23
by @gureenjoh
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)
Adabi Writers Association
Book 1
*Page Twenty Three*
Zaune a gaban Dr Ahmad dake ta murmushin ganinshi da yanayi na daban yace
"Na zo ne ina bukatar a yi min tests ba zan iya haƙurin cire folder da sauransu ba please do the needful"
Sarai ya gane shi their rude patients husband Dukda yanzu Meddy specialist sun karɓe musu ita sbd finsu kwarewa a harkar zuciya sai dae ya san Maami ya kuma san Umar tunda ta hannunshi suka karɓi ummi.
"Wani iri kenan?"
Numfashi ya ja kan yace
"Komai da komai, precisely HIV/AIDS"
Da sauri Dr Ahmad ya kalleshi, jingina yayi ya lumshe idanu yace
"don't be suprise, it might be the product of my sins"
Ajiyar zuciya Dr Ahmad ya sauƙe kan ya danna kiran wata ma'aikaciyar jinya ya bata umarnin zuwa da kayan diban jini, tubes biyar ya buƙata.
Ko da ta kawo da kanshi ya tashi yayi sticking finger ɗin shi for the rapid antibody test na HIV kan ya saka syringe ya zuƙi jini sossai a tubes din nan, a na karshen ne ya ɗaga kwalban sama yana kallon jinin for seconds kan ya ajiye kan tray ɗin, rubutu yayi a kan plain sheet me ɗan tsawo da Mukhtar ba zai iya tantancewa ba sbd rubutun likitoci ba irin na normal mutane bane ya bata yace ta kai lab please.
"Sai zuwa yaushe duk results din zasu fita?"
Dr Ahmad yace
"zai iya kaiwa five hours kan a kamallah komai sbd suna dayawa"
Miƙewa Mukhtar yayi ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha kan yace
"Zan dawo ko zuwa anjima, nd I will make the payments yanzu in na fita thank you very much"
Murmushi kwance a fuskan Dr. Ahmad shima ya bashi hannu kan ya juya ya fice, da kallo Dr. Ahmad ya bishi a fili ya furta
"Masha Allah, he's indeed a changed person"
Ko daga maganan shi ma ya fuskanci hakan.
Yana isa wurinta ya sakar mata murmushi tare da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe yace
"Sorry madam na ajiye ki ko?"
Girgiza kai tayi tana murmushi, bata tambayeshi abin da yaje yi ba sai dae ta fahimci kaman akwai abinda yake damunshi, yanayinshi ya sake sanyi har suka isa gida babu wadda yayi magana, a tare suka shiga parlor Maami na musu maraba da dawowa, duk amsa mata suka yi suka mata sannu da gida kan kowa ya nufi ɗakin shi don freshening, sai bayan la'asar ta fito ta zauna da Maami a parlor suna hira.
Chan shima ya shigo yayi joining ɗin su Dukda ba wani magana yake ba, a kusa da Maami ya zauna ya ɗaura kanshi akan shoulder ɗinta, tsoro ne fal ranshi, hankalinshi rabi baya jikinshi rabuwa da Alayah shine fargabarshi a yanzu ba ciwo ba, Maami ta tambayeshi ko akwai wani damuwa ne yace babu, yana ji suna maganan Ummi akan yadda babu wani improvement saboda sun ce damuwa yayi mata over ta yadda jinin da ya tashi hitting yayi sama ba na wasa ba kuma laluranta ma na rashin ji da magana kaman musababbin BP ɗinta ne.
Adu'ar samun lafiya duk suka mata, dab Magrib ya miƙe yace
"Maami zan ɗan fita zan tsaya wani wuri ina ga daga chan zan wuce wurin baba kawai"
Suka mishi Adu'ar dawowa lafiya ya fita.
"Maami baki lura kaman yana cikin damuwa ba?"
Alayah ta faɗa tana kallon Maami
"Kwarai kuwa na kula, sai dae kila tunanin rayuwa ne with time zai sake in sha Allah"
Zaune a gaban Dr. Ahmad bayan sun gaisa yace
"ya ake ciki? Sun fito results din?
"Yeah sun fito, for now babu HIV but ka san test na HIV yana ɗaukar 90 days ne kan ya zama successful, zaka dawo after 30days a sake yi haka after another 30 days again, sannan duk wasu STIs(Sexual transmitted infections) cututtuka da ake iya samunsu ta hanyar saduwa kaman su
Syphilis da gonorrhoea da sauransu duk babu"
Ajiyar zuciya ya sauƙe kan ya miƙa hannu ya ɗauki wani paper daban ya miƙa mai...
Tsawon mintuna talatin ya ɗauka cikin office ɗin kan ya fito, a cikin asibitin yayi isha kan ya isa wurin Baba suka yi karatu, Dukda baba ya lura kwazonshi ba kaman na jiya ba sai dae ya maida hankali sossai da sossai, daga nan ya tsaya ya saya masu gasashen kifi yayi gida.
****
Wasa wasa haka rayuwa ta zo ta sabar mishi da wani yanayi na daban, duk yadda yake karfafa zuciyarshi damuwarshi ba wani boyayye bane, yana iyakacin kokarin shi wurin bautar ubangijinshi kaman yadda yake matukar kula da Alayah da kuma Maami, bashi da wani buri illah ya shigo ya tarar dasu su biyu suna hira da raha hakan na kautar mishi da duk wani matsaltsalu na duniya, har ya sabar musu duk dare baya dawowa daga gidan baba hannu banza, ita kanta Alayah ta riga da ta saba bata cin komai sai ya dawo ya kawo ko balangu, tsire, kifi ko kaza gashi daban daban, yana riritata yana bata duk wani kulawa tsabar yadda hankalinta ke kwance Dukda yadda karatu yayi nisa wani irin kyau take narkawa tayi fresh abin ta.
Ta fannin mu'amalar aure bai taɓa nemanta ba wata huɗu ake nema kenan bata damu ba kasancewar ita wahalar abin kawai ta sani, ya kan rage zafi idan ta ciyoshi da gaske Dukda yana yawan shan tea me lemon tsami da gishiri, bata da wani matsala banda ciwon ummi da har yanzu babu wani cigaba, jiya e yau, duk ta tashi makaranta shi yake zuwa ya ɗaukota daga nan wucewa suke yi koyon tuƙi tun bata iyawa har ta soma kwarewa wani lokacin ma ita ke dawo dasu gida, in tace a watannin nan basu yi wani irin shakuwa na ban mamaki ba tayi ƙarya, yana bata duk wani kulawa da mace take fata ko buri, cikinta ya shiga wata na bakwai kenan duk zuwanta awo a tare suke zuwa, har yau babu wadda ya mishi maganan su koma gidansu ko ya ɗauke ta su tafi saboda daga Maami har Abba basa so su takura shi, kila ya fi so su zauna nan ɗin don duk wani shakuwa da be samu ba da Maami a yanzu ya same shi Dukda ya san ba kaman na umar da ita ba, amma kwarai zuwa yanzu sun shaku matuka.
Wani abu da yake yi yake ƙara burgesu shine yawan sadaka da taimako, har an san shi sai dae idan be ji taimako ba zai yi, abinci duk Litinin da juma'a yana ciyar da akallah mutane ɗari biyu zuwa uku, kuma lafiyayyen girki ba laga laga ba don a babban restuarant yake da contract, wani lokaci ma har ya ɗauketa su kai ziyara su orphanage, asibiti da sauransu a yanzu in ya ga rayuwarshi sai ya tsinci kanshi cikin zub da hawaye, lallai Allahnshi yana son shi.
***
Tsaye take gaban dressing mirror tana shafe tattausan skin ɗin ta da mai fitowanta wanka kenan, wani irin zafi take ji sannan kirjinta ya tokare sossai wadda rabon da ta ji ciwon zuciyarta ya motsa ta mance sai dae rashin ƙiba da nauyinta na nan, ta dae murje ta ƙara kyau sossai, cikinta ya fito sossai sossai bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarukan ta mabanbanta a take ɗakin ya bule da sassanyar kamshin, night gown da be da wani nauyi da tsawo ta saka tana kokarin tufke gashin kanta ya turo kofan ya shigo, ta madubi suka sakarwa juna murmushi.
A hankali ya ƙaraso ya ajiye tray din hannunshi kan ya nufeta slowly yayi Hugging ɗinta ta baya very tide yana zagaye hannunshi bisa kan cikinta a lokaci ɗaya ɗan cikin yayi motsi suka saki dariya a tare
"ka ji min yaro da gulma"
Yace
"kyaleshi ya marabci babanshi watarana sai labari"
Kallonshi tayi sai ta ga ya ɗan faɗa mata, sajen da ya tara ya mishi kyau ainun, tafin hannunta ta sanya ta ɗan shafa sajen tace
"Ya Mukhy menene yake damunka? Jikinka da ɗan zafi kuma ramarka tun bata fita har tana nunawa, can you please share ur problem with me? Karka manta turawa fa sun ce a problem shared is a problem solved"
Sakinta yayi ya karɓi ribbon ɗin hannunta yana tufke mata gashin yace
"bani da damuwar komai Fatee, in da ina dashi ba zan ƙi faɗa miki ko Maami ba saboda har duniya ta nade bani da tamkarku"
Bayan ya gama ya ja hannunta suka zauna bakin gado sbd zaman ƙasa na mata wahala yanzu, ya buɗe soyayyayiyar Irish da aka yi ta da liver sauce ya fara bata tana ci, sai da ta ƙoshi ta karɓi spoon ɗin ta dibo zata kai mai baki ya riƙe yana saukewa a hankali yace
"bani da apetite ba zan iya ci ba"
Tace
"kuma dai? Ya Mukhtar kullum fa haka kake cewa da matukar wahala ka sha wani abu ma bare ka ci abinci me nauyi"
Murmushi ya sakar mata.
Miƙewa yayi zai fita da kwanukan ta riƙe hannunshi
"zaka kwana anan? Ko in zo?"
Ya kalleta yace
"bari naje na dawo maman unborn tunda yau so ake a danne min kirji"
Tana dariya ya fice, toilet ta shiga tayi brush ta ƙarasa kimtsawa tana zama yana shigowa sanye da jallabiya coffee Brown me taushi, jallabiyar ya cire ya saura daga shi sai dogon wandon bacci ya haye gadon ta kuwa samu masauki a kirjinshi suka yi Light off bata jima ba bacci ya sure ta.
Sai da ya bari tayi nisa a baccin ya maidata kan pillow ya kwanta, baya so ya tashe ta cikin dare sbd ya san kanshi, juye juye kawai yake sbd baccin da baya samu a kwanakin gabaɗaya, chan kuma zufa yake ta karyo mai Dukda Ac dake ta aiki a ɗakin kusan kure wa tayi, ya yaye bargon yana cigaba da ɗan juye juye, wuraren sha biyu ta farka fitsari idanunta suka sauƙa kanshi.
Taɓa shi tayi sai taji hannunta ya sauƙa kan zufan dake ta gangara a jikinshi, wuta ta kunna sai suka haɗa idanu
"Ya Mukhtar zafi kake ji haka? Ko mu kunna standing fan?"
Yace
"No karki damu zan watsa ruwa yanzu ina jira ne ɗaya yayi gabaɗaya in miƙe nafilfili na"
Sauƙa tayi ta shiga toilet tayi fitsari kirjinta ke damunta da ciwo tana tunanin dole gobe taje meddy, ta fito ta zo ta kwanta ya kashe wutan don ya san bata iya bacci da wuta a kunne.
Bata iya ta yi baccin ba, tana ta kallonshi ga dukkan alama duk daren be yi bacci ba, ya kwana biyu da tayi noticing rashin baccin shi, in yayi ma baya wuce awa guda duk tsanani, tana ta kallonshi har ya sauka ya shiga toilet ya jima wadda ya tabbatar mata da wankan yayi kan ya fito ya sanya jallabiyanshi ya tafi wurin sallahnts ya fara nafilfili, tun tana kallon shi har bacci ya sure ta.
Karfe uku ta sake tashi fitsari ta samu yana karatun alqur'ani da yanzu yayi nisa sossai kuma yana fitar da duk wani makharij da kiyayewa sossai a karatu, ta jinjinawa namijin kokarin shi don yanzu ko ita bazata nuna mishi ibada ba, taje tayi fitsari itama tayi alwala ta zo tayi raka'a huɗu kan ta koma ta kwanta, sai asuba ya tashe ta ya wuce masallaci.
Ko da ya dawo a kitchen ya samu Maami tana shirin haɗa abin kari
"barka da safiya Maami na"
Tace
"barka dae my son Fatan ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah Maami yau ke da kanki ne a kitchen, to da me zan taya ki nima in samu ladan?"
Cikin raha tace
"Me ka iya? Da Kai da ɗan uwanka duk jirgi daya ya kwaso ku ruwan zafi wannan baku iya tafasawa ba in ba da kettle ba"
Yana dariya yace
"Ai kitchen ɗin nan sai ku mata Maami ina ganin kokarinku duk abu da ƙuna, yanka bani ciki"
Sukayi dariya a tare, Maggi ta bashi yana ɓare mata chan yace
"Maami autan ki zuciyarshi tayi yawa, har yau ya kasa sakewa da ni be san kuma bamu da wani lokaci ba"
Itama hakan na damunta har yau be zo ba, babanshi ma na complain na ko ya kira daga sun gaisa shikenan
"ko da shi ke ma Maami kyale shi, dama zaani ne ya tadda muje ni, ga hali kuma ga yanayin aikinshi"
Ya katse ta don ya san tunanin amsar da zata bashi don kar yaga tana kare umar ne ta bar shi take yi.
Wani hiran suka kama har ta gama breakfast din yana tare da ita, shi ne miko wannan miko wanchan, dibo ruwa.
Masu aikinta ne suka fitar da abincin zuwa dining daga shi har Maami suka je suka yi wanka kusan a tare su huɗun suka fito, Mukhtar ya ja wa Abba kujera yana zama yace
"Abba yau zaka ci girkina na san sai ya kai maka karo bari na tabbatar da lafiyar kujerar nan kar santi ya kwashe ka"
Dariya suka yi Abba yace
"tafi nan, da de bamu san asalin balbela bane kai yaushe ka iya ko kunna gas din ma? Ko binty ya iya?"
Ya faɗa kaman yadda ya riƙe bakinshi saboda yawan faɗan Binty da Maami take. tana dariyar yadda ya kwabe fuska tace
"Babu abin da ya iya Abba"
Yace
"Maami faɗa musu don Allah ba ni nayi ba?"
Tace
"kwarai kuwaaa"
Yadda ta faɗa da alamun tsokana a muryarta yasa suka kwashe da dariya Abba na cewa
"faɗi gaskiya dai daga jin wannan amsawan naki da walakin goro a miya"
Abincin suka fara ci cikin natsuwa, jujjuya cokalin kawai Alayah take yi, Mukhtar da ya lura yace
"Fatee lafiya? Ko wani abu na damun ki ne?"
Shima ba ci yake ba ruwan zafi yake ɗan kurba.
Maami tace
"Binty akwai matsala ne?"
A hankali tace
"Maami kirjina ke ciwo sossai"
Abba yace
"Subhallahi Meyasa baki yi magana tun ɗazu ba? Mukhtar tashi maza mu wucenku asibiti"
Duk abincin suka bari Maami taje ta ɗauko musu mayafi zuwa lokacin ko tsayuwa Alayah bata iya yi tuni suka yi meddy specialist hospital hankalinsu a tashe.