamar an ɗauki wani ƙatoton dutse mai nauyin gaske an danne tsakiyar zuciyarta da shi,
yana neman datse numfashinta.
A wannan daren na bakin ciki, Ubangiji ne kaɗai Ya yi ikonsa ga rayuwar Aunty Ramlat har ta sami damar kaiwa wayewar gari cikin ƙoshin lafiya da rayuwa...
Gari ya waye da wani sanyayan haske na asuba, yayin da sautin kiran sallah na fari ya gauraye sararin samaniya. Aunty Ramlat ta tashi da kyar saboda jikin nata da ya yi mata tsami saboda rashin barci da kuma nauyin dake jikinta.
Ta sauko daga kan gadon, ta yiwo al'wala sannan ta gabatar da nafila tare da sallar asuba cikin sanyin jiki da roƙon sassauci a wajen Ubangiji.
Bayan ta idar, ta ɗan zauna a kan sallaya tana gabatar da azkhar har sai da gari ya yi haske sosai dai-dai ƙarfe shida da rabi na safe.
ta mike dan zuwa yi wa yara abin kari ta kuma shirya su zuwa makaranta.
ta buɗe ƙofar ɗakin nata a hankali ta fito tsakar falon.
Idanunta suka sauka a kan doguwar kujerar da ta bar Mustapha da Amina a daren jiya.
Mustapha yana nan zaune har lokacin, kansa kishingiɗe a jikin kujera alamar barci ɓarawo ya sace shi saboda tsabar gajiyar jiyyar karya da ya kwana yi.
Amma abin mamakin shi ne, Amina ba ta nan a gurin!
Ramlat ta ɗan gyara tsayuwar tana dube-dube.
Ganin babban kofa na fita zuwa sashen Amina yana ɗan buɗe, ya ba ta tabbacin cewa Amina ta riga da ta koma sashenta tun da sassafe kafin Mustapha ya farka.
Ta taɓe baki cikin nuna rashin mamaki, ta nufi kicin domin ta soma ɗora a bin breakfast.
Tana cikin aikin ta, ta ji takun Mustapha ya ƙaraso kicin ɗin.
Ya shigo fuskarsa cike da alamun gajiyar rashin barci,
yana murza idanu, Ya dubi Ramlat cikin sanyin murya ya ce, "Ramlat, kin tashi lafiya? Don Allah ko kin ga fitar Amina? Na farka naga ba ta nan cikin falon."
Ramlat ta juyo tana kallonsa da sanyayyar fuska ta ce, "Lafiya lau Abban Mashkur. Ban ganta ba nima yanzu na fito. Amma na ga ƙofar waje a buɗe, kila ta koma sashenta ne don ta ɗan huta."
Mustapha ya sauke numfashi ya ce, "Haka ne kuwa. To Allah Ya sa jikin ya yi sauƙi, bari na leƙa na gani."
Ya juya da sauri ya fita, sai dai ɗakin Ramlat ya shiga tunawa da bai yi sallar asuba ba.
Tana kallon bayansa har ya fice. Bayan kamar minti goma, Ramlat ta fito da kofuna na shayi ta nufi ɗakin yaran domin tashe su.
tana shiga ta je kofunan ta wuce bayi tana ƙoƙarin haɗa musu ruwan wanka, ta jiyo dariyar Amina da maganar ta,
wan da window bayin yana ta jikin window falon ta ne hanya ce ta raba amma daga cikin bayin kana iya hango cikin falon nata.
Ta tsaya cak tana saurara. Muryar Amina ce ke tashi, babu alamar ciwo ko digon zazzabi a tare da ita.
Tana cewa, "Wlh Aunty Wasila daren jiya baki gani ba, da kyar na shawo kansa ya kwana a falo yana shafa min kai.
Ai dole na katse musu hanzari, ba zan bar ta ta sha romon kwananta ita kaɗai ba."
Daga ɗayan ɓangaren, muryar Aunty'n nata ne ke amsawa da cewa,
"Gaskiya Amina kinyi wayo, Karki sake ki yi wasa kin dai ji an ce uwarta,
ta mallake mijin da ta aura ƙarshe kishiyar ta ƴar kallo ta zama,
kuma kin san dai uwar tata bazata barta ta zauna haka kawai ba, itama dole zata shirya ta..."
Wani sabon daci ne ya sake turnuƙe zuciyar Aunty Ramlat.
Dama jiya tayi zargin shiri ne Amina ta shirya. yanzu kuma taji duk shirin nata a kunnen ta.
duk abin da ya faru na daren jiya ƙirƙirarren shiri ne na makirci domin a kuntata mata.
to me kuma ya kawo mahaifiyarta cikin wannan lamari?.
ta runtse idanunta, ta haɗiye ɓacin ran sannan ta ci gaba da abin da take. tana mai barwa Ubangiji ikonsa.
A b'angaren Mustapha kuwa bayan ya idar da sallar,
ɗakin Amina ya nufa.
yana tura ƙofar falon, ya iske ta zaune a kan kujera tana waya, fuskarta wasai tamkar ba ita ce ta kusa mutuwa a daren jiya ba.
Cikin mamaki ya ƙaraso yana fadin, "Amina! Har kinyi ƙarfin halin fitowa haka? Jikin ne ya yi sauƙi sosai haka?."
Amina ta hanzarta kashe wayar sannan ta canza fuska lokaci guda, ta ɗan dafe ciki taja numfashi...
tana wani nishi a dole ita gamai ciwo. muryarta ta koma ƙasa-ƙasa ta marairaice fuska tare da faɗin,
"A'a Yaya... har yanzu fa da sauran ciwon, ɗan daurewa nake yi kawai na dawo nan. dan na Barka kayi barci naga jiya baka samu kayi ba."
Mustapha ya ƙaraso cikin sanyin jiki, ya zauna a gefenta ya sanya hannu ya taɓa wuyanta don jin ko da zazzabi.
Ya sauke numfashi ya ce,
"To tunda har yanzu kina jin ciwon, maza tashi mu wuce asibiti kawai kafin rana ta yi nisa.
Ba zan iya barinki a haka ba."
Jin zancen asibiti ya sanya gaban Amina faɗuwa, domin ta sani sarai muddin likita ya duba ta, asirinta zai tonu cewa babu wani ciwo a jikinta.
Ta shashantar da zancen da sauri ta hanyar narkewa a jikinsa ta narke murya ,
"Yaya ni nasan ma idan muka je cewa za ayi allura za'ayi min. Kawai ka bari idan na sha magani zai lafa, ka koma wajen Ramlat kar hankalinta ya tashi.
kaga jiya baka samu ka keɓe da ita ba."
Mustapha ya gyada kai cike da gamsuwa da kalaman nata, ya ce, "Shikenan, bari na koma can na duba yaran kafin su wuce makaranta, amma ki tabbata kin sha tea kafin ki sha maganin."
Ya miƙe ya fice zuwa gefen Ramlat.
A ɓangaren Aunty Ramlat kuwa, tana gama shirya Mashkur da Muhsin cikin kayan makarantarsu,
ta fito da su falo don su yi breakfast.
Mustapha ya tura kofa ya shigo daidai lokacin da take zuba musu shayin.Ya kalli yaran cikin fara'a ya ce, "Yaran Abba, an shirya tafiya makaranta?"
Suka amsa masa cikin murna. Daga nan ya mayar da dubansa ga Ramlat wacce ke ta aikinta cikin natsuwa, fuskar nan tata babu alamar fushi.
Mustapha ya ɗan tsagaita, sannan ya ce,
"Ramlat, na dubi jikin Amina, da sauran ɗan zazzabi amma ta ce tana son ta huta a gida kawai kafin an jima. Dan Allah idan ba damuwa, ki ɗan riƙa leƙa ta kina duba yanayin jikin nata,
idan na fita gurin aiki."
Aunty Ramlat ta ajiye kofin tea ɗin dake hannunta,
wan da take fifita wa yaran ta juyo ta dube shi ido cikin ido.
Wani sanyayan murmushi mai cike da ma'anoni da yawa ya bayyana a fuskarta, wanda hakan ya sanya Mustapha jin wani iri a ransa.
Ta gyara zamanta sannan ta ce
"Abban Mashkur, ai ni ma ba lafiyar ce gareni ba,
ko ka mance ciki na ma yafi nata girma kawai ka zauna ka ci gaba da kulawa da ita."
tana kaiwa nan ta mike tsaye ta shige kichin.
ya bi bayan ta da kallo yana sauke numfashi a fili.
Bata fito ba har yaran suka gama, yau shi ya raka su makarantar ganin tun da ta shige kichin bata kuma fitowa ba.........!
*Masu tambayar HAMDAH FEERYAL KARSASHI dukan su 1500 ko wani ɗaya 500 kiyi min magana ta wannan number 👉🏻****
Mommyn Twins ce