AL'AJABIN SO

12

by @gureenjoh

AL'AJABIN SO

     (heart touching story)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

*Diddigar ƙaya... Paid*

*Rubutu a kan ruwa... Paid*

And now..

*AL'AJABIN SO*


*BOOK 1*

        *Page Twelve*


*Sometimes idan muna karanta labari mu kan ji kaman almara har mu kan yiwa kawunan mu tambayar cewa anya hakan na faruwa? Wannan Page is a dedication to waenda suke cikin ibtila'in auren mashayi, masu haƙuri da juriya da kaddararsu. Sadaukarwa ce ga uwar da Allah ya jarraba da haihuwar ɗa wanda jarrabawarshi ta zama shaye-shaye, Allah kana ji kana gani ya Allah ka shirya mana zuri'a, ya Allah ka kara musu haƙuri da juriya, ya Allah Alfarmar annabi da alqur'ani ka musanya musu kaddarorinsu daga baƙi zuwa fari* 

(Ni kaɗai na san what i went to wurin rubuta wannan Page, a painful True life story) 


A wurin wani wahalallen bacci ya kwasheta ba ita ta farka ba sai da aka kira assalatu, Miƙewa tayi ta shige toilet ruwa ta fara watsawa kan ta ɗaura alwala tana jin yanda zuciyarta yayi mugun nauyi haka dae tayi sallah ta nemi magunguna ta sha kan ta kwanta, bacci ta sake yi ba ita ta fito ba sai karfe tara sanye da hijabin da tayi sallahn asuba dama da shi ta kwanta, a parlorn ta tsaya tana kallon yanda suka maida shi, kyamar parlorn gabaɗaya ya shige ta, haka dae ta daure iya dauriya ta soma tattare parlorn har ta gama ta share ta fesa air freshner kan ta nufi kitchen don neman abinda zata ci.

     Bata gama dafa indomie din ba taji motsi, da sauri ta juya tana kallon kofan kitchen ɗin a tsorace sai suka haɗa idanu, babu kaya a jikinshi daga shi sai karamin wandon jeans, daga dukkan alamu har lokacin ba wai ya dawo daidai bane daga abubuwan da ya ɗurawa kanshi.


"ke wato ma ina wasa dake ko? Ni zaki dizga? U are very stupid...don ubanki sau nawa na buga miki kofa kika barni shanye ana min dariya?"


A tsorace take matsawa ganin yana kokarin cire belt din jikinshi muryarta na rawa tace

"Kayi haƙuri, don Allah ka saurareni ya Mukhtar..."

Tun kan ta sauƙe sunan ya fara zuba mata belt ɗin, be ji tausayinta ko na minti ɗaya ba sai da yayi mata duka har da kafa kan ya juya ya fice yana cewa gobe ta kara...

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Innalillahi wainna ilaihi rajiun" abinda take ta nanatawa kenan tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta ta miƙe ta nufi daki bayan ta kashe gas ɗin indomien da bata ci ba kenan, tana hawaye tayi wanka idonta ɗaya yayi jajazir jini ya kwanta gefen fuskanta ga shatin belt nan har kusan uku jikinta yayi wani irin Red abin ka da farar fata.


Cikin uniform ta shirya don ta yankewa zuciyarta duk wuya zata yi karatu ko don nan gaba ta iya tsayuwa da kafafunta idan Mukhtar be yi sanadin ta ba, ji take kaman zata mutu kwana kusa a yanda take jin kirjinta da ciwonshi da ya dawo sabo fiye ma da na baya, tafin hannunta ta ware ta ɗan zubawa idanu kan ta gimtse tana sake ajiyar zuciya me nauyi na tsantsar damuwa a haka ta tafi makarantar, dayake bata kula kowa babu wanda ya damu ya tambayi me ya sameta ko ya akayi ta ji rauni har aka tashi bata iya ta ci komai ba.


Bayan ta dawo ta haɗa custard ta sha ta sake shan magunguna kan ta janyo wayanta don jin lafiyar mahaifiyarta.


Wani irin sabon baabin wahalar rayuwa ne ya buɗe mata, Mukhtar bashi da tausayi ko imani ko na miskala zarratin, ga zafin zuciya matukar ya sakata yin abinda ya saɓawa addininta in ta ƙi haka yake mata dukan mutuwa, marin shi a gareta ya zama kaman man shafawa da da matukar wuya a wayi gari a yini be kai hannunshi jikinta ba, ga bautar yi masa girki da abokansa wanda ba kadan ba idan suka tashi zuwa, a kullum se sun nemi ganinta ita kuma bata fasa ƙin fita ba ta kulle kofan ta gam shi kuma da safe ya mata dukan mutuwa, ko yaushe in yana bukatarta haka ze je mata walau yana hayyacinshi walau yana cikin maye, duk wani alwashi da ta ci a farko akan Mukhtar bata iya ta soma tabuka komai ba don gani take har Abada Mukhtar baze chanza ba, bata da lafiya sossai don zuciyarta ya sake rauni kan rauni sede babu wanda ta faɗawa haka take lallaɓawa kuma take karatu.

     Yau suke gama waec ta yi jamb tun sati biyu da suka wuce, Alhamdulillah sun gama lafiya da Fatan jiran sakamako me kyau, a koyaushe tana jinjinawa Maami da irin jajircewarta a kanta Dukda wani sa'in idan muktar ya mata wani abin sai wata zuciyar ta raya mata dole ne ai Maami ta so ta don ta san zama da ɗan ta sai wanda iyayenshi suka sallama, da sauri kuma sai ta yi a'uziyya ta kawar da tunanin don ta san Maami da zuciya ɗaya take mata hidima kuma take tausayinta, babu wanda ze ganta ya shedata sbd wani irin rama da tayi a watannin da ta durfafi yi gidan muktar, tayi wani irin haske har kana ganin kalar green green a jikinta in kana kallonta, idanunta sun kara girma da haske haka hancinta ya sake fita zirrr, bata wani ado bare kwallaya in tayi wanka ta shafa mai ta sa kaya shikenan.


Yanzu da ta gama Waec zaman gidan ya zame mata kaman wacce take rufe a prison na karkashin ƙasa, Rita a gidan take rayuwa daga parlor zuwa kitchen duk nata ne yayinda Alaya ke ɗaki a koyaushe abinda ke fitar da ita yunwa sai kuma idan shine ya zo ya sakata girki amma bata yi ta ajiye kam don ba lallai ma wasu ranakun yana kwana a gidan ba, kaman yau, gabaɗaya yinin tayi shi ne ba daaɗi sbd hayaniyarsu da suka yini yi bidiri kala kala a gidan, kaman wani kwarya kwaryar lifaya ne suke yi a gidan, daga inda take a ɗakinta babu irin warin ababen Mayen da bata ji, tana dukunkune kan gado, tana bukatar shan sassanyar iska marar surki irin wannan, ji take kaman zata mutu ne sbd wari da tashin zuciya.


Kofan ta da ta kulle ne yinin ranar gabaɗaya don ko abinci bata iya fita ta nema ba taji ana bugawa da karfi, chan ta jiyo dakakkiyar muryarshi yana kiran ta da sunan da shine ya raɗa mata wato 

"ke! Ke!!"

Gabanta ya faɗi, zuciyarta ya hau tseren bugu me zata mishi a wannan yanayi da yake ciki? Kallon jikinta tayi idan tana son lafiyan jikinta kuma abu me sauƙi shine ta bude kofan taji me yake tafe dashi sede tsoro kaman ta narke ta ɓacewa gani da sauraranshi ya lullubeta, jin kaman ze ɓalla kofan ne yasa ta sanya kafafunta ƙasa kaman wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi kofan hannunta ɗaya na kan zuciyarta da bugawarshi har ya shafi numfashinta, hannunta na kakkarwa ta miƙa ta buɗe, banko kofan yayi sai gata gabanshi ya fisgo ta riƙo na mugunta yayi mata 

"yarinya in ba zaki bi abinda nake so ba kina cikin wahala, buɗe bakinki ki karɓa"


Girgiza kai tayi tana kauda kanta daga wani abu da yake shirin bata.

"Ya..m...mukhtar menene?"

Kashe idanu yayi yace 

"ko kin san menene ko baki sani ba dole zaki sha"

Ya karashe yana janyota zuwa fili abokan shi suka ɗauki shewa.

"Game muke kin san Truth or dare?"

Be jira amsanta ba yace 

"an yi daring ɗina na bugar dake don haka buɗe baki malama"

Idanunta gabaɗaya ta fitar, a lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki mazari, me yaya muktar ke nufi? Shayar da ita abun maye ze yi? Hawaye ne suka soma zuba babu birki cikin girgiza kai tace 

"Don Allah yaya Mukhtar kar ka yi, kar ka cutar dani, ya muktar hannuna zafi...kirjina ciwo don Allah kar ka sa ni saɓawa mahallicina a dole, karka zalunceni dayawa mana have a pity on...."

Bakin ya murɗe se sowa suke suna ambaton sunanshi ya soma bata, duk yanda tayi ganin ta kubce ko bata sha ba hakan be yiwu ba, gimtse hancinta yayi seda ta sha kaɗan kan ya sake ta ganin yana shirin kisa, a wurin ta zube ta tura yatsa cikin bakinta ta soma amai, tun tana yi har ta gigice ta fice hayyacinta gabaɗaya, wata ce a cikinsu da jikinta yayi sanyi da tausayin Alayar tace 

"Gaskiya baku kyauta ba, tunda bata sha me na shigo da ita cikin wannan game naku? Kullum baku da buri da ya wuce ku wulaƙanta ta, mu faɗawa kan mu gaskiya mana kai Mukhy kaine babban wawa, wanda be san abinda yake yi ba, taya zaka shigo da matar aurenka na sunna cikin wannan irin rayuwa, wani irin jahil....."


Gigitaccen marin da Muktar ya sake mata ne ya saka ta kwala ƙara ta yanke maganan, kan tayi motsi saurayinta ya tashi ya rama mata, kwalba mukhy ya janyo ya rotsa mai, a take jini ya fara tsiyaya kaman wasa sai gashi wurin na shirin zama karamin Abbatoir don faɗa ne sossai ya kaure tsakanin saurayin chan da shima ɗan wani ne da kuma Mukhtar kowanne kuma yana da abokan zagi, ita dae Alaya ta samu ta rarrafa ta faɗa ɗakinta ta datse kofa a wurin ta kwanta, kanta se juyawa yake da alama de kayan Mayen ya taba ta, tayi kuka har ta rasa hawaye, tana ta rokon Allah ya yafe mata yana gani ba laifinta bane, an fi awa biyu kan taji gidan yayi tsit, a wurin tayi bacci Washegari ma seda ta kai wuraren sha biyu kan ta farka sbd buga mata kofa da ake tayi kaman za'a ɓalla.


Dafe kanta dake sarawa tayi ko Sallar asuba bata yi ba, hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta share kan ta motsa a hankali ta miƙe dafe da gini ta miƙa hannu ta buɗe kofan jin bugun ba na ƙare bane, woman Police ce tsaye tana kallonta 

"Madam ko zaki iya ara mana mintuna biyu a cikin lokacin ki?"

Kaman bazata yi magana ba tace cikin dasashiyar muryarta

"Lafiya?".

"Shin kina cikin gidan nan gabaɗaya yinin jiya zuwa dare?"

Kai ta gyaɗa ba tare da ta amsa ba 

"ko kin shedi hatsaniyar da ya faru a jiyan?"

Nan ma ta girgiza kai tana kallon matar da take ta karantarta..


"Ba zaki samu ko wani sheda daga gareni ba, ko ma menene kike so pls ki samu waenda suka asassa abun, ina da uzuri se anjima" 

Ta ƙarasa a sanyaye kan ta tura kofan ta rufe ta juya zuwa bayi, seda tayi wanka ta zo tayi sallah tana rokon yafiyar Allah kan ta fita ta nemi abinda zata ci ta sake dawowa ta rufe ɗakin ruff ko bi ta kan wargajejjen parlorn bata yi ba, idan tace yanzu bata soma developing wani irin tsana na Mukhtar ba to wlh tayi ƙarya, a ƙasan ranta tayi ta ja mishi Allah ya isa kuma tana fata ya saka mata, ashe a chan kam case sossai aka yi sbd karfe da karfi ne suka haɗu sai da shudin Goshi case din ya mutu, nan Alhjnsu yayi ta mishi faɗa akan hakan ze iya ɓata mishi siyasa kar ya sake, ya dae ji ne ko da ya dawo ya tarar parlorn haka buga mata kofa yayi ta buɗe ba tare da ta kalleshi ba sai shima ya ji shakkan kallonta don fuskanta ba digon walwala ko farin ciki.


"Ki je ki gyara parlorn nan"

Yana kai nan ya juya ya fice, ta jima sossai kaman bazata yi ba se ta fito ta soma tattare parlorn incident ɗin jiya na dawo mata lokaci lokaci tana share hawayen baƙin ciki.


BAYAN WATA ƊAYA 


Yammaci ne sakaliya tun safe bata fita daga ɗakin ba, bata jin karfin jikinta sam ganin yunwa ze iya mata illa don daga kwance ma jiri take ji yasa ta miƙe ta fito sanye da dogon hijab as usual ta shiga kitchen.


Rabin taliya ta dafa da kwai dafaffe guda biyu ta zuba a plate, ta juya frigde don ɗauko ruwa se ga Rita ta shigo kai tsaye plate ɗin ta ɗauka zata fice, shan gabanta Alaya tayi tana jin ranta na ɓaci 


"Baiwar Allah lafiya?"

Da mamakin tsaurin idanun yarinyar Alaya tace 

"ba lafiya ba kam, taya zan dafa abinci don na ci ki zo kawai ki ɗauka ba magana ba komai kaman zamanki nake?"

Idanu Rita ta ɗan fitar cikin mamakin yau Alayar tayi magana haka ita bata taɓa ma jin dogon magana daga bakinta ba.

"Karfi ya ci daru ya danne, bani hanya in wuce hai village girl kawai"

Ranta ta sake ji ya zo mata wuya yarinya fitsararriya ta shigo har cikin gidanta tana zaune duk kauda kan da tayi be isa ba sai ta haɗa da zagi da cin zarafin ta ko da shi ke ba laifinta bane, cikin ɓacin rai tace


"Ai kuwa gwara da ni sau dubu saba'in in ma na amsa ni village girl din kenan, ko ba komai village girl ta fi ashawo...."

Watsa mata abincin gabaɗaya Rita tayi jiki yayinda ita kuma Alayah ta dauketa da zazzafar mari.

   hango Mukhtar bayan Alayar yasa ta dafa kumatu ta saki razananniyar ihu, cikin kuka tace 

"Wallahi yau zan bar maka gidanka Mukhy, har ni matarka zata ɗaga hannu ta mareni akan banza taliya? Ni dae?"


Da sauri Alayah ta juya zata yi magana ya kifa mata mari, yayi ball da ita bata san ta tafi kaman wacce iska ya ɗauka ba seda taji ta sauƙa a kafafun mutum, ɗagowa tayi bata gani daidai sai taga Maami ce da sauri ta miƙe ta faɗa jikinta ta soma kuka me cin rai, kan Maami tace tayi wani yunkurin kawai Alaya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa...


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Mukhtar ka kashe musu ƴa ka huta, nace ka huta.."

Tana nufo shi ne take maganan 

"wani irin zuciya ne da kai? Wani irin baƙin zuciya ne Allah ya halicceka da ita? Ashe baka da tausayi Mukhtar dubi yadda yar mutane ta koma"

Kwalan riganshi ta chakwamo

"Allah ya saka mata, wallahi Allah sai ya bi mata hakkin ta, Allah ya mata sakayya tun a duniya, mugu azzalumi.."

Hawaye take yi bibbiyu, hannunta yake kokarin cirewa a wuyan shi tana sakin shi kuwa ta soma zuba mishi maruka hagu da dama tana kuka.


Ganin hakan baze mata ba ta soma neman abinda zata kwada mai ko zata huta bata yi taku biyu ba itama ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Se a lokacin ya gigice cikin hanzari y dago ta yana kiran Maami Maami, sede Maami tayi nisa, daukanta yayi da gudu zuwa motanta driver ze ja yace ya jira shi, da sauri ya koma ya ɗauko Alayah da banda haushinta babu abinda yake ji dama tsakanin shi da mahaifiyar yaya gashi tana kara ɓatawa, ta wannan ne kawai zasu iya samun matsala da Abbansu don yana son matarshi.


A motanshi ya saka ta yana gaba drivern Maami na bin su a baya har asibiti, cikin gaggawa aka Karɓe su emergency, likitoci suka rufu a kansu wasa wasa har aka yi Magrib kan suka samu kan Maami, Alayah kam se kusan bayan isha ma likita mace ta fito tana kallon Mukhtar 

"kaine mijinta?"

Kai ya gyaɗa yana kallonta

"Toh Congratulations matarka tana ɗauke da ciki na tsawon sati biyar sede akwai karancin nutrient a jikinta, and ciwon zuciyanta yana so ya tsananta kaman yadda jininta ke hawa duka wannan illah ne ga lafiyarta a gaskiya ya kamata ku kiyaye, a ka'idar aiki ma bayan an mata wanchan aikin zuciyar be kamata kuma ya sake hitting haka ba"


Shi duk sauran jawaban ma baze ce ya ji ba banda batun cikin nan da ya ji.

"Ciki???"

Ya maimaita kan ya sake cewa 

"do you mean pregnency?"

Kai ta gyaɗa, ya ja wani dogon tsaki ga ta inda ya tsani auren ai, yarinya ta zo banda gidahumanci babu abinda take mishi kwata kwata ko shekara bata rufa ba ace wani ciki, shiyasa ya fi son hulda da wayayyun mata shi be shiryawa haihuwa yanzu ba...


"Look likita ina so ki zubar da shi ko nawa ne zan biya"

"wannan ba aikina bane, kuma bama haka a asibitin nan amma zaka iya zuwa gaba se ayi maka"

Har ta juya yace

"ko don lafiyanta? What if cikin ne yake triggaring ciwon zuciyar? I th....."


"MUKHTAR"

Maami ta kira sunan, se kawai ta sulale ta zauna a wurin tana hawaye a ranta tana istigfari bata san me zata yiwa Mukhtar ya shiryu ba, babu me fahimtar ciwon ranta babu me gane abinda take ji da takaici da haushin ɗan da ta haifa a cikinta se wacce jarabawa irin wannan ya faɗarwa, muryarta a rarrabe tace

"ka fice daga asibitin Mukhtar wallahi na tsani ganinka"

Da sauri ya ɗago ya kalleta, ze yi magana ta daka mishi tsawa tana dafe kanta dake juyawa.


"I Said Get outttt!"


Miƙewa yayi ya fice, da sauri likitar ta ƙaraso ta riketa ganin tana shirin sake collapsing.

"Se hakuri Aunty, Adu'a itace maganin komai ki kara akan wanda kike"

Maami na hawaye tace 

"Wallahi ina yi Likita, ina yi bana bacci amma kaman bana yi astagfirullah Allah na tuba Allah"

Tausayinta sossai ya rufe likitan, ita tayi ta kwantar mata da hankali amma ta koma ɗakinta firr ta ƙi tace zata zauna da Alayah gudun sharrin Mukhtar.


Se kallon yadda kasusuwa suka yiwa yarinyar sarka take yarinyar gwanin tausayi, rayuwarta duk ya daidaice sbd Mukhtar, matakin da ta yanke kawai shine na riketa ta nema mata saki wurin Mukhtar shine kwanciyar hankalinsu duka, in ya ga dama ya tara matan duniya a gidanshi yana zina dasu tunda abinda yake so kenan, share hawayenta tayi ganin Alayah na motsi ta riƙe hannunta....


"binty kin farka?"

Kai ta gyaɗa tana sake lumshe ido tace a hankali 

"Maami cikina kaman ana karta"

"ai dole, taya me juna biyu zata zauna da yunwa sossai haka har ya fitar da ke hayyacinki? Ruqayya na hanya bari in kirata tayi sauri"


"Juna biyu???"

Bata san a fili ta maimaita ba seda Maami ta ɗago ta kalleta tace

"Eh, kina dauke da juna biyu na tsawon sati biyar..."

Dibbbbbb haka duniyarta ya tsaya, komai nata ya tsaya chakk kaman robot ta sake maimaita

"Juna biyu dai?"