BABI NA SHA UKU
Kwanaki sun ci gaba da tafiya a gidan nasu, amma maimakon abubuwa su daidaita, sai dai su ƙara tsananta sosai. Babban damuwar da ta sake dabaibaye zuciyar Mama ba ta tsaya ga masifar Hansatu kaɗai ba.
face sabuwar barazanar da ɗan Hansatun, wato Habu, da ya sa a gaba yanzu fiye dana baya.
A kullum, yana bibiyar takun Rubaah yana jiran ranar da zai sami gurbi ya cimma burin sa...
Rana ce ta musamman da la'asar ta tafi ta bar sauran sanyin yamma.
Bayan dawowarta daga makarantar islamiyya ta ɗauki boket ɗin wanka ta nufi tsohon ban ɗakin dake tsakar gidan nasu.
Tana shiga ta datse ƙofar da ke na langa-langa.
ta tuɓe ta soma gudanar da wankan ta.
Habu daya zo zai shiga gida ya hango ta tana ƙoƙarin shiga bayin,
ya koma ya laɓe har sai da ta shiga kafin ya shigo cikin gidan yana waige-waige ganin cewa Hansatu ba ta nan sannan Mama ma bata sakar gidan,
su Zaliha kam ma kwata-kwata basa gidan. tsakar gidan ya yi tsit.
Ya soma takawa cikin sanda gami da lallabawa tamkar maciji, har ya ƙaraso jikin katangar ban ɗakin. Ya ɗaga ƙafafunsa sannan ya miƙe wuyansa sosai, yana ƙoƙarin leƙawa ta cikin wata 'yar buɗaɗɗiyar kofa ta sama.
Mama dake ɗaki zaune Zuciyar ta yaɗan buga, ta tsinci kanta da shiga fargaba.
haka kawai taji fargaba ya tsarga mata.
hakan ya sa ta fito daga ɗakinta cikin sauri. Idanunta suka sauka a kan Habu dake ta faman mika wuya yana leƙen ban ɗakin!
da alama dai bai kai ga samin abin da yake so ba sai kokari yake ya kara tsawon sa ta hanyar kokarin hawa kan dutsen da ke kusa da gun.
Wani irin waro ido Mama tayi fushi gami da razana suka cika zuciyar ta.
yana jin motsi ya juyo da sauri, ganin Mama ya sashi saurin sauke ƙafarsa ɗaya daya ɗaura kan dutsen yana ƙoƙarin haurawa, ya sunkuyar da kai kasa yana sosa kai ya shiga kame-kame da waige-waige kamar me niman wani abun...
Mama ta dube shi cike da ɗacin rai tana faɗin
"Ashe baka da kunya da ɗa'a Habu!? wani daɗi ne zakaji dan ka leka mutum yana wanka a ban ɗaki?
nayi mata iyaka da ƴata idan na sake kamaka da makamancin irin wannan laifin bazan kyale ka ba! zan haɗa ka da mahaifin ka sannan na kai ka gidan mai unguwa yaja maka layi sakanin ku..."
Hansatu da ta fito daga cikin ɗakin ta jin maganar da Mama take yi, ta dafa jikin kofa tana faɗin,
"To kulu uwashsharriii!, yau kuma da wannan kike tafe, idan baki kai shi gidan me unguwa ba ni za muje da ke,
domin kin matsa masa da mummunan sharri da kazafi, haba sharrin ya ishe Ni haka dole na kawo karshen abin yau. kai dun uban ka zo ka wuce,
ka tsaya kamar shashasha ana jifan ka da mummunan sharri."
Habu ya zo ya wuce tsimi-tsimi.
Hansatu ta juya ta koma ɗaki tana cigaba da faɗin
"Maƙiya sai dai ku mutu ba dai jinina ba kam ni Hansatu.
Mama ta yi murmushin takaici tare da faɗin
"Ita rana bata karya hatsin da ka shuka da hannunka ita zaka girbe,
Ni da kai na zanyi wa tufkar hanci."
Rubaah dake ciki tana jin duk abin da ke faruwa. ta yi saurin sanya kayanta ta fito fuskarta cike da ɓacin rai,
amma Mama ta dakatar da ita ta ce ta ta shige ɗaki ta zauna, bata so taji bakin ta.
Rubaah ta shige ɗaki badun ta so ba
ta cika tab kamar zata fashe sai ƙwafa take da taunar lips.
Daga wannan ranar, barci ya ƙaurace wa idanun Mama gaba ɗaya.
Ta fara gane cewa ci gaba da zaman Rubaah a wannan gidan babban hatsari ne ga rayuwarta da kuma mutuncinta,
domin Habu ba zai taɓa haƙura ba a yadda take ganin take taken sa.
Ta shiga neman mafita na yadda za ta ɗaga ɗiyarta daga gidan cikin gaggawa.
Da farko, tunaninta ya tafi ne ga gidan yayan ta Rabi'u.
amma, tana tsaka da lissafin, sai gaban ta ya faɗi sosai. tunawa da kowaye matar yaya Rabi'u wato Habi.
hakan zai zama abu mai matuƙar wuya da sanyaya gwuiwa, a cigaba da zaman Rubaah a gidan.
Matar yayan Rabi'u wato Habi, mace ce mara mutunci da bata da kirki ko kaɗan, kullum cikin hargagi da cin mutuncin mutane take.
zaman da sukayi a baya da Mama ba daɗi ta jiba.
Bayan haka kuma, Rubaah ba ta da haƙuri ko digon ƙasƙantar da kai; muddin aka tsokane ta ko aka musguna mata, ba za ta taɓa jurewa ba sai ta nemi hanyar ramawa.
Muddin ta kaita can, gidan zai iya zama filin fama... "To mene ne mafita?."
tayi wa kanta tambayar tana kuma rafka uban tagumi...
"Assalamualaikum ba mutane ne a gidan?."
Aunty Ramlat ta fito daga ɗaki tana amsa sallamar.
"Ca nayi ba mutane a gidan, tun daga bakin kofar shiga nake ta kwaɗa sallam."
"Yi hakuri wlh bacci ne ya ɗauke Ni, sannu da zuwa."
Aunty Ramlat tayi maganar da fara'a kan fuskar ta, dan ta gani fuskar mai sallamar duk da sau ɗaya ta taɓa ganin ta, ranar da suka zo da Nafisat.
Nadiya ta karaso ciki.
Aunty Ramlat ta kawo mata abun sha ta zauna suka fara gaisawa.
Nadiya ta ce
"Biki nazo ta kusa da ku, na ce bari na karaso mu gaisa."
"Ai kuwa kin kyauta na gode sosai."
Nadiya ta ɗan zamo bakin kujera tana faɗin
"Bari na wuce yanzu dan ba Ni kaɗai bace ƴan biki suna jirata a mota, amma ya kuke ciki da me gidan ki kun daidaita ko mai ya wuce?."
Aunty Ramlat ta ɗanyi murmushi tana mike wa kamar yadda Nadiya ta mike.
"Ina fatan hakan."
cewar Aunty Ramlat.
Nadiya ta zuba mata ido na wasu daƙiƙu.
Ta fahimci akwai abubuwa da yawa da Ramlat ta zaɓi ɓoyewa.
"Uhum wlh mata irin ki suna bani mamaki, kina mace kamar ke ga kyau ga diri har yaushe zan zauna; damuwar ɗa namiji ya kashe Ni. ai idan ka biyoni shinfiɗa kake miji,
idan kayi zaman ka abokin zama, Hmm bari na je, samin number ki zan taimaka miki dan kina bukatar taimakon."
Aunty Ramlat ta karɓi wayar da take mika mata ta saka mata lambar ta, tayi mata sallama ta fita tana sanar mata zata neme ta....
kwanaki uku ke nan Mama keta tunanin niman mafita.
da yamma, tana zaune cikin ɗakin ta ta zurfafa da tunanin mafita.
tajiyo sallamar Ɗahare,
Hansatu na tsakar gida tana aiki. tun da taga Ɗahare ce ta murtuke fuska tana amsa sallamar ciki-ciki kamar bazata amsa ba tana daɗa murtuke fuska.
Ɗahara tasan ko waye Hansatu dan haka bata damu da yadda ta amsa sallamar nata ba, dan tasan ko waye Hansatu,
tayi mutunci ma da yau data amsa sallamar nata haka.
"Sannu da gida Hansatu."
Ɗahare ta faɗa bata jira amsawar Hansatu ba kamar yadda dama bata sa rai da amsawar nata ba,
kai tsaye ɗaki Mama ta nufa tana kwaɗa sallama daga bakin kofa.
Mama ta amsa tana yi mata maraba da zuwa.
Ɗahare a miniyar Mama ce kawance ne na tun yaranta,
gidan iyayen su kusa da kusa bacci ne kaɗai ke raba su a wancan lokacin,
wani sa'ilin ma suna kwana a gidajen junan su,
abin ka da da lokacin duniya na kwance kalau.
aure ce ya raba su kowa yakai shi unguwa daban-daban.
ta kwana biyu basu haɗu ba shine ta kawowa Mama ziyara domin ta duba lafiyar ta.
Mama ta tare ta da fara'a, bayan ta zauna ta ɗibo ruwa a kofi ta kawo mana.
kana ta zauna
suna gaisawa da tambayar bayan rabuwa.
a cikin hirar tasu Ɗahare ke faɗin
"Maryamu yau sai naga duk kin canza min ba irin yadda nasaba zuwa na same ki ba,
hakan ya tabbatar min da halin Hansatu gaba yake ba baya ba."
Mama ta sauke numfashi ta kasa ɓoye daukacin damuwar da ke dankare a ƙirjinta.
Ta kuma sauke numfashi a karo na gaba,
ta dubi aminiyar tata kana ta ce:
"Ɗahare damuwar da nake fuskanta a cikin gidan nan yanzu,
tafi fitinar Hansatu, domin Hansatu sai naga dama na kula ta idan ta tashi haukanta.
ina cikin wani matuƙar tashin hankali da tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.
Rayuwar Rubaah tana cikin babban hatsari a gidan nan.
Wannan ɗan Hansatun, wato Habu, ya sanya mata idanu sosai, a kullum yana yunƙurin son keta mata mutunci ta ƙarfin tsiya.
Ranar nan har leƙen ta yake yi a ban ɗaki da ta je wanka sannan na gano shi,
hakan ba farau bane ya daɗe yana aikata ire-iren hakan wani lokacin na kamashi da ido na,
wanda Allah ya ɓoyewa gani na kuwa shi ya barwa kanshi shina,
akwai ranar da cikin dare su Zaliha basa nan sun je kwana gidan kakarsu,
Ya shiga ɗakin, ihun ta dana ji na fito shima yaji tsoron ihun da ta masa ya buɗe kofar gida ya gudu,
Duk da ta ce min bataga fuskar ko waye ba, amma zuciyata na bani shi ne,
idan na taso nayi magana a kan rashin ɗa'ar da yake yi, mahaifiyar sa tayi tsalle ta dire ta ce sharri nayi masa, na rasa ta in da zan ɓullu wa lamarin."
Ɗahare ta zaro idanu cikin firgici ta ce,
"Subhanallah!, wannan ai babban lamari ne.
Me yasa ba za ki cire ta daga gidan nan ba?, cigaba da zaman ta a gidan nan kamar barazana ce ka rayuwar ta, duk da dai zamanta a kusa dake shine samin kwanciyar hankalin ki.
to amma fa a wannan gaɓar kaucewar ta shine mafita ga tseratar da rayuwar ta,
dan waɗan nan yara ƴan shaye-shayen da kike ganin su.
sukan iya yin komai domin cimma burin su."
Mama ta jinjina kai cikin takaici ta ce, "Shi nake ta faman lissafawa tun jiya. Na so na kai ta gidan Yaya Rabi'u, amma ina ganin zaman Rubaah da Habi matar Yaya Rabi'u abu ne me wuya. Habi tana da wuyar sha'ani.
Sannan kuma ke kanki kin san halin Rubaah, ba ta da haƙurin jure raini ko kaɗan; muddin Habi ta taɓa ta, to kuwa ramawa za ta yi,
Rubaah bata da hakuri musamman a kan gaskiyar ta,
zaman ta da Habi abu ne mai wuya,
kin san nima hakuri nayi ta yi da ita har Allah yasa muka rabu lafiya,
Rubaah kuwa ba zatayi hakurin ba,
zaman tasu ba zatayi kyau ba ƙarshe Rubaah tayi ta mata tsiwa da rashin kunya,
cigaba da zaman ta a gidan nan kuma barazana ce ga rayuwar ta tabbas kamar yadda kike faɗa.
domin wannan yaro yadda naga ya matsalta da bibiyarta, ina tsoron a bin da ka iya faruwa watarana, bana fata,
amma zuciyata tana tsinkewa,
Daga baya na yanke hukuncin kai ta garin baban su, gun dangin mahaifan su, na ɗan watanni,
hakan kuma na nufin karatun ta zai tsaya ke nan, wlh Ɗahare na rasa yadda zan ɓullo wa lamarin, kullum a cikin fargaba nake."
Ɗahare ta kuma sauke numfashi a karo na sau ba adadi sannan ta ce,
"Lallai dole ki kasan ce cikin fargaba Maryamu, domin tarbiyyar ɗiya mace abu ne gaggarumi mai matukar girma,
Musamman a wannan lokacin da balaga ya kawo kai."
cike da tausaya wa halin da Mama ke ciki ta cigaba da faɗin
"Kin ga ni yarana duk maza ne, kuma duka-duka ɗakunan mu guda biyu ne kin sani, wlh da yau sai na jira Rubaah ta dawo daga makaranta na tafi da ita,
amma bazai yiwu na ɗauke ta ba,
bari na koma muyi shawara da babban su mugani, in yaso su mazan za'a nima musu ɗaki ko na alfarma ne a waje, in yaso ita sai ta rika kwana cikin ɗakin nasu."
Mama ta yi shiru zuciyarta cike tab da tunani iri-iri.
ta sinkayo muryar Ɗahare tana faɗin
"Bari na je gidan duk yadda muka yi zan dawo na sanar miki."
Sai sannan Mama ta ɗago idanunta data tafi tunani taga har Ɗahare ta mike ta ce
"To na gode sosai Ɗahare."
tayi mata rakiya har kofa sukayi sallama ta tafi........!
Mommyn Twins ce