16
by @gureenjoh
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Sixteen*
*Na riga na yi alkawari in ba haka ba ina zan iya typing karfe 12🥲 sorry guys class nayi da ba zan iya dodging ba*
Bakinta ta tura gaba ba tare da tayi magana ba Dukda tsallen da ƙirjinta ke yi kaman ana dakan sakwara, sai dai abu ɗaya da ta lura dashi da ya bata lasisin hakan shine ba'a chake yake ba kuma idan hakan ne ta san zafin ran nashi da sauƙi, ba zata taɓa gigin yi mishi hakan ba idan yana buge don zai iya ƙas da ita a wurin ba tare ma da ya san ya aikata hakan ba, ƙarasa sauƙa tayi tare da sanya silifas ɗin ta
"Ke! Ina miki magana kin mai da ni banza?"
Nan ma bata ce komai ba taku biyu tayi ya sanya hannu ya fusgo ta tayi baya luuu ya mata masauki a kan kafafunshi hannunshi ya sa ya zagaye ta yana me kurawa fuskanta idanu for the First time a rayuwarsu irin kallon nan na kurilla yace chan ƙasa
"ba da ke nake ba Fatee?"
Ba tare da ta kalleshi ba ta zumɓura baki tace
"to ai ni sunana ba ke bane, ba gashi da ka kira sunan na amsa ka ba??"
Ta karashe tana ɗagowa ta kalli idanunshi da suke nan launin jaja kuma a lumshe, runtse su yayi yana jin yadda wani abu ke fusgar shi zuwa gareta, ji yake zuciyarsa na tsukewa wuri guda ga dukkan alamu ginin da babu shakka na so ne yake ginuwa daki daki cikin zuciyar shi, ɗauke kai yayi daga kallonta tare da ɗan tureta, ta kuwa sake taɓe baki alamun kai ka jiyo dama ba ni na ajiye kai na ba, toilet ta shige ko da ta fito ma bata same shi ba.
Da yammacin ranar aka bata sallama, gida suka dawo Dukda ta so tsayawa asibitin sbd ummin ta amma kuma ba hali don har yanzu tana ICU ne ba'a yarda ba ma da isa kanta bare a fara jinyar ta, likitoci da nurses ne kaɗai ke zuwa kan ta, ko da suka koma gida ma bata bar zazzabin laulayi ba, kuma ta fahimci har lokacin babu shiri tsakanin Maami da Abba kai tsaye zata iya cewa sune sanadi, iya kokari Maami na yi wurin nuna mata komai lafiya ai dae bata san ta riga ta fahimta ba.
Kwance take kan kujera hannunta yalo ne take ci Dukda wani irin zazzabi da ya rufeta tana dukunkune sai rawan sanyi take kuma ta ƙi kashe Ac ko rage wa, Maami ta fita sai mama lami ne ke zuwa jin ko akwai wani abin da take buƙata ta kawo mata, bacci ne ya fara fusgar ta sam bata san Shigowar mutum ba ashe har ya kashe Acn bayan taɓa fuskanta da yayi ya ji jikinta raurau, baya baya yayi ya zauna kan kujera Red eyes ɗin shi ya zuba mata a ranshi yana ayyana dama haka mata suke fama ne ko ita ce kaɗai?
Tun da aka ce tana da cikin nan ba zai ce ga sadda ya risketa lafiya ƙalau cikin ƙarfi da kuzari ba, ko yaushe gata nan dai ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yake jin duk wani rayuwarshi na baya ya fita kanshi fit, iya kokari yayi na daina shaye-shaye haka matan ma rabon shi da mace zai iya cewa ya manta, bashi da wani aiki sai na tunanin wannan yarinyar, wani sa'in ma yana son zuwa ɗin ya kalleta sai kuma wani sashe na zuciyarshi ya mishi nauyi, kunyar Maami ya lalaɓo ya rufe shi ruff ta yadda baya so ko haɗa idanu su yi.
Shisha Pen da smart ya bashi ya fitar yana ɗan jujjuyawa sun ce zai rage mishi wannan damuwan da ya shiga a kwanakin sai dai yana shakka don ya san zasu iya sa wani abu na bugarwa ciki, bakinshi ya kai kaman ya sha sai ya ja tsaki yana ƙoƙarin sauƙewa suka haɗa idanu, girgiza kai tayi tare da Miƙewa bata ce mishi ci kanka ba ta zo zata wuce yayi saurin riƙe hannunta kula da yayi kaman ranta ya ɓaci kuma hakan ya nuna har a fuskanta, fisgewa taso yi ta mance ma riƙon maza ba irin na mata bane...wani zafi ne ya ratsa ta mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu a take ta fashe mishi da kuka sossai har sai da ya tsorata.
"Ni ka sakar min hannu..."
Da sauri ya miƙe yana kokarin duba hannun ko ta ji ciwo ne sam be san masu ciki da wannan mood swings ɗin ba ya haɗu kuma da wani tunani da tayi kanshi, ganin ya sake ta yasa ta nufi sama, taku biyu yayi ya tare ta
"Menene? Kin ji ciwo ne a hannun?"
"Ina ruwan ka da ni? Menene damuwarka? Ba tunani aka ce in yi akan auren mu ba? To na gama ba zan iya cigaba da zama da kai ba wallahi, tuban muzuru ne kayi ba na Allah da annabi ba..."
Shesheka ta ja tana matsawa baya ganin ya matso ta sossai yana kokarin taɓa ta don sam be fahimci inda matsalar ta taso ba tace
"kar ka taɓa ni, burin kowacce mace a rayuwa shine ta samu miji nagartacce, mai gaskiya da tausayi, wanda zata iya ƙarasa rayuwarta a tare dashi, sannan bayan aure su samu New wonderful family, burin kowace macece ta samu abokin rayuwa wadda zai agaza mata wurin cika duk burikan ta na rayuwa, ya taimaka mata a sadda take neman taimakonshi, ya so ta ya kasance mai kishin ta, sannan wadda zasu fuskanci duk wani matsalolin su a tare, ayi nishadi wasa da dariya, a yi salloli cikakku guda biyar a rana nd inspire one another to increase their deen, ayi respecting juna nd live peacefully in this nd the life hereafter, ka gayamin wanne kayi daga ciki? Ko kuma wanne kake shirin yi? Ya Mukhtar ɗan ka ne ke shirin zuwa duniya amma gaban idanunshi Shisha ne kake shirin sha wadda babu tantama na san flavor din ba zai rasa surkin abin bugarwa ba? Idan ba zaka ji kunyata ba ni karamar dangar ka da ka saba shawowa ka juye min shi be chanchanci kunyar ka ba? Maami bata chanchanci ka mata kawaici ba a cikin parlorn ta zaka yi shaye-shaye? Ka matsa min na wuce ka sha kayanka amma ka sani wallahi ni dae na gama zama da kai.."
Hawayenta ta share kan ta zagaye shi tayi sama da gudu tana kuka.
Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka yake jan kafafunshi jin gwiwowinshi na shirin sagewa su butulce mishi wurin kasa ɗaukar gangar jikinshi, zubewa yayi kan kujera zuciyarshi na wani irin yamutsuwa tare da kwakwalwan kanshi dake ta aikin tariyo kalamanta, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi a hankali zazzafar zazzabi ya soma sauƙo mishi, kalamanta sun mishi nauyi sossai, rashin fahimtar shi da bata yi ba sai ya so haukata shi,
Miƙewa yayi don barin gidan ko zai shaki iska mai kyau sai ga Maami ta shigo.
A hankali yace
"sannu da dawowa Maami"
Kallon shi tayi da mamaki don ba halin shi bane hakan, sai kuma ta kula kaman bashi da lafiya ne kaman bazata yi magana ba sai kuma tace
"yauwa! Lafiya kake kuwa? Ko dai cikin shaye-shayen ka shayo abin da yafi karfin ka?"
Idanunshi ya runtse da ƙarfin gaske wani zafin ya sake ratsa zuciyar shi, dama haka ake welcoming wadda ya ɗauki hanyar tuba? Dama wannan na daga cikin kalubale da illar shaye-shayen ko kuma daga mahaifiyarshi da matar shi ne?
Be iya ya tanka ba ya fice daga gidan, da kallo ta bishi har ya bace kan ta haura stairs, ɗakin Alayah ta tura don dubata sai ta sameta zaune tana game a wayanta kaman ma bata yi kukan matsalar gidan aurenta ba, taji sauƙin abin sossai da ta samu fitar da abin da ke ranta kuma da gaske ta gama zama da Mukhtar.
"Sannu da dawowa Maami"
"yauwa binty ana hutawa ne?"
Kai ta gyaɗa tana murmushi
"Maami kin yi waya da asibitin? Sun yarda zasu bari a ganta nan kusa?"
Kai ta gyaɗa tace
"Eh mun yi magana, baba ma dai ya bada shawarar a fitar da ita waje kawai amma dai muna nazarin hakan da umar, kar ki damu zata samu sauƙi in shaa Allahu. Yanzu dae albishir"
Murmushi ne kwance bisa fuskanta da ya ƙara mata kyau sossai tace
"Goro Maami fari ƙal ma ba ja ba"
"Kin samu admission a skyline university"
Tsalle ta tashi zata yi da hanzari Maami ta riƙe ta tana dariya, rungume Maamin tayi hawaye na tsillo mata tace
"Alhamdulillah Maami na gode, na gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki zuri'a, Allah ya amsa dukkanin Adu'o'in ki ya biya buƙatun alkhairi"
Cikin murmushi ta amsa da Ameen, sai kuma ta ɗago ta
"Amma me ya sa kika zaɓi cyber security bayan baya cikin duk courses da kika lissafo min kina so?"
Cikin murmushi tace
"haka kawai na ji ina son karantar shi, kila shine Allah ya zaɓa min"
Har daren ranar murna take da samun admission nata, Allah sarki Da ummi na cikin koshin lafiya da sai tafi kowa murna ta tabbatar da hakan.
Da dare ta isa jikin kofa don rufewa kenan taji kaman ana magana murya sama, idanunta ta lumshe babu shakka muryan Abba ne kuma ta tabbatar da Maami yake don kaman magana ne da ya dangancesu Dukda bata jin shi clearly, da jikin kofan ta jinginu ba zata taba son su kasance tasgaro ga rayuwar Maami ba, ita ce mutum na farko a rayuwarsu da ta nuna musu suma mutanene kaman kowa suna da muhimmanci kuma suna da Ƴancin rayuwa yadda kowane mutum ke yi, ita ta basu mafaka a sadda suke tsakiyar rana da kunar zafin ta, da ba don ita ba da kila yanzu babu Umminta don ta tabbatar ba jinya Abban meela ze yi mata ba, sannan ga damar karatu ta bata wadda zai sauya mizanin rayuwarta, amma su kuma suna kokarin dakile farin cikinta da zaman lafiyanta, tana jin irin barazanar Abba har da aurenta yayi mata kan ya zo ya wuce kaman iska.
Ta jima tsaye wurin kan ta isa ga gadonta ta kwanta idanunta runtse tunaninta ya tafi gabaɗaya ga neman mafitar wannan matsalar kuma, cikin bacci ta ji ana buga mata da sauri kuma a ɗan tsorace ta miƙe zaune, idanunta ta kaikaya kan ta sauko gabanta na faɗuwa ta tsaya nesa da kofan
"wa....waye?"
Shiru aka yi sai aka sake knocking
"waye ne?"
****
Zaune su ke a club ɗin shi dae ko idanunshi baya buɗewa in banda ma matsawar su Nawwaz babu abin da zai kawo shi club ɗin amma sune kaɗai abokan shi su ne masu debe mai kewa cikin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, En matan dake ta damunshi ne ɗaya ta matso ta shafa shi
"Mukhy whats wrong with you? We dont like this mukhy we want our old mukhy back, menene kake so? Ka zo mu debe maka kewa mu mantar da kai duk wani damuwa, mu baka farin cikin da ka jima baka samu ba..."
Hannun da take shafa shi ya ture ba tare da ya buɗe idanun ba
"don't you dare touch me again"
Ya faɗa chan ƙasa ƙasa har yanzu kalaman Alayah ne ke farautar rayuwarshi, idanunshi ya buɗe ya sauke kan smart dake rungume da yarinyar da ta gama lafaza shi a yanzu tsaki ya ja me karfi barikin fa kenan, Tsam ya miƙe tare da miƙawa smart din hannu ya bashi key.
Ture yarinyar smart yayi tare da Miƙewa
"ka san bama barin ka driving cikin situation din nan muje in kai ka inda zaka"
Nawwaz ma Miƙewa yayi suka fito su huɗu zuwa motar shi, da gudu suka bar club ɗin, sauran su biyu duk a Buge suke yayinda smart dake driving ke bankawa cikinshi Shisha, shi dae oga kwata Kwata na kishingide abin duniya ya dame shi, daidai wani unguwa motar ta tsaya chak, idanunshi ya buɗe ya dubi smart
"ya dai?"
"Wlh ban sani ba mukhy ko zaka duba mana don ko na je babu abin da idona zai gani?"
Gaban motar ya buɗe ya fice yayin da smart ya buɗe mai bonet daga ciki, ganin ya ɗan jima yasa duk suka fito, wurin shiru sannan hasken wurin ba sossai bane, layi ne a chakude da gidaje kala uku akwai na masu kuɗi jefi jefi haka akwai na daidai misali sai kuma na talakawa da suka fi yawa.
Wata yarinya ce da bata wuci 16 ba ta taho hannunta riƙe da tray tana kuka, kuɗin cinikin ta ta ɓatar gashi matar ubanta bata da sauƙi akan sana'arta shiyasa ta kai yi warhaka bata koma gida ba, ta sa baban ta da Yayanta yanzu sun dawo idan kum yaddikonta ta kanainayesu da maganganun ta ɗaure ta zata kara yi yau ta shiga uku da babanta tunda duk abinda yaddikonta ta faɗa daidai ne, har ta wuce su ma bata maida hankali kansu ba sbd nata matsalar.
Nawwaz ne yace
"kai yarinyar nan tayi smart, anya ba zamu latsa ba?"
Area ɗin suka dudduba jin shiru sossai yasa babu wani tunani yadda suka saba kayansu sa'i da lokaci suka bi bayanta, da bakinta suka fara da karfi suka ɗaure suka jata gefen ciyayi, sam Mukhtar be san me suke ba don hankalinshi na kan duba motar sbd babu abinda yake so a yanzu irin ya je gida ya kwanta ya cigaba da tunani.
"Smart tada motar mu ji"
Yayi maganan ba tare da ya ɗaga kai ba, jin shiru ya sa ya ɗago ya dae san sun fito waje to komawa suka yi? Sake motar yayi yana zagayowa sai de be ga kowa ciki ba, jin kaman nishi ya sanya shi ɗaga kai da sauri ya kallesu chan da alama ma sun gama lalata rayuwar yarinya da gudu ya isa ya ture Nawwaz, ɗagowa yayi ya tsinkawa smart mari
"Me kuka yi? Me kuka aikata? Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Daidai lokacin yarinyar ta kwalla ihu sai ga hasken touch ana kiran sunan da basu gama gane na wacece ba, da gudu suka yi mota Nawwaz janye da Mukhtar da da alama tsayuwa ya so yi, ihu yaron ya fara yayinda tuni smart ya figi motar baban ne da yake gani dishi dishi ya riƙe plate number ɗin, babu shakka sun kassara rayuwarsu ko daga yadda yayan yarinyar ke kuka sossai yana dagota ya rungume ya san hakan....
*Toh fa, Mukhtar sawu ka taka ko ya abin yake ne?*