AL'AJABIN SO

21

by @gureenjoh

AL'AJABIN SO

     (heart touching story)


Fatima Muhammad Gurin 

(Gureenjo)


Adabi Writers Association


Book 1

*Page Twenty one*


"Ya Mukhy ka dawo cikin hayyacinka Abba ne fa"

Abba da yake zaune shiru ba tare da ya ce komai ba duk maganganun Mukhtar ɗin ne suke dawo mishi, a hankali ya ɗago idanu ya kalli Maami da ta iso wurin ta tsaya ba tare da tace komai ba, ashe haka take jin nauyi da zafi a ranta a duk sadda yake ba Mukhtar goyon bayan faɗa mata abinda be dace ba ba tare da kwaɓa ba, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah kan ya buɗe ya kalli Mukhtar da ke ta huci har lokacin Alaya bata sauƙe hannunta daga kan lips ɗin shi ba yace 


"Fatima kyale shi, barshi ya faɗi duk abinda ke ranshi ko me zai faɗa na tabbatar babu ƙarya cikinta, na riga na cuci rayuwarshi na mishi illah, ban nemi yafiyarshi bane ba don ban yi nadama ba, nayi shiru ne saboda ban san me zan ce ba, ban kuma san ta wani hanya zan bi wurin taya shi gyara kuskuren da nine silar faruwarsa ba, amma ke ina rokon yafiyarki akan kalamaina na jiya"

Cokalin ya ajiye ya miƙe zai fita Alaya tace 

"Abba!"

Tsayawa yayi daidai kusa da Maami ba tare da ya juyo ba tace 

"abin da na faɗa a kotu ɗazu shi zan sake maimaitawa, kowa yana kuskure hakanan kowa na laifi saidai wadda ya fahimci laifin shi ya kuma tuba yayi niyyar gyarawa be yi kuskure ba, hasali ma abin da ake fata kenan, Don Allah karka saka damuwa a ranka Abba.

Ya Mukhtar na fahimci yadda kake ji a ranka, sai dae ba hakan ne ya baka daman aibata mahaifinka ba, babu inda ya bamu wannan daman idan har da gaske ka gyara kuma ka chanza daga Mukhtar na da to kayi kokarin saita harshenka wurin magana da iyaye don Allah ya ɗaga darajarsu.

Maami Don Allah da manzonsa kiyi haƙuri, fushi ko rashin yafiya duk ba zai chanza komai ba, mu haɗu duk mu gyara abin da ya ɓaci a baya adu'ar ki ce a yanzu Allah ya ƙarba, muyi kokarin zama one Big happy family Don Allah"


Mukhtar da kanshi ke ƙasa hawayenshi na ɗiga bisa kan dining ɗin a ranshi yake jin Alayah is too good for him, be yi abinda Allah zai bashi ita matsayin mata ba, bayan duk abubuwan da suka faru ji yadda take magana kaman be gallaza mata ba, har ta yafe mishi kenan? Lallai idan zata iya yafe mai kuma har ubangiji zai iya yafe mai ya barshi da mace irin Alayah to shi me zai hana shi yafewa Abba? Maami ya ɗago ya kalla tana zub da hawaye itama idanunta na kan Alayah, har ranta take son yarinyar Allah ya mata baiwa na daban, idanunta ta maida kan Abba da jikinshi yayi matukar sanyi, kwarai suna bukatar cikakken farin ciki na tsawon shekarun da suka rasa a gidan ko da kuwa ba zai tabbata ba, shiyasa yake ganin gazawarshi ya kuma tabbatar komai ya faru tun farko daga shi ne, idanunshi ya lumshe yana jin kanshi na sarawa babu tantama hawan jininshi ne.


Mukhtar ne ya yanke sad moment ɗin don tunda Alayah ta gama magana tayi shiru kowa da abinda yake saƙawa cikin ranshi, a hankali yake jan kafafunshi har ya isa gaban Maami ya zube bisa gwiwowinshi kanshi a ƙasa yace

"Na san ni gagarumin me laifi ne a gareki Maami, tabbas a da na zama wawa, jahili, marar amfani na bi sahun waenda Allah ya ƙira da Ƴan wuta nayi ta saɓa miki cikin sani da kuma rashin sani, kin yi kuka har ba adadi, kin shiga damuwar da har ki kan yanki jiki ki faɗi, amma duk da haka baki tsane ni ba, baki daena min adu'ar shiriya ba, baki zare hannunki a kaina ba ba kuma ki yi min mummunan furuci ba saboda ke uwa ce! A yanzu ina tsananin jin kunyar kaina da na mahallacina, ina jin nauyin neman gafararki saboda abubuwan dayawa, Don Allah Maami ki yafewa Mukhtar ɗinki, ki yafe mini ko zan samu kwarin gwiwar tunkarar mahallacina da neman gafara, Maami ki ɗaukeni kaman jinjirin yaron ki da kika haifa a tsumman goyo in baki ragamar rayuwata ki yi min sabon tarbiya uwa ta gari, na tuba don Allah"

Yadda yake kuka sai ya sa su duka kuka har Abba hawaye yake yi, kafaɗanshi ta kamo ta ɗago shi kawai ta rungumeshi Allah ya sani kukan farin ciki take, kukan jin daaɗi yau Mukhtar ya zama mutum, ɗagowa tayi tare da sanya hannu tayi cupping fuskanshi tana kallonshi cike da sabuwar soyayya tace 

"Na yafe maka Mukhtar, har Abada na yafe maka duk wasu laifukanka gareni da wadda na sani da ma wadda ban sani ba, Allah ya yafe maka... Ina so ka zama kaman ɗan uwanka a kusa dani duk abinda ya shige maka duhu a sabuwar tafiyar nan taka da zaka fara kar ka ji nauyi ko kunyar tambayata kaji?"


Hugging ɗinta ya sake yi, Abba ya sanya hannu ya share hawayenshi kan yayi taku kaɗan ya ƙaraso gabansu, Maami ya kalla

"Fatima ki yafemin na cutar dake a iya zaman mu, nayi kuskure me girma wadda ban farga ba sai a yanzu, bayan lalata tarbiyar Mukhtar na kuma nesanta ki da wadda zaki gani ki ji haske, lallai na tabbata mugu, azzalumi ban yi la'akari da cewar ke ɗin uwa ce ba, ban duba kasancewar ki mace me raunin zuciya ba ƴaƴa biyu da Allah ya baki duk na wargazasu na tauye farin cikin ki na tsawon shekaru na tuba"

Kai ta gyaɗa tace

"komai ya wuce Abba, in shaa Allah zamu ƙarasa sauran rayuwarmu wurin gyara duka waennan kuskuren"


Mukhtar ya kalla zai yi magana sai yayi hanzarin rungumeshi, a rungume dashi yace 

"Abba kayi haƙurin kalamaina na dazu, na san duk abubuwan da kayi min a yadda ka ɗauki soyayya kenan baka min da niyyan zalunci ko don in lalace ba, hasali ma mune muka zalunci Umar, na riga na yafe maka Abbana, Allah ya bamu ikon gyara laifukan mu"

Duk da Ameen suka amsa, sai a lokacin kowa ya iya sakin murmushi a cikinsu, dawowa suka yi Maami ta sake serving Abba sbd wanchan yayi sanyi, Alayah kuma tayi serving Mukhtar dake ta kallonta wadda hakan yake sakata jin kaman ta nutse cikin ƙasa.


Basu zauna ba suka yi cikin parlor suka zauna da Maami, Maami ce ta nuna mata cinyarta sai ta zame ta kwanta tare da yin matashin kai da shi, a hankali ta zame dankwalin kanta tace 

"Binty dai Allah yayi ki irin Maaminku, kema bakya son kitso sam"

Murmushi tayi tace 

"Maami ai tsoron kai ne da ni, daa ummi sai tayi da gaske take min kitso saboda rigima daga baya tace na girma in ma naki ni na sani, shikenan sai dae in wanke in shafa mai"

Murmushi Maami ta sake tana cigaba da ɗan sosa mata kan tace 

"Lallai Binty ke ɗin wata haske ce a cikin rayuwarmu, ina Alfahari da samun ki matsayin ƴa Allah ya albarkace ki ya ba ummi lafiya"

Tana lumshe idanu saboda baccin da yake son kwasheta don susan kan daaɗi yake mata tace 

"Bani da abin da zan saka miki Maami, illa iyaka a duk sallata na kan sanya ki a Adu'a Allah ya miki abin da zato be taɓa zato ba, tunanin ɗan Adam be taɓa kaiwa ba, Allah ya miki muhalli na musamman a cikin gidan Aljanna, haƙiƙa nayi matukar dacen samun ki a matsayin uwa"


Murmushi Maami ta saki, a hankali ta ɗaga kai sai ta ga Mukhtar da Abba ma hira suke ɗan yi a hankali, idanunta ta lumshe ina ma da umar yana wurin da farin cikinta ya zama cikakke, amma ta san irin zuciyarshi ga yanayin aikinshi Allah ya sa ya yafewa babanshi da ɗan uwanshi har su yi zama da mutunci.


Ko da Suka gama wurinta suka dawo, tuni Alayah tayi bacci kan kafafun Maami, hira suka cigaba da yi su ukun kaman komai be faru ba, shawaran karatuttukan da zai fara suka yanke inda a kullum da yamma zai tafi wurin baba sai goman dare ya dawo, tuni ya kira kakan nashi ya shaida mishi ze fara zuwa ɗaukar karatu har yar raha suka yi baban na cewa ya faɗi gaskiya ko furanshi na dare zai ke zuwa shanyewa kullum suka ɗan yi dariya, ya kula kowa so yake ya ja shi a jiki, kwarai hakan ya mishi matukar daaɗi don hakan ne kawai zai kasance ya san eh zai iya, zai iya zama na kirki, shima zai iya gyara kura-kuranshi, kuma he is accepted a welcome a familynshi.


Idanunshi gabaɗaya zube a kanta, murmushi ya ɗan saki yana kallon yadda ta sake lafewa jikin kujeran kaman mage, haƙuri na musamman yake son bata, sai dae baya tunanin a yanzu ne zai yi hakan, duk yadda yake jinta a ranshi da yadda yake jin a yanzu ita ce bugun numfashin shi zai mata adalci, dole sai ya zama nagartaccen mutum kaman kowa zai iya sake fuskantar ta da kokon barar matsuguni a cikin ranta.


Abin da be taɓa faruwa ba shi ya faru yau, sun yi hira sossai har la'asar cikin raha, sai tuno baya ake Maami na hiran yarantanshi yana dariya, dariyanshi ne ya tada Alayah, ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta watsa mishi, shima da baya mintuna biyu be kalleta ba idanunshi na kanta, bakinta ta turo mai na tana baccinta me daaɗi ya tashe ta, murmushi me kyau da bata taɓa gani a fuskanshi ba ya sakar mata, da sauri ta ɗauke kai tare da kokarin Miƙewa zaune.


"Sannu Fatima"

Abba ya faɗa tayi murmushi, Maami tace 

"kin tashi Binty? Ko yunwa ce ta tashe ki? A kawo miki wani abu ne?"

Jinta take ƴar gata, a da ana musu kallon kaskantattu marasa galihu babu wadda ya damu da damuwarsu, cin su, shan su ko lafiyar su amma duba a yau yadda waennan ahali suke mata, ai ko menene tayi musu bata faɗi ba.


"Maami bari dae na shiga kitchen ɗin da kaina"

Ta miƙe ta nufi kitchen ɗin, Masu aikin suna aikinsu cikin tsabta, Tabawa ce ta dubeta 

"Hajiya karama kina bukatar wani abu ne?"

Tayi murmushi tace 

"A'a ki yi aikinki baaba, bari na haɗa da kaina"

Indomie ta dafa guda biyu, anan ta zauna suna ƴar hira tana dariya har ta cinye kayanta, ko da ta fito ta samu duk basa nan a parlorn da alama sun je sallah, itama ɗakinta ta haura ta gabatar da la'asar din kan ta kwanta a wurin cikin tunanin umminta, Adu'a take tayi a ranta na Allah ya ba ummi lafiya, Allah ya tashi kafadunta don bata san ina zata kama ba in ba ummi, bata san kowa nasu ba, ko suna dashi ko basu dashi duk bata sani ba.


Maami bayan ta idar da sallah Umar ta ƙira, a natse suka gaisa take bashi labarin abinda ya duk ya faru, ya taya ta farin ciki don da farin cikinta shima yake samun farin ciki.

"Yanzu yaushe zaka shigo?"


Ɗan shiru yayi kan yace 

"in shaa Allah zan shigo idan na samu sararin aiki Maamina kar ki damu"

Ajiyar zuciya ta sauƙe tace

"Toh Don Allah idan cikinsu wani ya ƙiraka ka ɗaga ka ji? Yafiya abu ne me kyau wadda dukkanmu muna son shi a wurin mahallici, ashe don mu mun yafewa junanmu bamu faɗi ba ko kaɗan, na san irin zuciyarka ka daure a maida komai ba komai ba ka ji autan Maami?"

Murmushi ya saki me sauti har tana jinshi, saboda yadda ta ƙarasa maganan da lallami kaman ɗan yaro, ita ma murmushi ta saki suka yi sallama.


Kofan ɗakin aka yi knocking ta bada izinin shigowa, Mukhtar ne ya shigo zai yi magana daga chan tayi saurin miƙa mai hannu ya iso ya riƙe ta nuna mishi kusa da ita bakin gado ya zauna, ta san sabo sai a hankali amma with effort komai zai zama tarihi.


"Maami zan tafi wurin baba"

Murmushi ta saki tace 

"Toh a kula, a kuma maida hankali banda tuƙin ganganci Allah yayi albarka"

Wani irin farin ciki yaji marar misaltuwa

Yace 

"in shaa Allah sai na dawo"

Ya miƙe ya fito, ɗakin Alayah yayi knocking shiru ba response, ya sake yi shiru sai ya tura a hankali ya shiga tana nan kwance rigingine cikin tunani, a take yaji wani iri a jikinshi menene matsalar? A hankali ya isa ganganta ya tsuguna bata san zuwanshi ba sai hannunshi ta ji...