AL'AJABIN SO

9

by @gureenjoh

AL'AJABIN SO

     (heart touching story)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

*Diddigar ƙaya... Paid*

And now..

*AL'AJABIN SO*


*BOOK 1*

    *Page Nine*


Haki take saki tana juya bayanta ganin baya binta yasa ta dafe kirjinta, in wannan ɗan daban ya riƙe ta ai kashinta ya bushe, seda ta daidaita kanta kan ta kutsa cikin parlorn Maami ta gani zaune idanunta da hawaye, da sauri ta isa ta duƙa a gabanta kaman zata saki kuka aka ce zuciya tana son me kyautata mata jin matar take kaman Ummi tace

"Maami me ya faru kike zub da hawaye?" 

Shiru Maami tayi, babu me fahimtar halin da take ciki se uwar da Allah ya jarrabe ta da ɗa irin Mukhtar, ace kana ji kana gani yaro ya nemi gagararka? Allah kaɗai ya san me ya je ya sha ya zo yake mata rashin kunya akan matarshi, duk zafinta akan muktar ne tana da sanyin hali da tausayi shima kuma da farko ta bi dashi da lallami da nasiha saide abun yaci tura, ganin hakan mahaifinshi ke mishi yasa ita ta karɓi ragamar zama uwa da uban saide duk a banza man kare, zafin dake kirjinta ya wuce misali bata fata ta mutu ba tare da ta ga chanzawar Mukhtar ba, tana mishi tsoron fushin ubangiji tana kwaɗaita mishi rahamarsa...


"Maaami"

Alaya ta kira sunan hawaye na cika idanunta.

"Babu komai ɗiyata, je ki cire uniform ɗinki kizo ki ci abinci"

Gudun musu da Maamin yasa ta miƙe ta tabbatar be wuce muktar bane matsalar Maami, saƙe-saƙe kawai take har ta watsa ruwa ta sauko ta ci abinci bata samu Maami ba kila tayi wurin Alhj, wayanta ta ɗauko ta fara texting ummi sun jima suna magana kan ta miƙe ta shiga kitchen, ita tayi musu girkin daren ranar sbd gujewa tunanukan Muktar da ya addabe ta ta rasa me take ji a game dashi, tsoro ne, tausayin Maami da halin da yake jefa kanshi da fushinta ne ko zeal na son ganin ta kyautatawa matar da duk duniya itace mace ta farko da ta fara kyautata musu a rayuwa?


"woww daughter haka dama kika kware a girki?"

Maami tayi maganan tana gyaɗa kai, murmushi me sauti kawai Alaya ke yi, Alhj ma yayi ta yabon girkin shi dae Mukhtar ci kanku be ce musu ba.


Bayan gama cin abincin nasu ne Alhj ya mike yayi sama yana cewa

"Hajiya in ganki mana minti biyu"

Miƙewa tayi tabi bayanshi yayinda Alaya ke tattare kwanukan, tana kai na karshe zata juyo kenan taji tayi mugun karo da mutum, kafafunta suka Harɗe baya baya tayi zata faɗi yayi hanzarin riƙota, hannunshi yasa ya kama nata hannun ya matse kara ta saki tana me duƙawa kaɗan 

"Zafi Don Allah"


"zafin dama nake so ki ji, wato ba zaki ji magana ta ba ko?"


Hawaye ta fara sbd yadda yake murde hannun da tsantsar mugunta

"Kayi hakuri"

"ba hakuri nake son ji ba, sbd bani dashi kwata-kwata, abunda na sani shine kiyi gaggawar bin umarnina ko ki cigaba da karawa kanki laifukan da na rantse sai kin biya su ɗaya bayan daya"


Idanunta a runtse hawaye wani na bin wani, ganin azabar yayi mata yawa ne yasa cikin kuka tace 

"Na amince wlh zan mata mag..."

"MUKTAR"

Maami ta katse shi tana jin kaman ta rushe da kuka ko ta rufe shi da duka ko zata ji saukin abunda take ji akan shi.


"Ga nan irin abunda nake tsoron yasa na ki baka ita, amma zan kai maka ita cikin wani sati sai ka shirya ko ka riƙe ta saboda Allahn da ya halicce mu ko kuma ka zalunceta, Allah baya bacci kuma baya barin zalunci kuma ina faɗa maka kaji tsoron Adu'ar wadda aka zalunta don bashi da shamaki, fice ka bar min gida!"

Ta karashe da karfi tana nuna mishi kofa.


Tsayawa yayi yana kallonta sama da mintuna biyu kan ya wuce yana gunguni, da sauri ta ƙaraso wurin Alayar tana rike hannun tace 

"Sannu daughter, ya ji miki ciwo ko?"

Girgiza kai tayi tana me Miƙewa tace bari ta shiga ɗaki.


Da tunanin tarewar ta cinye satin ko fahimtar abin da ake yi a class bata yi tsabar tsoro, amma ya zata yi abu sede in ba'a sa mishi rana ba sai ga ranar ya zo, sisters ɗin ta guda biyu ta kira akan su rakata gidan ta don already an gama haɗa mata komai da komai har akwatunan an riga da an kai chan, tana kuka tana komai aka kaita gidan muktar a chan suka barta bayan doguwar nasiha.


Ta jima zaune bisa gadon har ta gaji ta kwanta bacci ya fara fusgarta taji ana bugu kaman hauka, a tsorace ta tashi tsaye tana zare idanu ganin tsayuwar ba zai mata ba gashi sai karuwa bugun ke yi yasa da sauri ta fita, duba agogon parlorn tayi karfe ɗaya saura mintuna.


"Waye ne?"

Ta faɗa muryarta na rawa 

"Wayewa! Ke dallah ki buɗewa mutane kofa in zaki buɗe.."

Muryar mace taji, a tsorace ta buɗe yarinyar na sarkafe da hannunta a kwankwason muktar ɗayan hannunshi na zagaye da kafaɗarta, ko be ɗago ba ka san ba karamin buguwa yayi ba, da sauri Alaya ta koma baya tana kama bakin ta da hannayenta, kukan sai ya ƙi zuwa sai idanu take bin su dashi har yarinyar ta shigo dashi tana karewa gidan kallo tana taɓe baki.


"Ke wato kin raina mutane ko? Waye ya baki iz....nin rrrrufe kofar nannn"

Cikin tsantsar maye yake maganar yana nuna ta da yatsa.


Bata ce musu komai ba..

"Kai muky wace irin dakikiya ka auro ne? Kina kallon mu ba zaki kama shi ki kai shi ɗaki ba?"


A tsorace taje ta fara kokarin riƙe shi yarinyar tayi tsaki tace 

"Muky am sleepy, good night"

A maimakon Alaya taga ta fice sai gani tayi tayi wani ɓari na gidan wanda ba inda Alayar ta fito ba, tana tunanin tana layi sbd yadda yake sakar mata jiki shima kuma Layin ne yake yi, a haka suka nufi ɗakinta hawaye na wanke mata fuska warin giyar kamar zai kashe ta, galau galau suka yi kaman zasu faɗi kokarin tare shi take sai kawai taji amai a jikinta, wani irin tashin zuciya ne ya kamata, hawaye wani na bin wani haka ta jefa shi kan gadon bayan ya gama amaye mata jiki, bata iya ganin amai ba hakan seda yayi sanadiyar nata aman babu komai cikinta, tayi ta wahala a bayin kan ta fito tana kau da ido ta samu ta kwashe.


Kayanta ta cire tayi wanka tana fitowa ta ganshi zaune yana kallonta.


"Ke zo nan!"

Har lokacin mayen be sake shi ba

"na'amm"

Ta ƙasan jajayen idanunshi yake kare mata kallo kan yace 

"kika bari na maimaita sai na lahira ya fiki jin daaɗi"

Cike da tsoro take takowa ko kan ta ƙaraso ya fusgota kaman wata ƴar tsana haka ta faɗa kirjin shi, toshe hancin ta take sbd gudun sake amai warin giyar gigitata yake ga tsananin tsoron abunda zai iya mata ko kan ta gama tunani taji hannunshi ya fara yawo a jikinta, idanunta ta zazzaro cikin sautin kuka tace 

"Me...menene Ya muktar?"


"Hakkina da kuka hanani zan karɓa"

Girgiza kai take da karfi, tana kokarin Miƙewa ya matse ta yana cusa fuskanshi wuyanta, gigitaccen kuka ta saki ta fara cewa 

"A'a don Allah, Don darajar Allah ba yau ba, ba cikin wannan hali ba! Karka zaɓi tarayya dani da kazantar abubuwa dayawa a jikinka... Ya....ya Mukhtar aure fa muka y..."


Bakinta ya rufe da nashi ta datse nata tana kakari sbd yadda abubuwan maye ke tashi a cikin bakin shi, kokarin kwatar kanta take Dukda ta san karfi ba ɗaya ba shima kuwa nuna mata ya fara yi cewa karfi ba ɗaya ba, dambe ne ya kaure a tsakaninsu, duk kokarin da tayi wurin ganin be samu abunda yake so ba ta kasa dakatar dashi, tayi kuka kaman zata cire ranta ta jefar, kirjinta yayi matukar nauyi, numfashi yayi mata wahalar shaƙa, ji tayi inama ta mutu a lokacin, be saurara mata ba seda ya samu natsuwa ya zube a kanta ya fara baccin hauka, nauyinshi ya kara mata nauyin kirjin da take ji, idanunta na kallon seiling yayin da hawaye ke ganganrawa gefen fuskanta wani na bin wani ta fara cewa cikin jiggata


"Ya Allah kaine Allah, Allah kai kaɗai ka san dalilin hadani da Mukhtar a matsayin miji, Allah kana gani kuma na san kana ji na, ka bani haƙuri da juriya a kanshi ya Allah, idan kuma mutuwata ce  hutu daga wannan radadin zuciyar ya Allah ka ɗauki raina a yanzu ya rabbi, idan kuma a rubuce yake a cikin kaddarata Ya Allah ka shiryar dashi ka kuma bani ikon yi mishi biyayya...."

Kuka me karfi ta fashe dashi ta saka ɗan karfin da ya rage mata ta fara kokarin ture shi, saide ta kasa duk yadda ta so tashi ta kasa, kaman yadda taga rana haka taga dare tayi kuka har ta rasa hawaye, jikinta ya dauki zafi, numfashinta ya fara nisa sbd tsananin ciwon da zuciyarta ya ɗauka, cikin tsananin rauni cike da ban tausayi take cewa chan ƙasa ƙasa

"Ummina ashe ba zan sake ganinki ba? Ashe ba zan taɓa jin muryarki a zahiri ba? Ashe ba zamu sake saduwa da ke ba! Ki yafemin in n...na taɓa saɓa miki, ummi ki yi min Adu'a zan tafi in samu Abbana....."

Ta karashe cikin jan wani wahalalliyar numfashi.


Mukhtar kuwa Ba shi ya farka ba seda gari yayi haske tarr, hantsilawa yayi gefen ta yana buɗe rinannun idanunshi ya zuba mata, ko motsi bata yi ba, fuskanta ya kurawa ido yayi wani haske yayi fayau, da sauri ya miƙe zaune ya ɗaga hannunta se yaga ya koma ya faɗi yaraf, kanshi ya ɗaura a kirjinta babu bugun zuciya..bai san sadda ya dirko daga gadon ba ya ɗauki boxers ɗin shi ya saka babu abunda yake tsoro se Maami, ya san idan har ya kashe yarinyar nan ko da me yake takama sai tayi shari'a dashi...


Da gudu ya kaita mota bayan ya sa mata riga wacce be tantance bata da tsawo ba seda suka shiga asibiti, a asibitin ma da gudu aka karɓeta zuwa emergency, likitan da ya iso cikin hanzari ya fara examining ɗin ta, girgiza kai yayi, yana saurin riƙo hannunta ya fara jin pulse ɗin ta....


"YA RABB I'M AFRAID WE LOST HER..."

Ya furta yana runtse idanunsa.