10
by @gureenjoh
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Ten*
"Dr Abdul what is the situation?"
Wani Babban likita ya ƙaraso yana yiwa wannan doctor da ya runtse idanu tambayar sanin cewa shi wannan intern ne kuma be gama gogewa a aikin ba.
Kallon Mukhtar dake tsaye ya zurawa gangar jikin Alayah idanu yayi yana cewa
"wannan fa? What is he doing here?"
Muktar da duk tunanin shi na ga Irin badakalar da zasu yi da Maami, sai kuma tunanin irin garɗin ni'imar da ya kwasa daga Alayah ace har ta mutu? Sau ɗaya kawai fa yayi?..
Idanunsa ya maida kan karamin likitar dake cewa babban
"her heart stopped beating doc, babu wani pulse dake harbawa a jikinta"
Maida kallonshi kan Mukhtar babban likitan yayi yace
"Me ya sameta? Me ke damunta?"
"blood?"
Ya faɗa ba tare da ya jira amsar Mukhtar da har lokacin yake tsaye ba, kallon kallo suka yi suka sake kallon muktar zuciyoyinsu na bijiro musu da abubuwa daban daban..
"Dr is she alive or dead?"
Yayi tambayar yana kallonta still.
"Meke damunta? Did you raped her? Gsky ba zamu iya taɓa ta ba sai da Police, this case is serious"
Tsawa ya daka wa doctorn
"she's my fucking wife, do something if she's still alive tana da congenital heart defect..! Do something before Its too late"
Jin hakan yasa doc saurin bawa nurses dake tsaye cirko cirko umarni, a take suka turo automatic external difibrillator, aka zuba mishi cream din ya dirza kan ya ɗaura mata a kirji, fusga tayi daga ita har gadon suka sake komawa yaraf, cikin gogewa a aiki ya sake murzawa ya danna mata ta kara jan numfashi tayi sama ta dawo kasa, a na huɗu ne ta ja wani dogon numfashi wadda ya dawo mata da numfashinta gabaɗaya, taimakon gaggawa suka fara bata yana kallon nurses biyu yace
"We really need Dr Abdulrahman and Dr Eshrat here Its urgent!"
Da gudu suka fita, shi kuma ya cigaba da abin da yake.
Kaman mintuna goma sai ga wasu doctors guda biyu nurses din na biye dasu, rufuwa suka yi a kanta suka fara bata taimako barin ma Abdulrahman da ya kasance kwararren likitan zuciya, seda ta daidaita kan Eshrat dake gynae ta duba jikinta da sauri ta runtse idanu tana me Miƙewa tsaye, idanunta ta maida kan Muktar dake tsaye ya zura musu idanu bazaka tantance halin da yake ciki ba, a ranta ta raya dole hakan ta kasance daga kallo daya da ta mishi ta san yana apawa, ga ingarman jikinshi da ya watsawa tattoos na ban mamaki, cinyoyinshi dake waje sbd wandon jikinshi ƙarami ne a mummurɗe.
"She needs stitches" ta faɗa tana kallon likitocin, Abdulrahman da ya gama daidaita mata bugun zuciya da taimakon Allah yace
"She also need an urgent heart surgery, the heart is so weak and fragile"
"yanzu da wanne za'a fara?"
Likitan farko ya faɗa cikin tausayinta tana kwance banda oxygen dake taimakonta da numfashi da zaka iya cewa gawa ce kai tsaye in ka kalleta.
"Dr Eshrat yi aikinki, before then relatives ɗin ta su yi duk wani abu da ya kamata har da blood da komai we will prepare for the surgery"
Yana kai nan ya fice.
Juyawa Drn farkon yayi wadda suke kira da Dr Ahmad ya kalli Mukhtar yace su je waje, ficewa suka yi zuwa office nashi, jallabiyarshi ya ɗauka ya miƙawa muktar wadda sabo ne tsaraba ce ma aka kawo mai sai ya mance a office ɗin, da wani irin kallo muktar ke bin jallabiyar shi fa ba sa irin abubuwan yake ba.
"Babu daaɗi kana yawo a kan patients haka, you need to wear this ka zauna in maka bayani"
Karɓa yayi ya bare a ledar ya saka, coffee Brown ce me sulɓi, wani irin amsarshi yayi shi ko se taɓe baki yake yana tsaki ƙadan kaɗan.
Bayani likitan ya fara mishi sai ya nuna idan kudi suke bukata ko nawa ne ze iya bayarwa ayi komai, tsoronshi Allah tsoronshi Maami kuma baya so yarinyar ta mutu don yana da buruka a kanta, yana so ya nunawa abokanshi daban daban cewa ya kere sa'a, yana kuma kwadayin sake ɗanɗanata.
Wani paper Dr Adam ya mika mishi bayan dogon typing, Miƙewa yayi ya fice zuwa reception anan ya biya duk abunda ake bukata, ko jinin ma seda wata nurse tace ko za'a gwada nashi yace a'a a saya a blood bank, bayan ya tabbatar babu wani abu ya fice abin shi.
Gida ya dawo yayi wanka ya sa kananun kayanshi as usual wando baya kaiwa ƙasa in ko ya kai to irin wasu mahaukatan crazy jeans ne da suke nan kaman palazo, da karamar riga marar hannu, daga nan ya leka Rita buduruwarshi bata nan ya tabbatar tana club don haka chan ya wuce, hayaniyar ganinshi ta hautsina club ɗin a take ya fara rabar da kyaututtukan giya sai rawa en mata suke yana shafasu cikin kwarewa da barikanci.
A asibiti kuwa aiki aka mata dukda anasthesia da take kai da kuma rashin hayyaci daga ka kalli fuskanta zaka san tana jin zafin stitches ɗin har aka gama, aka fara shirya batun surgery babu kowa nata aka shiga da ita theater, seda suka shafe sama da awanni bakwai kan suka fito, Alhamdulillah aiki yayi Kyau atleast zata ji saukin ciwonta ba kaman baya ba Dukda ba warkewa gabaɗaya tayi ba, abun mamaki har lokacin mijin be dawo ba kuma babu wadda yazo a family.
Aminity da ya bada umarni after the surgery nan suke so aka turata babu abunda take sai baccin wahala da gajiya, wasa wasa har dare sede nurses su zo su duba ta su tafi haka ta kwana be dawo ba, Washegari da misalin karfe goma na safe ta fara buɗe idanunta cike da kokonton kasancewar ta a duniya har a lokacin, ɗakin take karewa kallo a hankali hankali se ta fahimci asibiti ne nan ɗin, ga wasu na'urori jikinta, lumshe idanunta da suka faɗa sossai tayi ta sake buɗewa daidai lokacin wata nurse ta shigo ganinta ido biyu yasa ta koma ta kira Dr.
Checkup suka yi mata sossai kan suka rage na'urorin jikinta, Dr. Eshrat tace
"Fatima..."
Kaman yadda ta gani a rubuce a jikin file nata, da idanu Alaya ta bita.
"Waye ne ya kawo ki asibiti? Ina nufin me matsayinsa a wurinki?"
Tayi tambayar ne sbd su tabbatar da zancen Mukhtar kar karya ce ya musu gashi har yanzu yaki dawowa wani miji ne ze bar macen dake sharafan mutuwa ta yini ta kwana ta kuma hantse, har a mata surgry me hatsari irin na zuciya be dawo ba kuma ba aike?
Ta san mutum na karshe da ta kasance tare dashi Mukhtar ne, runtse idanunta tayi da karfi tana jin kuka na son zuwar mata tuna irin azabar da tasha a daren, a hankali cikin rawar murya tace
"mi..jinaa"
Ajiyar zuciya suka sauke me karfi, Dr Abdulrahman yace
"kina da iyaye a raye ko wasu Ƴan uwa?"
Cikin rawar murya ta sake cewa a raunace
"Ina da mahaifiya amma ba zan iya gayamata wannan hali da nake ciki ba, ku kira min mahaifiyar mijina"
Da mamaki suke kallonta, taya mahaifiyar mijinta zata iya taimakonta alhali ɗan ta ne ke da kaso mafi girma cikin abunda ya faru da ita?
Dr Ahmad ne ya karɓi Layin Allah ya sa ma ta riƙe sbd numbern special number ce, kira yayi cikin hikima ya sanar da ita komai nan take cikin tashin hankali tace gata nan zuwa.
Ba'a yi mintuna Talatin ba sai ga Maami, hawaye tayi ta zubarwa na tausayin Alayah wadda seda ta saka Alayar kuka, ƙanwarta ta kira tasa ta dafa mata abinci irin na marar lafiya ta kawo mata yanzu, Alhj hammad ta kira ta sanar dashi halin da ake ciki, sam ta ƙi ambaton sunan muktar sbd gudun mummunar kalma akan shi, iyayenmu mata kenan(ki kasance me gudun mummunar kalami akan yaron ki musamman idan ya kuntata miki sbd duk maganar da zaki yi a lokacin walau sharri walau alkhairi Allah na iya amsawa a take).
Har misalin sha ɗaya da wani abu sistern ta ta zo da abincin, da taimakon Maami tayi brush ta taimaka mata ta fara bata kakkauran shayin kan taci dankalin turawa da aka sarrafa shi cikin kayan ciki(offals) kaɗan, magunguna nurses suka zo suka bata, da wasu Iv injections aka sake ɗaura mata drip, wayan Maami ne yayi kira a hankali ta duba sunan se ta lumshe idanu kana ta sake buɗewa ta miƙe ta fice.
Sama da kusan mintuna Talatin ta dawo, bayanta Alhaji hammad ne, shi karan kanshi be ji daaɗin abunda Muktar yayi ba, barin ma watsar da ita a asibitin da yayi yanzu da bata rike Layin Maami ba fa? Sede fa Dukda haka ba wai ze mishi faɗa bane ko ya nuna mishi rashin kyautawarshi tana bacci don haka be zauna ba ya fice, a harabar asibitin ya tsaya ya kira Layin muktar, dagawa yayi cikin alamun baya ma cikin natsuwar shi.
"Kai kuma haka ake yi? Toh wlh ka tanadi abunda zaka kare kanka dashi a wurin maaminku ni kam ba ruwana"
A ɓangaren Mukhtar wara Red eyes ɗin shi yayi yace
"What? Maami tana asibitin? Ayyaa Abba duk bala'i karka bari ta rabani da yarinyar ba zan iya kyaleta ba"
"karka damu ai tunda kaine ke da igiyar aure a hannunka zancen maaminku ta raba ku be taso ba, amma fa ranta ya ɓaci kuma ta zub da hawaye sossai"
Cikin rashin nuna damuwa da hawayen mahaifiyar tashi yace.
"Maami kuma hawaye na mata karanci ne Abba? Bari dae ina wani abu zan shiga asibitin zuwa anjima, duk bala'i babu zancen rabani da Fatima daga Asibiti kuma se gidana"
Alhj hammad na gyara zamanshi yana kallon gefen titi sbd driver dake ja a natse yayi murmushi ya katse wayar, Abban Meelah ya kira ya sanar dashi an yiwa Alayah aikin zuciya sede be wani yi Adu'a ko nuna damuwa akan ciwon ba, kuma yace ba ze iya gayawa mamarta ba sbd baya so hankalinta ya tashi, sallama suka yi Alhj hammad na tayiwa Alhj Alhassan kirari.
Mukhtar be tashi shiga asibitin ba sai dare, Maami ta tafi sai Aunty rukayya da me aikinta da zata kwana asibitin, an ɗan ɗaga gadon Alayah na kwance a kishingiɗe idanunta a lumshe amma ba bacci take ba, tana masifar kewar umminta gashi ko sanin halin da take ciki ummin bata yi ba, wayanta na chan gida bare tayi mata message ko bata faɗa mata ba ta ji lafiyarta, kai tsaye ya shigo ɗakin ba tare da ya damu da sallama ba tunda yayi knock.
"Barka da dare Aunt"
Ya faɗa idanunshi na kan Alayah da takara runtse idanu gabanta na tsananta faɗuwa har jikinta na ɗaukan rawa.
Aunty rukayya dake ta kallonshi ta kasa cewa komai, kafada ya ɗaga yaje ya tsaya gaban gadon yana kallonta, sarai ya fahimci ba bacci take ba baki ya sake taɓewa, abunda ya hana shi zuwa asibitin kenan don be san uban da zs tsinana mata ba tana wannan abu kaman taga dodo, tsaki yaja ya juya ya fice abunshi a cewar shi yana da abin yi.
Haka ta shafe kwanaki goma curr a asibitin duka duka zuwanshi biyu shima se chan dare lokacin me aikin dake kwana da ita ce kawai, Maami tayi kokari sossai wurin ɗawainiya da ita hakan yasa dole ta koyawa kanta shanye damuwarta saboda damuwar matar, fargabarta ɗaya yadda zata koma gidan muktar, zata iya kuwa? To in bata koma ba ina zata je ga Abunda Abban Jameelah ya faɗa mata, sannan kuma bata Yiwa Maami kara ba Dukda har lokacin Maamin bata ce mata komai akan abunda ya farun ba.
Yau da take cika kwanaki goma sha biyu muktar ya zo da misalin karfe 12 na dare kai tsaye office na Dr in charge ya wuce
"Ina so ka bani takardar sallamar matata"
"wani irin sallama by this hour? Kuma ai tana da sauran medication da checkups"
"Yau bazata ƙarasa kwana a asibitin nan ba, duk kuma abunda ya saura ko ma menene zata zo daga baya"
Ganin fa baya ma cikakken hankalinshi kuma ze iya hautsina musu natsuwa anymoment sbd yanayin shi yasa babu yadda likitan ya iya duk yadda ya nuna mishi ya barta sai ko safiya ce ya ƙi haka ya bashi sallamar.
Tana kwance bacci ya fara ɗaukar ta bayan doguwar hira da idanunta suke yanzu kawai taji Shigowar mutum, da farko ma ta zata nurses ne sai taji muryarshi yana ce mata
"ke tashi mu tafi"
Mummunan faɗuwa gabanta yayi, taji gabaɗaya numfashi na shirin barin jikinta, ko kwakwaran motsi bata iya yi ba bare ta buɗe idanunta har ta fahimci shin shi ɗin ne ko ba shi bane, kuma da ita yake yi ko da wata....
"Kika sake Kika bari na maimaita kaina wallahi sai na lahira ya fiki jin daaɗi.."